← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 67

Sashe 30

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan jikina na fara cirewa a gaban madubi na tsaya ina ƙare wa kaina kallo tun daga kaina dake ɗauke da shuku tsoron yayi tsaye a tsakiyar kaina tsabar taurin gashin gira ta kamar aske wa ake kullum gashin idona ma haka shegun pimples ɗin nan kamar ƙara kiransu nake sun dabaibaye min fuska babu wani wuri a fuskata da babu pimples, goshi,hanci,ƙarƙashin haɓa,kumatu da sauran wurare wasu sun mutu sunyi baƙi ash ɗin idona ya ƙara duhu

Na kalli ƙirjina kamar in make wurin meyasa yake ban wahala har haka? Bayan abune da kowace mace ya kamata ace tana dashi meyasa nawa suke jan jiki wurin girma?kawai dan su ƙuntata min dan sun ga ina son su...

Nayi ƙasa da idona zuwa sauran sassan jikin nawa ba gaba ba baya a haka Jay D ke faɗar in sauya tunani na zuwa fozitf.(positive) wai sun ɗauka akwai sauƙi ne? Suna tsammanin nima ina jin daɗin yanda nake? Wasu zasu iya kallon abinda bai masu ba(flaws)su ɗauke ido wasu kuma idan suka ga abinda bai musu ba(Flaws) hankalin su bazai kwanta ba har sai sun gyara baxan iya cigaba ba har sai na sauya wannan abin dake tattare dani(flaws)dan ni Abeedah ina cikin sahun mutane na biyu

Sosai hawaye suke sauka daga idona kamar an buÉ—e pamfo nabar gaban madubin na shiga cikin ruwan data haÉ—a min nayi amfani da sabulan ta na ruwa nayi wanka sosai Harda kaina na wanke

Bayan na fito na tsaya gaban madubi na shafa man da muka shafa jiya na É—auki riga da skirt daga kayan dana zo dasu na saka.na fesa turarukanta ban shafa man bakin dana gani ba dan ina É—aukar shi a matsayin kwalliya amma ni zan fara kwalliya ne idan na samu na gyara (flaws) É—ina...

🍁: Allah baya kuskure wurin halitta Abeedah...

'' nasani ai...''

🍁: TOH me kike ƙoƙarin canjawa?

'' abinda na gama magana akai...''

'' baki da aibu you're flawless.mutane kawai su suke ganin aibun wani bayan basu ne sukayi halittar ba kiyi haƙuri ki zama mai ƙwarin guiwa mai self esteem da self lovenzaki gani kina da kyau kuma zaki karɓi kanki a yanda kike kuma zaki fi kasancewa cikin farin ciki...''

'' sauƙin faɗa ke dashi bake ce niba oti... baki san yanda ake jiba baki san irin kunyar da nake shiga ba baki san dararen da nake kasance wa ido biyu ba baki san irin gajiyar da nake yiba wurin tare gaban hijabi na ba idan ina tafiya bakisan irin faɗuwar gaban da ke riskata ba abduk sanda nazo wucewa inda akwai maza ba bakisan yanda na parka farin ciki na gefe ba ina jiran ranar da zan zama cikakkiyar mace lokacin kaɗai zan cigaba da farin ciki kada kiyi magana baki san yanda ake jiba ko kaɗan!!!!!''

'' lafiyar ki kuwa?" Jadeedah dake tsaya daga bakin ƙofa ta faɗa tana kallo na daga sama har ƙasa sai kuma ta dafe kumatun ta

'' oh my Bee baki ga yanda kika yi kyau ba...''

tazo ta tsaya gefe na saye da rigar material kore sosai tayi kyau sai ƙamshi take murmushi nayi mata

''.na gode '' kwalli ta ɗauka tana ƙoƙarin shafa min

'' a'a ni bana so..''

Bata jini ba sai data shafa min harda man bakin...ta tsaya baya na hannun ta a kafaÉ—u na,nikam ko kallon kaina banson yi

'' kalli yanda kikayi kyau dan girman rabbi amma mata kullum da ido kamar tsohuwar mayya É—ago ki kalli kanki mana!"

Ta faɗa da murna badan naso ba na kalli kaina ɗin nima nayi mamakin irin kyau'n da nayi sai dai duk da haka an fini kyau idona sai ƙyalli suke sun ƙara fitowa sak na mage ash ɗin ciki ya ƙara duhu turo baki nayi ina matsawa daga bayan ta

'' ba kamar keba''

na bata amsar da basarwa kafin na matsa bakin taga ina kallon waje yau asabar koya su Mama suka ji babu ni?

'' zaki canja ''

'' mutafi mu karya!"

saukowa nayi muka fita tare a dani muka iske maman su hakan yasa na kai har ƙasa na gaishe ta ta amsa da fara'a tana ta yabon kyau'n da nayi duk kunya ta kamani abin kari lafiyayye muka karya dashi bayan mun gama muka yi wanke wanke Maman su ta wuce ɗaki muka koma parlor nida Jay D inata kallon ko ina,sai ƙamshi ke tashi kuma ko ina tsab tsab...

Bayan tv'n ta kawo...tashar yan china ta fara sawa ganin ba wani abun kirki ake ba ta kalle ni

'' zaki kalli MSA?" Da rashin fahimta nace

'' Meye MSA?"

Ta miƙe daga inda muke zaune tana faɗin

'' yan katun ne (cartoons) kuma yana da kyau wallahi.. yaran iyakar su shekarun mu suma amma da turanci ake magana '' canja setting ɗin Jay D tayi daga Netflix zuwa You tube ta dawo ta zauna kusa dani.tayi rubutu inda akwatin nan me cokali (, search 🔍 box)

Sai ga shi ya fito da yawa Ta ɗauki ɗaya tasa muka fara kallo babu abinda nake ganewa ita take yimin bayani duk da haka sosai katun ɗin ya ƙayatar dani musamman yanda koda yaushe daga ƙarshe suna samun masoya da kuma yanda suke ƙawance da kuma komai da komai a cikin katun ɗin... Kafin in sani nima na fara son abun...

Can ta tafi kitchen ta dawo mana da abubuwan ciye ciye bayan mun gama ta fita dani daga parlorn tana nuna min ko ina na gidan...muka zauna cikin lambun su muna wasa da fulawowi...

Rayuwa a gidan su Jay D kamar wata duniya daban ne, lokaci na saurin wucewa,kafin kwanaki uku suka ƙare na koyi abubuwa da yawa harda yan kalmomin turanci sannan na gane ba duk masu kuɗi bane marasa mutunci ba kaɗan ba Jay D tayi ƙoƙarin ganar dani abinda take kira self love da self esteem (yanzu na iya faɗan kalmomin da kyau😅)

Kuma na fara koya fata ta tayi kyau da haske ranar Monday bamu je makaranta ba da yamma na shirya komawa Jay d kamar zata yi kuka sai kallona take a marairaice...nima dai kamar zanyi kukan wani ƙaramin akwati maman su ta siyo min,aciki akwai kaya atamfa guda biyar sai materiyal kala uku da shadda suma kala uku turaruka kala uku da singilet kusan guda biyar irin masu tsayawa a rabin ciki da kuma fararen turarukan da ake amfani dasu idan an gama al'ada,da hijabai suma guda uku Duk ta bani inata godiya da addu'oi kamar zan kife ita dai sai murmushi take

Bayan nan harda atamfofin da ba'a ɗinka ba da wasu turarukan na gida dana jiki ta bani in kaiwa Mama da ƙarfe biyar da rabi muna tsaye bakin mota idon Jay D sun ciko da hawaye ta rungume ni

'' sai nazo Bee...dan Allah kizo makaranta gobe kinji?"

Nima idona da hawaye na rungumet

'' zan zo...'' muka rabu na kalli ranar data kusa faÉ—uwa sannan na kalli Jay D sosai nake jin kaÉ—aicinta kuma nima ina cikin shi taban tausayi kamar in jawo ta mu tafi tare na sake kallon ko ina na gidan musamman lambu da inda akwai pipe É—azu da safe kamar bamu zo nan munyi wasa da ruwa ba...

Bye bye mukayiwa juna ta buɗe min ƙofar na shiga sannan ta rufe motar ta fara tafiya tana tsaye a wurin dana barta na cigaba da kallon ta har saida muka fita daga gidan duka naji kamar an tona rami an barshi buɗe a cikin zuciya ta naja dogon numfashi kewarta na mamaye ni... nayi ƙasa da glass ɗin motar ina kallon ranar data zama ja,iska mai sanyi na kaɗawa dogayen bishiyoyi inuwar su tayi wani irin tsawo lokacin da muka kawo inda trapic inata kalle kalle ina kallon yaran nan masu sayar da abubuwa yanda suke gudu nan da can yanda suke magana da ɗaga murya da kuma yanda muryoyin mutane ke nesa nesa kowa yana ta harkar gaban shi wasu suna dariya wasu suna tsallaka titi kowa da nashi a rayuwa farin ciki zaɓi ne a duk yanda kake zaka iya zaɓar farin ciki ko akasin hakan...amma nidai Abeedah ban yarda ba

Ƙarfe shida da minti goma muka kawo ƙofar gidan mu, ƙarƙashin bishiyar kaiwa direba ya paka..nake kallon yaran dake wasa a filin dake nesa kaɗan da gidan mu sai kuma na ƙara jin ina kewar Jay D,direba ya fito ya fara cire min kayana ya shigar min dasu har zaure fitowa nayi sanyin marece na duka na da ƙarfi

'' na gode sosai '' yayi murmushi

'' ba matsala '' sannan ya shige motar shi yabar wurin

Na daÉ—e tsaye a wurin ina jin kewar Jay D sosai kafin na shiga gidan

'' kewai Asma'u Matsala ta dake kin cika laƙaita.. mata kamar baki da jini a jiki mtschewww!"

'' toh keda kike da jini ai da kinyi ke kaÉ—ai!"

'' kada dai kice zaki gayamin magana yanzu in gyara maki zama wallahi!"

'' Toh kyanwa da ɓera... Bismillah marece yayi ko?"

Muryar da take kamar ta Mama kamar bata Mama ba ta katse su biyun ko su waye?

Akwatina na fara ja tare da buga sallama daidai ana dawo da wuta da ƙarfi

'' wa'alaikumussalam ''

nayi tsaye a wurin ina kallon matar data amsa min baki sake daidai nan Mama ta fito daga baye

'' A'a Tuwo kin dawo...'' sakin akwatin nayi na isa na rungume Mama inaji kamar zanyi kuka Mama tana dariya tace

'' ai na É—auka kin manta damu...'' batareda na É—ago ba na girgiza kaina

'' shin wai dama Abeedah ce? Na ɗauka ai wata baƙuwa ce akayi!"

Inji inna Sarai ƙanwar Mama sai na saki Mama na isa wurinta ina murmushi kamar bakina zai cire gefenta na zauna

'' wai kece?''

'' a'a bani bace uwarki ce...''ta bani amsa tana harara ta

'' da gaskiyar ki ƙanwar uwa itama ai uwace...''

na faÉ—a ina dariya sosai nake jin farin ciki

'' har yanzu kina nan da rashin kunyar ki ko?"

Ta tambaya tana tiƙa ta....na turo baki...'' ina Anaam?"

'' gani nan munafuka kike wani tambaya kamar kin damu!"

Doguwar yarinyar mai zubin fulani ta amsa min da jin haushi a muryarta tana harara ta...
Chapter 30 · 0% Book details