← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 67

Sashe 55

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' ƙarya kike..idan ke ba mayya bace contact lenses kike sawa kenan?" Kowa ya kafe ni da ido and I felt so helpless...daga cikin matan akwai wani kallo na musamman mai cike da tsana da nake ji har cikin ƙasusuwana da yasa gashin jikina miƙewa...na rasa sanin ko daga ina wannan kallon ke zuwa

Ƙatuwar matar ta tashi ta damƙo hannuna ''buɗe min idon in duba da kyau in gani''...inji Hajiya Momma tana ƙoƙarin tale min ido ta tsoma hannu ciki...na shiga uku ni Abeedah..kuma babu ɗaya daga cikin mutanen wurin dake ƙoƙarin hanata...su wa'yannan mutanen ata yin abun mugunta gaban su babu mai hanawa dan basu ake yimawa ba...

'' wallah...''

'' yimin shiru...'' ture ni ƙasa tayi ta zaune min ƙafafu ta riƙe hannayena..jajayen idonta abun tsoro..naji wasu daga cikin matan sun kwashe da dariya...abinda nayi ma Seraphina na sake maimaitawa

Wannan harda cizonta nayi...da alamu sauran matan sun tsorata dan tashi sukayi daga inda suke zaune suka maƙe wuri guda jikinsu na rawa...

Na dinga sakin ihu ina shille shille,na jefar da hijabina ina É—age riga kamar zan cire itama na samu na canja muryata zuwa ta abun tsoro convincingly baiwar da ban san ina da ita ba...sai wannan lokacin

Hajiya Momma tasha yagalgala daga gare ni...matar sai ihu take...Farzan ne ya shigo wurin ganina zaune saman ƙatuwar matar

Hajiya Momma tace'' Farzanu ka taimake ni...'' taban dariya sosai...zuwa yayi ya ɗage ni ya fitardani daga parlorn muka shiga elevator tare...naso in cigaba da acting ɗina, fahimtar ya gano ni yasa na dawo daidai,ina rungume hannayena a ƙirji kafin ya tambaya na shiga mashi bayani da fuskar tausayi

'' wai cewa tayi ni mayyace kuma so take ta tsiyayar min da ido...'' na gwalalo ido ina nuna mashi ƙwayar ciki da take dark gray... ɗauke idonshi yayi

'' and you decided to turn into a maniac huh? You are more dangerous than you seem" gumi naji ya É—an tsatstsafo min..na fahimci abinda ya faÉ—a amma ban san me yake nufi da..Uhmm..

🍁: Maniac

Ban san meyake nufi da maniac ba...amma sai na waske kada ya fahimci ban sani ba...

'' Next time xan barki kisha duka ne,who knows nan gaba your gray eyes will have silver in them and that's it! You're a witch!"zaro ido nayi jin abinda ya faÉ—a wai zan koma mayya

'' gashinki ma zai koma gray,at least a cikin littafai haka kamannin witches suke...'' da sauri na shafa kaina da hular ta faÉ—i,naji kunya ta kamani,na É—ago ido na slow naga ni yake kallo fuska a É—inke

gyaɗa kaina nayi kamar ƙadangare elevator ta buɗe a second floor..yai tafiyarshi nima na juya ina tafiya jiki a sanyaye..na kawo wurin wani ɗaki zan sha kwana naji an hankaɗa ni ciki an rufe ƙofar daga waje...duk yanda nake bubbuga ƙofar anƙi a buɗe

'' shegiya nan ciki zaki mutu!" Muryar Fauziyya ce ba kuskure... cigaba da buga ƙofar nayi tsoro na kama ni...ɗakin babu ko ɗigon haske kuma babu taga bare iska ya shigo..kenan babu oxygen..idan babu oxygen mutuwa zanyi...

Cigaba da buga ƙofar nayi numfashi ya fara min wahalar ja...ga uban zafi ga tarin ƙura..faɗuwa ƙasa nayi ina cigaba da buga ƙofar...na ɗauka mutuwa zanyi...idona sun fara rufewa naga an buɗe ƙofar wata yarinya da ban taɓa gani a gidan ba duk da buji buji nake ganin ta...ta shigo tana kiran sunana

04:00

BuÉ—e idona nayi na ganni a sashen mu Mama Asabe tayo kaina tana shafa goshina '' kin tashi?" GyaÉ—a kaina nayi na tashi zaune...'' sannu kawo ki akayi wai kin suma...''

'' Fauziyya ta rufe ni a wani É—aki mai duhu,ba wai na ganta bane amma naji muryarta tana faÉ—in in mutu...''

Mama Asabe ta kalleni da damuwa...'' dole mu faɗawa Madam..'' na jinjina kai ina tunani ai Fauziyya bata tsoron Madam Aatika sai da nayi sallah ina zaune aka kira Ni wai Madam na ƙasa tana jira...tashi nayi na tafi ƙasa ɗin na samu duk sauran ma'aikatan suma suna nan harda Fauziyya However ba Madam Aatika bace, Madam Amina..

Bayan na gaisheta ta tambaye ni meya faru? Ido na haÉ—a da Fauziyya take min alamun idan har na kira sunan ta zata kashe ni...É—auke idona nayi daga kallonta

Badan ina jin tsoronta ba na faɗi abinda ya faru amma ban kira sunan ta ba tunda bani da tabbaci... Madam Amina ta haye mu da faɗa tana ƙara gargaɗin mu akan irin wannan halayen...daga ƙarshe tace gobe kafin in tafi makaranta in haɗu da ita ..na jinjina kaina sannan ta tafi

Zan koma sama Fauziyya ta biyoni '' kin yima kan ki adalci da baki kira sunana ba..''

Kallon ta nayi nace ''.idan kina tunanin tsoron ki ake...well,ke ce mafi yaudarar kai a gidan nan!''

Ɗage kafaɗa tayi baki kyaɓe tace '' kuma ina shawartar kida ki rabu da sir Farzan! Duk inda kika ganshi ki kauce daga wurin kin jini ko?" ta damƙi cinyar hannu na riƙo bana wasa ba..toni ina ruwana dashi?

Cike da haushi na gatsa mata cizo kamar vampire ban sake cewa komai ba na barta da yarfin hannu...

A ƙasan raina nake tunanin ko wace mai mutunci ce a gidan ta taimake ni? oho...

Da daddare bayan na gama duk ayukkan daya dace nayi na sake hawa har 5th floor cikin lambu na shiga na tsaya daga gaban wurin ina kallon sama..duk da kuwa ance kada mu dinga yawo yau ba taurari saboda hadari daya taru...

naji ina nishaÉ—i dana tuna gobe zan fita daga gidan nan a karo na farko tunda nazo...zama a gidan nan is quite suffocating babu wanda zai san da hakan sai wanda yake a ciki...

Da ƙarfe goma lokacin aikin mu ya ƙare na sauko zan tafi sashen mu...na haɗu da Waleeda tayi min murmushi isa wurinta nayi ta riƙo hannuna muna tafiya tare muna hira

'' da ace mutum zai iya rubuta ƙaddarar shi,da ban kasance a nan ba...'' ta faɗa min

'' wata rana zamu girmi duk wannan ba zamu bautama wasu ba,sai dai a bauta mana!'' farin ciki nagani a fuskar ta sosai bayan nayi wannan maganar tace

'' tunda kin faÉ—a...zan fara addu'a akan hakan...ada na É—auka hakan kawai zai faru dani a mafalki duba da yanda rayuwata take lilo...you gave me hope...na gode..''

Jinjina kaina nayi ta rungume ni kafin mukayiwa juna sai da safe muka wuce É—akunan mu

Dana shiga É—akin mu har Mama Asabe tayi bacci banda Hansa'u dake danna waya... gado na haye na rufa badaÉ—ewa ba aka tsuge da ruwa

'' ashe ni ake jira in É—aura kaina a matashi...'' nayi murmushi da wannan tunanin...

Da safe kamar jiya haka Mama Asabe ta sake bani irin wancan abun,naso inƙi sha tace ai yana ciko mace ya gyara ta...naji kamar inyi dariya amma bana so in ɓata mata ƙoƙari yasa na shanye abun...na miƙe na shirya cikin uniforms ɗina da suke a goge amma fa sun tsufa..ban damu ba dai ..

Hula nasa ruwan toka,na shafa kwalli da turare mai daɗin ƙamshi...jakar leda ta na ɗauko ina duba komai da komai akwai a ciki...

Duk da Nasan ba kowa bane zai dawo ranar da aka dawo duk da haka na kasa haƙura da tafiya wannan ranar...kawai ina so in bar gidan nan ne...waya tana ɗauko na kira gida bayan mun gaisa na faɗa ma su Asma'u suzo makaranta...

Tare muka fito da Mama Asabe muka karya da sauran masu aiki a dining da babu abinda suke magana akai sai dawowar biyun nan a yau, cikin hirar tasu naji ana cewa É—aya daga cikin biyun É—an Italy ne..ko kaÉ—an banji ina so in ga suwaye ba...

Kafin a gama breakfast ɗin nasha harara da baƙaƙen maganganu a kaikace amma ɗokin zuwa makaranta ya hanani jin baƙin ciki...sai ma nake mayar musu da maganganu masu kyau maimakon biye masu taɓaci...

'' ke Abeedahtu ashe bakya sign-in..hakan zai iya zama matsala fa...'' Mama Asabe ta nuna min littafin ko sau ɗaya ban taɓa sign in ba ko sign out na manta duka

'' zan kiyaye...'' na faÉ—a sannan nayi sign in na yau kafin na fito saye da hijabi daban dana makaranta....

Kitchen na tafi dani da wasu ma'aikatan muka shirya abinci a dining...koda yan gidan suka hallaro har mun gama...duk wanda yazo sai mun risina mun gaishe shi..saɓanin koda yaushe da nake jin haushin hakan yau harda murmushi..babu abinda ya dameni kawai ayi a gama in tafi makaranta...

Harda hajiya Momma tazo...muna haɗa ido ta Harare ni da jajayen idonta murmushi nayi na sadda kai...yau hirar su ta ta'allaƙa akan mutane biyun da zasu dawo,yan matan kowa ka kalla zakaga fuskokinsu ɗauke da annuri nake mamakin waye wa'yannan? Kuma wane muƙami suke dashi a gidan da kowa ke maganar su..duk da samarin basa ɗoki kamar sauran....

Yau munci sa'a mu yan aiki cin mutuncin da aka saba yimana ya ragu sosai...

Farzan ne na ƙarshen zama ya gaishe da manyan fuskar shi ba annuri dama kuma ba wani fara'a ne dashi ba..ban taɓa ganin yayi murmushi ko dariya ba....

Nayi nisa cikin tunani naji ance '' ke!" A firgice na kalli Khaleesat dake harara ta '' baki ji ana magana bane ko kin kurmance?"

'' ai tunda tasa wa'yannan koɗaɗɗin kayan take jin kanta ya ƙara girma...aikin banza!" Jameelah ce tayi maganar tana harara ta

'' dalla miƙo min ketch up!" Ɗaukar ketchup ɗin nayi na miƙa mata '' oh ni zan zuba kenan?"

Danne takaicina nayi na buɗe abun na fara zubawa..sai ihu take min..bana son ɓata ranar farkon komawa makaranta yasa naja dogon numfashi bance komai ba

'' Hajiya Momma meya faru da hannun ki haka?" Ayaan ya tambaya yana bin hannun ta da kallo

'' wannan shegiyar yarinyar ce ta kusa illata Ni..'' ta nuna ni da mamaki kowa yake kallona

Gabana ya faÉ—i idan fa aka Kore Ni?

'' the girl is dangerous...ya kamata a kula da irin masu aikin da ake É—aukowa!" Alhaji Sulaiman ne ya faÉ—i hakan...

Itama Seraphina ta faÉ—i abinda nayi mata..kowa yayi min caaa!

'' ayi haƙuri Madam bada gangan bane hakan bazai sake ba...''

'' matsiyaciya ai haka zaki faɗa...'' ji nayi idona sun fara ƙaiƙayi..na taune leɓena amma na kasa haƙura
Chapter 55 · 0% Book details