← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 67

Sashe 43

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' amma dai kin san wannan soyayyar sai a littafi ko?" wata yarinya ta miƙe saman wurin zamanta tana riƙe ƙugu

'' yo dama fa? Mazan yanzu ko suna tafiya tare da matar su wata tazo wucewa sai sun bita dana mujiya na rasa uban me suke kallo...'' wata daban ta faÉ—a...

'' kuma sai ayi ta zuzuta kyaun jaruman abu zar takaici..kai mutum gaka ga kamar ka..ana ƙarasa mutum najin ɗaci...''

Nake sauraren su ina tankaɗe da rairaya akan kowane bayani da suke faɗi abu ya zama muhawara kowa yana bada nashi fahimta akan soyayya wasu na ganin irin soyayyar da ake yi a littafi har abada baza'a taɓa irin ta a rayuwar gaske ba...wasu kuma suna ganin zai yiwu

Hafsah tace '' ban sani ba koda gaske irin wannan soyayyar tana faruwa..amma ni...zan so in yarda da cewa,zata iya faruwa...tunda akwai Allah...kuma ina fatan samun irin wannan soyayyar ko fiye da haka...''

gungu mu kayi suna cigaba da hirar su akan soyayya nidai ina saurare amma a raina ba tun yau ba,nima ina fatan samun irin wannan soyayyar Jay d da Diyaam suma sun tofa albarkacin bakinsu...abu yayi ƙamari da har yan wani aji suna shigowa ajin mu dan ayi muhawarar dasu...wasu daga cikin masu zuwa littafan soyayya makaranta harda musaya suke...wannan yaba wancan wancan yaba wannan...nima na samu wani littafi Mai suna ' DA AKWAI CIWO CIKIN ZUCIYA TA...' Jay d ma ta ƙara min da wani na turanci tace '' tunda kin fara fahimtar turanci,karatun littafan turanci zai taimaka maki ki ƙara iyawa...'' duba littafin nayi... zanen cover wani namiji saye da baƙaƙen kaya irin na turawa da wata farar mata saye da baƙin gyale kamar hijabi ya riƙe fuskarta yana sumbatar goshinta sunan littafin ' HER SHIELD '

Shi kuma dizain ɗin littafin Hausar wata yarinya dafe da ƙirjinta da hawaye a fuskar ta...kamar ta karye fiye da yanda za'a iya gyarawa(broken beyond repair)

Jefa su nayi cikin jakar leda ta,hirar yan ajin namu na man daɗi sosai kowa sai kare abinda ya yarda dashi yake... suna kawo hujjoji masu wahalar sharewa...amma dai na zaɓi in yarda da cewa,wannan soyayyar zata iya faruwa a gaskiya kuma daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar nemo tawa...

Sanda ake koyar damu lesson bayan an tashi,na mayar da hankali na ina ƙoƙarin fahimta,duk da ba duka na fahimta ba na fahimta to some extent...

🍁🍁: Naji su Abeedahtuwo kamar anyi turanci?

Eh mana turanci nayi...baki ji nace yanzu ina fahimtar karatun ba kamar daba? ai kawai ku shirya daga yanzu ina magana ina haɗowa da turanci dan in ƙara ƙwarewa kuma a san na iya ehe...

🍁🍁:🤭

Sanda muka koma gida,muna gama cin abinci Kasancewar babu wani aiki da zanyi na shiga karatun littafan dana samo na fara dana turanci ina da saurin karatu sosai duk da wasu kalaman sai dai in tsallake dan ba iya karanta su nake ba,wani abun ma ban ganewa haushin daya cika ni yasa na ajiye na turanci na dawo karatun Hausa inda nafi ƙaimi...rayuwar jarumar abun tausayi wato ita ɗin kamar babu ta, babu wanda ke lura da ita,babu wanda ke ganin ta..ba wai dan ita fatalwa bace sai dai saboda kamar ita ɗin bata da muhimmanci baga iyalanta ba.baga sauran mutane ba ko ƙawaye bata da babu wanda ke son magana ko mu'amala da ita...

Idan da ace rayuwa ta zata koma kamar haka? Allah ya raba ƙila mutuwa zanyi ya zanji idan zan wayi gari ace su Mama sun dena kulani babu Jay d a tare dani?

Har dare ina abu guda kwanakin da suka biyo baya na ƙara tsoma kaina cikin labarin..dan an fara kawo wa wurin daɗi sannan a makaranta ina iyakar bakin ƙoƙari na kuma a duk sanda na samu lokaci ina cigaba da neman aiki na har yanzu bamu faɗi a gida ba kuɗin da ake nema mu biya a makaranta Jay d tana ƙara taimaka min itama a nata fannin rayuwa ta cigaba da tafiya..ina jin sauyi tattare dani kullum ina Cikin murmushi idan na tuna irin soyayyar da ake zubawa a cikin littafin da kuma yanda nake ƙudurin samo tawa soyayyar kowa dake tareda ni ya fahimci nishaɗi na...ko aiki nake nakan tsinci kaina da hasashen faɗawa soyayya da nawa namijin novel...

A haka kwanaki suka cigaba da tafiya..har ranar da zamu fara mock ta iso...nayi karatu sosai a gida,a makaranta ma munyi tare da Jay d da Diyaam wasu kam sai ƙoƙarin shiga suke da littafi da pepopin da aka rubuta amsa akai tsaye muke a gaban block ɗin ajujuwan mu mu yan SS 3,sunaye aka fara kira daga A-Z aka bamu lambobi Nice lamba 25 a ajin farko Jay d lamba 113,a aji na biyu Diyaam lamba 305 a ajin kusa dana ƙarshe Anaam lamba 205 ajin su ɗaya da Diyaam Asma'u lamba 101 ajin su ɗaya da Jay d...

Ana kiran mutum zai shige kowa da seat É—inshi...mun sha gargaÉ—i har kunnen mu yayi ciwo malamai kuma sai zagaye mu suke..duk dai irin abubuwan nan da ake idan za'a rubuta jarabawa dan tabbatar da cewa É—alibai basu samu damar satar amsa ba shi ake mana yanzu... Paper farko English ne....yawu na haÉ—iye ganin tambayoyin da suke hararata jikina yayi sanyi naji hankalina ya fara tashi..na É—aga kaina naga kowa na rubutu banda ni

'' ki tuna kada ki tsoro ta kija dogon numfashi idan baki fahimci tambayar ba ki tsallake ki amsa na gaba kada ki ɓata lokaci akan wanda baki sani ba...'' kalaman Jay d suka dawo min kamar lokacin take yinsu badan na yarda dacewa jan numfashin zaiyi wani abu ba naja ɗin na ɗauki biro na shiga rubutu...

Wanda ban sani ba in tsallake nayi mamaki dana ga cewa ina amsa tambayoyin da sauƙi... to da yake dai nayi karatu..na ɗago kenan naga wasu suna fito da littafi daga cikin hijabin su.. wai suna duba amsa taɓe baki nayi dan Jay d tace babu amsa a cikin littafi na mayarda hankali na akan paper ta bada daɗewa ba mukaji ance '' KAI KU TASHI!!!"

Sai da naji hanjina sun kaɗa da sauri na ɗago naga ashe waya'nda suka fito da littafi ne aka kama taɓ ɗi jam sun wulaƙanta gaskiya Da ƙarfe sha biyu muka gama jarabawar ko kaɗan bana son yanda aka wani zauna ana faɗar amsar da ba daidai ba da wacce ke daidai hakan na tayar min da hankali '' ya jarabawar?" Diyaam ta tambaya '' jarabawa da godiya Allah yasa munci...''

''.haha..kada ki damu wannan ba itace mai muhimmancin ba gwaji ne kawai'' na gyaɗa kaina muka zauna ƙarƙashin bishiya bada daɗewa ba su Jay suka ƙaraso'' ya jarabawar?" Murmushi tayi min ta zauna kusa dani

'' dama wannan jarabawa ce?'' tayi maganar da dariya nayi murmushi..itafa na manta...ashe yar baiwa ce....

Mutane da yawa suka taru a ƙarƙashin bishiyar muna hira,dayawa daga cikin mu sun damu da idan abinda suka rubuta daidai ne .. wa'yanda basu damu da sakamakon suba,suna burgeni cewa sukeyi abu mai muhimmanci da kansu suka rubuta sannan kuma sun yi iya ƙoƙarin su,sun barwa Allah saura irin wannan tawakkali shine zuciya ta take mutuwar son samu amma na kasa a koda yaushe Nasan da cewa akwai mutane da yawa da yanayin su yafi nawa ɓaci amma kullum suna rayuwa da murmushi da gode Allah..meyasa nima baxan zama kamar suba?

'' kai dan Rabbi kuzo muyi wasa...'' Hameeda ta miƙe tsaye tana gyara rigarta...'' wace wasa zamuyi?" Wata daban ta tambaya

'' kacha (catcher) ni zanyi...'' Hameeda ta amsa mata...da yawa muka yarda.. muka shigo cikin wasar...tayi daɗi kamar kada mu dena amma lokaci yayi saurin tafiya. da ƙarfe ɗaya muka baro makaranta Diyaam ta tafi motarsu tana mana bye bye mu kuma muka bi Jay D a tata motar...gidan su zamu saboda lesson ɗin data ce zata dinga koya min...

Lokacin da muka iso Anaam bakinta ya kasa rufuwa sai santin girma da kyau'n gidan take itama Asma'u ta yaba...

Da muka shiga ciki Anaam harda yin luuu kamar zata faÉ—i tsabar ita yar drama ce

'' ashe Aljannar duniya kike rayuwa a ciki Jadeedah?" Inji Anaam tana kallon ko ina ido waje da alamu ba ƙaramin burgeta gidan yayi ba samun innarsu mukayi zaune a parlor dukan mu muka gaishe ta da girmamawa ta amsa mana da fara'a da sakin fuska... '' Umma karatu zamuyi kin san mun fara jarabawa...ina Deen?"

'' Deen bai dawo ba su kuma ki sama masu abinci kafin ku fara...'' godiya muka yi mata Jay d taja mu zuwa ɗakinta Anaam ta ƙara ruɗewa da ganin kyaun ɗakin... Asma'u take kallon ko ina amma bata taɓa komai ba,ba kamar Anaam ba...hijabin mu muka cire, ɗaya bayan ɗaya mukayo alwala mukayi salla muka sake komawa ƙasa har kitchen ta jawo mu ta buɗe fridge akwai abinci daban daban tace kowa ya zaɓi abinda zaici Anaam ita tafi kowo ɗaukar kaso mai yawa.ta bamu kunya ba kaɗan ba bayan mun gama duk wannan nida Anaam muka zauna Jay d na koyar damu ita kuma Asma'u take kallo a ƙatuwar TV'n su Jay d tunda ita bata buƙatar a koyar da ita. Study session ɗin yayi min daɗi sai da aka kawo wurin math naji raina ya fara ɓaci..amma Alhmadulillah sauran subjects ɗin na fahimta...sai bayan la'asar muka koma gida ...

Ranakun da suka biyo baya cike suke da wahala a wurina...kullum idan an tashi muke biyo Jay d gida don study session É—in mu,bayan mun gama idan mun koma gida da wuri zan shirya in tafi neman aiki har sabon gari kasuwar kwari..da sauran wuraren da nake tsammanin zan samu aiki amma babu wani cigaba...ga jarabawar mu ta mock yanzu na fara jin wahalar ta har naga nawar mu gama...
Chapter 43 · 0% Book details