← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 67

Sashe 48

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' shigo...'' Mama ta katse ni...

'' Abeedah jeki É—iba mata ruwa...''

Na tashi na nufi inda ake ajiye ruwa..matar ta shigo suka gaisa dasu Mama a mutunce ta kawo kayanta wurin baranda can naji su suna ƙara gaishe gaishen yaushe rabo ashe sun san juna

''.ina yini..''.matar ta kalle ni da murmushin mutunci tace '' lafiya lau...Ameena wannan itace Abeedahtu ko?" Mama ta gyaÉ—a kai

'' Ma sha Allahu... yarinya ta zama kyakkyawar budurwa...'' nayi murmushin kunya kafin na dawo na zauna inda na tashi ita kuma ta wuce baye... Inna sarai ta tafi kitchen ta juye shinkafar data gama tsincewa a cikin ruwan da suka tafasa...

Ba daɗe Matar mai suna inna sabuwa ta fito daga baye...tazo ta zauna suka buɗe shafin hira...hmm kundai san yanda idan mamansu mutum suka haɗu da wani wanda suka sani ake shafe awa da awanni ana hira...nikam har abun ya fara cimin tuwo a ƙwarya...

Da ƙarfe biyar da rabi abinci yayi..aka xubo sai da aka ta roƙon matar akan ta zauna taci tana bata so...kafin aka shawo kanta... nidai idan mutum yazo gida na...na bashi abinci yace bazai ciba bazan roƙe shi ba...

Muna tsaka dacin abinci wayarta tayi ringing..lalubo wayar tayi daga kwagirinta dake ɗaure a ƙugunta ta amsa murya a sama...muna jin duk abinda ake faɗa...wai ana neman masu aiki guda biyar mata a gidan wasu masu kuɗi...zare hannu na nayi daga abincin ina sauraren wayar matar... jikina har tsuma yake dana ji ance albashi dubu hamsin...amma mutum zai dinga zama a can gidan masu kuɗin dawowa gida sau ɗaya a ƙarshen wata...

Mama ta lura da yanda nake É—oki yasa tayi min kallon gargaÉ—i...Anaaam ma ta lura dan haka bayan matar ta ajiye waya tana sake faÉ—awa Mama abinda aka faÉ—a duk da munji da sauri Anaaam tace '' Laa kin koga Abeedah tun tuni take ta neman aiki amma ba nasara...yanzu wannan dan Allah ba babbar dama bace?"

Da sauri Asma'u tace '' na sani ko? Itama ta huta da biye biyen rana...'' Mama da inna sarai basu ce komai ba...sai da Inna sabuwa tayi ma Mama magana..hararar mu tayi sannan tace '' manta dasu sabuwa ... Abeedah aiki kaɗai ta taɓayi a restaurant...''

'' hakan ma ya wadatar...'' inna sabuwa ta katse Mama...Inna sarai Mama ta kalla tana neman ceto dan dai bata son inyi nesa da ita...

duk inda ta ɓullo inna sabuwa sai ta toshe daga ƙarshe ta tabbatar mata data san shugabar ma'aikatan gidan sannan bani kaɗai bace akwai sauran mata...kuma zata sa matar ta saka min ido,makaranta ma zan cigaba da zuwa......badan Mama taso ba tayi saranda...kamar in zuba ruwa ƙasa in sha...ashe Allah yasan abinda yake tanadar min shine yasa ban samu aiki a duk inda na nema ba..oh Allah na gode maka...

'' Congratulations.. Abeedahtu...yar wahala '' Anaaam ta faÉ—a tana juya ido...ni ban damu ba..sai murna nake

'' za'a iya ba Abeedahtu advance payment na wata biyar...dan mu samu mu biya kuɗin makarantar mu?" Asma'u ta tambaya...jim inna sabuwa tayi kafin tace zata gwada tambaya...farin cikina ya ƙaru..inna sarai na tayani ....

...anan tace wai gobe goben nan da rana zamu tafi... Raina fes nace '' Allah ya kaimu ''

Fuskar Mama dai ba fara'a...da daddare bini bini ta ɗago ta kalle ni... Har lokacin ban fahimci girman abinda nake shirin shiga ba sai da muka tafi ɗakin mu... bayan an kashe wuta...bayan zolaya da surutun su Asma'u yayi ƙasa..na kasance idona biyu a duhu..na fahimci cewa..gobe zan bar gidan mu...zan bar su Mama in tafi wani wurin da ban sani ba...ban san abinda yake jirana a can gefen ba...zan iya ɗauka? A duk sanda nake baƙin ciki na da koke koke na,su Mama na nan don kwantar min da hankali yanzu kuma zan tafi inda babu su..ya zanyi?

Ban taɓa yin nesa dasu ba sai wannan karon...anya kuwa?

' tunani akan abinda zai faru a nan gaba yana haifar da anxiety..ciwon damuwa...' maganar Jay d take amsa kuwwa acikin kaina...sauƙina guda zan dinga haɗuwa dasu a makaranta banda Mama da inna sarai... numfashi na sauke na lumshe idona...ban san tsawon yaushe na ɗauka ba kafin bacci ya ɗauke ni...

Da safe kamar akwai wani baƙin hadari dake maƙale a saman gidan mu..jikin kowa ya mutu babu mai magana daga uhm sai uhm Uhmm..sai bin juna da ido...ni kaina jikina ba ƙaramin mutuwa yayi ba...naji zuciya ta tayi nauyi...su ɗin iyalai nane..yanzu kuma zan rabu dasu in fara sabuwar rayuwa a wani wuri inda bani da tabbas... Kewar su nake tun kafin mu rabu...ido muka haɗa da Anaaam ta sakar min Murmushi mai kashe jiki..naji kamar zanyi kuka...

Inna sarai ita take shirya min kayana cikin jaka tana min nasiha da wa'azi akan in kula da kaina, addini na da mutun cina...

Su Asma'u jikin su yayi la'asar kamar ni...bayan mun gama sallar Azahar Mama ta kira ni ɗakinta...samun ta nayi zaune saman abun sallah tana tasbihi...na zauna kusa da ita ba kamar koda yaushe da nake kwantar da kaina a cinyarta ba.... wayarta ta miƙo min bayan ta gama tasbihin...

Sannan ta fara magana '' bana buƙatar ince komai..Nasan kin san abinda yake dai dai da wanda ba daidai ba Abeedahtu..na yarda da tarbiyyar dana maki...amma duk da haka...ki kula da mutuncin ki..ki kiyaye Allah...kada ki bari duniya ta ruɗe ki..ko don Kinga bama kusa kice zakiyi wani abinda kin san ba zamu ji daɗi ba...''

ta juyo tana kallona daidai ina share hawaye ta cigaba da faÉ—in

'' abu mai muhimmanci da nake so in faɗa maki shine,idan kin gaji...idan duniyar tayi maki zafi ..idan baki san inda zaki juya ki samu sanyi a ranki ba...kina da Mama Abeedah...ki dawo gida a koda yaushe ƙofar a buɗe take,kada ki manta da Mama dan Allah....'' Muryar ta take rawa..itama tana ƙoƙarin danne kukan da take ji

Rungume ta nayi ina cigaba da nawa kukan...taya zan manta da Mama?

'' Mama ga inna sabuwa nan...'' Asma'u ta ɗago labulen tana kallon mu...jaye ni daga jikinta Mama tayi ta miƙe ta fita.. Asma'u ta shigo ciki...sai ga Anaam ita ma...muka rungume juna...never in my life nayi tsammanin wannan ranar zata zo...kuma ban taɓa tsammanin ɗacin ta zai kai haka ba...

Bayan wani lokaci inna sarai tace '' toh Abeedah ki fito ku tafi...'' jiki ba ƙwari na miƙe tare da ɗaukar hijabina baƙi dake saman gadon Mama nasa idona sunyi ja haka ma nasu Asma'u...ina fitowa Inna sarai ta rungume ni itama '' Allah yasa kin fara a sa'a Abeedahtu ya kaɗe bala'i da masifa daga afka maki...''

saki na tayi na isa inda Mama take tsaye da inna sabuwa itama na sake rungume ta '' Mamaaa....'' na kira da muryar kuka...

''.au Dena kuka Abeedahtu nan da ƙarshen wata ai zaki dawo...''.inna sabuwa take lallashina...ɗago ni daga jikinta Mama tayi tana shanye nata kukan...ta goge min hawaye na '' Allah ya tsare ya kare min ke Abeedah...'' aka amsa da Ameen

Na ƙara kallon su Asma'u dake tsaye daga bakin ƙofar ɗakin mu kowa da hawaye a idon shi kafin na fita...wani sashe na zuciya ta maƙale da gidan mu...rana ta ɓoye bayan gajimare...tana ƙara sani a ƙunci... kamar inyi zamana kada in tafi...

Nayi tsaye bakin ƙofa ina kallon motar da take kamar bus da aka faka gaban gidan mu ga wasu yara zaune a ciki suma...

Su Inna sarai dasu Anaam suka fito...inna sarai riƙe da kayana..wani yaro daga gaban motar ya fito ya karɓa ya samin a bayan buut...share ƙwallar dake idonta inna sarai tayi ta taimaka min na shiga motar na zauna gaba gaba bakin taga...ina ƙarewa unguwar mu da kuma maƙotan mu kallo...yau zan bar abinda na sani...zuwa wanda ban sani ba... The future...my future is uncertain...

Idona sukayi jawur kamar an zuba yaji ciki...ƙila wannan shine farkon abinda nake ta addu'a akai...dama wanda ban san dashi ba?

Inna sabuwa ta fito bada daÉ—ewa ba tare da Mama...sai godiya take mata.. sannan ta shigo motar..driver ya tada muka fara tafiya..su Asma'u suna yimin bye bye kafin Asma'u da Anaam suka rungume juna... fashewa nayi da kuka...zuciya ta tayi min nauyi...

...ina kallon gidan mu..da sabuwar anguwar mu...bishiyar nan dake ƙofar gidan mu da yaran dake wasa saman lilo wasu na faɗa....wasar da muke da yaran maƙwabta...muka wuce filin ƙwallon nan da koda yaushe yara da masu sayarda abubuwa suke cika wurin dan su kalli ƙwallo...nake kallon ƙananan shuke shuken nan da suka fara bushewa..su tafasa dasu sanga sanga...nake kallon makarantar almajiran nan da kuma ƙaton bohol ɗin da ake ɗibar ruwa duk da bamu taɓa zuwa wurin ba...

Nake kallon wani ƙaton dutse da nake da burin hawa amma ban samu na hawo ba...yau gashi zan bar unguwar mu...gidan mu da kowa nawa...in fara rayuwa a wani sabon wuri...na shirya? Me yake jirana? yanzu babu Mama babu Jay D a kusa dani ya zanyi?...

nake jin wani irin ƙaton abu ya tokare min a maƙoshi... musamman da muka hawo kan titi nake ta kallon waje..kamar ince a ajiye ni in koma gida taya zan rayu babu su Mama?...

Lumshe idona nayi...ina addu'a a cikin raina koma meye ne a gaba Allah yabani ikon iyawa dashi sannan ya dafa min...

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived

By Autumn 17 🍁🍁

20. ...Ranar farko...🖊️

Gyara zama na nayi bayan na share hawaye na,na juyo ina kallon mutanen dake cikin motar,duka duka mu Ashirin ne, mafi yawanci daga shekaru sha bakwai zuwa Ashirin da biyu ne,sai wata yarinya ƙwaya ɗaya yar shekaru sha uku...kuma babu wanda yayi kama da ɗan ƙauye ...ganin kallon da suke bina dashi har wasu suna yan ƙus ƙus yasa na ɗauke idona daga kallon su...
Chapter 48 · 0% Book details