← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 67

Sashe 40

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cewar Anaam, bayan tafiyar inna sarai Asma'u tayi wata yar iskar dariya mai ƙular da mutum ...ina jinsu amma ban tanka ba..toh mema zance? Da gaskiyar ta ai..nidai bani da Sa'a...
Maganganun Jay d akan zama pozitif (positive) suka faɗo raina...wani siririn hawaye ya sulalo min..taya zan zama pozitif bayan abinda yake faruwa ba hasashen shi nake ba...da gaske ne? Taya zan mayar da duk wannan a bayan ƙwaƙwalwa ta in cigaba da rayuwa kamar babu abinda ke damuna? taya zanyi farin ciki bayan abinda zai sani farin cikin banda shi? Fita su Asma'u sukayi ya rage ni kaɗai cikin ɗakin...

miƙewa nayi da jajayen idona na isa gaban madubi naja doguwar riga ta baya ina kallon ƙirjina kamar ƙara shafewa yake a kowace rana... cikina ma ƙato sannan ƙuguna da bayana duka a shafe..meyasa? Fuskata kam bana son kallo ba ƙaramin ɗacin rai hakan ke sani ba...gashin gira ta yanzu a ɗan kwai shi amma bai da yawa...gashin idona har yanzu baida tsawo..sai dogon wuya duk ƙasusuwa da nake fama dashi...niɗin dai mummuna ce ta ƙarshe ma...

sakin rigar nayi ina tunani..akwai abinda nake ba daidai bane? Ko banda yaƙini ne kamar yanda ake cewa mutum yayi addu'a da yaƙini... ko akwai wani zunubin da nake aikatawa wanda yake hana addu'oi na karɓuwa? Wannan tambayoyin sun zama wani sashe na rayuwata..wanda har yanzu na kasa samun amsar su...

Cike da baƙin ciki na baro gaban madubin nazo na zauna saman katifar mu..Anaam ta shigo tana magana da kanta ƙasa ƙasa ban ma san abinda take faɗa ba wurin kayanta ta nufa tana neman wani abu..bin bayanta nayi da kallo..tana da faffaɗan ƙugu mazaunan ta manya...juyowar data yi yabani damar ganin yanda ƙirjinta ya ƙara girma cikin yan kwanakin da sukayi a tare damu...da bahaka suke ba,ƙanana ne ko ganin su ba'ayi amma yanzu har sunyi wannan girman ban taɓa lura ba sai yanzu...ƙasa nayi da kaina zuciya tana barazanar tarwatse wa...murya na rawa nace

''...n..i..ta dabance?'' na rasa inda zan sa kaina gaba É—aya duniyar tayi min faÉ—i ban san inda zan kama ba...

Magana ta fara yimin da ba'a tana dariya...a ƙufule nace

'' abinda kike min dariyar akai..yanda nake bani nayi kaina ba kuma bani na zaɓi zama hakan ba ki dena bana so bani nayi kaina ba bani na zaɓi hakan ba''

murya ta tafito kamar raɗa hawayen da nake ta riƙewa suna rige rigen wanke fuskata kamar an ɗaura min wani abu a maƙoshi na kasa numfashi da kyau...jikinta ne yayi sanyi...nadama bayyane a fuskar ta bata ce komai ba ta fita ta barni ni kaɗai...

Washegari bayan mun gama kari inna sarai ta kawo wani abu da bansan Meye shiba ta kirani a tsakar gida Mama na zaune daga baranda tana kallo..shafa min shi ta fara yi tana faÉ—in zai tafiyar da pimples É—in sosai naji daÉ—i amma daÉ—in da sauri ya gushe...idan fa baiyi aiki ba?

Su Asma'u daga gefe suna kallo wurin awa ɗaya abin yayi a fuskata koda aka wanke na duba madubi babu abinda ya ragu...kuma nasa rai koda za'a wanke inga fuska ta ta dawo lafiya lau ashe dai ni wawuya ce dana yi tunanin hakan.... Aloe vera ta ƙara shafamin bayan minti shabiyar ta wanke..ina jin Asma'u na faɗin wannan abin ba aiki zai yi ba...ban bi takansu ba...

Bayan lokaci itama aloe vera'r aka wanke ban damu kaina da duba madubi ba dan dai Nasan labarin gizo baya wuce ƙoƙi...

Ranar haka ta wuce zuciya ta ɗauke da nauyin daya kasa sauka...na ƙuntata nake ji kamar duk nauyin duniyar ne a kafaɗu na babu abinda ke min daɗi...abun ya ƙara tsanani da washe gari aka tashi rana bata fito ba ko ina yayi shiru yaran dake taruwa a gaban gida yau ma basu fito ba,da kosu mutum ya gani ƙila yaji sanyi a ranshi Da ƙarfe goma na fita sayen pad duk a takure nake hannu na gaban hijabi,iska na kaɗawa a hankali faɗuwa gaba na yayi dana ga hanyar da zanbi in wuce akwai dandazon maza da yawa na taka burki ina ji kamar in koma amma ina matuƙar buƙatar pad ɗin...dogon numfashi naja zuciya tana dukan tara tara na cigaba da tafiya

'' a'a kaga wata yar silandiyon nan tafe...'' wani daga cikin mazan ya nuna ni

'' doguwa yar shafal shafal...inama zata saki hijabin sai mu auna....'' wani ya faÉ—a yana tsareni da shegun idonshi da suke ja

Nidai cikin raina sai addu'a nake jikina duk yayi sanyi tsoro ya shige ni ta shi wani daga cikinsu yayi ina kawo wa daidai wurin su ya jera dani muna tafiya Innalillahi ji nayi kamar in zura da gudu..abokanshi sai shaƙiyanci suke mana...hankalina yayi mummunan tashi

'' yan mata ya yau...'' Muryar shi kamar irin na riƙaƙƙun yan shaye shaye,ban amsa ba nayi sauri nayi gaba yana biye dani a baya iska yake kwashe min hijabi naji kamar inyi kuka ban ƙara shiga yanayi ba sai dana isa shagon naga nan ma akwai maza da yawa zaune a wurin...taya zance a bani pad yanzu?

Allah yasa akwai mutane da yawa kafin ni...sai binmu suke da kallo...

'' kaga wata mai idon mage...'' wani ya taɓa abokinshi yana nuna mashi ni.. ƙin kallon sashen su nayi babban burina a wannan lokacin shine inga na isa gida

'' yan mata mai za'a baki?" Mai shagon ya tambaya da murmushi a fuskar shi...numfashina na riƙe ina tunanin abinda zan faɗa mashi batareda wa'yannan sunji ba biro idona ya hango min sai na ɗauka na rubuta saman kuɗin ' Pad'na miƙa mashi...karantawa yayi a ranshi cike da fahimta ya juya ya ɗauko yasa cikin baƙar leda...

'' na gode...'' na faÉ—a da sassauci a raina.

.'' yauwa...'' na ƙara gyara hijabina sannan na juya Zan fita

'' kalla kalla idonta wallahi kamar na mage...'' wani daban yayi maganar da hanzari nabar wurin

Wannan gayen da ya biyo ni yana nan tsaye muna haɗa ido ya sakar min wani murmushin dayasa naji cikina ya bada ƙuuu..gaba ɗaya zubin shi bai yi kama dana mutanen arziƙi ba...

Wuce shi nayi ina tafiya da sauri...yana biye dani babu abinda nake faÉ—a sai Lailaha illa anta subhanak inni kuntu minazzalimeen

'' yan mata ji mana..'' ya sha gabana saura kaÉ—an jikin mu ya haÉ—u.. nayi saurin ja baya

'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...'' na furta hawaye na ƙwace min wasu biyu daga cikin ƙawayen nashi suka zagaye ni suna maganganu ba daɗin saurare

'' ni yanzu wa zai taimake ni?" Nayi ma kaina tambayar cikin raina..ina kallon su da idona da sukayi ja ash ɗin ya ƙara duhu

'' ku kalli ƙwayar idonta kamar ruwan toka...''

'' eh lallai ba shakka hakane...''

'' daɗin ta na daban ne da alamu...'' suka kwashe da dariya ni kuwa babu abinda jiki na keyi banda rawa...na zama kamar tunkiya a tsakiyar kuraye..ban ƙara ruɗewa ba sai da naji ana jan hijabina daga baya...

Na fashe da kuka '' wallahi ƙwayar idonta da shape ɗinsu ƙara tsumani suke.. ''

Na shiga tashin hankali na tsorata sosai..fara matsoni suka yi dukan su babu mai kyau'n gani sai jajayen idanu...

wani daga cikin su ya riƙe hannu na dana damƙe hijabina dashi..ihu na kurma gaba ɗaya na fice hayyacina na shiga wani irin yanayi da nima ban fahimta ba sakina yayi suka dafe kunnuwansu kafin kuma suka fara tserewa sakamakon ihun da nayi ya jawo hankalin wani mutum dake wucewa ...da sassarfa ya ƙaraso inda nake nikam na rufe idona sai ihu nake...

'' baiwar Allah...'' mutumin ya kira da ƙarfi fuskarshi da damuwa..buɗe idona da suke rufe nayi...suka sauka akan fuskar shi...ido guda manne da plaster ɗayan kuma lafiya lau..''.kina lafiya?" Ya tambaye ni

Girgiza mashi kaina nayi...duƙawa yayi ya ɗaukar min ledar pad ɗina data faɗi

'' mu tafi in raka ki...'' ban Musa ba nayi gaba yana biye dani duk a ruÉ—e nake... babu abinda nake banda hawaye ina tafiya da sassarfa kamar zan kife..yana faÉ—in inbi a hankali...

Jikin Mama na faɗa na rushe da kuka tana tambaya ta mai ya faru...inna sarai kuma ta fita zuwa ƙofar gida saboda sallamar da mutumin keyi...na tafi na barshi da pad...

Anaam ma tazo ta zauna daga gefe haka ma Asma'u...hankalin Mama ya tashi.. sassauta kukan nayi na faÉ—a mata abinda ya faru...ta rungume ni tana shafa baya na...'' Allah yasa bawan Allah'n nan da Asma'u ta jiwa ciwo yana kusa shine ya ceceta..gashi har yanzu bamusan sunan Shiba...''.inna sarai ta faÉ—a da alhini...

Anaam da Asma'u suke taywy Mama lallashina a haka har bacci ya É—auke ni.... gaba É—aya babu wanda yaji daÉ—in abinda ya faru...

Ranar Monday da wuri muka isa makaranta har ma muka samu assembly kuma Diyaam da Jay D suma har sun iso...hakan yayi min daÉ—i '' uniform É—in sunyi maki kyau..'' Murmushi Anaam tayi da jin Diyaam ta yabe ta '' na gode...''

'' Attention..'' Assembly pirifet ta ɗaga murya..hakan yasa yan SS 1 da 2 sun yi ƙasa da surutun da suke..kowa ya shiga layi..nice a baya gaba ɗaya dan wurin gyaran layi mun rabu sannan dama nafi son kasacewa a ƙarshe bana son kowa yana goga min jikin shi a baya bayan anyi addu'oi, national anthem da national pledge principal ta hawo saman dakalin ta fara magana akan jarabawar dake ƙaratowa... Tayi mana nasiha da kuma ƙarfafa mana guiwa da muyi karatu sosai

Bayan tagama ezzam master (exam master) shima ya hawo bayan ya gama cika mu da surutu yake faɗin kuɗin waec da neco dubu saba'in da biyar...'' hmmm!!" Wurin ya ɗauka da surutu wasu kamar zasu dake shi jin uwayen kuɗin daya ambato ya ƙara da faɗin wani sati za'a fara mock exam ɗin...naji gabana ya faɗi...idan fa banci jarabawar ba? Idan fa na faɗi?

Ƙasa nayi da idona na ɗaura hannu na a gaban goshi na saboda ranar data fito...gashi ko kuɗin wannan term ɗin bamu biya ba...kuma mu uku ne..kenan kusan dubu ɗari biyu da wani abu zamu biya...BALA'I!! Ji nayi zufa tana wanke ni daga ko wacce kusurwa ta jikina..jini ya janye daga fuska ta...

Sai da suka gama yi mana gargaÉ—i akan mu da ake bi bashi muyi sauri mu biya idan ba haka ba,bamu ba rubuta jarabawa.. sannan aka sallame mu...
Chapter 40 · 0% Book details