← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 67

Sashe 20

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Oti ki kiyayi abunda zaki faɗawa mutum koda da wasa ne,zai iya kasancewa a gareki ba komai bane amma su kuma wannan maganar zata zauna dasu tasa su dinga tunanin ta dare da rana suna masu tsananin baƙin ciki dan a gare su abunda aka faɗa ɗin gaskiya ne koba haka ba

🍁🍁: NOTED ABEEDAH 🥹

Ina tafe ina sharar hawaye,taya Mama zata faÉ—i haka!

Ba daɗewa na kawo wurin sani me niƙa..kuɗin niƙan naira ɗari ne,na biya na ɗauki niƙan dake da bala'in nauyi..ga hanyar duk ruwa sun taru ba kyau duk inda mutum ya tsoma ƙafa sai ya taka kashi ko ya jefa ƙafa cikin kwata...

Har yanzu kuma gari bai washe ba..kamar akwai hadari...kowane juyi sai mutum yaga gungun maza zaune idan mutum yazo wucewa su bishi da ido..kuma Allah ya gani hannu na dana sa ina tare hijabina tagaba ya fara ciwo ga ɗayan dana riƙe garin dashi shima ya gaji

Ga yunwa data ƙara salsale min ciki..Ni Abeedahtuwo naga rayuwa wallahi!

'' Yan mata ina zuwa ne!"

Wani gaye dake tsaye bakin wata motar data ga duniya ta gode Allah tsakanin leɓenshi wani siririn karan taba...bakin nan yayi baƙi ƙirin haka ma idonshi sunyi ja...sai wasu banzayen ƙananan kaya daya ke saye dasu,cikin shi kamar na me ciki wata uku..yana wani shafawa nidai yayi min kama da ɗan iska wallahi...

Kuma tunkaro ni yake yana jimana..yan mata me ruwan tokan ido...ji nayi kuka na shirin ƙwace min gashi babu mutane a hanyar fa... Na ƙara sauri inayi ina juyowa...da naga abun yaci tura sai kawai na saki garin na kwasa da gudu shima biye dani a tamanin

'' wayyo Allah..mutane a taimake ni...kwarto!!!"

Na faɗa da iya kar muryata ina ƙara ƙarfin gudu na...

'' ke ki tsaya mana magana nake so muyi!"

Wai Magana yake so muyi shine yake bina da gudu haka

Haka muka dinga kwasar gudu kamar wasu mahaukata gashi na gaji, wallahi idan a tambaye ni bansan inda nake sa ƙafa ba

Sai kwararo kwararo muke bi...Ni ban masan ko yana nan biye dani ba, kayan jikina duk sun ɓaci da jar laka saboda yanda slippers ɗina ke ɗibar lakar yana watsa ta sama zuwa ga kayana!

Sulɓucewa nayi na faɗi ƙasa tim, fuska farko cikin wasu jajayen ruwan laka kaya na da jikina suka ɓaci...cikina ya bugu da ƙasa... slippers ɗina suka bar ƙafafuna...naji wani arnen ciwo yana ratsa Ni...

Mutanen dake tsaye wurin suka juyo suna kallona suna magana ƙasa ƙasa

'' Subhanallahi! Ashsha tashi tashi...''

wani mutumi ya faɗa tare da miƙar dani...sauran mutanen suka fara min sannu mafiyawancin su maza ne..naji kunya ta kama ni...da ƙyar nake iya tsayuwa

'' sannu yan mata baki ji ciwo bako?"

Wani mutum daban ya tambaya gyaÉ—a kai nayi ina sakin wani marayan kuka

Sai kuma na shiga tafiya batareda na tanka masu maganganun suba..ko tambayoyin su

Sai da nayi tafiya mai nisa na gane cewa ashe har na fito babban titi...inda akwai tituna da yawa sannan saman gada nake ina hango ƙasan gada...da gine gine daga nesa... Gaba da baya titi ne...babban titin jahar kano... Sai kuma rana ta ƙwalle da wani uban haske da zafi...ga sauran hadari ... Ban kosan inda nake ba.. Innalillahi wa inna ilaihi raji'una... Dama na faɗa ma mama ƙila ɓacewa zanyi amma wallahi dana ce bazan dawo ba da wasa nake ...wayyo Allah...na cigaba da kuka na ina tafiya daƙyar kaya na na ɗiga da ruwan datti..idona sunyi mahaukacin ja jan ajiyar zuciya kamar zan shiɗe

Babu abinda yafi tada min hankali irin kasancewar bansan inda nake ba..kuma bansan inda zani ba...kuɗin dake hannuna sun faɗi ko takalmi babu a ƙafata

Mutanen dake wuce wa saman gadar sai kallo na suke...kuma har lokacin hannu na banyi ƙasa dashi ba a ƙirji..ga tsoro daya cika ni kuma ban san ko ƙarfe nawa ba

A nan gida mama ganin har ƙarfe huɗu kuma tuwo bata dawo ba, hankalin ta ya tashi ,kada dai ace Abeedah ta ɗauki maganar ta har zuci, zata shiga bayi taji sallamar Asma'u '' Salam alaikum!"

A gaggauce Mama ta amsa sallamar tace

'' Ma'u zoki bi man bayan Tuwo,tun ɗazu dana aikata ta ɗauko niƙa bata dawo ba..''

da damuwa a fuskarta tayi maganar

Ajiye jakarta Asma'u tayi daga bakin kitchen

'' ƙila baiyi niƙan ba sai yanzu yake yi ko ƙila mashin ɗin ya samu matsala...bari in tafi yanzu!"

Ta faÉ—a tare da shiga kitchen tasha ruwa sannan ta fita

Mama ta sauke ajiyar zuciya

'' karfa ki jirani Mama baxan dawo ba!" Maganar tuwo ta maimaitu a ƙwaƙwalwarta gabanta ya faɗi...

'' zaki dawo Abeedah kuma zan baki haƙuri..kidawo kawai!" Ta faɗa cikin ƙarfafa kai kafin ta shige baye zuciya da nauyi

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

Free pages

11. ... there's life in art...🖊️

Mama na Safa da marwa a tsakar gida Asma'u ta shigo kamar zatayi kuka Mama ta tsaya cak tana kallon ta,

'' Mama wai yace tun ɗaxu ta bar wurin shi bayan ta karɓi niƙan...'' ta ƙarashe da hawaye

'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una... ya Allah ina É—iya ta tashiga ne..ka karemun ita..''

Mama ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe kukanta.. idonta sunyi ja fuskar ta a ƙuntace kamar zuciyar ta... sai kuma ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta ita da Asma'u suka fito daga gidan suka shiga neman tuwo..duk wanda ya gansu ya tambaye su, Mama take musu bayani da karyayyar murya cewa bata ga Tuwo ba sai su dinga taya ta nema...

Ni kam cigaba nayi da zurarawa kuma har lokacin bansan takamammen inda nake ba,idan na tambayi mutane..sai suyi ta bani mabanbantan wurare wani yace airport road,wani yace É—orayi.. wani yace..wani yace...

Hawaye sai zuba suke daga idona ba tsayawa..ga yunwa ta fara ƙarar da ƙarfi na harda ƙishirwa

'' wayyo Allah..ka kaini gida da wuri.. Mama ta damu nasani...dan Allah ko cikin addu'oin dana ke ne da baka amsa ba,ka amsa wannan na yafe sauran...''

na faɗa cikin kuka irin sosai sosai ɗin nan...kukan motocin nan dake wuce wa zut zut ba ƙaramin tayarmin da hankali suke ba..danji nake kamar zasu make ni...

Zaune suke cikin wata baƙar mota me tinted glasses.. Khaleel a baya saye da riga blue da jeans shima blue...ga jacket black color daga gefen shi,hannun sa saye da silver wrist watch... Askin kanshi low cut lips ɗin shi kamar ya shafa lipstick

Hannunshi riƙe da waya yana video call da wata baturiya cikin deep voice ɗinshi yace

'' i missed you too Leona... Ji nake kamar inyi Fika fiki in ganni America!" Ya ƙarashe yana shafa kanshi haɗe da kashe mata ido

'' Awwnn... Abraham i love You so much...'' ta faɗa tana blowing kiss...ya wani taune leɓenshi yana mata kallon ƙasa ƙasa

Daga seat ɗin gaba driver ne saye da fararen uniforms..daga gefen shi kuma gayen nan ne..kamar koda yaushe saye yake da facemask... Sai baƙar T shirt mai dogon hannu an rubuta' VOID' da kuma jeans baƙi, ya ɗaura rigar sanyin saƙa baƙi asama...jet black hair ɗinshi ya zubo har saman girar shi..hunter eyes ɗinshi kafe akan littafin drawing dake hannunshi yana drawing ɗin wata mace...his vertiver scent filled the car kamar wanda yayi mugun abu yake ɓoyewa da ƙamshin turare tsabar ƙarfin turaren,ga wani mysterious aura emanating from him

... Ɗago idonshi yayi yaɗan kalli gaban motar can ya hangi wata yarinya na tafiya duk tayi daƙun daƙun sai kalle kalle take kamar tana ƙoƙarin tsallaka titi...ɗauke idonshi yayi ya mayar akan sketching pad dake cinyarsa ya cigaba da zanen shi...

Khalil na dariya ya juyar da kanshi gefe..daidai Abeedah ta juyowa da fuskarta..his heart skipped,duk da baiga fuskar ta da kyau ba,zai iya rantsewa itace! '' za muyi magana anjima babe!" Ya faɗa cikin wayar yana gyara zaman shi ya taɓa gayen dake zaune a gaba '' ROM,waccan ba Abeedah bace?" Ya tambaya ido waje yana sake kallon bayan su dan har sun wuce ta

da deep baritone voice ɗinshi yace '' why are you asking me?" ya dawo masa da tambayar batareda ya ɓamɓare idonsa daga sketch pad ɗin ba,Khalil ya fisge littafin

'' come on don't be heartless!" Banza dashi Roman yayi yana kallon cinyarsa that was now empty,ya watsa ma Khalil wani banzan kallo as if he had stolen his life

''you have five...'' ya ɗago fararen yatsun shi guda biyar ya cigaba da faɗin ''just five seconds to return my book!" Ya ƙarashe his hunter eyes dangerously cold,cold enough to slice the air

quietly Khalil ya ajiye masa littafinsa inda ya É—auka for peace to reign

'' Allah ya baka haƙuri!"

Roman bai sake kallon Khalil ba ya cigaba da abinda yake

Khalil ya Kalli driver'' Habu kayi U turn mu koma wurin yarinyar can!"

'' toh oga!" Driver'n ya faɗa kafin ya canja hanya... Mayarda bayanshi Khalil yayi ya jingina da seat yana tapping ƙafafunsa restlessly

Ina tsaka da tafiya naji anata wani peef peef da mota bayana..haushi naji ya ƙara ƙume ni wallahi..kamar in tsaya in zazzage musu abinda ke raina amma ban tsaya ɗin ba saboda rana ta faɗi kuma babu alamun zan kai gida da wuri...zuciya ta sai bugu take da ƙarfi idan fa ban isa ba? Idan fa ƙara ɓacewa nake batareda na sani ba?

Hawaye na da suka tsaya suka shiga rige rigen saukowa da sauri... Sai kuma kuka ya biyo baya ga wannan banzar motar dake bina da peef peef kome na tsare musu ban sani ba !

Tsayawa nayi na rarume wani dutse na juyo a fusace na jefa a glass ɗin gaban motar duk baƙin ciki da tsoron da nake ji na sauke shi akan su

'' dalla wai meye haka kun wani bikun ishe Ni da peef peef me na tsare muku ne eh? Duk wannan hanyar da aka bar muku bai ishe ku ba sai kunzo kuna cika min kunne da wani peef peef can...an san kuna da mota dalla ku matsa kuba mutane wuri....''
Chapter 20 · 0% Book details