← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 67

Sashe 53

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka cigaba da ci min mutunci...naji duniyar tayi min zafi...na wulaƙanta...raina har ɗaci yake...da ɗaya da ɗaya suka bar wurin," ki tabbatar a koda yaushe kina dining...safe,rana da dare...'' Seraphina dake ƙarshen fita ta faɗa... sauran ma'aikatan suka shiga gyara wurin...

Aina'u ta matso kusa ta rungume ni tana bani haƙuri... ...da ƙarfe huɗu na koma sashen mu Mama Asabe tayi min nasiha da kuma nuna min illar biye musu

'' yanzu dukansu zasu iya targeting ɗinki su dinga bullying ɗinki ... ki kiyaye kinji?" Kaina kawai na jinjina hawaye na rige rigen sauka a fuskata... Wurin ƙarfe biyar muka sake komawa bakin aiki,ɗakin Seraphina aka turani wai tana nema na...

Batareda wani shayi ba na isa ɗakin da ya tsaru sosai...samun ta nayi kwance saman gado da bumshort da half cut... Baƙin gashinta ta raba shi gida biyu ya sauko har zuwa kafaɗarta...fararen ƙafafunta sun sha nail polish ita kanta yarinyar kyakkyawa ce daka ganta kaga jinin larabawa...in banda zuciyarta da take mummuna bata da aibu...

'' Gani Madam Saratena...'' zabura tayi ta xauna dan kawai na kira ta da saratena..'' me kika kirani?"

'' Madam Saratena!" Na maimaita badan ban iya kiran sunan ba sai dai dan hakan naga damar kiranta

'' witch,sunana Seraphina ba Saratena ba...'' duk da ta gyara min yi nayi kamar baxan iya kiran sunan ba nacigaba da ɓatawa '' Oh my God! You know what..ki kira ni da Sarah!" Ta faɗa da ihu kamar zata dake ni

'' toh Madam Sanah...'' da takaici ta nunamin bayenta...'' akwai kayan dana jiƙa a ciki...kije ki wanke...''

Bayen na wuce batareda nace komai ba..ta saki murmushin gefen baki...ban fahimci ma'anar hakan ba Saida na shiga na iske pants ɗin tane datayi jinin al'ada dasu suka gama ɓaci ta jiƙa na tsawon lokaci har sun fara wani arnen wari take so in wanke...ji nayi kamar zanyi amai

'' kuma ki tabbatar sun fita bana son naga stain..'' ta faÉ—a daga waje like an absolute witch...

Hijabina na cire na ɗaure hancina na shiga wanke wa amma duk yanda nayi ƙoƙarin ganin na wanke su da kyau sunƙi fita...daga ƙarshe na tsantsame su..na gyara bayen na fesa air freshener duk zufa ta wanke ni.tana gani na ta sheƙe da dariya harda riƙe ciki ..haushi yasa banyi wata wata ba na juye mata wankakkun pants ɗin a fuska....

'' Oh my Goooood...witch!!!" Ta saki ihu tana hankaɗe pants ɗin daga jikinta da ƙyanƙyami...dama can warin bai fita ba

'' ewwww!!!!!!!"...

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17🍁🍁

22. ...Farzan...🖊️

Yawu na haɗiye ganin yanda Seraphina ke ihu kamar mahaukaciya...sai kuma ta miƙe tayo kaina tana huci...ja baya nayi da zufa tsakanin cinyoyi na,ƙafafuna sunyi sanyi...Fuskarta tayi ja da alamu idan ta cimman mari zan sha...

Abu guda ne ke yawo a kaina a wannan lokaci...sakin bokitin dake hannu na nayi tare da sakin ihu na riƙe kaina....na jujjuyar da idona...gray ɗin ciki ya ɓace duka farin kawai ake gani...na cigaba da ihu ina jujjuya kai ina gurnani...

Tsayawa Seraphina tayi ido waje tsoro ya bayyana a fuskarta...ƙirjinta ya fara sama da ƙasa....wani irin juyowa nayi inda take da ƙarfi kamar zombie na saki murmushin daba murmushi ba...irin wanda kesa mutum ya tsorata

'' Oh... SERAPHINA....'' na fara matsota ina tafiya a murÉ—e kuma har lokacin idona basu koma daidai ba

Ja baya ta shiga yi tana kalle kalle... na tabbata a wannan lokacin jinin ta ya hau kamar yanda jinin mutum zai hau idan yana kallon fim É—in horor...

'' s...stay ..'' kasa Magana tayi sai ihu data saki ta faɗa Baye ta rufe da mukulli.. da sauri na isa wurin ina buga ƙofar da ƙarfi ina kiran sunanta da Muryar tsoro..daga ciki take kiran innarta ta ceceta....

Ganin nayi nasarar ceton kaina,kada in cigaba da acting ta gano ƙarya ne in shiga uku yasa nabar pants ɗin nan na fita daga ɗakin a guje kamar wacce ke gudu daga abin tsoro...gaban wata ƙofa Ash na tsaya a ƙarshen hallway ɗin na fashe da dariya tuna yanda fuskarta ta kasance a wancan lokacin...

dena dariyar na juyo ina kallon ƙatuwar ƙofar...kamar wani abu daga ciki na kira na ... meyasa wannan kaɗaice ƙofar da kalar ta yake daban da sauran ƙofofin? A maimakon numba, XXXX ukune rubuce a sama...matsawa nayi kamar wadda aka asirce na ɗaura tafin hannu na a sama ido waje baki sake..har zan tura ƙofar

'' Wacece ke?" Firgita nayi na juyo da ƙarfi..ƙafata ta gurɗe na faɗi ƙasa zuciya tana tsananin bugu...kallon wanda ke gabana nayi..dogon gaye ne fari tass,sumar kanshi ja yana da ember eyes kamar na vampire,ga lips piercing da yan kunne da fuskar rashin mutunci...idonshi kamar na shaho,akwai wani tabo tsakanin girar shi...Muryar shi kamar ƙanzo...damtsen shi duk ya zane da tattoo yana ƙare min kallo...

Rasa murya ta nayi...nake haÉ—iyar yawu'' mage ta cinye harshen kine?" Ya haÉ—e gira da irin kallon da yake min Nasan bai sona ko kaÉ—an,nayi mamakin hausa a bakin shin kamar jakin kano..da yake dai É—an kano'n ne

'' Uhmm... yar aiki ce Ni...UHM...zanyi aiki ne...'' ɗage gira yayi,idon shi a nawa,na haɗiye yawu ganin ya mayarda kallon shi a ƙofar na fara rarrafe zan bar wurin

'' nace ki tafi ne?" Ya tambaya da daga murya...da sauri na zauna wurin ina matsa ƙafata...'' gwadawa nake in gani ko ƙafata lafiyar ta lau...kwanakin baya na faɗo daga bishiya...'' riƙe numfashina nayi da irin kallon da yake min..sai yayi ƙwafa yabar wurin...

Ajiyar zuciya na sauke na miƙe tsaye da sauri na kama gabana...ina mamakin meye bayan wannan ƙatuwar ƙofar?

sanda na shiga sashen mu ƙarfe shida da rabi,duka sauran ma'aikatan sun dawo harda su Fauziyya... wuri na samu a nan parlor na zauna ina tunanin waccan ƙofar..ina so in San meye a baya..

'' Sir Farzan ya dawo fake Fauxeey!" Rasheedah ta zauna kusa da Fauziyya dake latsa wayarta tana cin cingum ƙaras ƙaras...da yawa daga cikin ma'aikatan suka ɗago '' dan Allah?" Duk da badasu take ba suka tambaya suna dafe ƙirji ido waje

'' sosai ma,ƙarya zan maku ne?"...girgiza kansu sukayi kafin suka cigaba da hira akan sauran biyun da zasu dawo ranar Monday..wanda Allah ya gani bana farin ciki da dawowarsu koma su waye su....

Aina'u da Waleeda suka zauna kusa dani muna yar hirar mu..duk da bamu san juna sosai ba,amma ai tare muka zoko?

'' da yake Allah yasa ni ranar Monday makaranta zani...aikina zai ragu!" Na faÉ—a da jin sanyi a raina,zanje inga su Asma'u da Jay d...naga nawar Monday tazo

'' wasu basa son aiki sai kawai son banza da kuma a biya su...hmm ba haka abubuwa ke faruwa anan gidan bafa...dole mutum yayi aiki ehe!" Fauziyya ce tayi maganar kuma nasan dani take

'' kema dai kya faÉ—a,tun kafin aje ko ina,yar wata har tafara gajiya....'' Amrah ta goya mata baya.. dama naga alamun itama yarinyar wani kallo kallo take min sannan itace tasa min uniform a hannu batareda tayi min bayani ba...

'' ɗazu ba kunan da kunga yanda Madam Seraphina da sauran yan uwanta suka ci mata mutunci...wai harda kiranta flat board...da gaskiyar sufa amma!" Dukan su dariya suka sa dajin abinda Habeeba ta faɗa...idona suka fara ƙaiƙayi hawaye suka taru ciki... Aina'u da Waleeda suka dafa hannu na alamun tausasawa...

Koda basu tausashe niba ai dole in tausashi kaina... da gaskiyar su,ko acikin masu aikin bayan waleeda tunda ita ƙarama ce,nice wacce gaba ɗaya bata da shape kuma take da fuska mai pimples dayawa....

Tashi nayi na nufi ɗakin mu daga bayana ina jin yanda suke dariya suna shewa..suna ƙara kirana da sunayen cin mutunci...

Rufe ƙofar nayi na faɗi zaune a baya na fashe da kuka mai cin rai...har Saida kaina ya fara ciwo..jin kiran Sallah na miƙe na isa bakin taga na kware labule da jajayen idona ina kallon tsakiyar gidan ba kowa...rana har ta faɗi..haske mai ɗan duhu ya sauka irin na maghrib sai bishiyoyin dake nan da can saboda iska dake kaɗa su...ji nake kamar ana matse min zuciya ta,kamar an ɗaura min abu mai nauyi...

Barin bakin tagar nayi na shiga Baye nayi alwala nazo nayi sallah...can anjima kaɗan Mama Asabe ta shigo ɗakin takalli fuskata...da farko batace komai ba sai data gama sallah sannan ta juyo sashen da nake zaune ta tambaye ni mai ya faru...da naso in ɓoye mata,ban sani ba ko saboda yanda tayi tambayar a tausashe ne yasa na faɗa mata komai batare da na ɓoye yanda nake ji a duk sanda na kalli kaina ba ko idan aka yi magana akan yanda nake...

Ta lallashe ni tare da faɗin zata taimaka min... murmushi kawai nayi..naji wa'yannan kalmomin fiye da a ƙirga daga ƙarshe babu abinda ke canjawa...

Bayan Sallar Isha'i kamar yanda Seraphina tace ina tsaye sanda suke cin abincin su na dare...every now and then sai ance in miƙo wannan ko wancan...idan nayi ha daidai ba nasha faɗa... sauran ma'aikatan kawai suka zama by standers babu wanda ke wani abu sai Ni

'' duh! Ke baki iya yin abu daidai ne?" Heedayah tayi maganar tana harara ta...naso in mayar mata da baƙar magana sai kawai nayi shiru..na ɗauki abinda take so ɗin na miƙa mata...take huci kamar tunkiya...

'' ke miƙo min sushi...'' Mukhtar ne ya faɗi hakan yana min wani banzan kallo...na gama kalle table ɗin Ni banga wani abu ba can wai shi shi..'' ban san Shiba...SIR!" Na faɗa da takaicin kallon shi da baya ƙarewa

Ayaan ne ya nuna min tsushi ɗin...abin yaban ƙazanta...dole sai dana zagaya na ɗauko tsushi ɗin nazo inda yake na miƙa mashi...amma sai cewa yayi in zuba mashi,na tsaya ta bayan shi ina tsaka da zubawa ya kwanto da kanshi ya gogi ƙirjina...zabura nayi badan nayi niyar hakan ba,tsushi ɗin dake hannu na ya zube mashi a jiki...

'' Ahhh!!!" Ya saki ihu dan abin nada zafi...

'' subhanallahi!!" Naja baya...mutan gidan kuwa suka hau yimashi sannu kafin lokaci guda manyan su da ƙananan su suka yimin caaa suna zagina ta uwa ta uba..naji kamar zuciya ta zata fashe...
Chapter 53 · 0% Book details