← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 67

Sashe 44

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gefe ɗaya kuma ina cigaba da karatun littafai na...ina ɗan ƙara iya turancin..duk kalmar da ban san ma'anar taba,nakan rubuta idan na haɗu da Jay d sai in tambayeta ma'anar kalmar... A duk sanda na tuna kuɗin da ake tsammanin mu biya sai naji hankalina ya tashi gabana ya faɗi...ban san inda zamu samu wa'yannan maƙodan kuɗaɗen ba...duk sanda nake tunanin na fara samun sararin shan iska daga matsalolina sai wata ƙatuwar matsala ta kunno kai ta sake tayarda wayan'can na bayan da nake tunanin ba zasu sake damu na ba...

Zaune muke a parlon su Jay d muna kallon wani fim ɗin Hausa..dukan mu mun mayarda hankali ko ƙiftawa bama san yi...

Takun da mukaji a matattakala yasa muka juyo ba shiri dan dai mun san mu kaɗai ne a gidan,Maman su Jay d ta fita mamaki ya hanani motsi ganin wanda ke wurin shima yayi tsaye yana min murmushi..saye da baƙin wandon Gucci da farar riga da slippers...

'' Name sa...'' kafin ya iyar Anaam data sheƙo da gudu daga ɗakin Jay d tayo cikin shi ta bangaje shi dama ya kawo ƙarshen stairs ɗin faɗuwa yayi Itama garin ƙoƙarin taimaka mashi ta biyo shi suka faɗi tare ita a sama

'' Ahhh!!!"miƙewa mukayi muka isa wurin su muna musu sannu Abeed yayi kwance fuskarshi a yamutse alamun yaji zafin faɗuwar hakan yasa ya kasa motsi ya buɗe ido yana kallon sama..da sauri Anaam ta miƙe tana rarrabar ido

'' sannu Deen tashi...'' Jadeedah ta miƙa mashi hannu ya kama ya miƙe da ƙyar hannun shi dafe da ƙugu... ta taimaka mashi ya isa ya zauna saman kujera muka bi bayansu da sannu Anaam ta tsaya kusa da benen tana cizon yatsa da zarar ido...

'' yauwa...wash Allah na...ta kusa karya Ni...'' ya furta yana lumshe ido tareda jingina da kujerar...mu uku muna fuskantar shi

'' ni ban ma san kana nan ba...'' murmushi yayi yana kallona nima shi nake kallo na kasa yarda da cewa shine Deen É—an uwan Jay d da take magana akai koda yaushe...

'' Bee wannan shine yaya na da nake ta faÉ—a maki...Deen...'' ta juyo gefe na

'' kina nufin Abeed ɗin da nake baki labari muna aiki tare?" haɗe girar ta tayi take kallon tsakanin nida shi shafa ƙeyarshi yayi

'' yeah nine...'' nama rasa abin faÉ—a haka ma Jay d kamar bata san cewa shima a maina hotels yake aiki ba...

'' haka kawai muka neme ki muka rasa...'' ya furta.na sauke numfashi nace '' ai korata sukayi ba bayani kuma ko suba ni notis wallahi...''

'' haba dai?" Ya gyara zaman shi njina kaina nayi muka cigaba da hira a hankali Anaam ta ƙaraso ta zauna daga gefen Asma'u ya juyo gefenta

'' wannan yar fullo yar uwar kuce?" ƙasa da kanta Anaam tayi Abeed na mata kwarjini sai satar kallon shi take tunda ta zauna wurin yanzu kuma da yake kallonta ta kasa haɗa ido dashi

'' eh baka ga kama ba wannan Asma'u kuma ƙanwa ta sai Jay d da nake ta faɗa maka ƙawata...'' mukayi dariya dukan mu banda Asma'u da Anaam da tayi ƙasa da kanta jin yanda Abeed ke kallonta...duk ta takura...

'' Mu tafi gida...dare yafara yi...'' ta faÉ—a min tana turo baki

'' ƙarfe biyar fa..yadai yar fullo? Tserewa kike ƙoƙarin yi baki ban haƙuri ba?" Ɗauke fuskar ta tayi tana ƙara zumɓuro baki gaba tana ƙunƙuni ya girgiza kanshi cigaba da azalzalar mu tayi akan mu tafi dole muka miƙe ba shiri

'' bari in sauke ku...'' inji Abeed,Anaam kamar zata yi bindiga..dama dan yana wurin tace su tafi yanzu kuma shi zai sauke su gaskiya dai da sauri tace

'' a'a ka barshi kawai,za muyi essa sais (exercise)...'' É—age gira yayi tayi saurin É—auke idonta

'' nima bari inzo mu tafi...'' Jay d ta ruga sama da sauri ta ɗauko mayafi muka fito tare bayan Abeed ya ɗauki mukulli muna tafe muna hira..sai naga kamar ya ƙara girma ya ƙara zama wani kamili... Anaam itace a baya...

Mu uku muka shiga baya...Anaam tana zuwa taga mun cika wurin ta nemi da in dawo gaba naƙi badan taso ba ta shiga gaba ta zauna,yanayin zaman naga kamar tana zaune saman garwashi sai hura hanci take...

Tada motar Abeed yayi muka fita masu gadi na mana Allah ya kiyaye...nida Jay d muke ƙara yin revision akan abubuwan data koya mana a yau har muka kawo. godiya mukayi mashi,Jay d ta shigo ciki ta gaishe da Mama...kafin suka tafi...

Bayan Isha'i muna kallo a ɗakin su Mama a ba zata Anaam tace '' inna wai kin san kuɗin waec ɗin mu..ina nufin kuɗin jarabawar mu ta ƙarewa..dubu tamanin da biyu!" Dafe ƙirji inna sarai tayi ido waje tace da ƙarfi '' Dubu tamanin da biyu? Ina za'a samu wayan nan kuɗin ma ku uku?" Tashi zaune nayi ina kallon fuskar Mama data canja damuwa ta mamaye ta a tashi guda.... Asma'u tace

'' ai ke zaki zauna idan munyi graduating sai daga baya kiyi ko Abeedah wani dai daga cikin k..m''

'' sannun ki uwar yan son kai...!" Anaam take hararar Asma'u kamar idonta zai zubo...a sanyaye nace '' ina cigaba da neman aiki ai...''

'' toh wane aikin zasu biya ki koda dubu ashirin ne bale har yakai dubu tamanin faɗa min inji?" Anaam ta jefa min tambayar..na kasa bata amsa..kuma ma idan nace zan dinga tarawa ai lokaci ya ƙure

'' gashi azumi ya kusa kenan bamu da kayan salla" Ita baƙin cikinta kenan babu wanda ya tanka ta daga ƙarshe muka kwanta kowa zuciya da ɗaci... Washegari bani da jarabawa yasa na shirya nake neman aiki daga restaurant zuwa restaurants harda hotels duk na gaji amma da yake ina tafiya ina ɗan imajinashon ɗin haɗuwa da saurayi kamar yanda yake faruwa a novel naji gajiyar bata wani durƙusar Dani ba...sai wurin ƙarfe biyar da rabi na koma gida a gajiye babu Sa'a Mama tace '' da kin bar neman aikin nan..wata rana kina zaune zaman ki aiki zai zo ya same ki...'' jinta kawai nayi badan na yarda da abinda ta faɗa ba

'' yaushe ne azumi?" Na canja topic '' nan da kwana takwas..'' zaro ido nayi ashe har azumin ya ƙarato kusa kusa haka...

Na sauke ajiyar zuciya...rayuwa ta cigaba da shillawa yau da farin ciki gobe da baƙin ciki...har yau ya rage azumi saura kwana biyu kacal...kuma yau muka gama jarabawar mock...sunce zasu bamu sakamako idan an dawo daga hutun azumi amma muyi karatu sosai dan cikin wannan hutun kalandar mu ta rubuta jarabawa zata fito...

Bayan an watse daga assembly muka koma aji ana hirar ƙarshe dan wasu ba zasu dawo ba...wasu yan aiki ne kuma uwayen gidan su bazasu biya musu ba...wasu kuma aure xasuyi wasu basu da halin biya...muma mun faɗa cikin jerin wa'yanda basu da halin biya...Amma ni Abeedahtu baxan bari mu rasa wannan damar ta mallakar satifiket ba... zanyi iya ƙoƙarina dan ganin na samo kuɗin nan...

Da ƙarfe sha biyu aka gargaɗa mu akan mu tafi gida makaranta ta rufe sai bayan azumi...mukayi bankwana da ƙawayen mu

anan Jay d take gaya mana ashe banan ƙasar zasu yi azumi ba..umra zasu...a karo na farko naji ina ma ace nice ita...'' Allah ya dawo daku lafiya...'' na rungume ta..itama Diyaam tazo ta rungume mu...tace '' ki kawo min yashin Madina....''

'' ke dalla yan Najeriya ke kiranshi yashin Madina..babu wani yashin madina da ake sayarwa....'' inji Anaam,ta murguÉ—a min baki...Jay d tayi dariya

'' kada ki damu zan kawo maki tsaraba...''

Daga nan muka rabu ta shige motar su mu kuma muka kama hanyar gida...

Wasu yara su uku muka samu suna jiran Asma'u sunzo kitso da lalle...ajiye Jakarta tayi ya canja kaya zuwa wani tsohon zane da riga tazo ta zauna ta fara da ƙaramar nima wanka nayi ma canja kaya..na shiga kitchen abincin da yarage jiya tuwon masara miyar kuka badan naso ba na zuba ma kaina naci...bayan na gama na fita farautar aiki...yauma kamar kullum ba nasara..wai ni kodai wani ya jefe nine?

Tsaki naja takaici na cika zuciya ta na dawo gida....Washe gari ban wahalar da kaina ba nayi zaune na gida...da yamma kuma dukan mu muka shiga gyaran gida saboda gobe azumi...

Kowa na murna banda Anaam saboda za'a katse mata jin daÉ—i a nata cewar....unguwar duka babu abinda kowa ke magana akai sai azumi...

Washegari aka tashi da azumi...Anaam ta dinga ɗirkar abinci kamar hakan zai sa kada taji yunwa sai gashi tun kafin a kai ko ina tayi lamo...daga lokaci zuwa lokaci take shiga baye ta jiƙo kanta da ruwan sanyi... nima dai yunwar bata yimin da daɗi ba wallahi naji kamar an yashe min ciki kamar banci komai ba...magana ma daƙyar nake yi.. Asma'u tana ta mana dariya..ita kamar ba azumi take ba sai nan da can take kazar kazar abunta...

Da aka sha ruwa cup É—aya na ruwan sanyi Anaam ta shanye tana sauke ajiyar zuciya nidai ruwan zafi na fara sha... muka yima juna Barka da shan ruwa...bakin Anaam ya buÉ—e choin choin choin...

Bayan mun gama buÉ—a baki mukayi sallah anan saman baranda lokacin Isha'i muka wuce masallaci wurin sallar alkareji (taraweeh) masallacin ya cika sosai...

Wuri muka samu muka tsaya...bayan sallar isha'i, round guda kaɗai akayi nida Anaam muka ɓuge da bacci dan mu muka fi kowa cika ciki sanda aka sha ruwa...

'' Malamai sai ku tashi mu tafi ko?" Asma'u ta faÉ—a bayan taga ma jibgar mu wai ita tashe mu take..Anaam kamar zata kama da wuta...barinta wurin Asma'u tayi ta fice daga masallacin...

Da muka isa gida,su mama na zaune saman baranda ga bandir ɗin kuɗi gaban su...ƙarasowa mukayi bayan munyi sallama sun amsa '' mama daga ina wa'yannan kuɗin?" Na tambaye ina jawo bokitin da aka jiƙa jolly juice ciki Anaam ta zauna gefe na muna sha tare... '' Jadeedahtu ce ta kawo...tace sauri suke zasu tafi airport jirgin su zai tashi..shine ta biyo kuyi bankwana...'' tiyarar da nake sha naji ta fitar min arai na ture gefe '' da yake ba rabon ku haɗu..ke kina masallaci lokacin kuma baku daɗe da fita ba...'' inji inna sarai... kawai na jinjina kaina Ina jin ba daɗi...
Chapter 44 · 0% Book details