← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 67

Sashe 16

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin dake fuskar shi ya ɓace ganin yanda idona sukayi jawur, yamutse fuska yayi kafin cike da damuwa yace '' Are You okay?" jina yi tambayar taban haushi na ɗago da jajayen idona a ɗan tsiwace nace '' nayi maka kama da wacce ke lafiya?" ƙiftawa yayi sau dayawa sai kuma a sanyaye yace ''yi haƙuri.. faɗa min Meya faru?" share idona nayi batareda na kalleshi ba nace '' babu komai... kawai ina...babu komai!" na faɗa a dake gyaɗa kanshi yayi yana kallona da idon nan nashi dake sani ina rasa natsuwa ta... ban san yanda zan fasalta ba amma wani irin kallo yake bina dashi wanda nake ji har cikin ƙasusuwana... turo baki nayi inaja baya nace '' wai kai baka gajiya da kallo? bafa nasan kallo!''

yar ƙaramar dariya yayi yace '' ni kam ina son kallon ki ABEEDAH...'' ya kira sunana da wani irin salo da yasa na kalleshi da idona da sukayi ja ƙwayar idona ya ƙara zama dark ash colored...murnushin shi ya ƙara faɗi har ina ganin haƙoran shi..samun kaina nayi dajin kunya na juya da sauri nabar wurin

'' Bamu gama magana ba kitten!" ya faÉ—a yana É—aga murya banma jishi ba nikam...

Shafa fuskarshi yayi..
'' My little kitten..🐈" ya furta kafin ya juya yabar wurin yana tafiya a nutse....

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

9. ... Babban darasi...🖊️

tsaye nake a tsakiyar gida ina mayarda numfashi idona cikin na Mama data gama alwala, nayi ƙasa da nawa '' daga ina kike?" ta tambaya tana miƙa min butar '' gulbi '' na amsa mata ina wasa da hijabina

Asma'u ce ta fito da tabarma ta shimfiÉ—a ta kabbarta sallah,duk da kamar akwai Magana bakin Mama batace komai ba... ta wuce É—aki ta É—auko hijabi tazo ta kabbarta sallah

kitchen na shiga na É—ebo gari na zauna nasha bayan sun gama sallah sunyi azkar,kiran mu Mama tayi ta zaunar damu tana mana nasiha me ratsa zukata,sosai nasihar ta tashige ni kuma zanyi amfani da ita insha Allah...

washegari koda muka isa makaranta munyi latti hakan yasa aka yi mana bulala biyar biyar, muka wuce aji kuma nida Asma'u bamuyi magana ba

Jadeedah ta lura da yanayi na lokacin break ta matsa min da tambaya babu yanda na iya dole na faɗa mata abinda Asma'u ta faɗa min plus ankoreni daga aiki sannan abincin mu ya ƙare, tayi mamaki sosai da komai dana faɗa,jakarta ta jawo ta ciro kuɗi kusan dubu biyar ta bani amma ni Abeedatu bana son yama kalmar

🍁🍁: Favours
bana son favours gani nake kamar daga baya mutum zai min gori akan hakan

'' rance nake baki idan kin samu sai ki biyani!" tayi saurin faɗa dan tasan tsaf zanƙi amsa... kallon kuɗin nake ina saƙe saƙe a raina,hannu na ta jawo ta tura min kuɗin '' Idan ban taimake ki ba bansan wazan taimaka ba Bee me yasa har yanzu kin kasa sakin jikin ki dani ne?" girgiza kaina nayi amma nakasa cewa komai,daga ƙarshe sai canja topic nayi '' Spelling bee nake so zan shiga Jay!" riƙo hannu na tayi cike da murna kamar ita zata shiga muka doshi office ɗin'' baki san irin farin cikin da nayi da jin haka ba,awwn,Bee ta fara girma!" Ta ƙarashe tana dariya,wani irin kallon na watsa mata '' da ban girma ba?" ɗan waro idonta tayi sai tace

'' a'a ba irin wannan girman ba,kin kuwa fahimci cewa wannan shine karo na farko da kikayi initiating babban abu irin wannan? Oh my God Bee kin fara yarda da kanki!"

ta juyo tana jijjiga kafaɗuna fararen haƙoranta a waje,ɗauke idona nayi daga kallonta..ni ban kawo duk wannan a rai ba da gaskiyar ta fa.. murmushi ne ya wanzu a fuskata kafin kuma na fashe da dariya tana taya ni naji wani irin farin ciki ya mamaye zuciya ta..da gaskiyar Jay D

'' you know what?" Sai ta matso kusa tare da riƙon hannu na '' I'm proud of you...ina nufin ina alfahari dake!"

Tayi saurin yimin bayani ganin ina harararta, sai kuma ta rungume ni..da sauri naja baya ina ɗan ƙaramin tsuki

'' such a buzz kill!" ta furta fuska a haÉ—e...ganin kamar bata ji daÉ—i ba yasa nayi dariya mai sauti sannan na matso na rungume ta

'' ni ina abinda yafi alfahari dake!" ina jin sautin ƙirjinta a nawa tsabar yanda take tayani farin ciki...

muka nufi office É—in event master,

saida malamin yayi min kallon sama da ƙasa ya taɓe baki kafin ya tambaye ni sunana bayan yayi min registering ya bani wata farar paper Godiya Jay tayi mashi nidai bance komai ba saboda yanda yake min wannan banzan kallon sai naji farin cikina ya ɗan ragu '' come on,kada ki bari ya ɓata maki rai..'' sai tayi ƙasa da murya ta raɗa min a kunne

'' nan gaba zance ya kalli madubi kafin yayi fuskarshi haka,kin kuwa ga yanda yayi kama da birin da aka shafawa lip stick da eye shadow a É—uwawu? Harda yar powder nan ta jarirai ma!"

Kafin in iya hana kaina na fara ɓaɓɓakar dariya...samun Jay d kusa dani babban magani ne

lokacin da aka koma aji wasu mutane..yan mata dai kamar likitoci suka sa aka taro masu yan matan ss3 dukan mu,suka zaunar damu aji É—aya suna mana Magana akan menturechon

🍁🍁: Menstruation!

Ke Oti ɗin nan kin cika iyayi 🙄🙄

🍁🍁: Autumn

koma menene, ,yan da zamu kula da kan mu lokacin jinin haila,yan mata da yawa sunji kunya akan wannan topic ɗin,amma nidai na ƙaru..daga baya suka bamu audugar mata..ni nama manta da sunan masana'antar tasu abu me muhimmanci shine nasamu pad dama wanda nake amfani dashi ya kusa ƙarewa

idona ne ya haɗu dana wani malami shima dai danginsu macijin sari ka noƙe..ɗauke idona nayi suka sauka akan Macijin sari ka noken shima kallo na yake..mamaki nayi wannan ai abinda ya shafi mata ne to me maza sukeyi a wurin? tsuki naja Batareda nasan danayi hakan ba..duk aka wani juyo ana kallo na fuskewa nayi kamar bansan ni ake kallo ba...

bayan an kammala wannan bayane bayanen muka koma aji,kowa sai maganganu suke

'' wai a canja pad duk bayan awa huÉ—u hauka ake?" Muhsina ta faÉ—a, A'ishah ta taya ta faÉ—in

'' sun raina ma kansu wayo kuɗin haƙo su ake ko kyauta zasu bamu?"

'' hmm..Ni wallahi idan nasa wannan abu wuni nake dashi ina naga kuɗin canjawa duk bayan awa huɗu?" Hafsa ta ƙara

'' ku gara kuma kuna da kuÉ—in siya,nidai idan ba kyauta aka bamu ba saidai inyi amfani da tsumma ato '' inji Labeebah

'' Amma dai kunsan kasancewa da wannan abun a jiki na tsawon lokaci yana da illa ko?"
'' pftt!! To illa ta nawa kuma? ai saidai ɗan baƙari!" muhsina taba Fateema amsa nida Jay D muka bisu da ido bamu ce komai ba

ana tashi daga makaranta motar su jay d tazo ɗaukar ta,duk yanda tayi in shigo su rage min hanya naƙi dole ta barni
.shagon su Saleh na tafi har yanzu baiji sauƙi ba dan haka bai dawo duty ba
.shinkafa tiya huÉ—u na auno mana na haÉ—a da wake da taliya sai kuma garin kwaki duk da yanda bana sonshi amma yana iya? Daga nan na haÉ—o da magunguna da kuma kayan miya sannan na bar wurin raina a sake..kuma har yanzu Ban biya buba mai kayan masarufi kuÉ—inshi ba

da Mama ta tambaye ni inda na samu kuɗin ban ɓoye mata ba..gyaɗa kanta tayi fuska ba walwala.. Asma'u tayi mana shinkafa dafe duka da wake ta kumayi mugun daɗi

bayan mun gama cin abincin wanka nayi na shirya cikin kayan aiki na nayi masu sallama na fita... zuciya ta cike da nauyi na fara zageye zagayen gari ina neman aiki ido rufe amma har lokacin tashi daga aiki na yayi ban samu ba

kusan kullum haka nake abun ya zame min jiki harna ma manta da wata rana za'a iya kamani..a ɗayan ɓangeren kuma ina nan ina koyon wannan mugun spelling Bee ɗin,a gida Mama ke koya min dan dama tayi daga primary zuwa secondary a makaranta Jay D, Asma'u bata da aikin yi sai gwale ni amma bana bi takanta.. oh itama ashe harda ita cikin masu yin spelling bee ɗin...

Jay D dai Saida ta ƙara nanata min cewa Asma'u kishi take dani amma har lokacin banyarda ba kuma bazan taɓa yarda ba..duk bata da wani uzuri nayimin abin da take min

lokacin da wata ya ƙare Mama nata zuba ido inkawo albashi sai nuƙu nuƙu nake..turnuƙe ni tayi akan saina faɗa mata gaskiya,cikin hawaye na sanar da ita an kore ni aiki

bata ji daɗin ɓoye matan da nayi ba... Daga nan itama ta shiga neman aiki haka ma Asma'u na tsawon lokaci babu wanda yazo neman kitso da lalle wurinta...

gaba ɗaya sai abubuwan ƙunci suka ƙara yimin yawa, Mama na matuƙar ban tausayi ina kuma baƙin cikin ganin ta tana yawo gida gida neman aiki ban ƙarajin cewa niɗin mara amfani bace sai da na farko da daddare naji Mama na kuka saman sallaya tana koro addu'oi... ji nayi wani sabon ƙunci da baƙin ciki sun mamaye ni dama na lura kwanakin nan kamar ƙasan idonta yayi duhu sannan idonta sunyi ja,na ɗauka rashin baccine ashe ba haka ba...

da safe ma da muka tashi ɗan abincin dana kawo ya ƙare babu komai har gari, muka koma talakawa talaf talaf kullum sai Mama ta bamu haƙuri akan gazawarta amma ni a ganina nice na gaza... da wannan dalilin ɗan iska Macijin sari ka noƙe yayi ƙoƙarin lalata Asma'u da alƙawarin zai biyata Alhamdulillah kafin yayi mata illa na ganoshi har office ɗin principal nakai ƙarar shi duk da nasan ba wani abu za'a yi ba dan baban shi ƙaramin ƙwaro ne a gomnati...
Chapter 16 · 0% Book details