← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 67

Sashe 28

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna nan zaune muna kallo har ƙarfe biyar sai lokacin na fara shirya kayana Mama ta kira Ni ɗakin ta tayi min nasiha kamar garin zan bari duka bazan dawo ba Maman mu kenan Da ƙarfe shida da rabi direba yazo ɗaukar mu,Mama harda yan kayan miya kamar su daddawa da su tafarnuwa su masoro ta bani in kaiwa maman su Jay D sosai Jay D tayi godiya Asma'u da Mama suka rako mu har bakin ƙofa, Asma'u kamar zatayi kuka Nima haka kamar bazamu sake haɗuwa ba

'' sai Monday Mama!" Jay D tayi musu bye ta riƙo hannu na sai juyawa nake ina kallon su mama tana murmushi take mana bye Asma'u ta wuce ciki da gudu

buɗe min ƙofa tayi na shiga,direba ya buɗe mata buut tasa kaya na sannan itama ta shiga tana cigaba dayi musu bye bye har muka bar wurin...

Cikin mota inata sharar hawaye..itakam sai murmushi take...tafiyar minti arba'in muka kawo gidan su duk da dare ne bakina ya kasa rufuwa,idan na kalli makeken gidan dake gabana sai in kalli Jay D..ban taɓa tsammanin a irin wannan wurin take zama ba,na ɗauka ƙananan masu kuɗi ne ashe ashe Rufe min bakina tayi ganin yanda yake wangale

Bayan ya paka gaban gidan muka fito na kalli ƙasan da tayis (tiles) ne malale a ƙasa A tsakiyar gidan ga shuke shuke nan ƙanana a gaban ƙofar kuma (entrance) fulawowine daga gefe da gefe da yar ƙaramar hanya a tsakiya sannan gidan sama da ƙasa ne sai wani ɗan ƙaramin gida a sama

🍁:attic

Yauwa atika

🍁: ba Atika ba Attic

'' koma meye...ai dai sun gane '' ƙofar shigar ma glass ne haka tagogi ƙofar glass ne dasu...sai wata kujera mai tsananin laushi, tsakiyar gidan yanada faɗi sosai kuma haske ta ko ina kamar rana ...lallausan hannunta naji a nawa

'' mu tafi!" Ta riƙo hannu na,na kasa warkewa tura ƙofar tayi muka shiga da sallama daddaɗan ƙamshin abinci haɗe dana turare ya fara dukan hancin na haɗe da sassanyan A'c... Ma sha Allah na furta cikin raina dan ba ƙaramin haɗuwa gidan yayi ba...

Ban taɓa ganin gidan da yayi min kyau ba irin nasu Jay D

Har saman lallausar kujerar suta zaunar dani '' ina zuwa '' ta faɗa sannan ta haye sama da jakar kayana,na cigaba da kalle kalle kafin na mayarda kallona a TV'n ina kallon cartoons ɗin da ake nunawa MSA naji tafiyar su akan stes ɗin da sauri na miƙe tsaye

Ganin maman su Jadeedah saye da baƙin hijabi har ƙasa Jadeedah maƙale a gefenta kamar wasu ƙawaye sosai suke kama duk da haka naji tayi min kwarjini ina wasa da ƙarshen hijabina zuciya tana bugu da ƙarfi..naji labari kuma na kalla a TV yanda maman su masu kuɗi ke cin mutuncin talaka kafin su koreshi..idan fa nima

'' lale lale..barka da zuwan babbar ƙawar mu Abeedah...'' naɗan zaro ido jin abinda ta faɗa har suka ƙaraso inda nake nikam nayi tsaye baki sagam dan banyi tsammanin haka ba naji saukar hannun ta akan kafaɗa ta da sauri nakai ƙasa ina gaishe ta da fara'a ta amsa min..tana kallo na sosai

'' Ma sha Allah.. kyakkyawa ''

ta furta hakan ya ƙara ban mamaki sai nayi ƙasa da kaina ina murmushi kuma naji daɗin yabon da tayi min duk da nan da anjima kaɗan Zan koma gayawa kaina akasin hakan.. Jay D tana ta murmushi

Zama mamansu tayi ta nuna min gefenta in zauna naɗan kalli Jay D data zauna ɗayan gefen sai nima na zauna ina cigaba da wasa da hijabina '' meyasa tuntuni baki zoba? Kusan kullum sai Jiddah ta bani labarin ki...'' na ɗan saci kallon Jay D data wani langaɓar da kanta gefe tana kallo

'' ban saba yin nesa dasu Mama ba!" dajin amsa ta sai tayi dariya

'' yar Mama kenan..'' nayi murmushi kawai ban ce komai ba

'' Jidderh ai tace saboda ba kya son masu kÉ—ine!" kallon Jay d nayi ta É—auke kanta gefe,sai na dawo da idona kan Mamar su

nayi ƙasa da kaina '' haka ne,amma duk wani ra'ayina game da su, Jadeedah ta canja shi koda ba duka ba..ita ɗin ta daban ce!bana son cin mutunci" Maman su take kallona har lokacin murmushin ta bai gushe ba

'' No wonder jidderh ta laƙe maki, turned out she found a gem!"

Nidai ban fahimci abinda ta faÉ—a ba nadai ga Jay d tana dariya kafin tace '' dan ma baku zauna tare bane,ina faÉ—a maki ba zaki so ku rabu ba!"

nayi ƙasa da kaina ina sauraren su yanda take ta zuzuta ni a gaban maman su yasa na shiga tambayar kaina idan da gaske hakan nake kodai dan ni ƙawarta ce take faɗan hakan....

Can dai muka miƙe muka nufi dining abinci kala da iri harda na turawa duk na kasa sakin jiki duk da yanda mamansu take jana da hira abincin ma sama sama nake ci mamansu tace '' duk wannan abincin danke nefa kici iya cinki!"naɗan zaro ido dan ni?

na gyaɗa kaina ina cigaba da cin abincin can Jay D ta tafi inda na zauna ta ɗauko sakon Mama ta miƙa ma mamansu..nayi mamakin farin cikin dana gani a fuskar ta akan ɗan wannan abun tana ta godiya...

Daga nan ta tashi tabar wurin ya rage daga Ni sai Jay D '' kici abincin danke aka dafa fa'' ta sake maimata min kafin ta dinga jawo abincin kala kala tana zuba min..yanzu da babu mamansu a wajen na saki jiki ina ci kuma nafi jin daɗin abincin yanzu cewar dan ni aka dafa duk wannan yasa na ji kamar ni ta musamman ce... Abinda yayi saura na daga abincin muka kwashe muka kai kitchen nan ma abun kallo bai ƙare ba Muka saka abincin cikin fridge bayan mun kwashe shi a wani roba daban sannan mukayi wanke wanke

Bayan mun gama tajani zuwa ɗakin ta mai kyau shima babu wani tarkace da yawa ƙasa kapet pitch da ash color ne gadon shimfiɗe da bedsheet fari pillow baƙaƙe da pitch sai wani ɗan ƙaramin table da aka saka ma pitch ɗin ƙyallen tebr shima pitch mai laushi daga gaban gadon..daga bayan gadon akwai taga da labulaye pitch da aka raba gefe da gefe sai madubi da kujerar gaban madubi da wardrobe harda wata yar shuka a gaban madubin...duk wannan a gefen hagu ne...a gefen dama wata farar ƙofar da zan iya cewa baye ne...da kuma madubi dogo har ƙasa.... sai wardrobe mai tsawo da faɗi... Ga A'c dake kunne...sai irin lantarkin nan da ake ajewa gefen gado.. nata popl (purple bed side lamp)

Ta rufe ƙofar nidai na zama kamar bani ba duk na rasa ƙwarin jiki na ganina a haka yasa tace'' zo muyi salla muyi wanka mu kwanta '' na yarda da abinda ta faɗa dan har wani bacci nake ji bayan mun gama sallah ta haɗa min ruwa cikin wannan abin na masu kuɗi

🍁:Bath tub

Da na shiga nayi mamakin ganin shi battob (bath tub) ɗin da kuma wani wuri da yake a sakaye da glass sai akwai wani irin shaya a sama...da tsakiya da kuma ƙasa...na saman yana zuba kamar rariya zai jiƙe mutum daga sama har ƙasa...na tsakiya kuma yana fisa ma mutum ruwa daga ƙirji zuwa ƙasan ciki...na ƙasa kuma daga ƙasan ciki zuwa ƙafafu....

Taɓe baki nayi kafin na cire doguwar rigar jikina ina juyo wa naci karo da madubi ya nuna min kaina daga sama har ƙasa zuciya ta tafara nauyi kafin idona suka fara ƙaiƙayi da sauri na ɗauke kallona na shiga cikin ruwan data haɗa min masu daddaɗan ƙamshi da ƙyar na gama wankan batare da bacci ya ɗauke ni ba saboda daɗin ruwan...

Wani farin towel na É—aura na fito babu kowa a É—akin sai kayan bacci riga da wando masu hoton zaki da na gani saman gado da kuma paper an rubuta '' kisa wannan" ajiye paper nayi na É—auki kayan ina dubawa kafin nasa ina tajan rigar daga gaba

Na kalli ƙwayar idona da ash ɗin yayi duhu farin ciki yayi ja irin idan mutum yayi kuka Jay D ta shigo da irin kayan dake jikina tana dariya tace

'' kinyi kyau fa ''

ɗauke idona nayi daga kallonta kayan sun mata kyau suna ƙara nuna abinda bani dashi

'' zaki shafa mai?''

'' da daddaren nan?"

pink É—in robar mai dake gaban madubin ta jawo mu biyun muna shafawa

'' naga baki saki jiki ba...ko baki son gidan mu?" Da sauri na girgiza kai

'' ba haka bane kawai ina kewar su mama ne kuma wannan shine karo na farko dana taɓa yin nesa dasu shine yasa ''

na bata amsar da rabi gaskiya ne rabi kuma saboda kaina ne

'' zaki saba ai shine yasa nake cewa kizo gidan mu da yanzu kin saba..abincin yayi daÉ—i?"

'' yayi daɗi sosai...har naji ina kewar abincin daban ciba,idan na koma gida duk sanda zan tuna wannan lokacin sai na ranƙwashi kaina '' mukayi dariya naji raina ya ɗan saki...

Barin gaban madubin tayi ni kuma na cigaba da shafa man..kafin na faÉ—a duniyar tunani

'' it's not daÉ—in baki...''

Sai na saki dariya tuna yanda Khalil ya faÉ—i hakan'' kina ta blushing lafiyar ki kuwa ko saurayi kikayi?" Jay D ta tambaya ta baro saman gado tazo ta tsaya kusa dani da kallon tuhuma dariya na sake yi kafin nabar wurin na wuce saman gadonta na juya gefe É—aya kashe wutar tayi take wannan popl É—in lantarkin ya kawo ta hauro saman gadon

'' faÉ—a min waye shi?" Ta tambaya da zolaya rufe fuska ta nayi da hannu na'' ba saurayi na bane bafa!"

Sai na juya ina kallon ceiling itama ta kwanta a irin haka...'' sunan shi Ibrahim..amma nidai ina kiranshi Khalil '' ta zaburo ta juyo tareda tallafo fuskarta da hannayenta '' dan Allah..faÉ—a min yana da kyau? Ina kuka haÉ—u?"

'' yana da kyau mana, sosai ma....''.nan na bata labarin yanda muka haÉ—u da Khalil da komai ma

'' bari mu fara neman anko'' ta faÉ—a tana min cakulkuli....ina ta dariya '' sai kunyi soyayya kuma da alamu ke zaki fara kamuwa!" Tayi maganar da kwantawa gefe na tana haki sai dana ja dogon numfashi sannan nace
Chapter 28 · 0% Book details