Sashe 56
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'' ka kuwa san abinda ake nufi da hakan?" Na kalli Arman da yayi maganar ido cikin ido...kusan pausing sukayi da abincin dake gaban su
'' tsiya ba shine kasancewar mutum talaka ba,tsiya shine rashin wadatar zuci...rashin sanin darajar ɗan Adam! Dan kawai Allah ya baku kuɗi mu kuma ya ajiye mu a ƙarƙashin ku,ba finmu kuka yiba! Ba kuma dabarar kubace ta sa ya baku!''
'' wannan yarinyar ta cika shegen ji da kai da girman kai! Wai meyasa baza'a kore taba?" Hajiya Momma ta faÉ—a
Mufeedah tace'' yarinyar da alamu mayyace ta cinye mu ta lashe shine yasa!"
Ranar dai nasha faɗa da ɓacin rai nabar gidan bayan na haɗu da Madam Amina ta tura ni makaranta da wani daga cikin ma'aikatan gidan don a biya kuɗin makarantar mu...da alamu na samu advance payment ...
Bayan mun isa makaranta mutumin ya biya kuÉ—in aka bani receipt guda uku,nawa, Asma'u da Anaam...nayi farin ciki sosai
Nayi mashi godiya da muka fito filin makarantar kuÉ—i ya ciro daga aljihun yace idan an tashi in hawo abin hawa in dawo gida sannan ya tafi....
Makarantar na kalla hakukuwa da ciyayi sun girma sunyi tsawo... ganyayyakin bishiyoyi sun bushe sun faÉ—o...
Murmushi nayi na isa wurin ƙaraurawa na buga ina dariya... mutane tsirara ne a makarantar ajin mu na wuce ba kowa...
Zama nayi bakin taga bada daɗewa ba mutane suka taru....muka zauna muna hirar yaushe gamo kafin assembly prefect ta buga ƙaraurawa muka taru a assembly ground...inata kallon inda zan gasu Asma'u...kuma yan SS 3 ne kawai hutun su ya ƙare...
Muhimman abubuwan daya kamata mu sani suka faÉ—a mana kafin suka samu kwasar desk daga office É—in principal zuwa ajujuwan da zamu zana jarabawa ciki...
Wurin ƙarfe goma duk yanayi na ya canja na fidda rai daga zuwan su Asma'u naji an rufe min ido daga baya...kafin in juyo ƙamshinta ya sanar dani wacece...Jay D
Juyowa nayi tareda sakin ihu na rungumeta...itama ta ƙanƙame ni....'' wayyo Allah na Jay D...''
'' Bee...'' ta kira da farin ciki..naji baƙin cikina ya ragu sosai...muka rabu muna kallon juna...naga ta ƙara min kyau...
'' Abeedah kin ga yanda kika ƙara kyau kikayi fresh kuwa?" Dariya nayi sosai '' ji wadda ke magana...''
'' da gaske nake...da muka dawo na tafi gidan baki nan...''
'' ina tsaraba ta?" Na miƙa hannu kamar na bata ajiya
'' banyi tsammanin zaki zoba sai gobe!"
'' Abeedatuwoooo!!!!!'' Anaam tayi tsalle ta haye ni...muka faɗi ƙasa Asma'u ta faɗo kan mu...Jay d ta tsaya daga gefe tana dariya...
'' wash zaki karye ni!" Anaam na dariya tace '' duk cikin murna ne...'' tashi mukayi
Muna kallon juna kafin muka sake rungumewa..naga duk sun canja suma sai faÉ—i suke na canja...
Ƙarƙashin bishiya muka zauna muna hira nake basu labarin wurin aiki na duk da ban faɗa masu wahalar dake ciki ba...na ɗauki receipt na miƙa masu....
Farin cikin dana gani a fuskar su yasa na ajiye a raina zan jure komai a gidan nan har sai mun kai tsayawa da kan mu...
Wasu daga cikin yan ajin mu suka ƙaraso ana hirar dasu cikin farin ciki da nishaɗi...
'' ina Diyaam?" Na tambaya amma babu wanda yasan wani abu game da ita
Lokacin tashi su Asma'u suka ce in biyo su mu tafi gida amma baxan iya ba saboda Madam Amina ta gargaÉ—e ni...
Badan mun soba muka rabu bayan Jay d tabani lambar ta...yau gani ina bin hanyar da mutane da yawa ke bi amma bana farin ciki saboda babu su Jay d...
Yau babu rana kun dai san yanda yanayi yake kasancewa idan rana bata fito ba kuma mutum na cikin baƙin ciki...nake ji kamar an ɗaura nauyin duniya a kafaɗa ta...da sauri nayi ƙoƙarin saita yanayi na...ranar ta kasance mai daɗi kuma zamu sake haɗuwa gobe...kada in bari rabuwar mu tasani a baƙin ciki ko?
Da wannan tunanin farin ciki ya dawo min nake tafiya a hankali ina lura da abubuwan da tafiyar mu ta farko ban lura dasu ba
Na ɗauka tafiya ƙasa mai sauƙi ne kuma zan isa gidan da wuri...da sauri na fahimci kuskure ne dan Saida na shafe awa biyu ina tafiya kafin na kawo ...
Na É—au lokaci ina kallon unguwar abinda ban samu damar yiba a karon farko...wurin nada kyau sosai... murmushi nayi sai kuma na fara tafiya da sauri na isa bakin gate...buÉ—e wa sukayi na shigo na gaishe da gayen dake wurin...sannan na wuce sashen mu
Ma'aikatan na samu suna magana akan yanda ɗaya daga cikin biyun ya ƙara kyau da komai...a gajiye nake yasa bayan na gaishe su na wuce ɗakin mu...Mama Asabe bata nan..Baye na shiga nayi wanka na sauya kaya zuwa uniforms Brown da suka dace da kalar fatata na fesa turare kaɗan nayi sallah..har xan kwanta na canja shawara...sabon hijabi na ɗauka ash na fita daga ɗakin... kitchen ɗin mu na shiga na zubo abinci waleeda da Aina'u suka zauna gefe na muna hira suke faɗa min sunga ɗaya daga cikin biyu ɗin,amma na biyun yanzu da yamma zai dawo...
Ina sauraren su har na gama muka wuce babban gidan tare...wurin Madam Amina na fara zuwa na gaisheta nayi mata godiya ta samin albarka
Kowa daga cikin mu ya kama aiki...plate aka cika da kayan ciye ciye aka bamu mukai ma yan gidan a Movie room dukan su suna can...
Ɗauka mukayi... muna ƙunƙuni akan hawan stairs... Aina'u take bamu labarin garin su yanda suke hawa bishiya da kuma wasannin da suke da tafiya rafi ɗibar ruwa wata rana wani Mutum ya biyo su suka saki tulukansu suka kwasa da gudu...
Muna dariya nida waleeda har muka iso movie room ɗin,mun ɗauka harda yan mata..mazan kawai muka iske suna kallon fim ɗin iskanci....a tare jikin mu ya ɗau rawa...mukayi tsaye daga bakin ƙofa babu wanda keda niyar matsawa cikin mu
'' anan zaku cigaba da tsayuwa ne?" Abdul Jalal yayi maganar da alamun jin haushi saurin suka bimu da kallon rashin ɗa'a...ƙarasawa mukayi a tsorace muka ajiye abubuwan dake hannun mu...da sauri muka fita daga wurin zuciyoyin mu na dukan tara tara musamman ni da nake jin idon Mukhtar akai na....
Bari na sukayi suka nufi 3rd floor Dan suna da aikin da suke a can suda sauran ma'aikata... kitchen na sake komawa...
Leonardo ya nuna min sabon faranti da aka cika da wani abu da turanci yace '' ana kiran shi da ðŸ¦ðŸ¦ shrimps..master yana son su shine yasa na dafa...ki É—auka ki kai Room no 207...'' yayi min bayani ganin kallon da nake bin abun dashi
''.ka tabbatar bazasu cije ni ba?" Na zaro ido dan gani nake kamar suna da rai...sauran masu girkin suka sa dariya Naeem yace '' baki ga an soya suba? Koke idan aka soya ki zaki iya motsi...''
Harara na jefa mashi nace'' ko zaka gwada ne?" Matso ni ya shiga yi yana wasa wuƙa...da sauri na figi farantin na tsere daga kitchen ina jiyo dariyar su...Nima murmushi nayi... wannan shine karo na farko da mukayi magana mai tsawo...
Stairs na fara hawa ƙafafuna suna tsananin ciwo saboda tafiyar da nayi a ƙasa...ƙwanƙwasa ƙofar nayi ina sauke ajiyar zuciya daga ƙarshe dai na kawo...
'' Come in..'' murya mai zurfi ta amsa daga ciki..tura ƙofar nayi da sallama na wuce parlorn zuwa ɗakin bacci... ɗakin da muka gyara ne ɗazu duk da ba haske saboda labulayen masu nauyi da aka saki ƙamshin turare da air freshener ne ke tashi...ganin wanda keda muryar nayi kwance saman gado ya rufe daga ƙugunshi zuwa ƙasa da bargo faffaɗan bayan shi a buɗe...gabana ya faɗi sai kuma naji haushin sa ya cika ni...
'' yallaɓai ga abincin ka!!"nayi maganar da takaici kamar in kife masa shrimps ɗin a jiki! da kasala ya nuna min table a gaban gadon yace
'' ajiye nan...'' ƙarasawa nayi na ajiye ya sake faɗin
''kwashe labulen''...na matsa zan kwashe labulen ya yunƙura ya tashi zaune,sai nayi pausing
Nabi bayanshi da kallo ƙatone sosai saye yake da baƙin jeans amma ba abinda ya dameni ba kenan..gani nayi ya nufi ƙofa...yawu na haɗiye garƙame ni zaiyi ne?
Zuciyata ta fara abinda ta saba...tsoro yasa na dena motsi...ban san me yayi ma ƙofar ba na dai ga ya taɓa handle sound ɗin rufewa da mukulli ya shiga kunne na... Innalillahi... ya juyo
Rufe idona nayi na kurma ihu kamar zan cire mashi dodon kunne...ganin yana tunkaro ni yasa na fashe da kuka ina roƙon shi akan ya rabu dani tsayawa yayi gabana yace '' what nonsense!" Ji nayi kamar muryar na taɓa jinta amma firgici ya hanani tantancewa... saukar tattausan hannun shi a nawa yasa a rikice na zare hannuna daga fuskata hawaye na sintiri kamar an buɗe pamfo zan fara roƙo...
Zaro ido nayi ganin Khalil tsaye gabana fuskarshi a É—aure... eventually mamaki ya bayyana a fuskar shi shima....
'' kitten?.."
+2349138091955
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta +2349138091955
Autumn writes 📖🖋ï¸
RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 ðŸðŸ
24. ...a massive jerk!...🖊ï¸
Faɗin mamakin dana shiga ɓata lokaci ne... never in my wildest dream nayi tsammanin ganin shi,hawaye na suka tsaya kamar anyi ruwa an ɗauke...share min hawaye na yake da damuwa a fuskar shi '' did I scare you?...''
Ture Hannunshi nayi daga fuskata wannan tambayar ta ƙara fusatani abu a zahiri yake tambaya?
Na tashi tsaye shima ya miƙe yana kallona da alamun tambaya a kyakkyawar fuskar sai naga kamar ya ƙara kyau fiye da lokaci na ƙarshe da muka haɗu...'' me kike yi anan?"
Hararar shi nayi da jajayen idona takaici na kamani...bai ga uniforms ɗin dake jikina bane? '' wasa nake ai ka gani!" nake ji kamar in kwaɗe shi yayi murmushi yana bina da kallon nan nashi da har yau ban san ma'anar shiba...zagaye shi nayi zan wuce ya riƙo hannu na ya rungume ni yana dariya...gwalalo ido nayi ƙirjina na gaba da baya... yace
'' toh muyi wasan tare!" mamaki ya hanani motsi ko ƙoƙarin ƙwatar kaina..muna tsaye aka turo ƙofa da sauri muka rabu..ko ya rabu dani cikin rashin gaskiya...naji kunya ta lulluɓe ni kumatuna suka ɗau zafi...