← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 67

Sashe 7

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nake ji araina kenan bani kaɗai bace mai wannan sef istim ɗin? ke nan low self esteem ɗin kesa ina kushe halitta ta kuma ina haɗa kaina da Asma'u,low self esteem kesa inason in cire pimples daga fuskata sannan in zama me kyau don a yabe Ni? badon hakan shine abunda nake so daga ƙasan zuciya taba!

tunani na ya katse lokacin da naji Malamar na faɗin '' nasan dayawa daga cikin ku abinda ke damun ku kenan,akwai abubuwa dayawa da zaku iya yi amma saboda kuna gudun kada a kushe ku ko kada ku faɗi sai ku ƙiyi...da yawa daga cikin ku kuna kallon kanku kamar munana ko idan jikin ku bai girma ba, dan baki da ƙaton ƙirji ko ƙaton ɗuwawu ko girman hips ko idan kina da wannan masu girma da suka girmi shekarunki sai ki dinga jin kunya.. kina gudun abinda mutane zasu ce...ya zama rayuwar ki gaba ɗaya ke burin ki ki burge mutane ko dai ki tsira daga maganganun su....idan har kina ji yanda kike bakya son kanki a haka,kina ji yanda mutane suke so ki kasance haka kema kike so ki kasance to kina da low self esteem!"

tayi shiru tana kallon mu kamar tana ƙoƙarin gano idan mun fahimce ta tacigaba da faɗin '' ku kalle Ni,ku kalli fuskata duk pimples, shekaruna ashirin da bakwai amma wasun ku sunfini girman ƙirji da ɗuwawu da hips.. kin gane ni idan ina tafiya ina nuƙu nuƙu?"

'' a'a'' muka bata amsa muna ƙara kallon ta da kyau yau nima naga wadda ta girme ni kuma take a shafe kamar ni hakan ba ƙaramin ɗaukaka sef istim ɗina yayi ba tacigaba da faɗin '' wasun ku suna tafiya suna nuƙu nuƙu cikin hijabi badan suna jin kunyar Allah ba sai dai saboda suna gudun maganganun mutane...ku dena kunyar yanda Allah ya halicce ku,kuso kanku yanda kuke... babu wata wacce tafi ki,you're beautiful a yanda kike bakya buƙatar saiwani ya faɗa maki... love your self! abinda wani yake tunani game dake ba damuwarki bane,abu me muhimmanci ya kika ɗauki kanki? kina da HIGH SELF ESTEEM OR LOW SELF ESTEEM shine kawai" ta ƙarashe maganar tana kwasar littafan ta

miƙewa nayi tsaye na fara mata tafi haka ma sauran yan aji suka bini juyowa tayi ta kalle mu tana murmushi muma muna dariya '' muna sonki sosai malam Hafsah '' muka faɗa kusan atare dariya tayi tana mana bye bye tace'' nima ina son ku '' sannan ta fita.....

+2349138091955
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta +2349138091955
Autumn writes 📖🖋

️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

4. ...laifina ne...🖋️

har aka tashi break ina tunanin abinda aka koyar da mu, shine karo na farko da akayi karatu naji na fahimta kuma naji abun ya taɓa zuciya ta,duk abinda ta faɗa ya shafe ni....sai dai taya zan zama mai high sef istim? abun yanada sauƙin faɗa amma aiwatarwar ne da wahala, nasan dacewa yanzu na rage nuƙu nuƙu cikin hijabi kamar yanda ta faɗa, amma har yanzu ina matuƙar jin kaina a takure musamman idan ina gaban maza

ranar ina wucewa ta filin ƙwallo,akwai mata da yawa da suka wuce kafin ni kuma ko wace mace idan ta wuce mazan dake wurin sai sun bita da kallo suna maganganun da basu dace ba...ina zuwa naji wani na faɗin '' wannan kamar sandar sluka (snooker)... idan mutum ya rungumeta ciwon ƙirji zata sashi!" abun ya bala'in yimin zafi kunya ta rufeni lokacin da suka kwashe da dariya naji kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiye ni,duk yanda naso in bashi martani kasawa nayi dole nabar wurin zuciya ta na tsananin zafi..

Numfashi na sauke ina kalle kalle, kwanakin nan Asma'u ta dena zuwa amsar kuɗin break ɗinta sai nata neman ta kafin inganta bayan da ba haka bane to Meya sauya? rashin amsa yasa na miƙe na fara neman ta na zagaye makarantar duka har bayan masallaci na tafi amma bangan ta ba

'' Habeeba kinga Asma'u?" na tambaye yar ajinsu '' tana wurin Macijin sari ka noƙe !" tabarni tsaye a wurin da tsananin faɗuwar gaba! meya kai ta wurin ɗan iskan nan dan Allah? bata yimin alƙawarin bazata sake zuwa wurin shiba? kodai ƙarya take basu rabu ba?

da wani irin sauri ƙafafuna suke tafiya har na shigo office ɗin shi,samun shi nayi tsaye dab da Asma'u dake maƙe da bango idonta sun fito tsabar tsoro hannun shi riƙe danata yana Magana cikin kashe murya '' I love you...kin san hakan kema bansan dalilin da yasa kike wahalar da zuciya ta ba ma'u...'' katse shi tayi a tsorace '' Abeeda tace...tace in dena...kulaka!" fushin dake cin shi ya danne yana ƙara matso ta kafin ya ɗaura hannunta a ƙirjinshi

ƙoƙarin cire hannun take daga jikin shi ya riƙe da ƙarfi yana mata wani ɗan iskan kallo yace '' kina kuwa jin yanda zuciya ta ke bugu saboda soyayyar ki ma'u?" ɗago idonta tayi tana kallon shi kafin da sauri tayi ƙasa da su ya cigaba da faɗin '' yayar nan taki burinta ta raba mu dan taga kin fita kyau da zubi bake kika faɗa min cewa babu wanda ya taɓa cewa yana sonta ba?" gyaɗa kai Asma'u tayi... nikuwa naji wani irin abu ya soki zuciya ta,kenan Asma'u...kafin in gama tunanin naji yana sake faɗin '' kuma kikace akoda yaushe sai ta haɗa kanta dake ba?" nan ma kai ta gyaɗa..naji ƙafafuna sunyi sanyi... wannan sirri nane kuma abinda ya shafi rayuwar mu taya zata faɗa masa wannan?

'' kishi take na faɗa miki baki so kiji idan mun rabu na tabbatar zata zo tace tana sona! kin san yan mata nawa kuwa keson mu'amala dani amma na zaɓe ki ma'u? ki saki jikin ki dani kinji!" yayi maganar yana ƙara jawo ta jikinshi duk da a tsorace take bata hanashi ba

hakan ya tabbatar min dacewa maganganun shi sunyi tasiri akan ta, idona suka É—au zafi cike da hawaye akan komai dana gani kuma naji

'' Tsohon É—an iska munafiki,dallah sake ta!" a wani irin firgice su biyun suka juyo suna kallona musamman ita, wani irin kallo nake binsu dashi su biyun amma dayake É—an iska ne sai Kallon ta yayi yana faÉ—in '' Babe kinga ni ko? na faÉ—a maki kishi take dake!"

'' Rufe ma mutane baki!!!" na daka mashi tsawa idona suka ƙara duhu..farin ciki ya rine, '' babu abinda ka iya sai lalata yaran mutane kawani riƙe ta a kwana kana cusa mata maganganu... wallahi tallahi idan har baka fita daga harkar Asma'u ba zan iya kashe ka nima daga baya a kashe ni!" zaro ido yayi yana kallona hannun shi dafe da bakin shi dan yagani a idona Abinda na faɗa ɗin da gaske nake...

'' Abeeda ki den...'' kafin ta gama faÉ—ar abinda zata faÉ—a na wanke fuskar ta da mari shock rubuce a fuskar ta take kallo na,ni kuma ina kallon ta cike da fushin cin amanar datayi min'' akan wannan É—an iskan zaki gaya min magana har kike kira na Abee..''hawaye na sauka a idonta a tsawace tace

'' eh! an kiraki Abeeda ba sunan ki bane? ina son shi shine yasa kika gan mu tare ki dena shiga rayuwa ta..da gaskiyar mutane kishi na kike kawai ba wani abu ba..so kike in rabu dashi don ke ki samu ki maƙale mashi kuma bazan rabu dashi ɗin ba!" ta fita daga office ɗin kamar zata tashi sama nabi bayanta da kallo...

dariyar macijin sari ka noƙe ce ta dawo dani daga shock ɗin da har yanzu Ban dena jin shiba

zagayowa yayi ya tsaya bayana ya ranƙwafo yana wani hura min iska a fuska '' huɗubata tayi aiki ko? yanzu zaki iya raba mu? ki sani sai na samu Abinda nake so daga ƙanwarki iya karki kallo don babu wani abinda zaki iya yi akai!" kasa cewa komai nayi tsabar yanda jiki na da zuciya ta suka min nauyi

tureshi nayi daga hanya ta na fita ina layi hawaye suka ciko idona..da gudu na ruga na ɓoye bayan masallaci ina risgar kuka duk dacewa an koma aji...yau Asma'u da bakinta ke irin wannan maganar? ashe dama ƙarya take da tace zata rabu dashi? Kuma dama itama tun tuni tana gani na a matsayin mai kishi da ita har take faɗar sirrika na mawani banza can? zuciya ta ta karye fiye da zaton mai karatu

har aka tashi short break ina kuka sai dai na canja wuri saboda masu zuwa wurin...sai lokacin Sallah na gama kukan idona sunyi luhu luhu sun ƙanƙance sunyi jawur.. alwala nayi na shiga Masallacin mukayi sallah

da aka gama ban koma class ba sai lokacin tashi naje na ɗauki jakata ban jira kowa ba nayi gaba abuna...wata doguwar hanyar danake bi a duk sanda rayuwa tayi min zafi ko nake buƙatar kaɗaici nabi ina tafiya ina tunani zuciya ta na ƙara ƙuna a duk sanda na tuna abinda Asma'u ta faɗa min '' laifi nane!" na faɗa da shaƙaƙƙar murya ina goge hawayen da suka silalo min...da ace na iya son kaina a yanda nake ..da ace inada ƙwarin guiwa..da ace na gode Allah yanda yayi ni..da babu wanda zai faɗi maganar da zata sosai raina...hawaye kamar ruwa suke kwaranya daga idona sai dai nake sa bayan hannu na ina sharewa

wurin ƙarfe uku da rabi nakai gida samunta nayi tsaye kusa da bishiyar mangoro tana jirana dan bazata iya shiga ita kaɗai ba... ina ƙarasowa ta miƙe muka cigaba da tafiya babu wanda yace uffan cikin mu har muka shiga ciki

Muka iske Mama tsakar gida riƙe da hijabi fuskar ta ɗauke da damuwanmu muka tsaya kallonta jin tsayuwar mutum yasa ta juyo ganin mune ta sauke ajiyar zuciya '' ina kuka ts..'' kafin ta gama magana na saki jakata na ruga na rungumeta tareda fashewa da kuka mai ƙarfi ''Maamaaaa!" zuciyata na ƙara karyewa hankalin Mama ya tashi sosai hakama Asma'u ɗago Ni daga jikinta tayi duk ta daburce baiwar Allah'' meya faru yar Mama faɗa min!" take share min hawaye na da suka kasa tsayawa... wani irin rauni da baƙin ciki ke ɗawainiya da zuciya ta...
Chapter 7 · 0% Book details