← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 67

Sashe 4

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin in ƙarasa, Asma'u ta fashe da dariya.

“Ke, tuwo! Amino acid ake cewa, ba Aminu acid ba!”

tsaki na ja kamar bakina zai katse,ganin yadda suka maidani abun dariya ya ƙara ba ni haushi.

“Ko uban me ake kiran shi! Shi Aminu acid ɗin yana sa gashi ya yi ƙarfi sannan yana haɓaka girman gashi!”

Na faɗa a harzuƙe...Mama ta kalle ni da murmushi.

“Ke da gashin ki yake nan kamar ƙirigi, har da comb kika karya mana tsabar yadda yake da tauri, shine kike neman wani ƙarfin gashi kuma?”

Na daure fuska.

“Idan gashin yayi tsawo zan sa masa relaxer! yayi kamar irin na indiyawa..”

Wata irin muguwar dariya Asma'u ta saki har da riƙe ciki.

“Waih! Sallar da ta wuce kin manta abin da relaxer ta yi miki kenan? Ta kwashe gashin ki kika koma kamar talle mai shayi! Black Indian!”

Miƙewa na yi na bi ta da gudu...itama bata jira niba ta ɓoye bayan Mama su biyun suna dariya...

“Ayi haƙuri Anty Tuwo!”

Niko sai huci nake kamar wata zakanya.

“cewa fa tayi ina kama da talle mai shayi!”

Mama ta É—aga gira.

“Toh, ko shine surukin namu?”

Wata irin ƙara na fasa, na faɗi ina birgima.

Su kuma suka cigaba da dariya.

Kafin daga ƙarshe Mama ta jawo ni jikinta.

Asma'u ma ta rungumeni ta baya.

Mama ta shafa bayana a hankali.

“Ina roƙon Allah Ya nuna min ranar da za ki karɓi kanki yadda Allah Ya yi ki, Abeedah. Ya nuna min mijin da za ku aura ku biyun nan. Kuma ya nuna min ranar da Tuwo za ta girma ta dena shagwaɓa...”

Ta faÉ—a cikin wani yanayi mai wuyar fassara.

Na ji Asma'u ta ce,

“Ameen.”

Ni kuwa na yi shiru.

Ban sani ba ko zan iya rayuwa wata rana ba tare da Mama da Asma'u ba.

Ina matuƙar son rayuwarmu yadda take.

Ba na son komai ya canja.

Bana son komai ya yi yawa.

Ko ya yi kaÉ—an.

Ina son komai ya kasance yadda yake.

A ganina, yawan abu yana sa mutum ya É—auki ni'ima a matsayin abin da ba komai ba, har ya kasa ganin albarkar da Allah Ya ba shi.

Amma idan abu bai yi yawa ba, sai mutum ya koyi tattali.

Ya koyi godiya.

Ya koyi ganin abin da yake da shi a matsayin ni'imar Allah.

“Tuwo, ba ki ce Ameen ba!”

Asma'u ta katse min tunani....

“Na ce a zuciyata munafuka.”

Na amsa ina jan gashinta.

Ta yi dariya.

“Kada ki ɓaɓɓake min gashi, ni dai!”

Mama ta girgiza kai.

“Ku ɗaga ni kada ku ƙarasa ni!”

Sakin gashin Asma'u na yi, na ƙara shigewa cikin jikin Mama na kwantar da kaina.

Asma'u ta tashi ta ɗauko ruwan shinkafar, ta miƙa wa Mama, sannan ta koma ta cigaba da aikinta.

Mama ta fara shafa min ruwan a gashina, tana yi min tausa a hankali.

Na lumshe idanuwana.

A wannan lokacin, zuciyata ta yi shiru.

Kuma a cikin wannan shiru, na yi wata addu'a.

Ba don ƙirji na ya girma ba.

Ba don pimples ɗina su ɓace ba.

Ba don gashina ya yi tsawo ba.

Sai don wata rana Allah Ya kawo min ranar da zan amshi kaina yanda nake.'..babu abinda yakai karɓar kanka a yanda kake daɗi

Ranar da zan kalli madubi ba tare da na tsani abin da nake gani ba.

Ranar da zan iya tafiya ba tare da hannuna ya riƙe hijabi saboda tsoron maganganun mutane ba.

Ranar da kalmomin mutane ba za su ƙara samun ikon karya ni ba.

Ranar da zan iya cewa:

“Wannan ni ce.”

“Kuma ban da abin da zan gyara domin in cancanci a so ni.”

Ban san cewa a wannan lokacin, ina addu'a ne ga wata rayuwar da ba zan taɓa iya hasashen yadda za ta zo ba.

Ban san cewa wata rana zan waiwayi wannan ƙaramar yarinyar da ke kwance a cinyar mahaifiyarta, ina kallon ruwan shinkafa yana jika gashinta, sannan in fahimci ainihin ma'anar kalmar da ban taɓa ɗaukar muhimmancinta ba.*

Be careful what you wish for.

Domin wani lokaci...

Allah yana amsa addu'arka.

Amma amsar ba koyaushe take zuwa cikin irin yanayin da ka zata ba.

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

2. ...a mafalkina...🖋️

'' Albishirin ki tuwo " Mama ta furta tare da dakatawa da shafa min ruwan shinkafa a kai tashi zaune nayi ina kallon ta kafin in kalli Asma'u dake riƙe dariyar ta hmm...ban yarda da su biyun ba amma sai nace ''goro'' ina kallon Mama cike da ƙoƙonto, basarwa tayi tace '' Yau tuwon masara za'ayi da daddare!" zaro ido nayi baki sake ina kallon ta kafin kuma fuska ta,ta sauya kamar wadda ruwan sama sukayi ma duka, juyowa nayi na kalli Asma'u ta tuntsire da dariya ji nayi kamar in haukace '' Mama wane irin tuwon masara kuma?" na furta baki na rawa,na tsani tuwon masara a rayuwa gara tuwon dawa sau dubu

tace '' tuwon masara dai da kika sani da miyar kuka!" dafe zuciya ta nayi kamar mai ciwon zuciya baƙin ciki na turnuƙe ni sosai fuuu na miƙe na shige ɗakin mu dake ɗauke da ledar da taga yaƙin duniya ta gode rabbi na kwanta saman gadon daya girme mu nida Asma'u ina risgar kuka,shekaran jiya da jiya duk wannan mugun abun mukaci shine kuma yanzu ma za'a dafa mana shi... share hawaye na nayi sai kuma na ƙara fashewa da kuka harda dukan gadon

'' kada ki sabauta mana gado Dan Allah '' inji Asma'u tana cigaba da ayyukan ta...
da daddare bayan sallar isha'i zaune muke cikin duhu kafin Mama ta shigo da fitila a hannun ta ɗayan hannun riƙe da plate ɗin tuwo, ajiyar zuciya na sauke lokacin da ta ajiye plate ɗin tsakiyar mu ta zauna hannu suka zura su biyu suna ci niko na zuba musu ido

'' bazaki ciba?" Inji Asma'u,Mama ta kalle ni, saida na harare plate ɗin sannan na zura hannu muka cigaba da ci kuma ba ƙarya abincin yayi daɗi sosai daga ƙarshe har da janye plate ɗin nayi na iyarda cinyewa na siɗe taɓe baki mama tayi '' ai na ɗauka da yunwa kike shirin kwana..dama kince cikin ki yayi ƙato...'' idona kamar zasu faɗi hakane fa!

bana so ciki na yayi ƙato wasu lokuta abincin ma bari nake saboda hakan, daidai nan aka kawo nepa da sauri na miƙe na isa gaban mirror dake maƙale da tsohuwar wardrobe ɗin mu daga gefe kuma ƙaramar TV

tun kafin in É—aga rigata naga yanda ciki na ya turo kamar me ciki, ihu na fasa Mama dai tayi zugum tana kallona kafin taja tsuki ta fita daga É—akin daidai Asma'u data tafi wanke hannu ta shigo

jawota nayi da ƙarfi na tsayar da ita gefe bata cemin komai ba sai ma tayani ɗaga rigarta da tayi fuska a tsuke... kallon cikinta nayi gashi nan a ɗame kamar bataci komai ba...waist ɗinta ɗan ƙarami hips ɗinta manya tsabar yanda waist ɗinta yake gani nake kamar idan mutum ya riƙe da ƙarfi karye wa zai yi

ƙwace rigarta tayi ta wuce ta kunna tv ta zauna bakin gado tana kallo,na kalli kai na a cikin madubi kamar wacce akayi ma albishir da mutuwa kife kaina nayi a saman table ɗin kwalliyar mu ina furta kalmar turancin dana fi sani '' why!" Ina kukan daba hawaye amma ciwon danake ji da gaske ne

ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tana faɗin '' dama zaki kalli kanki yanda nake kallon ki,ina son yanda kike komai naki tuwo toh ke meyasa ba zaki karɓi kanki ba?" Sharply na juyo ina kallon ta da wani expression a fuska ta '' sauƙin faɗa ne dashi saboda bake kike fuskantar abinda nake fuskanta ba sannan bake kike jin yanda nake ji ba!" nayi maganar ina hararar ta,taɓe baki tayi kafin ta zare ɗan kwalinta gashinta ya fara walwalewa ya zuba har tsakiyar bayanta wani kuma ya zubo ta gaba

sakin baki nayi ina kallon ta kafin na kalli nawa kan dake ɗauke da kitso all back '' why he!!!!" na sake furtawa ina dukan table ɗin bada ƙarfi ba '' why me ake cewa ba he ba,idan kika ce he kina nufin namiji kenan!"

É—ago idona na nayi ina hararar ta'' to kun alijabe turatu uwar turai '' (queen Elizabeth)

'' bafa kun alijabe ba elizabe...'' kafin ta iyar na ɗauki powder na jefe ta dashi ya same ta a goshi '' idan ina turanci kada ki ƙara gyara min!" shafa wurin dana jefeta tayi tare da faɗin '' mugunta dai ba kyau!" kafin ta mayar da hankali tana kallon Chinese drama ɗin da ake yi

nima zuwa nayi na zauna kusa da ita muna kallo tare idan aka nuno wata ko wani mai gashi inyita santi,riƙo hannu na tayi ta ɗaura saman gashin ta ta kwantar da kanta saman cinyata '' ɗan shafa min kaina kinji!" tayi maganar a sheɗanan ce, kamar in ture kanta amma saboda yanda nake son gashi na kasa cike da jin haushi na dinga jan gashin muna kallo tare

'' Tuwo xoki kwaso kayan da Asma'u ta shanya ruwa za'ayi!" Mama ta faÉ—a tana tattara kayan dake tsakar gida ta kai kitchen '' ga ninan tafe'' na bata amsa amma banida niyar tashi '' yaushe hadari ya taru? nasan yanzu zasuyi gaba da wutar su...'' Asma'u ta faÉ—a tana tashi daga jiki na,da takaici nace '' dan Allah kada kiyima mutane baki'' sannan na fita naje kwaso uniform

Muna shigowa cikin ɗakin aka fara ruwa da mugun ƙarfi tule ma Asma'u kayan nayi a jiki ina faɗin'' ki lunke'' fara ninke kayan tayi na zauna kusa da ita mama a gefe muna kallo bayan na banko murya saboda ƙarfin ruwan baya bari aji magana...dama kuma dai ba turanci nake ji ba kawai kyaun mutanen da yanda suke tashi da kuma kayansu da gashin suke burgeni
Chapter 4 · 0% Book details