← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 67

Sashe 17

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na ƙara shiga tashin hankali bayan na fahimci abinda Asma'u ke shirin yi kenan.. rayuwar mu ta wani irin ƙuntata musamman ni...damuwar su itace damuwa ta,farin cikin su shine nawa naga nawar ayi ayi wannan spelling bee ɗin in samu kuɗin da gidan in fitardamu daga wannan ƙangin rayuwar... wata rana aka tara mu ake faɗa mana anfasa spelling bee ɗin..ji nayi duniyata ta faɗo ta ruguje duhu ya sake mamaye ni..ɗan spelling bee ɗin dana ƙwallafa rai akai... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ranar nasha kuka kamar raina zai fita amma duk da haka ban dena karatun spelling bee ɗin ba sannan mu dukan mu bamu dena neman aiki ba

har na tsawon wata uku rayuwar mu ta cigaba da gudana cikin ciwon rashi..da ƙyar muke samu muna ci muna sha,ba sau guda ba ina kama Mama tana kuka hakan ba ƙaramin karya zuciya ta yake ba..kuma yakan ƙara tunamin dacewa na kasa sharema ƙanwata da mamata hawaye...gefe ɗaya kuma ga self esteem ɗina dake ƙara raunana ƙila ma ya ƙate tass yanzu dan kamar idon kowa ya dawo akaina ne ko a makaranta haka idan ana bada misali sai ayi dani,,,harda ji nayi wata me suna Saddiqa tana faɗin '' abuna kamar na ƙananan yara..ita ta kasa ganewa koni macece ko akasin hakan...'' kasa tsayawa nayi inji ta har ƙarshe dan kuka ne yaci ƙarfi na meyasa bazan iya jurewa ba in basar kamar ban damu ba? ko faɗa muke daga sanda aka zagi halitta ta shike nan an gama wannan faɗan sai kuka

da misalin ƙarfe huɗu ina zaune a ƙarƙashin bishiyar mangoron nan na kusa da gida saman benci.. hannu na riƙe da spelling bee ina karantawa saye da uniforms ɗina Dan banso in koma gida, jinginar da kaina nayi na jawo jakata ina duba pen dan inyi ticking kalmomin da ban iyaba,

na ɗauki pen ina maki har na gama mayarwa nayi na sake jinginar da kaina ina tunanin yauma haka zamu kwana ciki rabbana? ƙamshin turaren shi ne kamar kullum ya shiga hancina kafin naji zaman shi kusa dani idanun shi akaina..zuciya ta tashiga bugu da ƙarfi... wani irin zafi ya turnuƙe ni daga ciki har waje,na rasa dalilin dayasa nake jin haka a duk sanda yake kusa dani,ƙila saboda yana da kyau ne kuma ni ga yarda nake

'' Kitten...'' ya kira ƙasan maƙoshi,matse ƙafafuna nayi da idona kafin na shiga buɗe su ahankali ganin shi nayi zaune kusa dani dama kuma nasan yana kusa dani ɗin '' Meye kuma wani kichin can?" na tambaya gira ɗage

batareda ya dena kallona ba murmushin shi a faɗaɗe yace '' kitten..na nufin jinjirar mage...'' wani irin tashi zaune nayi da kyau ina hararar shi a ƙufule nace '' oh,wato ni kake haɗawa da mage ko? nayi maka kama da mage ne?" wani irin lumshe idanunsa yayi tareda tallafo gefe da gefen fuskarshi da hannayen shi
yana bina da kallon ƙasan ido da yasa zuciya ta neman fitowa ta baki yace '' Eh mana, musamman idanun ki... da yanda kike min tsiwa kullum idan mun haɗu..i like your eyes.. they're beautiful!"

Ƙifta idona nayi cike da jin haushi nace '' na faɗa maka ban jin turanci ka dena min turanci amma baka ji!" dariya kaɗan yayi sannan yace '' Allah ya gafarci ranki ya daɗe..bazan sake ba!" ɗauke kaina nayi daga kallon shi

'' Abeedah...'' ya kira irin yanayi da ban fahimta ba, juyowa nayi idona suka shiga cikin nashi a wani irin kasalance yace
'' ina son Idanun ki... suna da kyau sosai!"

Naji kamar shock ya ziyarci ilahirin gangar jikina,kamar yanda mutum zaiji idan ya taɓa wayar nepa...banan kaɗai ba harda wani wurin da bazan iya faɗa ba...'' a'udhu billahi '' na faɗa cikin raina ina ɗauke kaina daga kallonshi,wanda shi a wurin shi a bune me wuyar aiwatar wa dan dai ya cigaba da kallo na '' toh ko cirewa zanyi in baka?" Yana wani shu'umin murmushi ya jinginar da bayanshi ga bishiyar '' gashi ban zo da kayan aiki ba da mun gwada...'' sakin baki nayi da abinda ya faɗa...na ɗauke ido na daga kallon shi...

'' muzama ƙawaye mana!" ya sake furtawa a kasalance to ko bacci yake ji? Ko dai shegantaka ce irin ta maza yake ƙoƙarin gwadawa a kaina? Na kalle shi da takaici a fuskata kafin na maƙe kafaɗa '' Pls!" ya furta da murya me zurfi ya cigaba da faɗin '' ko nawa ne zan biya just pls ''

miƙewa nayi na ɗauki jakata shima ya miƙe batareda na kalleshi ba nace '' matsalar masu kuɗi gani suke kamar zasu iya sayen kowa...''

kallo na yake da damuwa jin abinda na faÉ—a shiba haka yake nufi ba sam '' ki fahimce ni..''

'' shhh..!" na katse shi ta hanyar ɗaura hannu na a baki na,ragema idona girma nayi sannan na ƙara da faɗin ''bakada kuɗin da zaka saye ni KHALIL!" na juya na tafi

Yabi bayanta da kallo'' hmm fiesty little kitten! we're tangled" ya furta word by word sai ya juya yabar wurin

dana koma gida ganin Mama da Asma'u nayi suna dawowa daga inda ban sani ba na matsa na gaida Mama ta amsa da tambayar ina nake..kawai na faɗa mata ina zaune ƙasan bishiyar mangoro....

washegari da muka tafi makaranta a mugun mugun bazata aka kwashe mu yan spelling bee muka tafi kwampetishon..babu wanda ya shirya cikin mu sai Zufa muke

wasu harda hawayen tsoro Asma'u taso ta dizgani gaban mutane amma hakan bai yiyu ba
lokacin da muka isa mun É—auka round round ne abun idan an zubar daku wannan round É—in zaku iya shiga a wani round a wani sati amma ba haka bane, round guda ne makarantu biyar harda tamu... Sannan kowa kanshi zai amsa mawa ba kamar yanda muka tsamma ta ba

tashin hankali mun shige shi, musamman ni, ganin anata zubar da mutane masu kwanya ina gani danake daƙiƙiya? lokacin da aka kawo kaina jikina ya hau ɓari dole aka tsallake ni aka yima wa'yanda suka shirya...

mafiyawancin su ko point guda basu samu. da aka kawo kan Asma'u harda wani É—an iskan kallo tayimin irin na ki kalla ki koya

amma sai Asma'u tayi dumkun kum da aka tambaye ta sai rarrabar ido take, tama ƙasa magana ko tsoro take ji ne?..

nice ta ƙarshe kuma Alhamdulillah na samu point uku cikin biyar... ba ƙaramin mamaki kowa da kowa yayi ba harni kaina

daga ƙarshe akayi announcing result,gidan nan dai da nayi burin samar mana na sameshi harda ƙarin dubu ɗari biyu...

Wasu yara daga wata government school sukayo na É—aya da na biyu sai wata yarinya itama tayo na na uku ni nayi na huÉ—u exactly position É—in da nake so.... kuma fa ba mata kaÉ—ai bane akwai maza

yan makarantar mu sun tayani murna ba kaÉ—an ba banda Asma'u data yi kamar zatayi kuka har na tanadi maganar da zan faÉ—a mata amma ganin yanayin ta yasa nayi shiru

nan gaban jama'a aka mallaka ma kowa mukullin gidan dayaci kuÉ—i cikin envelope

nayi matuƙar farin ciki harda hawaye shikenan matsalar mu taƙare...

da muka koma makaranta dubu É—ari aka barni dasu, dubu É—ari kuma wa'yanda muka tafi tareda su dasu malaman dasu ka kaimu suka raba...

da gudu na isa gida na faɗa jikin Mama na fashe da kuka, lallashina ta fara duk da batasan dalilin kukan ba saida na huta daga kukan sannan na faɗa mata aiko ta faɗi tayi sujoodush shukoor bawai dan abinda naci ba, a'a karo na farko dana nuna cewa niba daƙiƙiya bace.. tayi murna sosai tamin addu'a

Asma'u kuwa kamar xatayi kuka Mama ta É—auka Saboda bataci bane ta dinga lallashinta amma dalilin wani abune daban...

makullin gidan na miƙa mata ta karɓa ta ajiye tareda kuɗinu

'' yaushe zamu koma gidan Mama?" jim tayi kafin tace a sanyaye '' yaushe kuke so mu koma?" '' ko ranar Lahadi haka '' na bata amsa

'' Allah ya kaimu!"

washegari da muka tafi makaranta harda assembly aka tara don a karramani yan ajin mu sun kasa yarda wai tuwo tayi na huÉ—u da addu'a suka bini, lokacin munyi sharholiya duk dan su tayani jin daÉ—i...

ranar da muka koma gida bayan mun gama cin abincin mun huta muka shirya muka tafi unguwar da gidan yake, unguwar masu ƙaramin hali ce dai kamar tamu amma hanyoyin wannan unguwar sunfi na tsohuwar unguwar mu kyau,daɗi da ƙari bishiyar kashuna ( cashew nut) daidai ƙofar gidan mu har tayi mashi runfa kaɗan...

sauke mu me mashin yayi daidai ƙofar gida Mama ta biyashi kafin ta buɗe ƙofar da mukullin,zauren gidan anyi cementi a ƙasa haka ma bangon anyi plaster.. tsakiyar gidan m haka,ɗakuna biyu ne suna kallon juna sai dakalin da aka sama tiles a tsakani

Sai kitchen da baye sosai gidan ya burge Ni , Asma'u kuwa a ƙuntace take har lokacin, Mama nata yaba kyaun tsakar gidan...cikin ɗaki Munyi mamakin ganin akwai komai da muke buƙata sannan harda baye

Akwai gado da wardrobe da dressing mirror harda TV a ɗaya daga ɗakunan, sannan tiles ne a ƙasa ɗakunan suna da faɗi sosai komai sak... saidai ɗakin da nida zamu zauna ba tv...

sosai Mama take samin albarka, bayan mungama ganin gida muka koma...

nan na gane cewa, wasu lokutan zama me ƙoƙari bai wadatar ba idan babu aiki tuƙuru sannan mutum ya zama me tawali'u sai ya fita daga kunya,girman kai da jiji da kai bashi da amfani

kuma mafi girman darasin dana koya shine kawai mutum na zama abunda ya yardar ma kanshi ne,ni ba daƙiƙiya bace na zama hakan ne kawai dan nayarda niɗin daƙiƙiya ce da gaske...

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

10... Kada ki jira ni Mama...🖊️

ÆŠauke da farin ciki muka koma gida muna hira cikin adaidaita sahu, saida muka fara biyawa wurin buba mai kayan masarufi Mama ta biya shi kuÉ—in daya ke binmu ... Duk wannan ran Asma'u a cunkushe bata ce uffan ba cikin hirar mu

'' wai Asma'u lafiya kike kuwa?"

Mama ta tambaye ta bayan mun shiga daga ciki,da basarwa tace
Chapter 17 · 0% Book details