← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 67

Sashe 51

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Atika ta jagorance mu,muka bar wurin tana bani shawara '' Kiyi kamar baki ji abinda suke faÉ—a ba..wata rana sai labari '' na gyaÉ—a kaina hawaye sun rufe ganina

Muna shiga ɗakin mu Hansa'u ta fashe da dariyar ƙeta tana nuna ni da yatsa..ban bi takanta ba nayi tsaye dan ban san inda zan kwanta ba...

Mama Asabe ta fito daga baye '' Meya faru?" Girgiza kaina nayi bana son faÉ—in ainahin abinda ya faru amma Hansa'u tayi saurin faÉ—a mata dan aci mutunci na...na fashe da kuka

Ƙarasowa tayi ta rungume ni tana bani baki har na daina kukan...

'' ni nake kwana a gadon ƙasa...ki kwanta a na biyu...''

'' wallahi bata isa ba...ni zan kwanta nan!" Hansa'u tayi tsalle ta dire akan bazata canja wuri ba...ganin kawai kamar Mama Asabe tana da sanyin hali...harda hawa tayi bake bake..a fusace Mama Asabe ta ɗauki wayar caji ta zabgawa Hansa'u a cinyarta dake kware ta saki ihu...dariya na fashe da ita tun daga ƙasan zuciya ta

'' TOH sai ki buge ni...'' tayi maganar tana taɓune fuska duk munin ta ya ƙara bayyana..tana wani turo baki kamar mutum yayi amai..

'' wallahi idan baki sauka ba sai na ƙara maki...'' badan Hansa'u taso ba ta sauko tare da hararata ta haye gadon sama

'' na gode sosai Mama Asabe...''

'' bakomai yar nan..Meye sunanki?"

'' Abeedah...''na haye lallausan gadon ina rufe jikina da

'' Allah ya tashe mu Abeedah'' na amsa da Amin takashe wutar, mukayi shiru ...sai Hansa'u dake ƙunƙuni...juyawa nayi ina kallon saman gadon Hansa'u.. maganar mutanen nan tana maimaituwa akaina...dan kawai suna da kuɗi,babu wanda ya basu damar cin zarafin mu marasa kuɗi...hawaye suke sauka ta gefen idona batarada na sani ba... na daɗe ina juye juye kafin bacci ya ɗauke ni...

+2349138091955

RU'UYAA…📖

₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta +2349138091955

Autumn writes 📖🖋️

RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 🍁🍁

21. ...an absolute witch...🖊️

Washegari da ƙarfe biyar na tashi naga Mama Asabe saman abun sallah , gaishe ta nayi ta amsa min da kulawa,na sauko na shiga baye...wanka nayi tare da alwala na mayar da kayan dana cire na fito daga bayen, wardrobe na buɗe na ɗauki hijabi ash nasa na kabbarta sallah gefen Mama Asabe..bayan na gama na sake ɗauko Qur'ani na fara muraji'a kamar yanda muke yi a gida...sai da hasken rana ya fara fitowa sannan na rufe Qur'anin na sake gaishe ta,ta amsa da murmushi...

Na kalli tagar da labulen bai iyarda rufewa da kyau ba,hakan yabawa hasken rana damar shigowa...sai ɗakin ya kasance ba mai duhu ba sosai duk da dama can akwai wani ƙaramin globe kunne...nayi kewar su Mama...da sassarfa na ɗauko wayata daga wardrobe daga tsaye na shiga contact na kira number inna sarai..kamar ana jira aka ɗauka...nayi dariyar farin ciki muka gaisa da ita tabani Mama daga nan su Asma'u kafin mukayi sallama...

Mayarda wayar nayi na isa wurin Hansa'u ina tayarda ita tayi sallah '' inke kike karɓar sallah'r kada ki amsa...'' ta juya kwanci kamar lokacin dare yayi...

''.kinga rabu da ita kawai...'' barin kusa da ita nayi,na zauna akan kujera ɗaya dake ɗakin bada daɗewa ba aka ƙwanƙwasa ƙofar na tashi na buɗe... yarinyar dake gabana ban isheta kallo ba ta turo min uniforms ba bayani ta ƙara gaba...oh ni Abeedah suba masu gida ba,suda jiji da kai...

Rufe ƙofar nayi '' ga abinda ta bani...''na nuna ma Mama Asabe

'' kije ki canja zuwa wannan ki ajiye wa wannan yarinyar ɗaya...'' Baye na shiga na canja kayan..nake kallon kaina a madubin dayake nuna sama har zuwa ƙasa...kayan ash wanda ya dace da kalar idona...kayan sunyi min girma musamman wandon amma naji daɗin kasancewar su masu girma...gefen aljihu harda sunana a rubuce kamar sanda ina aiki a maina hotels...

Fitowa bayen nayi bayan na kimtsa kayan dana cire, wardrobe na nufa na É—auki hula ruwan toka da hijabi rabin guiwa na É—aura sama...na kafe kaina da kallo abu na taso min,da sauri nabar wurin na koma na zauna... koba komai yau ne ranar farko ya kamata in fara da murmushi

'' Ma sha Allah,kinyi kyau...''.

'' na gode..'' na duƙar da kaina a kunyace...tashi tayi daga inda take zaune..'' bari inyi wanka mu tafi kada mu makara..''

'' toh...''

****

### **DOKA DA TSARI - NA YAN AIKI**

**1. Lokacin Aiki Da Bacci**
Lokacin tashi: 5;30 na safe. Dole ne a gama tsaftace gida kafin 7:00.
- Lokacin bacci: 10:00 na dare. Ba tare da izini ba, ba za a iya fita daga sashe ba bayan wannan lokaci.

- Ranar hutu: ƙarshen kowane wata na rana biyu.... cikkaken wata ɗaya a shekara

**2. Ayyuka Na Gida**
- Tsaftace É—akunan girkin abinci, wankin kaya...da ban É—akuna
- An haramta shiga É—akin Alhaji ko Hajiya ba tare da an knock ba.
- Duk kayan da suka lalace dole ne a ba da rahoto nan take.

3. Ladabi Da Halaye

- A amsa da "Eh Madam / Eh sir" cikin ladabi.
- An haramta yin waya mai tsawo, kallon TV mai yawa, ko gayyatar abokai zuwa gida.
- Dole ne a rika sanya uniform mai tsafta kowane lokaci.
- An haramta É—aukar wani abu na gida ba tare da izini ba. Ana kallon hakan a matsayin sata.

**4. Sirri Na Gida
- Abin da ya faru a cikin gida dole ne ya tsaya a cikin gida. Bayyana shi a waje laifi ne.
- An haramta yin magana game da iyalin gidan ga maƙwabta ko a social media.

5 Albashi Da Hukunci
- Albashi yana biya ranar 30 na kowane wata.
- Zama a baya sau 3 ba tare da dalili ba = Rage albashi.
- Yaudara, sata, ko rashin mutunci = Korewa nan take.

-6 Muhimman Bayanai
- Duk baƙon da ya zo dole ne a ba da rahoto ga Madam.
- Idan kina rashin lafiya, sai a faÉ—a tun da wuri don a sami taimako.
-Gidan yana da tsarin kamara CCTV don tsaro.

Abi doka..a zauna lafiya...

Wannan shine abinda mu sababbin zuwa muke karantawa a dining sanda muka zo karin kumallo tsofaffin ma'aikata har sun tafi harda Mama Asabe duk data makara hakan yasa ko karyawan bata yi ba...

Hansa'u tasha faÉ—a wurin Madam Aatika dan ita taje ta tashe ta...hararata take kamar zata kashe ni ..share ta nayi na ajiye paper na fara cin abinda ke gabana.. suma sauran haka sukayi...bayan mun gama kowa ya wanke abinda ya lalata muka zauna dining cikin shiru dan bamusan abinda zamuyi ba

Nake kallon waleeda, yarinyar ƙarama ce bata da jiki kuma bata da tsawo, uniforms ɗin sunyi mata yawa... murmushin kunya tayi min da idon mu ya haɗu '' shekarun ki nawa?" Na tambaya da mayar mata murmushi...

'' sha uku...''

'' na É—auka goma...''

'' nima haka...'' Aina'u ta furta cikin rashin yarda... waleeda bata samu damar yin magana ba,É—aya daga cikin tsofaffin ma'aikatan ta shigo '' kuzo muje...''

Tashi mukayi muka bi bayanta zuwa babban gidan,har ahalin sun fara hallara domin karin kumallo... elevator muka shiga zuwa 4th floor...ɗakuna daban daban ta tura mu...'' a canja zanen gado,a share ɗaki ayi mopping, a wanke Baye a goge ko ina...kayan da sukayi datti a fito dasu zuwa ɗakin wanki...'' tana gama wannan bayanin tayi gaba...kallon lambar ɗakin dake gabana nayi room no 202...tura ƙofar nayi na shiga da sallama babu kowa ciki,na isa ɗakin,makeken gadon na nufa da kamar anyi dambe a sama na gyara na canja zanen gado,na tsince kayan dake ƙasa harda na ciki...na shiga Baye na wanke tass na goge ko ina na ƙyalli..fita nayi zuwa inda ake ajiye abubuwan shara na ɗauko na share ɗakin nayi mopping na fesa air freshener na kwashe labule sannan na fita na rufe ƙofar

Na shiga ɗaki na gaba...shima nayi irin haka...a ɗaki na uku na zauna ƙasa ina hutawa kaɗan...wannan aikine mai sauƙi? Ko kaɗan! Har naji na gaji wasu sassa na jikina sun ɗau zafi... Minti biyar na miƙe na cigaba da gyara gyaren ɗakin, na gama na nufi ɗaki na gaba...zan tura in shiga naji ana magana '' aunty Muf...''

Maganar ta katse sakamakon saukar mari...na rufe baki na...'' ke dan ubanki ina magana kina magana ko? Nan gidan ubanki ne?" Banji amsar da wacce aka mara ta bayar ba sai sheshsheƙar kukanta

Wata murya daban da wa'yannan biyun tace '' ai dan taga tana zaune cikin mune tana cin abinda muke ci ta kwana a irin inda muke kwana...ban san abinda kike tunani game dashi ba ..amma ki sani you're just a maid kuma bazaki taɓa canjawa daga yar aiki ba...tausayin ki dayaji ne kawai yasa ya sama maki wuri a nan.. nothing more!"

Koma wacece tayi maganar tana gamawa tayo hanyar fita...da sauri na matsa na ɓoye a bayan wani abu kamar table dake wurin...har tazo ta wuce saye da kayan bacci...ta biyun ma tafito su biyun suna tafiya suna magana...

Miƙewa nayi bayan sun shige elevator na shiga ɗakin bakina ɗauke da sallama..babu kowa ciki sai dai ƙarar saukar ruwa a Baye...kayan aikina na ajiye na shiga gyara ɗakin,ina jin tausayin koma wacece aka mara yanzu...har nayi na gama bata fito ba yasa na kwashe kayana na fita...

Kitchen na koma a 1st floor,a can na samu da yawa daga cikin ma'aikatan suna kai komo...wurin Madam Aatika na tafi na faÉ—a mata na gama aikin da aka bani..

Ta gyaÉ—a kanta tare da nuna min wasu tsofaffin ma'aikata dake wanke wanke in taya su...yawu na haÉ—iye dan wanke wanken nada yawa kamar dutsen mareri...magana suke akan wani da ban san ko waye ba

'' oh kinji cewa wani sati zai dawo?" Ɗayar ta kalli wacce suke aiki tare da murna a muryarta '' da gaske... Innalillahi daga ƙarshe nima dai zanga wannan kyakkyawan...har naji...''

Da sauri wacce tayi magana da farko ta rufe mata baki...tana mata alama da tayi shiru saboda ina wurin...

'' kece wannan mara kunyar data tasar ma Fauziyya ko?...'' É—age gira nayi tare da fuskantar su

'' well,kidai bi a hankali, Fauziyya hatsabibiyar yarinya ce..''
Chapter 51 · 0% Book details