← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 67

Sashe 49

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' Hmm...anya kuwa yar wata zata samu aiki? Kun kuwa ga idon ta kamar na mayu...''juyowa nayi na kalli wacce tayi maganar daga yanda muryarta ke fita da kuma kallon rainin da take bina dashi na fahimci nayi sabuwar maƙiyyiya tun kafin in fara aiki amma ban ce komai ba suka mayarda ni abun hirar su amma ni ban damu ba ko kaɗan..har wani sashe na zuciya ta na fatan kada a ɗauke ni don in dawo gida in cigaba da rayuwa dasu Mama....

Ɗauke kaina nayi ina kallon window da abubuwan da muke wucewa da sauri,na ɗauka dukan mu wuri guda zamuyi aiki amma a mamakina sai naga munata tsayawa a gidaje ɗaya ɗaya har gida uku na masu kuɗi ana tafiya da mutum biyar a kowacce tsayawa...daga ƙarshe ya rage mu biyar,ni, yarinyar nan da bazata wuce shakaru sha uku ba,wata mai shekaru sha tara...da wata mai shekaru ashirin da biyu..da kuma cikin rashin Sa'a yarinyar data ce ba lallai in samu aiki ba Naji inama ace harda ita aka ajiye a wani gida daban...

Wata unguwa muka kawo ta masu kuɗi, gine ginen wurin kamar a ƙasar waje, guntuwar gina kamar yanda turawa sukeyi,manya manyan gates.. tsakanin wani gida da wani akwai tazara...ƙasan wurin interlock ne sai bishiyoyi masu tsawo da korayen ganyayyaki ...

korayen ciyayi da kuma wurin zama a ƙarƙashin ko wace bishiya..sannan kowane gida nada lamba...unguwar ta haɗu kuma ba ƙaramin tafiya dani tayi ba...

Ina tsaka da kalle kalle naga mun kawo wani makeken gida kamar ƙaramar masarauta....bani kaɗai ba,har da sauran dake cikin motar duka muka saki baki da ido muna kallo...fa tabarakallahu Ahsanul khaliƙin baƙin gate ɗin da kanshi ya buɗe sai da muka yi yar tafiya mai tazara kafin muka kawo gaban wani ƙaramin sashe dake gefen ƙaton gidan...wata tsohuwar mata biye da ita matashiyar budurwa suka fito daga wannan sashen suka yo inda motar mu take....

'' Ku fito...'' inna sabuwa ta fara sauka sannan ɗaya bayan ɗaya muka fito yarinyar nan da ban san sunan ta ba ta tsaya dai dai ni take ƙare min kallon ƙasƙanci '' da nice ke da nayi zama na gudun rasa fuska...''

Miƙewa tsaye nayi na bangaje ta sai datayi tangal tangal kamar zata faɗi tayi saurin riƙe kujera fuskarta ɗauke da fushi take kallo na... Na tsaya bakin ƙofar na juyo ina kallon ta

'' amma bake ce niba...sai ki adanawa kanki wannan shawarar...''

Na sauka daga motar bana son ko kaɗan mutane suna faɗa min nasu ra'ayi game da yanda ya kamata in tafiyar da rayuwata...ƙila da badan na kasance ina sauraren suba,da ban kasance mai yawan jin kanta a ƙasƙance ba...

Gefen sauran na tsaya ake sauko mana da kayan mu,inna sabuwa da wannan matar kuma suka nufi babban gidan...tana bawa waccen matashiyar umarni data shigar damu ciki...

Sai yanzu na samu damar kalle kalle da kyau...ƙasan gidan tyles ne,sai wani taskar ruwa a tsakiyar gidan a gaban babban gidan

ÆŠaya bayan É—aya muka É—auke kayan mu biye da Wannan matar data kai mu har ciki...

A gidan tuni akwai ma’aikata kusan ashirin ko fiye...

- Masu girki 4,uku yan ƙasar waje ɗaya na Nigeria
- Masu tsaftace gida 4
- Masu kula da lambu 3
- Direbobi 4
- Manajan gida 2
Sai sauran masu yan gyare gyare,wanke wanke,share share..da sauran su wanda muma cikin su muke

Aatika ta jagorance mu kai tsaye zuwa ƙofar ma’aikata da ke gefen babban gidan.

Ƙofar ƙarfe ce mai keypad. Ta danna lambar, sai ƙofar ta buɗe da ƙarar beep.

Da muka shiga, iska mai sanyi ya buge mu. Falon yalwatacce ne, kuma shiru ya mamaye wajen.

Aka fara kai mu zuwa Basement ɗin Ma’aikata (Floor B1).inda a ciki akwai

Ɗakin rajistar aiki,Ƙaramin tebur, babban littafin rajista, da kyamarar CCTV a kusurwa. Matar tace mana

"Ku sa hannu a nan. Lokacin aikinku Litinin zuwa lahadi daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 na yamma."..na zaro ido kenan bamu da hutu? Suma sauran kusan abinda suke tunani kenan..daga nan taja mu zuwa ɗakin
Akwai lockers guda 21, sauran shashidan suna É—auke da sunayen masu su..mu da muke sabbabi za'a É—auki sunayen mu..a cikin kowace loka akwai

- uniforms guda huɗu,baƙaƙe ɗaya,ruwan toka, ruwan ƙasa da kuma farare...

nake kallon komai kamar a mafalki ko fim daga nan taja mu zuwa É—akin cin abinci.. inda akwai
Dogon tebur, jarkokin ruwa, da firiji mai abinci

"A nan za ku ci. Ba a saman gida ba." Kamar zan juya idona,dan Allah daga zuwan mu sai wannan? Meyasa baza'a fara bamu abinci a bamu wuri muyi salla ba? Daga nan taja mu inda
Taswirar gidan Wannan shi ne abin da ya fi ba bani mamaki kamar wasu masu gano ma'adanan ƙasa harda taswira a gidan?

"Za ku riƙa ɓacewa. Ku haddace wannan taswira." Yanda matar take magana business kawai ba fara'a..murya ƙamas ƙamas...cikin kamewa yasa naji kewar su Mama na tasomin kamar zanyi kuka

Sai ta nuna sama dukan mu muka bi wurin da kallo

"Gidan nan yana da bene shida. Idan kuka yi yawo ba tare da izini ba, CCTV za ta gan ku. Don haka kada ku yi yawo."

Muka gyaɗa kai ina addu'ar Allah yasa wannan shine ƙarshe,fita tayi muna biye da ita benen dake tsakiyar parlorn muka hawo sai ga ɗakunan bacci harda doguwar kujera ƙwaya ɗaya gaban wani ɗaki ta tsaya kafin ta juyo kalle mu na tsawon lokaci sannan ta raba mu,ta haɗa nida yarinyar nan data tsane ni tace ɗakin mu ɗaya sauran ma ta nunawa kowa ɗakin shi... yarinyar nan na kalla naga ta sakar min wani mugun murmushi Jikina yayi sanyi idanfa ta dinga cuta ta kuma na kasa tsaya ma kaina ya zanyi?

'' Oya...ku faÉ—a min sunayen ku...'' maganar matar ta katse ni daga tunanin dana shiga

Ta nuna ni '' Abeedah...'' na faɗa a sanyaye,kafe ni tayi da ido tana duba ni bada hukunci ba sai dai kamar tana ƙoƙarin fahimtar wani abu...can ta gyaɗa kanta ta juya ga sauran

Waleedah, yarinyar mai shekaru sha uku,Ayna'u yarinyar mai shekaru sha tara...sai Rahma yarinyar mai shekaru ashirin da biyu... muguwar nan sunan ta Hansa'u shekarun su É—aya da Aina'u...

GyaÉ—a kanta matar tayi ta bamu shawara,ko nasiha take mana,ko faÉ—a ban fahimta ba '' duk wacce tayi ciki a gidan nan,gidan iyayen ta zata koma babu hanya biyu game da wannan!,ku shiga ciki kuyi wanka ku canja kaya..anjima za'a kai ku babban gida a gabatar daku.." Tabar mu tsaye a wurin ta wuce muka shiga kallon kallo gabana naji ya fara faÉ—uwa...

Ture ni Hansa'u tayi ta shiga ɗakin mu nabi Bayan ta...babu tarkace da yawa a ciki...gadon nan mai hawan mutum uku,da wardrobe guda uku labule fari da kuma baye sai fanka da farin ƙwai ko TV babu ...

Nake tunanin..akwai gado uku,kuma mu biyu ne waye na ukun? Baye na nufa Hansa'u ta sha gaba na

'' ni zan fara shiga..'' tayi maganar da izza bana son faɗa shine yasa kawai naja baya..tayi ƙwafa sannan ta shige bayen ta ɓata lokaci kafin ta fito nima na shiga.. duk tayi ma bayen kaca kaca...ga kashi da tayi bata yi flushing ba baye duk ya gume...cikin ɗacin rai na tsaftace bayen sannan nayi amfani dashi..

Sanda na fito har an kawo mana kayan mu,naji daɗin hakan,na duba riga da wando marasa nauyi da singlet nasa,na ɗauki hijabina na kabbarta sallah Hansa'u tayi kwance saman gado tana latsa waya ƙila bata salla,ina nan zaune har Saida akayi maghrib...bayan mun gama,wata mata ko yarinya ce oho..tazo ta kira mu wurin cin abinci..kusan a tare mu sabbabin zuwa muka fito daga ɗakunan mu...lokacin ƙarfe bakwai da yan mintuna dan haka tsofaffin ma'aikatan sun dawo...

suke bin mu da kallon dana kasa fassarawa..muna tafiya a tsorace muka iso dining É—in,muka gaishe da waya'nda ke wurin wasu suka amsa ba yabo ba fallasa wasu kuma ko kallo bamu ishe suba...

Matar farkon nan data shigo damu wurin tace muje kitchen mu zuba ma kanmu abinci...a sanyaye muka wuce kitchen É—in muka zubo abincin muka dawo tace mu zauna a seats É—in da babu wanda ke zaune saman su...mutane da yawa a wurin ransu bai so ba...

Tace '' bari in fara da kaina...sunana Ateeka nice mataimakiyar shugabar ma'aikatan gidan nan... wa'yannan...'' ta nuna sauran tana gabatar mana dasu,yawansu yasa ban riƙe sunan kowa ba.. taci gaba da faɗin

'' a gidan nan babu seniority,wani baya aikin wani...kada ku bari wani ya cutar da ku,kuma kada ku cutar da wani,amma duk da haka akwai girmama juna..wanda ya girme ka ya girme ka...''

Ta dakata tana kallon mu dan fahimtar ko mun fahimci abinda ta faɗa ko akasin haka ta ƙarashe maganar da faɗin '' akwai rules and regulations a gidan nan..za'a ba kowa copy ya ajiye idan mutum ya cika karye ƙa'ida zai bar gidan nan! Fatan zaku kiyaye?"

'' Insha Allah '' muka amsa...nake ji gidan ya zama kamar kurkuku duk da har yanzu babu wani gagarumin abu daya faru...a hankali nake cin abinci na..ina jina duk a takure

'' kuyi sauri ku gama mu tafi main house bayan sallar isha'i..'' muka jinjina kan mu tabar wurin... tsofaffin ma'aikatan suna cin abinci suna hira akan aikin su naji inama ace nima ba sabuwar ma'aikaciya bace...'' Ke!" É—agowa nayi daga abincina ina kallon wacce ta kira ni da 'ke' hararata tayi...'' contact lenses kike sawa?" Sauran suka juyo suna kallona da sauri na fahimci abinda take nufi ganin kallon zargin da ake bina dashi...'' haka idona suke..''

'' ƙarya kike..maza tafi ki cire wannan abun daga mummunar fuskar ki...'' yarinyar maganganun ta na cin mutuncin ne..take naji idona sun ciko da hawaye kuma babu wanda ke mata magana...

'' haba Fauziyya bai kama...''

'' Babu ruwanki Mama Asabe!" Fauziyyar ta katse matar da É—aga murya, matar ta fara tsufa kuma insha Allah zata haifeta,sannan ta sake juyowa inda nake '' ba zaki tashi ba?"

Da takaicin abinda tayi ma tsohuwar nace '' eh bazan Tashi ba,idan kin damu kizo ki cire da kanki...'' wurin yayi tsit da tension...nida fauziyya idon mu cikin na juna...naji cikina ya kaÉ—a..amma duk da haka...waya bata ikon cin mutun cina da kuma na tsohowar? Ina girmamawar da akace ana yiwa na gaba da kai?
Chapter 49 · 0% Book details