← Book details Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 67

Sashe 42

Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' Ni babban abinda yafi damuna kuma yake ban tsoro saratu shine idan fa wata rana sukayi ƙoƙarin....'' ɗaga labulen da nayi ya katse Mama daga ƙarasa faɗar abinda take faɗa duka su biyun suka jiyo suna kallona kyakkyawar fuskar Mama dake ɗauke da damuwa tayi saurin canja wa zuwa mai walwala inna sarai take zarar ido...su biyun daka gansu kasan yaya da ƙanwa ne, nayi nadamar ɗaga labulen dama na bari na gama jin abinda zata faɗa amma kuma ata wani fannin Haramun ne laɓe aiko? na sassautawa kaina...

'' Abeedah har kin dawo?" Inji inna sarai da alamun rashin gaskiya jinjina kaina kawai nayi...sai na shigo cikin É—akin na zauna gefen Mama tareda kwantar da kaina saman cinyarta,ta É—aura hannun ta saman goshina... '' Mama dan Allah ayi fate yau...''

'' wai fate,na bishi da gudu ba wando...!" Anaam ta hankaÉ—o labulen tana harara ta

'' to uwar yan marasa kunya shi za'ayi bari in tashi ma kigani...'' kwantawa wurin Anaam tayi tana birgima ita ala dole baza'ayi fate ba

'' yauwa inna sarai sai dake...'' na faɗa ina dariya da son ƙular da Anaam...

'' ai sai dai in kwana da yunwa wallahi...''

'' cikin ki kona wani? Ke kika sani...'' miƙewa inna sarai tayi ta fita Anaam biye da ita...nikam na raka su da dariya

'' Ya kike?" Mama ta tambaya da kulawa, mirginawa nayi ta yanda ina kallon fuskarta batareda na tashi daga jikinta ba...ita da Asma'u kamar an tsaga kara duk da Mama ta tsufa idan ka kalleta zaka gane ba ƙaramar kyakkyawar budurwa akayi ba lokacin yarinta

'' dama banda lafiya ne?" Na mayar mata da tambayar tayi murmushi

'' ba wannan rashin lafiyar nake tambaya ba Abeedah...ina nufin ya kike ji a ranki yanzu?"

'' oh...'' sautin ya fito daga bakina ya nake ji yanzu? Babu komai bana farin ciki bana baƙin ciki a dai dai wannan lokaci ban san nan da anjima kaɗan ba

'' babu abinda nake ji'' na mirgina na koma gefe...'' wani abu ya faru a waje?" Tambayar data yi yasa na juyo na kalli fuskar ta...'' na lura da sanda kika shigo...''

'' A'e ce tace wai Fuskata kamar anyi ƙunar baƙin wake...'' murya ba amo maganar ta fita

'' hmm..ke kuma me kika faÉ—a mata?"

'' nace ƙila idonta ne bai gani da kyau tunda ido ɗaya ne da ita...kuma na faɗa masu bana son wasan banza tunda sunce wai wasa suke niban iya ɗaukar wasa ba...Mama meyasa mutane basa tunani kafin su faɗi magana ne?"

'' kowa da yanda yake Abeedah..ba zaki iya sa mutane suyi yanda kike so ba...'' ta fara sai na juyo ina kallon fuskar ta,ta cigaba da faɗin '' amma kina da damar zaɓin yanda zaki tunkari abinda suka faɗa ko sukayi....zaki iya kallon alkhairi ko gaskiyar dake cikin maganar su,sai Kiyi aiki da wannan,Kiyi farin ciki ki cigaba da rayuwar ki...ko ki kalli sharri da ƙaryar dake cikin maganganun su,sai ki bari hakan yayi tasiri a kanki sai ki kasance cikin baƙin ciki da damuwa da rashin karsashi....''

Ƙasa tayi da kanta idonta cikin nawa '' ina so koda yaushe ki kasance mai tunani mai kyau koda baki fahimci abinda ke faruwa ba..Kiyi tawakkali ki fuskanci gaba da ƙwarin guiwa da kuma yarda da cewa Allah ya isar maki abinda yayi shine daidai...'' gyaɗa kaina nayi duk da ban fahimci inda maganar tata ta dosa ba...naso inyi mata magana akan abinda naji suna magana akai itada inna sarai,kafin in tambaye ta naji inna sarai tana ƙwala min kira '' tashi ki tafi...''

Tashi nayi na fita daga É—akin ina jujjuya maganganun ta amma na kasa fahimtar me take nufi...

Anaam na fara gani a tsakiyar gida tana jajjagen kayan miya bakin na yayi tsawo kamar mazurari... Asma'u tana baye inna sarai a kitchen tana fita wuta..duk hayaƙi ya baɗe wurin ... '' xoki kula da wutar bari in wanke tsaki...'' tayi maganar idonta cike da hawaye hanci majina ba shiri na saki dariya '' gaskiya dai bari in wanke tsakin ke kyaji da wuta...''

'' ke uwar son banza ko?" Girgiza kaina nayi ina cigaba da dariya na shiga na ɗauki tsakin dake cikin ƙwarya... Ɗakin Mama Asma'u ta wuce bayan ta fito daga baye... ba kamar Abeedah ba nesa da Mama ta zauna tana binta da ido da alamun magana a bakinta

'' ƙaraso nan...'' sai ta tashi ta isa inda Mama take,ta kwantar da kanta saman cinyar ta, zame ɗan kwalin kanta Mama tayi tana shafa gashin ta tace

'' akwai abinda zaki faÉ—amin ne?" Asma'u tayi shiru na lokaci dan batasan inda zata fara ba kuma bata san me zata ce ba

'' zaki iya faɗamin ko meye ne...ni Maman kice...'' mama ta ƙarfafa mata guiwa

'' ina son Khalil...'' shiru ne ya biyo bayan maganarta hannun Mama dake motsi saman gashinta ya tsaya cak... hawaye Masu ɗumi suka silalo daga idon Asma'u...kafin kuka mai ƙarfi ya biyo baya jikin Mama yayi sanyi.haɗiye damuwarta tayi da taushin murya tace

'' meyasa kike kuka?" Tashi zaune Asma'u tayi ta riƙo hannun Mama ta ɗaura saitin zuciyarta '' duk da yanda zuciya ta ke kiranshi...shiɗin burine da bazai taɓa kasancewa ba Mama...na tabbatar yana da masoya da yawa..kuma daga ƙarshe niɗin yarince kawai daga cikin wa'yannan ɗinbi jama'ar... I'm Just a girl part of the crowd...'' rasa abin faɗa Mama tayi kawai sai ta jawo Asma'u ta rungume ta tana shafa bayanta...'' akwai Allah Asma'u...ki cigaba da addu'a...''

*****
Bayan Isha'i dukan mu zaune muke saman baranda yau ma ba wuta sai fitilar da muka kunna daga gefe, akwai iska mai sanyi da taurari kaɗan kuma akwai hadari ,cikin wani ƙaton tire inna sarai ta zubo faten da cokula kowa ɗaya ɗaya muka zauna a cycle nida Asma'u gefe da gefen Mama..inna sarai da Anaam gefe ɗaya,ƙamshin faten mai sa yawun mutum su tsinke amma dai a ganina yayi yawa... '' kai wannan fate yayi mana yawa inna sarai...'' Asma'u ta rigani faɗa taɓe baki inna sarai tayi '' munanan daku wannan mai cikin zanen saita nemi ƙari shine yasa na ciko faranti....'' dukan mu muka yi dariya harda Mama

tana harare harare tace'' ai dai lafiya ke ci.yanzu idan mutum baida lafiya ko kaza aka ajiye gaban shi sai dai yayi ta lasar baki..ku barni inci abinci na dan Allah...''

'' Ina bayan ki Sha'awanatu...'' Mama ta goyi bayanta,ajiye cokalin Anaam tayi taje ta wanko hannu ta dawo ta tsunbula ciki,kowa nashan fate da cokali ita da hannu take sha harda wani ' zuruf zuruf 'take...inna sarai ba abinda take sai aika mata harara faten yayi daɗi sosai bayan mun gama muka zauna a wurin Anaam tana bamu labarin garinsu mun sha dariya ba kaɗan ba...'' akwai wata yarinya mai suna Salame kusa da gidan mu suke wai ɗan ƙaramin bunsuru take goyawa a baya a matsayin jaririnta ko bari batayi ya taka ƙasa...ɗan bunsuru ko ya kafa tsuwa musamman idan tasa zane ta goye shi....''

'' Haahaa! kai.wai mutum da goyon bunsuru ina Lafiya..'' inji Mama...

'' wallahi ko..ranar an É—aura sanwa saman wuta,bunsuru garin kwaÉ—ayi ya toye baki yana ta tsala ihu '' Inna sarai tayi maganar wurin dariya har saida ciki na yayi ciwo...kuma naji daÉ—in kasancewar mu tare a wannan lokacin..hakan ya rage min girman damuwa ta ba kaÉ—an ba....

Washegari da muka tafi makaranta,na iske Jay d da Diyaam har sun iso sannan ajin shiru,kusan kowa ya mayar da hankali yana rubutu akan wata farar paper wurin zaman mu muka isa nida Anaam muka gaishe da wa'yanda ke kusa kusa,farar paper nima ta miƙo min.. Diyaam kuma taba Anaam... '' me zan yi dashi?" Dakatawa tayi da rubutun ta '' ai dole sai da wannan su xasuyi amfani dashi wurin cika bayanan ki,suna, ranar da aka haife ki,me kike so ki zama da sauran su...''

'' oh...'' na furta a hankali...na dawo da idona kan paper,me nake so in zama? Ban taɓa tunani akan wannan ba tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin wani abun daya birge ni ba naji ina so in zama sunana na rubuta da sauran abubuwan da aka buƙata na ajiye biron batareda na cika inda aka tambayi me muke so mu zama ba''.na gani...'' Diyaam ta ɗauki paper tana dubawa kafin ta ajiye tana nuna min

'' nan baki sa komai ba...'' É—agowa Jay d tayi

'' baki fahimci bayanin da na maki bane?" Ɗage kafaɗuna nayi '' ban san me nake so in zama ba ban taɓa tunani akai ba...''

Suka kalli juna kamar na faÉ—i wani gagarumin abu'' nima ban san abinda nake so in zama ba...'' Jameelah dake zaune daga gaban mu ta juyo...

Wasu ma daga cikin yan ajin mu sukace basu san abinda suke so su zama ba.. wasu kuma kawai suna rubutawa ne badan abinda suka rubuta ɗin shine burin suba...wasu kuma daga gida aka zaɓar masu abinda zasu zama...

'' kuna buƙatar career counseling...'' Jay d ta furta tana kallon mu... Ta sake fita ta tsaya gaban allo ta shiga rubuta sunan abubuwan abinda mutum zai iya zama.. tana bayani akai...

Daga nan waya'nda suka fahimta ko suka ji abin yayi musu sai su zaɓa...nidai har lokacin ban sani ba...bana son in shiga abinda bana ra'ayi...

Wata yarinya daga can gefe...kowa na rubutu banda ita,ta mayarda kanta tana kallon waje..'' Amina kefa? Bazaki yi rubutun ba?" Hameeda ta tambayi yarinyar kowa ya mayar da hankali akanta ta sauke numfashi sannan tace '' idan akwai abinda nake so in zama ina so in zama ƙwararriya a fannin soyayya...wannan shine kawai...''

'' Oh abinda kaÉ—ai ke ranki kenan?"

'' aure kike so ko meye?...''

'' awwn...kamar saliha...''

Sai zolayar ta ake ita dai murmushi ne nata tafa hannayen ta Jay d tayi kowa ya mayar da hankalin shi wurin ta '' eh...akwai...zaki iya zama love coach..mai bawa mutane shawara fanin soyayya..amma meyasa kike so ki zama wannan?"
Jay d ta tambaya... murmushin yarinyar ya ƙara faɗaɗa...'' saboda idan nayi aure in sace zuciyar mijina ni kaɗai bazai kalli wata mace ba.. kamar yanda yake faruwa a littafi.. yarinyar da suke so ita kaɗai suke gani...''

'' ayyiriririri!!!!!ohhhhhh!" Yan aji suka É—auka
Ameena ta rufe fuskarta da hijabin ta
Chapter 42 · 0% Book details