Sashe 12
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kitchen na shiga nace a haÉ—a tuwon dawa miyar kuka..duk da sunyi mamaki hakan bai hanasu haÉ—awa ba,plates uku kuwa..zama nayi har suka gama aka haÉ—o min tuwon dawa miyar kuka da ruwa...É—aukar tray É—in nayi ina tafiya a hankali tun daga nesa nake jin idonshi akaina...na rasa Uwar me yake nema
na kawo wurin su ina tsaka da ajiye tray ɗin ta rugo da gudu '' Beeeee!!!! ''tayi tsalle ta haye ni trayn ya faɗi daga hannu na abincin ya juye musu a jiki nida Jay D muka faɗi ƙasa...suma da sauri suka miƙe saboda yanda miyar kukan ke basu ƙyama.... wurin kowa ya dawo da kallon shi akan mu...Jay D ta fara miƙewa tayi hiri hiri da ido kafin nima na miƙe
Gayen nan mai farin gashi yake magana da Yaren da ban taɓa jiba...fuskarsa ba kyaun gani tsabar ɓacin rai...
mai facemask kuwa kamar wanda ya shiga shock sai kallon kayan jikinshi yake... Khalil babu abinda ya samu nashi kayan..in wani abu sai gimtse dariya yake...nima nawa idon kamar zasu fito,harda yar zufa naji tana sauka a gadon baya na..na haɗiye yawu sanda mai saye da facemask ya watsa min wani shegen kallo har cikin ƙasusuwana.. ƙirjinsa na sama da ƙasa..kamar zai ƙona ni da idonshi...Jay D ta riƙe hannuna muka yi taku ɗaya baya ..
wurin yayi shiru kowa mu yake kallo, ƙafafuna babu abinda suke sai rawa..zagayowa mai facemask yayi zai damƙo ni,da sauri Ibrahim da ɗayan gayen suka tare shi
" Calmati Di caprio (kwantar da hankalin ka Di caprio)!"mai farin gashi ya furta da yaren da ban sani ba, Ibrahim na shafa ƙirjin gayen..ture su biyun yayi a tsananin fusace ya nuna ni da muryar shi kamar ana tuƙa tsohuwar mota yace
''Come faccio a calmarmi?! Ma è pazza?! Mi ha rovinato i vestiti, maledetta!(taya zan kwantar da hankalina? bata da hankali ne? ta ɓata min kaya..damn girl!)
" Calmati! calmati!" kawai gayen mai farin kaya yake maimaitawa...shima Ibrahim yana taya bada haƙuri... ido na ya haɗu dana mai face mask...naga idon shi ya ƙara duhu..can kuma ya dunƙule hannunshi..sama da ƙasan ƙirjinshi na ƙaruwa kamar kallona kawai na ƙara kunna shi...da sauri na cire idona daga nashi na kalli Ibrahim da shima ni yake kallo..murya ba amo nace
'' dan Allah kayi...''
'' SHUT UP!!!!" Mai facemask ya daka min tsawa sai dana kusa faɗuwa,Jay d ma ta tsorata da alamu ta ƙara ƙame ni...
'' calm down Ro..''
da wani irin yanayin magana(accent )wanda bai yi kama da yanda masu turanci ke magana ba yace '' this is all your darn fault BRAHAM!'' Ibrahim ya gyaɗa kanshi da ban haƙuri a fuskar shi...
nifa gayen ya fara ban haushi tuntuni sai haƙuri ake bashi amma yaƙi ya sake harara ta
'' Abeedah mubar wurin nan...'' jay d ta raÉ—a min a kunne...gyaÉ—a kaina nayi muka fara ja baya a tare..mai facemask sai banbamin bala'i yake da shegen yaren su mara daÉ—in ji
ido na sake haÉ—awa da Ibrahim '' in kawo maku wani sabon tuwon?" na waro mashi idona,dama ace abincin kan shi ya zube..amma naji daÉ—i daya zuba kan wannan mara mutuncin...É—an zaro ido yayi sai ya girgiza kai yana nuna min gayen nan da idon shi...wata irin dariya na kwashe da ita ba shiri...kowa yake kallona a wurin kamar na haukace
gane hakan yasa na miƙe da kyau tare da haɗa hannayena wuri guda '' yi haƙ...''
'' if you open that your dirty mouth again,I will slap you hard across the face!" yayi maganar a mugun fusace.. jim nayi ina ƙoƙarin fahimtar abinda yake nufi can ƙwaƙwalwata,ta tattaro bayanai da ƙyar...haɗe fuska nayi cin mutuncin yayi yawa'' baƙin ciki kake min ko? Allah ya bani baki wanda bai wari ba saina sa fes mas ba shi...'' kafin in gama naga ya wani harzuƙo mun bansan sanda na warto hannun Jay D muka kwasa da gudu ba sai kitchen
bayan mun gama haki sai kuma muka rungume juna muna dariya '' ke Bee, wannan gabjejen mutumin idan ya same ki ai shemar dake zaiyi da bugu É—aya!"
'' yoni hauka nake da zan bari ya same ni?" na bata amsa mu biyun muna miƙewa tsaye ganin manager, fuskar shi a murtuke...kafin ya fara magana na fara kukan ƙarya '' Jay D bayana ji nake kamar ƙashin bayana ya karye!" nayi maganar ina juya mata baya da ƙifta ido '' yi haƙuri Bee laifi nane..'' ganin dramar mu manager ya ɗauka da gaske ne ya shiga bamu haƙuri daga nan ya bamu dubu biyar yace Jay D ta kaini kyamis
yana fita muka ƙara rungume juna muna dariya sannan muka fita ta baya, a parking lot na hango Asma'u... da sauri muka isa wurin datake '' me kike yi anan?" Jay D ta tambaya nabi ta da ido,faɗawa jikina tayi murya kamar zatayi kuka '' dan Allah Tuwo kiyi haƙuri...'' kallon kallo mukayi nida Jay D shafa kanta nayi '' ba komai!" na faɗa ina ɗagota murmushin ta me kyau tayi min
'' Mutafi mu hole da dubu biyar ɗin manager!" Jay D ta faɗa tana riƙo hannu na,har zamu bar wurin saiga Malam samin macijin sari ka noƙe ya shigo shida wata yarinya, hannun shi riƙe da ƙugunta,yana mata raɗa a kunne kafin kuma suka haɗe baki wuri guda kis,zaro ido mukayi mu biyu kafin mukalli Asma'u dake hawaye, lallashinta muka fara yi amma ina kukanta ƙara sauti yayi da ya jawo hankalin su akan mu... tsaye yayi wuri guda shima yana kallon mu idonshi kamar zasu faɗo firgici bayyane a fuskar shi musamman dayaga yanda Asma'u ke risgar kuka
. takowa ya fara zai zo wurin mu ta tsere tabar wurin ,bin bayanta Jay D tayi kallon sama da ƙasa nayi mashi '' Sheɗanin banza ɗan iska!" na faɗa a fuskar shi kafin nima nabar wurin
Asma'u kuka take kamar ranta zai fita lallashinta ba ƙaramin aiki bane, jan mu Jay D tayi zuwa wani wuri inda ake sayarda su abincin gefen hanya,irin su suya,ice cream da sauran su,wasu dubu biyar ta ƙara akan wanda manager ya bamu muka kwashi Gara
suya ta siya mana ta dubu biyu da ice cream na dubu ɗaya da ɗari biyar kowa ɗaya, duk wani kayan maƙulashe saida Jay D ta siya mana daga ƙarshe sai wurin maghrib muka bar wurin bayan mun ƙara sayen suya ta dubu biyu muka wuce da ita gida.... Jadeedah ma ta wuce gida bayan ta bamu dubu biyu mu riƙe
munyi mata godiya sosai...
'' Tuwo kiyi haƙuri akan duk abinda na maki bazan sake ba insha Allah '' Asma'u ta faɗa tana shafa min ruwan shinkafa akai,yau akwai wuta, Mama tana tsakar gida tana kalkamta kaya dan akwai hadari..
'' nayi farin ciki..yanzu dai nasan kinga Abinda nake faÉ—i ko? Wannan yarinyar ba itace ta farko ba,ya kawo mata da yawa...bai dace dake ba!" gyaÉ—a kanta tayi hawayen ta na faÉ—owa a fuska ta da sauri ta goge su kada Mama ta gani...
washegari jumu'a yasa Mama bata bamu ko kwabo ba,ina ta ture turen baki kamar ƙaramar yarinya taɓe baki Mama ta ɗauke ido
'' Mama abincin jiya ya rage?" Asma'u ta tambaya '' a'a, shinkafar ma ta ƙare yau idan kun dawo sai dai ku sha garin kwaki'' Mama ta bata amsa jida nayi ance babu shinkafa yasa naji wani iri a zuciya ta '' yanzu tuwo zamu dinga kilma ko?" wani kallo Mama tayi min '' ai shima tuwon babu .. abincin ya ƙare duka!" kallon kallo mukayi nida Asma'u kuma fa wata baiyi nisa ba balle ince an kusa biyan mu albashi...
'' kuyi sauri kada ku makara har rana ta fito '' Mama ta faɗa tana miƙo mana kunun mu karɓa nayi raina a cunkushe yanzu ya zamuyi?
nasan buba me kayan masarufi bazai bamu bashi ba dan har yanzu akwai sauran bashin shi a kan mu..har na shanye kunun bansan na shanye ba tsabar yanda nayi nisa cikin tunani, ajiye cup ɗin nayi na goge baki itama Asma'u ta ajiye nata muka saka hijaban mu dake rataye a igiya jakunkunan mu a hannu '' mun tafi..'' miƙewa Mama tayi ta biyo mu da nasiha da addu'oi har bakin ƙofa '' a dawo lafiya.."
yau Ban hawo bishiyar mangoro ba makaranta muka wuce daret babu wanda ke magana cikin mu,sanda muka isa an kusa gama assembly bada daɗewa ba muka shiga aji...abin da ya ƙara min baƙin ciki..Jay D bata zoba! dama ita doja ce ta bugawa a jarida
lokacin break na cigaba da tunanin ya zanyi da abincin da babu a gida? shawara na yanke zan karɓi rabin albashi na hakan ya ɗan sanyaya min ruhi
da gaske da muka dawo garin kwaki muka sha ba suga ba giɗa babu ƙuli... Kamar inyi kuka,muna gamawa muka ɗauki bucket gidan wani Alhaji babba muka tafi ɗibar ruwa, akwai layi dayawa dan haka muka shashance da wasa...sai wurin ƙarfe uku muka kawo bokiti guda guda Mama tana tayi mana faɗa...da muka koma layi ya rage da sauri muka ɗibi ruwan muka cika komai kafin na shirya na wuce wurin aiki bayan nayi wanka
Sai dai me? an kore ni daga aikin ba bayani ba komai kuma an canja manager,duk yanda naso in ji dalilin korata babu wani takamammen bayani... albashin ma an hanani...a dai dai wannan gaɓar ji nayi rayuwa tayi min zafi, duk yanda naso in daure na kasa na fara surfa masifa....sabon manager'n yasa securities su fitar dani daga wurin wai ina damun customer ɗinsu... haka wa'yannan gaɓa gaɓan abubuwan suka saɓani a kafaɗa suka jefar dani waje kamar buhun shinkafa...
zagi da Allah ya isa sai wanda na manta kafin na duƙe a wurin ina sharɓar kuka...ban ankara ba ashe har dare yayi miƙewa nayi na fara tafiya gani nayi kamar akwai wata mota a baya na amma ban kawo komai a raina ba har Saida na sha wata corner inda babu mutane sosai motar nan tasha gabana....
PAGE 7 A AREWA PEN
+2349138091955
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account É—in 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta +2349138091955
Autumn writes 📖🖋ï¸
RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 ðŸðŸ
Free pages
7. ...Ya xanyi ... 🖊ï¸