Sashe 27
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'' Ni Jadeedah ko wata daban?"
Ta tambaya tana kalle kalle sai kuma ta nuna kanta
'' a'a ta bayanki!"
Asma'u ta amsa tana juya ido
'' I thought as much!" Jadeedah ta furta haɗe da taɓe baki
'' nidai mu tafi...''
sai muka yi gaba
Wurin fita daga get duk anbi an matse ma mutum kayan ciki,kamar idan munyi da É—ai É—ai baza a fitan ba
wasu suna dukan juna suna gudu tare da faÉ—in '' na sha ta anjima'' wasu kuma suna ma juna bye bye wasu suna faÉ—in sai Monday
hanyar da muke bi mutane ƙalilan ke bin hanyar ɗayan hanyar kusan rabin makarantar mu nan ne hanyar su
'' sai Monday Jadeedah da Tuwo!"
Wasu yan ajin mu su dayawa suka faÉ—a suna bin hanyar can
'' sai Monday '' nida Jadeedah muka faÉ—a tare muna musu bye
a hankali na juyo ina kallon hanyar nan dake cike da mutane,Mu hanyar mu yamma ne inda rana ke faɗuwa su kuma hanyar su gabas inda rana ke fitowa nake jin kaɗaici a duk sanda na juya naga mutane da yawa suna bin hanya guda mu kuma yan ƙalilan a tamu hanyar kamar inbi inda mutanen masu yawa kebi duk da nasan ba dukan mu bane uhm..
Autumn: destination
Ba dukan mu bane zamu isa destineshon É—aya ba duk da haka
Jay D take jana da hira anan ne Asma'u tasan zan tafi gidansu tayi ƙasa da kanta tana sauke ajiyar zuciya...
'' akwai matsala ne?''
na É—an kalleta jin ajiyar zuciya'n data sauke
'' babu''
ta bani amsa da murmushi sai ta shigo cikin hirar mu abinda bai faru ba da daÉ—ewa ita da Jay D basu yi faÉ—a ba kamar yanda suka saba wannan babban canji ne gaskiya
Muna kaiwa bakin hanya motarsu Jay D ta iso, ta buɗe mana ƙofa muka shiga a tare muka gaishe da Musa direba ya amsa da fara'a tare da faɗin
'' yau Abeedah ce a motar mu gaske naga hadari ya taru!"
Asma'u da Jay D suka yi dariya kafin tace
'' ai baka san artabun da nasha ba kafin ta shigo shine yasa'' na taka ƙafarta tayi shiru murmushi yayi kafin ya fara tuƙi
'' ɗan bani wayarka in kira Ummi'' miƙa mata wayar yayi
Ta kira mamansu sukayi magana '' toh ba matsala me kike so a dafa kafin ku iso?" ta tambaya,Jay d ta kalle ni
'' Bee me kike so kici?" Nida Asma'u muka bita da ido
'' kawai adafa abinci mai daɗi'' ta ɗage kafaɗa suka ƙara magana kafin ta katse kiran daidai an kawo gidan mu godiya muka yiwa direba sannan Jay D ta faɗa mashi yazo ya ɗauke mu da ƙarfe shida da rabi
Sallama mukayi muka shiga ciki muka iske Mama tana sharar tsakar gida
Jin baƙuwar murya yasa bayan ta amsa ta miƙe tsaye har muka ɓullo daga zauren
'' a'a a'a..maraba maraba da Jadeedahtu.. '' Jay D ta rufe fuskarta tana dariya kafin takai ƙasa ta gaishe da Mama
Mama ta amsa tare da ɗago ta suna cigaba da gaisawa muka wuce ciki Mama ta rako Jay da har ɗakin mu sannan ta wuce kitchen Cire hijabinta Jay d tayi amma tana da hula akai kallonta nake dakyau da kyau Ni ban taɓa lura ba amma Jay D tana da wani irin kyau na daban uniform ba ƙaramin rage ta suke ba girar ta da hancin ta kamar zana su akayi idonta manya ƙwayar ciki fari sosai baƙin ciki baƙi wulik ga wani gashi daya kwanta a bayan wuyanta bakinta ɗan ƙarami amma ba pink bane kamar na Asma'u amma duk da haka
ni idan za'a ce in zaɓi wanda yafi kyau cikin su biyun Jay D ce ban taɓa ganin ta babu hijab ba sai yau. Fuskarta kyakkyawa surar jikinta? ɗauke idona nayi daga kallonta sai kuma naji nauyin cire nawa hijabin kowa a cikin ɗakin yafini komai kunya kamani dana kalli ƙirjina ta cikin madubi
'' Bee ki cire hijabin mana'' Jay D tayi rashe rashe saman gadon mu,ajiye jakata nayi na fara cire hijabin kamar a wata ƙasa ƙarshen hijabin yake
Mama ta shigo da shinkafa da miya cikin plates harda cokula guda uku da ruwa da sauri Jay D ta tashi ta karɓa suna ma juna murmushi Asma'u dai bata ce komai ba sai kallo take
Da ƙyar na samu na gama cire hijabin ƙirjina yayi min nauyi ajiye abincin tayi a tsakar ɗaki muka zauna a saikul kowa ya ɗauki cokali tana murmushi ta kai baki tana ta santi tun ina jin kunya har na saki jiki
Kuma ma dukan mu mata ne ai ko? Eh hakane amma kasancewar mu mata bai hana ni jin abinda nake ji ba bayan mun gama cin abincin nakai mata ruwa a bayi ta shiga tayi wanka ni kuma na wuce É—akin Mama Asma'u tunda Jadeedah ta cire hijabi take binta da kallo tana analyzing kowane curve na jikin Jadeedah dan ma sha Allah,ta tashi ta isa gaban madubi tana duba kanta duk da itama tana da nata amma na Jadeedah was on another level tsuki taja tabar gaban madubin ta koma ta kwanta
Ina tsaka da magana da Mama naji Muryar Jay d'' Bee zoki ban kaya in sa!" na miƙe na fita zuwa ɗakin mu na tsaya daga gefen ta gaban wardrobe ɗina ban yarda na kalle taba na jawo wata doguwar rigar atamfa ja na miƙa mata
'' na gode ƙawar!" Murmushi nayi, ta karɓa ta tsaya a wata yar kwana ta canja duk da maneji tayi dan kayan sun matse ta fiye da ƙima bayan ni har yawo nake cikin su
gashinta dake naɗe cikin hijabi ta saki ya sauko har zuwa mazaunan ta baƙi wulik ko daga ido mutum yasan ba ƙaramin laushi ne dashi ba,na kafe ta da ido ko ƙiftawa banyi
wannan shine karo na farko dana taɓa ganin gashin Jay D,kullum a makaranta daga fuska sai tafin hannun ta nake gani zan iya rantsewa ko ƙafarta ban taɓa gani ba Asma'u dake kallo daga gefe ta tashi zaune daga kwancen da take...
'' kai...ashe haka gashin ki yake da tsawo?" Hannu tasa tana baza shi tace '' ji nake kamar insa almakashi in yanka da badan ummi dake hanani ba wallahi dana aske shi''
Na matsa inda take ina taɓawa nace '' ai ko dana sa bulala na miki raɗam..in zane ki yanda ko tafiya ba zaki iya yi ba!" Tayi dariya
''.dama ace idan mutum ya yanke gashin shi zai iya ba wani da kin bani ai!"
Na faÉ—a mata ina auna tsawon,ita kam tayi sa'a ga kyau'n fuska na hali da kuma na jiki. Allah ya kashe ya bata....
Asma'u tazo itama tana taɓa sumar tana gyaɗa kai Jay D bata ce mata komai ba..'' Bee ki kamamin mana kalba biyu! Ko tsoro biyu irin na turawa!"
Na nufi ƙofa '' bari inyi sauri inyi wanka sai inzo in miki!" Na ɗibi ruwa na wuce baye,na cika kofin wanka na juye a kaina ruwan na sauka zuwa sauran sassan jikina haɗe da hawayen da nake ta riƙewa a ɗaki
Ina kallon jiki namusamman ƙirjina da har lokacin bai canja ba kamar yanda ƙirjin mace yake kasancewa idan ta fara fitar da uhm uhm ai kun gane ko? To nima haka nawa yake amma meyasa? na kalli gefe da gefe na da kuma bayana duk a shafe ba kamar nasu ba, nita dabance? Ko akwai inda nake yin ba daidai ba a addu'a ta? Meyasa nima bazan samu irin abinda suke dashi ba? Kafin in sani na shiga gwada kaina dasu na manta da maganar Malama Hafsah comparison is the thief of joy,ina ƙara tuna duk addu'oina na baya. na duƙe a wurin ina kuka ƙasa ƙasa ina jin na tsani kaina da kuma rayuwa ta ko kallon kaina bana son yi na daɗe a bayen kafin na fito
Nayi alwala na shige ɗaki cike da jin kunya Asma'u ta tashi ta fita Jadeedah kuma sallah take a gaggauce na shirya cikin irin kayan dake jikin Jay d na kalli kaina a madubi ƙunci na ƙara turnuke ni da sauri na ɗauki hijabi nazo na tsaya gefen ta na kabbarta sallah
Na daɗe ina addu'oi na riƙe hawaye na kada aga ina kuka a tambaye ni bani da amsa
Bayan na gama na daÉ—e zaune a wurin, Jadeedah ta tafi É—akin Mama sai da tayi sallama mama tabata izini sannan ta shiga kamar yanda ta faÉ—a kuwa ta tsara zance har mama ta yarda da In tafi gidan nasu in kwana data gayamin banyi mamaki ba
Ta lura da yanayina amma bata tambaye ni mai ya faru ba ina son hakan game da ita tana da hankali bata matsamin da tambaya a irin wannan halin sai dai kawai inji tana zayyano min dalilin daya sani a yanayi...tana da
ðŸ: observation
Tana da obzabeshon sosai...miƙar dani tayi muka isa bakin madubi na shiga gyara mata gashinta idona kafe a kanta naƙi yarda in kalli ƙasa da hakan
Asma'u ta shigo itama ɗaure da towel dai duk sune nice a baya meyasa ni? naji kuka ya fara taso min saukar hannun Jay D a nawa yasa na fahimci abinda ke zuciya ta ya fara bayyana a fili,nayi ƙasa da idona hawaye na barazanar saukowa murza hannu na ta farayi,da ƙyar naja dogon numfashi na mayarda hawayen na sakar mata murmushin da yafi kuka ciwo itama ta mayar min da mai sanyi
Bayan duk mun gama komai muna zaune muna hira aka dawo da nepa, dukan mu É—akin Mama muka wuce, tv'n na kawowa da sauri nasa tashar yan china daidai ana fim É—ina ' waild fulawa ''
''.ashe kema kina kallon wannan series É—in?"
Jay d ta faÉ—a da murna
'' sosai ma kuwa..kuma wannan mai sa baƙaƙen kaya mugun nan shi nafi so!" Na bata amsa
'' bani mukashe!"
Ta faɗa tana ɗaga hannunta...muka haɗe itama shi take so Asma'u ta taɓe baki
'' Jadeedahtu gyaran gashin ki yayi kyau masha Allah" Mama ta faÉ—a tana kallon tsoro biyun dana yima Jay D fuskar ta kamar irin na yar tsana
'' na gode..Bee tayi min!" Ta amsa Mama