Sashe 10
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'' oh.. Allah sarki...so you're a witch?" Ɗaure fuska nayi dan bana jin turanci can can...kuma ban gane abinda ya faɗa ba...sai na gyaɗa kai kawai ..na ɗauka ya rabu dani...ƙara matso ni yayi..nima na sake shigewa cikin bango..ƙafafuna manne da bangon...yanda yayi min runfa da jikinshi idan mutum ya shigo bama zai san da akwai ni a wurin ba...
'' i surprisingly have a thing for witches with gray eyes...can I kiss you?" Batareda na fahimci abinda ya faɗa ba na shiga gyaɗa kai kamar ƙadangare nidai kawai ya barni in tafi...tsawon shekarun dana kwashe ina aiki a hotel ɗin nan ba'a taɓa rutsani har haka ba...sai dana haɗu da wannan kyakkyawan ɗan tashan...har lokacin idona sunƙi komawa dai dai..duk na gama tsora ta...na ɗauka nan ne ƙarshe yanzu kawai zai yi dariya ya juya ya koma wurin abincin shi amma a mamakina sai
ya sauke yatsan shi saman laɓɓana yana kallon cikin idona wani irin abu naji yana min yawo tun daga tsakiyar kaina har yatsun ƙafafuna kuma naji kamar jikina ya mutu, karkace kanshi yayi tare da lumshe ido zai sumbace ni,
wata irin gigitacciyar ƙara na saki,tare da buga mashi guiwata tsakanin ƙafafun shi na kwasa da gudu..nabar shi da durƙushewa ƙasa yana zagi da turanci...yau kallon fim ɗin China yayi min rana...
Kamar makauniya naji naci karo da mutum ..kuma wannan mutum ɗin bai yi komai dan taro ni ba lokacin da nayi tangal tangal kafin ɗuwawuna su sha ƙasa
runtse idona nayi saboda zafi, kafin na buɗe su ina kallon mutumin dake tsaye gabana,saye da ƙananan kaya riga mai dogon hannu ash color wando baƙi ya ɗan tattare shi daga ƙasa fuskar shi sakaye da face mask...sumar kanshi baƙa wulik ga wani sihirtaccen ƙamshi da yake zubawa...yana kallona da baƙaƙen idonshi kamar na maijin bacci da sauri na miƙe ina kallon shi a masife nace '' baka ganine? baka ga ka ture niba?idan wannan ramen dake fuskarka bai aiki,abunda xaka iyayi dan taimakon kanka da kowa ma shine ka zauna cikin ɗaki basai kazo kana bangaje mutane ba!'' na ɗanyi nadamar yanda na zage shi amma ban bashi haƙuri ba..sai ma
nayi tsammanin yabani haƙuri amma sai cewa yayi '' Get.Out.of.My.Way!" yayi maganar da wata irin ƙatuwar murya idonshi suka ƙanƙance a kaina...daga yanayin maganar shi zaka san ba ɗan Nigeria bane ..abinda ya faɗa aiko wanda baije makaranta ba aka cema get out yasan abinda ake nufi gyara tsayuwata nayi gaban shi nace '' bazan matsa ba ka..!" ban gama sentence ɗina ba ya wani bangajeni gefe saura kaɗan in faɗi yayi tafiyar shi.. sakin baki nayi kafin naja wata gora dake saman wani cart ɗin abinci da aka aje a hanyar na saita bayan kanshi na jefe shi...sai ga ƙeya.. juyowa yayi yana kallona, hannu dunƙule kamar zai naushe ni
gwalo nayi mashi na kwasa da gudu ina dariya aini ɗin bata wasa bace... ganin lokacin sallah yayi yasa na wuce masallaci bayan na shiga Baye nayi tsalki saboda yanda mutumin nan yasa nayi fitsari a wando,ana gama sallah na dawo na cigaba da aiki..sai ƙarfe tara shift ɗina ya ƙare har nayi sign out naga Macijin sari ka noƙe da wata mata zaune a wani table....jinayi haushi ya kamani dole inyi wani abu akan abinda ya faɗa min ɗazu
tare suke saukowa daga stairs cikin shiga iri ɗaya baƙaƙen riguna da baƙar jacket a sama sai baƙin wando jeans suna zuba ƙamshi, har yanzu da face mask baƙi a fuskar shi Ibrahim kuma magana yake masa idonshi ya sauka akan tuwo data karɓi plate daga hannun wani waiter tana tafiya kamar bada gangan ba ta juye duk abinda ke cikin plate akan Macijin sari ka noƙe dake riƙe da hannun yarinyar da suke tare...daga gani yarinyar bazata wuce sa'ar Tuwo ba... tsayawa sukayi su biyun suna kallo... Macijin sari ka noƙe ya wani miƙe kamar wanda aka watsa ma ruwan sanyi '' Abeeda wannan wane irin rashin hankali ne?" kukan ƙarya Tuwo ta fara tana faɗin bada gangan bane amma ya zaƙe sai faɗa yake mata
ganin irin kallon da mutanen wurin ke masa kamar na wani mara tausayi yasa ya shanye fushin shi sai kuma a fusace yabar restaurant É—in yarinyar da yazo tare da ita ta matso wurin Abeeda '' Nagode!" ta raÉ—a ma Tuwo a kunne kafin ta bar wurin
'' i like that girl!Ro..?" Ibrahim ya faÉ—a ma gayen dake kusa dashi amma koda ya juyo yaga wurin babu kowa... murmushi yayi yabi bayanshi..
Batareda wani damuwa ba nima nafita daga restaurant ɗin ina tafiya ina tsalle tsalle iskan hadarin na ƙara ratsani,ni tuni ma na mance da wannan mutumin da muka haɗu dashi a hotel '' hi kyakkyawa '' naji Muryar shi daga bayana da sauri na juyo ina kallon shi dan harabar hotel ɗin akwai haske sosai kamar rana..take na gane shi, haɗe rai nayi na juyo a masiface nace '' yawwa ɗazu dana shigo ɗakin ka shine zaka wani yimin runfa kana laguda ta ko? toh bari kaji niba yar iska bace idan wani abu ya sake haɗa mu ka taɓani sai na tsinka ma mari a fuska !" Ya shafa fuskar shi tare da matsowa dab dani ba shiri naja baya
'' ai saida na tambaya idan zan iya sumbatar ki,kika ce eh remember?" É—aure fuska nayi
'' taya ni ban tuna ba?"
'' not my fault if you have short memory!" ya kashe min ido...naji kamar in soka mashi yatsa cikin ido...naja tsuki ƙasa ƙasa zan bar wurin ya jawo ni ya rungume da ƙarfi
da duk ƙarfin da Allah yayi min na gantsara mashi cizo a gefen wuya
'' ahhh!!" ya sake ni tare da ja baya...da wannan damar nayi amfani zan gudu ya damƙo hijabina,ba shiri na ƙame ƙam...
''ki gudu mana!" Ya raɗa min a kunne..oh ni tuwo na shiga uku waye wannan mutumin wai? gabana sai faɗuwa yake...ƙamshin turaren sa ya dabaibaye ni kamar ni na shafa.. iska na haɗiye ina kalle kalle koda Allah zai sa wani ya kawo min ɗauki
'' ashe ke vampire ce? a freaking vampire in a modern society!...'' sai yayi dariya tare da sakina ya zagayo gabana hannu a aljihu...
Autumn: what an absolute moron!
Abeedah: ashe kin gane...ji nayi kamar in naushi muguwar fuskar shi
'' Meye sunan ki'' ya dawo dani daga duniyar tunanin dana shiga..ko kaÉ—an bai burgeni ba..na É—age mashi kafaÉ—a
'' nima ban sani ba!" na amsa ina ja baya..hannu ya miƙa zai ɗage min hijabi
'' wai meye haka?" na faÉ—a murya a sama
'' sunan ki nake so in gani...''
''.sunana Khadijah!" Na faɗa mashi sunan daya faɗo raina...gyaɗa kanshi yayi ya zaro wayarshi daga aljihu ya miƙa min
'' your digits!" Daga shi har wayar tashi binsu nayi da kallo ƙwaƙwalwa ta na loading a 360...tunda muka haɗu sai turanci yake ni kuma baji nake ba...
'' lambar ki!" Ya É—an waro min idonshi...É—auke nawa nayi nasa mashi lambar da ban san kota waye ba..mufa bamu da waya..sai ta mama dake ringin sau É—aya a shekaru masu yawa...har da saving na mashi cikin style
''Cardy..I like the sound of it..sai munyi waya..goodnight ..Khadija!'' ya sakar min Murmushi kafin yayi gaba ya barni tsaye...
ajiyar zuciya na sauke tare da fashewa da dariya '' ace wacce zai kira É—iyar soja ce...kuma babanta ya É—auki wayar a wannan lokacin?" wata sabuwar dariya na kwashe da ita kafin nabar wurin kada ya dawo ya same ni
koda na koma gida Mama na zaune a tsakiyar gida suna hira itada da Asma'u na kuma san ni suke jira '' salama alaikum '' nayi sallama na shiga '' wa'alaikumssalam '' Mama ta amsa da sauri nazo na faɗa jikinta '' Mama antaso!" '' maraba maraba!" Mama ta amsa min, miƙewa nayi na shiga kitchen na zubo abinci Batareda na cire hijabin ba nashiga ci..
su biyun suka kafeni da ido...''.akwai wani abu ne?"
'' ina kika samu wannan turaren...ƙamshin sa irin na maza?" Mama ta ƙanƙantar da idon ta...sarƙewa nayi da abincin dake cike a bakina...da sauri Asma'u ta kawo min ruwa amma naƙi sha...kamar zan mutu amma kuma tunanin ƙaryar dazan sharara nake..mutumin nan ya gama dani wallahi
Mama taƙi dena kallo na...sai dana gama tarin ido jawur nace '' zainab ta kawo..na yayanta ne...''
saida mama tayi min irin kallon da ban san ma'anar shiba ta gyaÉ—a kai..
ina tsaka dacin abinci aka fara ruwa ba sallama,da sauri muka faɗa ɗaki '' ruwa ba sallama ba iska". inji Asma'u Mama tace '' shikuma hadarin da yake nan baki gani ba ko?"...saida na cinye abincina tass sannan na ɗauki zane na fito waje rataya zanen nayi a bakin taga na kwaɓe uniforms ɗina ya rage daga Ni sai pant da singlet na shiga cikin ruwa...ina tsalle tsalle
'' waini Allah yaushe Tuwo zata girma?" inji Mama tana shafa kan Asma'u dake saman cinyarta...sai wurin ƙarfe goma sannan na cire pant ɗin da singlet na ɗaura zani na shiga ɗaki ina rawar sanyi Mama ta bini da ido kasancewar fitilar da aka kunna yasa nake ganin inda nake saka ƙafa...wata doguwar riga rabin cinya nasa na saka pant na faɗa saman gado,Mama ta gyara ma Asma'u kwanciya sannan ta rufe mana ƙofa ta kwanta... matsawa nayi kusa da ita na riƙo hannunta '' ke wai yaushe zaki girma?" ta tambaya tana ƙwace hannun ta,turo baki nayi '' to Ni ban iya bacci saina riƙe wani abu!" tsuki taja ta juya min baya kawai sai na rungumeta tabaya...lumshe idona nayi inaji yanda ruwa ke dukan kwanon mu...har bacci yayi gaba dani