Sashe 1
Ruuyaa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

PROLOGUE
Wani lokaci, mutum ba ya tsayawa gaban madubi ne don ganin fuskarsa kawai… yana tsayawa ne don yin hukunci da kansa.
Kin taɓa tsayawa a hankali ki kalli kanki? Ba da ido na wucewa ba, amma da idon da ke neman aibi a kowane sashe na jiki—kamar duk abin da ke jikinki yana buƙatar gyara kafin a ce kin isa a kalle ki?
Pimples da ke fuskarki su fara zama kamar sun fi Æ™arfinki magana. Sauyin jiki ya fara zama kamar tambaya mai nauyi wadda ba ki da amsa. Wani É“angare na zuciyarki yana tambaya: “Me yasa ni ban zama kamar su ba?â€
A waje kuwa, duniya na tafiya. Wasu suna dariya cikin sauƙi, suna tafiya da kwarin gwiwa, suna jin kamar komai yana musu daidai. Amma ke… kina jin kamar kowace ido da ta kalle ki tana ɗauke da hukunci a cikinta—ko da ba gaskiya ba ne.
Kin taɓa jin bugun zuciya yana ƙaruwa idan kina tafiya kusa da mutane, hannunki a gaban hijabinki ba don ado ba, amma don ɓoye abin da kike jin zai jawo kallon da ba ki so?
Kin taɓa jin kalma daga wani ta zama kamar dutse a zuciya? Kalma ɗaya kawai… amma ta iya canza yadda kike ganin kanki na tsawon lokaci. Har sai zuciya ta fara maimaita ta ko da babu wanda ke magana.
Sannu a hankali, mutum zai fara zama mai kallo a rayuwarsa—ba mai rayuwa ba. Yana kallon kansa daga nesa, yana kwatanta kansa da kowa, yana rage kansa a duk inda ya ga wani ya fi haske.
Wasu mutane suna kiran hakan “rauni.†Wasu kuma ba sa ganin shi ma. Amma ga wanda ke ciki… yana zama nauyi da ba a gani.
Ni Abeedah…
Na san wannan nauyin.
Na san yadda kalma ɗaya za ta iya zama kamar tana bin mutum har cikin dare. Na san yadda mutum zai iya fara jin kamar ba shi da kyau, ba shi da ƙima, ba shi da wani abu da zai sa a tsaya a kalle shi sau biyu. Na san yadda hankali zai iya zama kurkuku—inda mutum kansa ne mai tsare kansa da tunanin wasu.
Akwai waɗanda suka koyi ɓoye rauni da murmushi. Akwai waɗanda suka koyi yin dariya duk da zafin ciki. Amma akwai wasu—waɗanda komai ke shiga musu kai tsaye, su riƙe shi, su maimaita shi, har ya zama gaskiyarsu.
Ba kowa ne yake neman soyayya kawai ba.
Wasu suna neman a gan su ne.
A yarda da su.
A ce suna da muhimmanci.
Amma abin da ke da ban tsoro shi ne—lokacin da wannan buƙata ta fara cin mutum fiye da yadda ya ke sarrafa ta, sai ta fara mayar da shi baƙo a cikin kansa.
Ni ba cikakkiyar jaruma ba ce. Ba ni da labarin da aka riga aka rubuta da nasara. Ni ce sakamakon duk abin da na ji, duk abin da aka faÉ—a min, da duk abin da na fara gaskatawa game da kaina.
Kuma wannan ba labarin kamala ba ne…
Labarin ne na girma.
Labarin ne na yadda zuciya ke karyewa a hankali, sannan ta fara neman hanyar sake haÉ—uwa.
Idan ka bi wannan labari, ka shirya jin abin da ba a saba faɗa ba—domin wannan ba labarin kyawawan kalmomi ba ne...Labarin gaskiya ne!!
Sometimes the hardest person to love is yourself... Ni Abeedah na fahimci hakan
Story about self esteem and self love over coming challenges and learning to love yourself even though SOME TIMES THE HARDEST PERSON TO LOVE IS YOURSELF BUT YOU LEARN TO LOVE ANYWAYS...
RU'UYAA
The dreams we never lived
By Autumn 17 ðŸ ðŸ
A love that grew in_silence
Aheart that hoped to be chosen And a destiny that has been decided
SADAUKARWA
Ga duk wanda ya taɓa yin mafarki mai girma... amma rayuwa ta rubuta masa wani labari daban.
Ga waɗanda suka rasa kansu suna ƙoƙarin zama abin daduniya take so su zama.
Ga waɗanda suke yaƙi da insecurities,low self esteemow self worth,self love da self-doubt a kullum, duk da cewa suna nuna ƙarfin da ba su ji suna da shi ba.
Ga duk wanda ya taɓa kallon madubi ya ga flaws kafin ya ga kyawunsa.
Ga waÉ—anda suke É—auke da ciwon da babu wanda ke gani..
The ones who laugh the loudest, yet cry in silence.
The ones who keep saying "I'm fine" when their hearts are anything but fine.
Rayuwa ba koyaushe take ba mu abin da muka nema ba.
Sometimes the prayer remains unanswered.
Sometimes the door remains closed.
Sometimes the dream stays a dream.
Kuma wani lokacin, abin da ya fi cutarwa ba rasa abin da kake so ba ne...
It's losing yourself while chasing it.
Wannan littafin ba wai game da perfect people ba ne.
Yana magana ne game da real people.
Mutanen da suke jin tsoro.
Mutanen da suke kuskure.
Mutanen da suke son a ƙaunace su.
Mutanen da suke neman kansu a cikin duniya da ke sa su ji ba su isa ba.
Idan ka taɓa jin cewa baka isa ba...
Idan ka taɓa jin kamar kowa yana tafiya gaba yayin da kai ka tsaya a wuri ɗaya...
Idan ka taɓa rasa wani ɓangare na kanka saboda neman karɓuwa daga wasu...
Then this story is for you.
May these pages remind you that your scars do not make you less beautiful.
Your failures do not make you less worthy.
And the dreams that never came true do not define the rest of your life.
Because sometimes...
the greatest journey is not finding love.
It is finding yourself.
— Autumn 17 RU'UYAA: The Dreams We Never Lived ✨🌹
â¤ï¸ðŸ“–✨
NOTE:Free pages zasu kasance a first person's point of view (1st POV) paid pages kuma narrative point of view
SHIMFIÆŠA...
OSLO, NORWAY...
05:30 P.M
Garin yana cikin duhu mai nauyi.
Ba duhun yamma kaɗai ba ne,wani irin duhu ne da yake sa komai ya yi kama da ba shi da rai. Sama ta lulluɓe Oslo da gajimare masu kauri, hasken fitilun titi kuwa ya narke cikin ɗigon ruwan sama kamar ƙananan fitilu da aka manta a tsakiyar ruwa.
Ruwan ya ɗan tsagaita, amma ƙasa ta riga ta jiƙe.
Mutane na ta gudu daga nan zuwa can, wasu suna neman mafaka a ƙarƙashin rumfuna, wasu kuma suna tsaye a kan gefen titin ba tare da sanin inda za su dosa ba. Hanyar kwalta ta yi sheƙi da ruwa, tana ɗaukar hasken manyan gine-ginen kamfanoni da gidajen da ke gefenta. Bishiyoyin gefen titi suna jijjiga a hankali saboda iska, kusa da su kuma akwai dogayen kujeru da ake zama domin hutu,amma yau babu wanda ya damu da zama.
Kowa yana da abin da yake nema.
Kowa yana da abin da yake ji.
A kan manyan billboards da aka jera a wurin, ake hasko hotunan hatsarin jirgin saman da ya faru jiya da rana.
Hotunan sun sake maimaituwa.
Jirgi.
Wuta.
Hayaki.
Taro.
Kuka.
Mutane da dama sun taru a wurin, idanunsu manne da allon. Wasu suna kuka a fili. Wasu kuma sun sunkuyar da kawunansu, kamar har yanzu hankalinsu bai amince da abin da ya faru ba. Wata mata ta riƙe baƙin cikinta da hannaye biyu tana kuka ba tare da ta damu da yayyafin ruwan da ke sauka a fuskarta ba.
Hayaniyar jama'a ta gauraye da sautin motoci da iska.
Amma a tsakiyar wannan hayaniyar
akwai wata tsaye ...ba ta jin komai.
Ta tsaya can nesa da taron... kamar kasancewa daga nesan zai sa tafita daga cikin jerin wa'yanda abin ya shafa
Sanye take da baƙar coat, ƙaramin mayafi ya rufe kanta da wuyanta. Hannayenta sun zurfafa cikin aljihun coat ɗin, amma ba don sanyi ba.
Saboda hannayenta sun kasa daina rawa,
Idonta sun yi jajir,Ba wai saboda rashin barci ba,ba saboda sanyi ba.
Saboda abin da ta gani a kan allon ya riga ya shiga inda babu ruwan sama da zai iya wanke shi.
Ta kalli hoton jirgin na É—an lokaci sai ta É—auke idanunta, ta sake kallo,ta sake kau da su.
Kamar idan ta ƙi kallon hoton, abin da yake nufi zai daina zama gaskiya.
Amma gaskiya ba ta taɓa bukatar izinin mutum kafin ta karya shi.
Numfashinta ya fara fita da sauri, gajere-gajere. Ƙirjinta na matsewa kamar an ɗaure shi da igiya.
Sai ta juya ta fara tafiya
Mataki ɗaya,na biyu,na uku kafin ta ƙara sauri,ba ta san inda take zuwa ba.
Ta dai san cewa dole ta bar wurin
dole ta bar waÉ—ancan hotunan
dole ta bar muryoyin mutane
Dole ta gudu daga kalmar da babu wanda ya faÉ—a amma take ihu a kunnenta tun jiya
ya tafi..a'a! hakan ba daidai bane...zai dawo..wasa yake da yace bazai dawo ba...wasa yake that most be it!!!amma ina yake???
Hawaye suka fara zubo mata,tun tana sharewa har ta fashe da kuka.
Ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, tana jin kamar an cire zuciyarta daga cikin kirjinta aka ajiye ta wani wuri da ba za ta iya kaiwa ba... numfashinta kamar irin na mai asthma
Sanyin ruwan sama ya daki fuskarta,amma bai kai inda ciwon yake ba...ko kusa
Domin akwai wasu ciwon da ba'a gani...da ba sa konewa a fata.
Suna konewa a cikin mutum...babu halin sosawa bare kaji sauƙi
Ta bi wata ƙaramar hanya da babu kowa a cikinta. Takalmanta suna taka ruwan da ya taru a kan interlock, amma ba ta ma lura da hakan ba.
Hawayenta sun ƙi tsayawa,ta goge su,sabbi suka zo,ta sake gogewa.
Sai wasu suka sake gangarowa..
Kamar zuciyarta ta yanke shawarar cewa babu abin da zai iya hana ta yin kuka...kukan girman rashinta...
Har ta isa wani wuri mai natsuwa.
Akwai wata babbar bishiya a wurin—cike take da ƙananan fararen furanni.
Iskar sanyi na motsa rassanta a hankali, furannin suna zubewa ɗaya bayan ɗaya a ƙasa.
A gabanta kuma akwai teku.
An katange bakin tekun da ƙananan tubalin bango, ruwan yana bugawa a hankali yana ja da baya.
Gaba da baya... batareda tsayawa ba.. tare da iska mai sanyin dake ratsa ƙasusuwa
Kamar wani abu da yake ƙoƙarin komawa inda ya fito, amma ba zai iya ba.
tsayawa tayi,ta kalli tekun... tana ji inama zata iya mayarda rayuwar ta baya koda na yan daƙiƙun daya kasance tare da ita ne...