← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 62

Sashe 9

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

gadin yasan ba lafiya. Da Gudu gudu yanufi part din Mahaifiyarsa da suke kira da Hajja. Hamshakiyar Kyakykyawar mace Fara tasKallo daya zaka mata ka hango tsantsar kamar su da Abdulmalik din, Tana zaune cikin hadadden palournta daya gaji da haduwa tamkar fadar wata sarauniya tsabar yanda aka tsarashi kai dagani kasan Naira tayi kuka a gurin. Sanye take da wani hadadden Lace Wanda ko ba'a fada ba Ya lashi daruruwan Nairori daga siyanshi har zuwa dinkin Bubu irin na manyan Mata da suka ci suka tada kai da akayi masa. Kyalkyalin da wuyanta da hannayenta sukeyi ya isa (nidai nace idan aka sace Hajja wannan barawo ya gama yin kudi). Kwalliyarta sak irinta isassun matan SHUWA. Hajiya FATTU kenan Uwar gidan ALH KAMALU DALA. Hajia fattu ko muce Hajja Itace Mace ta Farko cikin jerin matan auransa Alhaji Kamalu guda hudu kuma mahaifiyar Abdulmalik. Macece mai matukar izzah, takama, Da Isa. Tana da son kanta Hakanan bata hada komai da soyayyar Yayan ta ba. Takan bata da mutum duk yanda suke Indai har ze taba mata Yaya dan kwata kwata bata ganin lefin yayan ta. Tsabar Bala'inta yasa shikanshi Alh Kamal din yake shakkarta Wanda har wasu suke gani Kaman asirine sedai ko daya wannan ba halinta bane Dan tace ba wani Malamin karya dazata bawa kudinta yai mata abinda bata yiwa kanta ba. Hajja Fattu kenan.
Chapter 9 · 0% Book details