Sashe 2
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take tana sauron wakar Eidsheren me taken shape of you harta isa inda tasaba yin parking ta ajiye motan sannan tashiga class. 2:00pm tai closing suka fito suna hira akan bikin Aysha daya ke karatowa "kunga wannan hirar tamu ba karewa zatayiba kuma aron mota nayo kar ayi fushi gobe a hanani "Afeeya ce ta amsa mata da cewa "Ai kedai kin banu wallahi Ina taki motar duk nacinki dai Mumcy bazata hakura tabar miki tata ba" "kamar kuwa kinsan plan dina So nake Abbah ya gaji da rabon fada yasiyamin irinta" daidai Sanda suka karasa gurin motar sedai me wani yayi parking bayanta in a way that bazata iya fita ba seya janye tasa motar. Baba tsoho kamar yanda suke kiran tsohon dake zama agurin yana Dan kular musu da motocine ya taso yana cewa"yarinya ta an tashi ko?" "Eh wlh Baba ko kaga Wanda ya ajiye wannan motar?" Tanuna masa latest BMW din dake pake bayan ta ta. "Eh aikuwa me wancan office dinne Dan ina sallah yazo kafin kuma in idar yabar gurin". Jitayi ranta ya baci ta tsani abin haushi "inba shirme ba how can you block some ones car ko angaya masa zama nazoyi makaranatar".fuu ta nufi office din da Baban ya kwatanta mata bata ko saurari Maryam dake sanar mata da office din waye ba. A cukule ta karasa kallon kofar tayi taga an rubuta Dr AA Galadima. Knocking tayi Amma taji shiru kuma dae dae zuwanta taga wani yafito daga ciki harta tambaye shi ya shaida mata da mutum a ciki hakan yasa ta saka kai kawai tashiga. Yana zaune akan kujera ya juya baya da waya akunnansa, yanda yake maganarne ya tabbatar mata da mace yake sedai kalaman daya ke amfani dasu sam basu yi kama da na soyayya ba hasalaima sun fi kama da cin fuska ko wulakanci duk da muryarsa a kasa take. Gashin kansa takalla tayasha gyara style din askin yafita sosai aranta tace "Kaman Abdul dina". Tunda ta Shiga Kallo daya yai mata ya ci gaba wayarsa, ganin abinnasa harda rainin wayo yasa ta cewa "Sir wurinka fa nazo" akalla yakara kusan minti 5 sannan ya kashe lokacin Hamdah tagama cika fam. "Yes inajinki" ya amsa mata cike da izza. seda ta harareshi ta gefen ido Wanda sarai yana lura da duk wani cuna baki datakeyi sannan tace "Nazo zan dauka mota nane..."se akacemiki tana gurina" yai saurin katseta. Wannan karon harda murguda baki tace sannan race "Niba haka naceba nadaiga Mota a gurin kuma ance taka ce". Gefen table din yanuna mata tareda cewa "You can take the key ki matsar da ita seki kawomin "kallon sa kawai tayi tana jinjina rainin hankali irinna Guru kamar zatayi magana sedai kome ta tuna oho ta saki murmushi mai ma'anoni dayawa tareda cewa "Ok Sir" tadauka tafice. Tana tafe tana murmushi harta karasa inda tabarsu Maryam, kallonta suke da mamaki ganin dadewar datayi gashi kuma tafito da fara'a. Maryam ta cillawa key din motar Mumcy tace "drive it home please "lokacin da take kokarin kunna motar Guru. Tsabar mamaki kasa magana sukayi Afeeya data gama hango abinda ke shirin faruwa tai saurin tareta ta hanyar cewa "Aa Hamdah karki haka wata rigimar tafi gaban wasa" "Naki kallo daga kaina baze kara rainawa wani hankali haka ba" taja mota fuu tayi gaba abinta, basuda zabi illah suka bita a daya motar Dan tuni Hamdah tafice daga cikin makarantar. ***************************************** *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 Shaf Guru ya manta da lamarin wata Hamdah harya gama abubuwan da zeyi yai shirin tafiya gida. Mukullin motarsa ya shiga nema Amma yace daukeni inda ka ajiye, wani abokin aikinsa ne ya leka office din jin motsin mutum "Dr ashe kadawo dazu naga fitarka Ina ta daga maka hannu baka ganiba". Kallonsa yayi da mamaki aransa yana tunanin yaushe ne ma ya fita "So she took my car" ya fada a fili sedai instead yaji haushi se kawai yaji ta birgeshi kawae, gaskiya tana da liver shi kuma yana son mutum mara tsoro. Wayarsa yadauka kawai yakira drivernsa akan yazo yadaukeshi aransa yace "let see if she will return it". Akan kwanar layinsu suka hadu da Mumcy data gaji da zaman jiranta "su Hamdah kuma yau wa aka tsokano Nidai babu ruwana wlh karma ki lossafani cikin rigimarki. Me tsaya miki kiyi rashin jin baya nan ga kuma yayanku can Baffa yazo". Baki ta cuna takarawa motar wuta aranta tana cewa "ita Mumcy kullum nice mara gaskiya bayan batasan me mutuminnan Dan rainin hankali Yayi min ba ai dai shiya fara tsokanata" guri me kyau ta samarwa motar ta ajiye sannan ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo gidan seya kalli motar dan dae sunsan babu me irinta a gidan, sanin Hali yasa Babu Wanda yabi takan ta bare motar da ta shigo da ita Dan in da sabo Halin Hamdah ne tada zaune tsaye. Seda aka Kwana biyu a tsakani Yah Baffa ya tasata agaba da tambayar Inda ta samo mota. Rasa abin ce mata yayi illa Kallon ta kawae da yake, amsar da tabashi tayi bala'in daure masa kai Wae "Motar Malamin muce" "Shine yabaki aro ko yaya?" "Aa" "Se akayi yaya?" Tiryan tiryan ta labarta masa yanda abin ya faru Tundaga farko. "kyaci ubanki ranar da kika dauko fadan dazesa adaureki shashasha me kalar salahai se masifar fitina azuciya". Cuna baki tayi abinda yazame mata jiki tana kunkuni "Mutum kullum bashida aiki seyiwa mutane fada wae ma meya kawo shi gidan oho". "Ki fada afili mana karamar mara kunya wlh duk Abbah ne ya lalataki inba haka ba tsabar tsaurin ido kidaukowa mutum mota". ita dai ko ajikinta Dan ko ba komai ta koyawa guru hankali" ya taka da kafa ko ya hau lift" ta fada a zuciyarta. Ranar baccin ta tayi harda minshari cike da kwanciyar hankali. Washe garin ranar kasan cewar bata da lecture yasa ta wuni a gida, ido kawai Mumcy ta zuba mata tun tana jiran taga anzo daukar mota har dare yayi taji shiru, gajiya tayi ta tambayeta "Wai Hamdah yaushe zaki mayar musu da motarsu ne?" "In mayar ko suzo su karba?" tabawa Mumcy amsa hakan yasa takama bakinta tayi shiru aranta ko addu'a take Allah ya kawo Abubakar a gobe juma'a Dan shi kadai ke taka mata birki kan duk iskancin da takeyi. fatanta Allah ya shirya mata Hamdahnta Dan fitinar yarinyar tayi yawa kwata kwata bata da tsoro. Ranar Monday 8:00am tai mata a class Dan bata so tabar wata kofa da abu ze hadasu bare ya wulakantata tunda Akwai jikakkiya a tsakaninsu. kamar kullum be kara ko minti daya ba yashiga ajin, idonsa akan ta yafara sauka yadan kalleta for some seconds Wanda har mayun yammata masu kallonsa suka hankalta da inda yake kallo nan fa kishin Hamdan ya kamasu Dan asaninsu babu wata mace data ishi Guru kallo Amma se gashi yana kallon wannan fitsararriyar yarinyar da bata ganin kan kowa da gashi. Ammani Kaman yanda suke kiranta zan iya cewa babu Wanda besantaba afadin BUK both new nd old site. Kasancewarta kyakykyawar mace ajin farko. Fara ce tas koma mu kirata yellow Dan hasken Hamdah har kashe ido yake.bata da tsaho can haka ba gajeriya bace tana dai tsakiya haka girman jikinta sam bata da kiba Amma Allah ya mata kira mai kyau domin saman ta da kasan ta acike yake dam. Babbab abinda ke daukar hankalin Maza akan ta shine kalar kwayar idonta data kasance Grey colour da wani irin sparks Kaman na gold dole in ka kalleta kasake kallo gata da shiru shiru a fuska. Kyanta ya tarar da gayu dukda Hamdah bata kwalliya a fuska amma tana shiga ta burgewa da komai hassadarka dole ta burgeka dan kusan duk wani abin gayu ko kyalekyale na mata a kaf campus din a wurinta ake fara koya. Mutane da dama nayi mata kallon me girman kai kodan rashin shiga sabgar mutane da batayi sefa wadanda suka Santa ko wadanda suke good time ba. ZAHIRIN HAMDAH kenan A badini kuwa sunan da Ake kiranta a gida shine Fitilar sharri Dan Idan kanason siyan balai da kudinka to ka takali Hamdah. Bata da tsoro ko kadan sannan bata san wani abu rufa rufa ba. Gaba gadi take komai nata. Tana tsananin son abinda take so hakanan tana tsananta kiyayyah ga abinda bata so hakanan bata da Wuyar sabo ko kadan in har jininku ya hadu.Wannan itace HAMDAH AHMAD AMMANI a takaice. Awa biyu (2hrs) lecture ta daukesu Kaman kullum bayan yagama ya basu short gun test tareda Assignment. Sit by sit yake bi yana tattara takaddun "Meet me in my office" kunnanta yajiyo mata dai-dai lokacin da yazare ta ta takardar Wanda kafin ta dago har ya wuce illah kamshin turarensa dana mouth fresh dinsa daya barmata. Da harara tabi bayansa ta murguda baki sannan tace "se kazo ka daukeni ae kamar wata yarka kana commanding dina" kasa kasa tayi maganar dan ko Afeeya dake kusa da ita be zama lallai taji me tace ba amma yanda yake watching moves dinta bakinta kawae ya kalla ya gane abinda tafada tsaf, se yai murmushi, da ido ya mata alama da "karkizo zakiga abinda zanyi". Yana fita kuwa ta dane kan desk tana tsarawa kawayenta irin dinki da shigar da zasuyi ranar Dinner Aysha. Agogo ya kalla for the second time kimanin 1hour kenan da barinsa class din. bayan fitarsa sarai yasan basuda wata lecture Dan haka yayi qwafa sannan ya miki ya nufin ajin, Clique members dinta ne zaune Dukkansu Maza da Mata sun zagayeta Banda dariya Babu abinda sukeyi. Labarin wani Bayeraben Professor Abokin Aikin Abbanta a University take basu Dayake sonta. yanda take kwatanta fuskar mutumin Wai dayaga picture dinta seka rantse da Allah tana gurin "I'm telling you Prof Balogun yafi mutuminnan kyau kai A swear ko Obasanjo albarka munin mutuminnan ze iya saka meciki tayi miscarriage Wae shi be yadda ba sona yakeyi" yanda take exergirating Abun ne yake qara basu dariya Shigowarsa tasa kasu yin shiru Dif kaman ruwa ya cinyesu banda Oga Hamda dake kokarin nemo picture din Prof Monkey Tana ci gaba da cewa "wae fa da Abba ya hadamu a waya mugaisa harda wani Babe yake cemin niko dariya nake kaman kaina ya kwance..." daga