← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 62

Sashe 14

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

na zuba a idonta tace "Aa karkimin haka Mum addu'a kawai zaki tayani da ita bani da kowa sai shi, bazan iya rayuwa babu Abdulmalik ba soyayyarsa tabi duk wani bangare na jikina Mumcy cire shi lokaci daya abune me wahala..." *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 Sosai tausayin Hamdah a kama Dr Maryam, lokaci daya duk ta zabge tayi wata irin rama. Ta tabbatar dole ta damu ba abune me sauki a rabaka da masoyinka ba. Tausarta ta shigayi da qoqarin nuna mata da ta fawwalawa Allah komai, babu wanda ya isa ya canza *_RUBUTACCIYAR QADDARAR SA_*. Dan Haka ko da Abbah ya mata Maganar ce masa tayi "Abban yara mubarwa Allah komai, Damu da su babu wanda ya isa ya hana faruwar wannan al'amari in Allah ya nufi haduwarsa haka duk soyayyarmu da ayi in babu Rabon se dai mu hakura". Seda yayi dogon nazari sannan yace "Hakane Dr Allah to ya zaba mata mafi alkairi" ta amsa masa da Amin. Daurewa kawai takeyi harta fara zuwa gurin aikinta, cikin polytechnic take serving ba qaramin qoqari take ba wurin ganin ta cire damuwar komai a Zuciyarta. Kamar kullum tana zaune a compound wayarta abokiyar hirarta a hnnunta. Da tunanin Abdul'ahad ta tashi, wata irin kewarsa take ji kamar me tundazu take gwada kiransa se ta kasa ganin babu sarki se Allah ya sakata yin qundumbalar kiransa kawai sedai as usual wayar a kashe take. Dafa kanta tayi tanajin kaman tayi kuka, ita yanzu a ina zata nemo sa? Maryam ce ta fado mata a rai kota kirata tasan Yusuf baze rasa sanin inda yake ba dan haka kawai ta shiga dialing number Maryam.
Chapter 14 · 0% Book details