← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 62

Sashe 36

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana jijjiga Hajjah dake zaune kaman an ajiye gunki. Kallonsu taringayi daddaya kusan babu wanda baya gurin cikin yayan gidan mata da Mazansu dayawansu kuka sukeyi se masu qarfin zuciyane kadai suma kallo daya zaka musu ka karanto zallar tashin hankalin da suke ciki mutum biyu ne babu a ciki Abdulmalik se Aliyu dayake karatu abroad. Cikeda karfin gwuiwa tareda son qaryata zuciyrta ta karasa tsakiyar falon idonta akan mutumin dake kwance lullube da zanin gado tayi saurin dauke kanta tana so ta goge duk wani mugun tunanin dayake gaya mata Abdulmalik ne Aa kilan Aliyu ne Amma anya kuwa ai kuma Hajia Shuwa ya kamata ta gani cikin irin Halin da Hajja take ciki da haka ta qarasa tayi zaman dirshen gaban gawar da takejin kamar tana janta da mayan karfe. "Abdulmalik" ta furta a hankali dason tabbatar da abinda idonta ya gani, seta maida mayafin ta rufe tana mayar da numfashi kamar wadda tayi tsere. Qara budewa tayi a karo na biyu ta yi saurin juyar da fuskarta tareda runtse idonta, Inama wani ya tasheta ya gaya mata cikin bacci take wannan mugun Mafarkin. Abdulmalik dinta ne kwance fuskarsa fes tamkar ka kirashi ya amsa, farar shaddar daya saka ta dade da rinewa zuwa jar kala sakamakon jinin dake zuba daga jikinsa Wanda har zuwa yanzu be tsaya ba. Allah sarki Hamdah, sai gashi itama tabi sahun Hajjah, gefe ta samu ta makure bata qara cewa kowa kalaba. 11:30am Adaidai lokacin da fadar gomnati ta cika makil da mutane masu jiran zuwan ango a daura aure tuni wasu suka fara tafiya dan suna da uzuri. Duk irin kiran da Alhaji da yayyensa suka ringa yi yana kwance a hotel room din da ya kama be daga ba. Ahmad da bakinsa kamar ze qara tsaho saboda magana yana tsaye akansa ya rasa ya yake ao yayi, kiran wayar Hajja ne ya shigo wayar Ahmad ba shiri ya daga tareda sakata a Handsfree "Ahmad ka gaya wa Abdulmalik ban yafe Nono na daya shaba in har be saki waccan tsinanniyar mayyar data lashe mas zuciya ba sannan kagaya masa koya tashi ya tafi daurin auran nan ko na tsine masa" kit ta kashe. Be saurari Ahmad ba ya fice daga dakin ya dauki motarsa ya fita daga Hotel din cikin tsautayi da qarar kwana daidai ya hau wata Gada ya rasa control din motar ya gangaro haka ta ringa juyi dashi kafin ta kife acan gefen titi kafin mutane sukai masa wani taimako har rai yayi halinsa. Kiran wayar Ahmad da ya shiga wayar wani mutum ya daga, shi ya sahida masa abinda ya faru tsabar rudu rasa me zeyi ma yayi seda ya tattaro yayyen Abdul din sannan suka qarasa inda abin ya faru kafin suje har Yan sanda sun kai gawar asibiti acan suka karbeshi suka wuce da Gawar gida. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Tunda ta zauna ta sunkuyar da kanta bata qara bari sun hada ido da kowa ba. Taqi yarda da abinda ta gani, har a lokacin jira take taji ta farka akan gado alamar mafarki ne, a maimako sema iface iface da suka cika mata kunne. Ko da yangidansu suka iso kallo daya Mumcy tayi mata ta dauke kanta ta samu guri itama ta zauna dan zuciyarta tarigada ta karaya. Tunda taji sakon mutuwar hankalinta yai matukar tashi ba kadan ba. Tausayi da jimamin halin da diyar tata zata shiga kawai takeyi. "Allah sarki Abdulmalik ashe rayuwar ba me tsaho bace anyi gwagwar maya ubangiji Ya karbeka baquncinka, Allah yasa annabi yasan da zuwanka Abdulmalik Allah yasa can din tafi nan" Abinda Abba ya fada kenan yana juya kansa cikin matuqar kidima. Mutuwar ta gigitashi kamar Dan cikinsa ya rasa maganganunsu na qarshe a jiya da daddare dajaje gaisheshi kamar yadda ya saba duk Juma'a, sun dade sosai suna magana akan wani project dayake so yayi akan Manfetur, "Idan Allah ya tabbatar da abin nan to ina gaya maka nan da shekara biyu sedai kaga sunanka cikin Top 10 richest Men in Africa" Abban ya fada masa cikin sigar tsokana se yayi dariya sannan yace "Abba to waya sani ko zamu ga gobe ma bare wata shekarar" da wannan sukayi sallama ya tafi. Wani palour daban aka ajiye gawar bayan an gama shiryashi. Umar ne yashiga inda matan suke yace suzo inji Alhaji Babba suyi wa Abdulmalik sallama za'a fita dashi inda dubban Jama'a ke dakon yi masa Sallah. Nan fa sabon kuka ya fara seda Wani Kawunsu ya tsawatar musu sannan suka ringa zuwa sunayi masa Addu'a. Hamdah dake zaune bata da niyyar tashi har kusan kowa ya gama se Goggo Habiba ta kama hannunta tace "Daurewa zakiyi Hamdah Allah kadai yasan yaya kikeji daure kije kiyiwa mijinki addu'a ita yafi buqata a yanzu sama da komai itace babbar soyayyar da zaki nuna masa" bata mata musu ba ta mike duk suka bita da kallon tausayi. Har kan gawar ta kaita sannan ta saki hannunta. Durqusawa tayi a gefensa ta dora hannunta na dama akan qirjinsa, karon farko tun bayan data samu baqin labarin tayi magana "Dana sani ban tayarda hankalina ba, dana sani na qarbi kaddarar data zo mana nasan da kaima kayi hakuri ka karbeta amma babu wanda ze kankare _Rubutacciyar qaddararsa_. Mutuwa dole ce amma Abdul tayi sauri ta dauke ka a lokacin dana fi buqatar rayuwa dakai" se ta dakata ta share siraran hawayen da suka zubo mata, jarumta ta aro ta sakawa kanta ta shiga karanto masa Addu'ar da Annabi ya koya mana da muyiwa mamaci, ta dade tana masa addu'a da roqa masa rahamar ubangiji da saukin tsananin kabari. "Ya Ubangiji Abdulmalik bawanka ne me yawan ibadah, me yawan azumi, me haquri, me kyakykyawar mu'amala. Abdul ya kasance me biyayya ga iyaye ya sauke haqqin aure, ya ubangiji kayi masa sakayya da mafificin lada ka bashi aljanna madaukakiya badan ayyukansa ba sedan ka kasance me rahma. Ya ubangiji ka kyautata makwancinsa ka tarbeshi kana farin ciki da dawowarsa gareka ka haskaka masa kabarinsa da haskenka, ka shayar dashi iska daga ni'imarka ni kuma ka bani haquri da juriyar rashinsa...." Seta kakare saboda numfashinta da taji yana barazanar barin jikinta kawai seta sulale ta kwanta ajikin sa. Da Amin su ringa amsa mata babu wanda bata birge ba a gurin. Fauziyya ce ta qarasa ta dagata daga jikinnasa tana kuka tamkar ranta ze fita se gashi wai Hamdan ce take basu hakuri akan su dena kukan. Lokacin da aka fara kokarin fita dashi domin yi masa sallah sai a sannan Hajjah tafasa wata kara tareda riko gawar tana cewa "Na shiga uku na kashe Dana dakaina, Abdulmalin kayafemin, kakance me tsananin biyayya a gareni amma na biyewa son zuciyata akan naka muradin dama ka fada min amma na toshe kunnena naki jinka yau gashi son zuciyar ya kaini ya baroni na hanaka zaman lafiya da Matar ka na uzzurawa rayuwarku yau gashi is tafi kabarni da tarin nadama da dana sani ina zan kai haqqinka gashi baka raye bare na nemi yafiyarka nasan kana jina dan girman Allah na tuba kayafemin kayafemin Abdul..." Haka taringa surutai dai marasa kan gado da kyar aka janyeta ana fita dashi kuwa ta sulale a gurin sumammiya. Allahu akbar rayuwa kenan. Aka ce ana bikin duniya ake na qiyama se gashi mutanen da suka taru domin murnar daurin aure sun juye zuwa zaman makoki. A wannan rana ta Asabat dubban mutane ne suka raka Abdulmalik Kamalu Dala zuwa gidansa na gaskiya cike da alhini rabuwa dashi kasancewarsa mutum na mutane, a tsahon rayuwarsa babu Wanda zaice ga abokin fadansa domin shi mutum ne mai yawan yafiya. Da akwai wata hira da aka tabayi dashi a gidan wata Tv reporter yake tambayeshi menene makamin nasarar sa a rayuwa se yace masa Haquri da yafiya, bai taba kwana da baqin cikin wani a zuciyarsa ba komai girman laifin da yayi masa kuwa, sannan ya riqe dare, qiyamullaili itace abar debe masa kewa, ya kuma riqi azumin Litinin da Alhamis, ya bi iyayensa sannan ya kyautatawa matarsa wadannan abubuwa kadai na riqe sune makamina. Abdulmalik nada barkwanci ga tausayi ga na kasa dashi, ya samu shaida ta gari daga yawancin mutane wadda ko wanne mamaci yake fatan samu sai muce Allah yasa kyawawan halinsa su bishi. A bangaren gidan su Amarya Haula kuwa Sai gashi gidan biki ya koma na mutuwa, Hauka ne kadai batayiba a lokacin data samu labarin rasuwar Angon nata. Hajia Hauwa ko lokaci daya Wani tsoro ya shigeta tareda Nadama. A lokacin da Al-amin yayan Haula yashiga gidan da rigarsa da hula a hannu tana tsaye a dakinta tana waya da Bokan da yake mata aiki akan Maganar auran tana shaida masa ance haryanzu Ango beje gurin daurin ba gashi har mutanenn da aka tara sun fara tafiya. Ce mata yayi duk abinda take ta bari tazo akwai abin da ze bata sunansa qare aiki tana haramar fita Al'amin din ya kwaza musu maganar mutuwar seta nemi guri ta zauna zuciyarta na bugawa. Rayuwar kenan ashe duk hauka sukeyi tana shirin tafiya karbo qare aiki aahe shi tasa rayuwar ma ta kare gaba daya. Haka suka tattaro suka dunguma gidansu Abdul din anan ta tarar da Halin da Aminiyar tata take ciki wanda ita ce sula. Ta suma yafi cikin kwando da an samu ta farfado minti kadan zata koma se ihu da fizgefizge take ita a barta ta dakko danta be mutu ba, seda aka jona mata ruwa da alluran bacci sannan aka sami sa'ida. Lamarin Hamdah kuwa ya ya zama se addu'a kawai domin har zuwa yau kwana biyu da rasuwar babu Wanda zece yaji maganarta, tana zaune sedai ta tashi tayi sallah ta koma same spot datake zaune ko gaisuwa aka zo mata sedai ta amsa musu da kai kawa. Ba yanda basuyi da ita ba akan tayi kuka Amma taki tadai zama kamar wata wacce tayi loosing memory bata uhm bata umum sedai duk abinda akace tayi zatayi ko abinci aka kawo mata zata karba ta ajiye dan baze iya wucewa ta makoshinta ba Mama Shuwa ce take dama mata kunu ba laifi tana dan samu tasha ko rabin kofi a lokaci ammafa bazakaji muryarta ba. Sau tari Mumcy zata sakata agaba tayita kuka ganin
Chapter 36 · 0% Book details