← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 62

Sashe 55

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

barshi kana kallon halin da yar mutane take ciki" Hajia Maimuna ta katse masa tunanin daya tafi, gaba daya ya diririce ya kasa kallon Dr Maryam data harde hannuwanta biyu a qirji Allah kadai yasan me take saqawa a ranta. Tun dazu take ayyana dauke yarta kawai ta tafi da ita amma ta dakata sabida Abubakar daya ce ta Jira Prof Ammani daya taho daga Abuja ya qaraso dan bayaso kanwar tasa ta koma gida da sauran nauyin Abdurrahman akanta dole ayi wadda za'ayi kawai. Shigowar Zahra da Mijinta se Amrah da Afra da sukayo kama kaman basket din data jero kayan abinci a ciki. Idanuwanta kawai zaka kalla kasan tasha kuka hatta da Baban su Amrah taqi koda yadda tayi magana dashi gani take kaman shi ya jawowa Hamdah wannan wahalar, badan shiba kila da batayi wannan qaddararren auran da be qareta da komai ba se wahala da ciwo. Tunda Mumcy ta kirata addu'arta daya Ubangiji Allah yasa maganin be mata wani lahani da ze cutar da ita a gaba ba aure dai an gama shi bi jahi rasulullah bazata koma wannan gidan ba. Kusada Momcy ta zauna ta dage kanta sama dan ko Hajiyar Abdul din bata ji zata iya gaisarwa, haka suka ci gaba da zaman shiru a gurin babu me magana a cikinsu. Se wurin qarfe biyu Prof Ammani ya qaraso asibitin, kallo daya yayi wa Hamdah ta cikin glass din ya dauke kai zuciyarsa tana masa wata irin quna wai yarsa ce haka kwance cikin mawuyacin hali. Zuwa yanzu kam yaje bango baya tunanin ze iya ci gaba da zuba ido akan abubuwan da suke faruwa seya kalli Farouk daya kame a cone r daya yana ta muzurai tun dazun yace "Umar kaje Near by police station kayi Filing case akansa Abdurrahaman Ibrahim Khalil yayi attempting kisan kai ka kuma tsayawa yar uwarka a kotu ka tabbatar ka kwato mata haqqinta saboda haifarta mukayi kamar kowacce ya bawai siyota nayi a kanti ba amma kafin sannan Alhaji inaso Takardar sakinta ta rigani isa Kano Dan Allah" ya qarasa magana idonsa akan Senator Ibrahim Khalil daya waro idanuwa jin zancen Kotu, se ya mike jiki na rawa ya isa inda Prof yake tsaye, magana ya shiga yi masa yana cewa "Prof ba haka za'ayi ba inaga wannan duk ba wata babbar matsala bace gaba daya bata fi mu sasantata a cikin gida ba ba lallai se hukuma ta shigo ciki ba saboda qarshe ni abin ze shafa ze bata min siyasata ne kaga ace Dana na cikina ana tuhumarsa da laifin yunqurin kisan matarsa...." "Ka qara da ya kashe Yayansa guda biyu kaga yanda abinda zefi tafiya daidai, siyasa kuma da kake magana kai ta shafa inda ka lura da tarbiyyar danka da bata kawo mu da haka ba tun farkon hasashen nagarta nayi masa ashe ni ban hango daidai ba to nagodewa Allah daya taqaita samuwar zuri'a a tsakani kaga babu sauran wani abinda ya rage mana mu daku sedai mu ce wanda ya cuci wani Allah ya saka masa, kai Abubakar nemo likitan nan ya rubuta mata sallama Maryam kuje can gidan keda Su Hamidah ku hada mata abinda zaku iya ni kuma zan wuce da Mamana ina da rai bazan bari ta wukaqanta ba" yanda yake maganar kadai ya isa ya nuna maka tsantsar bacin ran dayake ciki. Hatta da fuskarsa ta chanza kamar ba Professor Ammani ba wannan me yawan fara'a da sakin fuska. Zuciyar Mumcy qal ta miqe ko ba komai mijin nata ya yanke hukunci daidai da yanda take ra'ayi dan haka babu bata lokaci suka nufi gidan Abdurrahman din kamar yanda Abba yace ita da Zahra da Inteesar Matar Baffa da suka taho da ita. Hatta da Zahra me tsohon ciki haka ta zage seda suka hade mata kayanta tsaf wadanda za'a kwance kawai suka bari kafin su gama tuni Farouk ya nemo Mota da masu kwance Gadajen suka shiga loda kaya baji ba gani. Babu irin roko da Kukan da Hajia Maimuna batayi ba akan suyi hakuri dan tuni suka baro asibitin bayan Abbah ya dauki Hamdah a Ambulance suka wuce Kano dukda irin magiyar da Dr Huzaifa yaringayi masa shima akan ya barta suga yanayin lafiyar ta amma yace Aa, bazata qara koda minti a qarqashin kulawarsu ba kuma su tabbata duk inda Abdurrahman yake ya sakar masa yarsa dan baya su su shiga kotu da sauran wata alaqa a tsakaninsu bare har ayi tunanin ze dubi alaqar auratayya ya raga masa. Tun kafin su Isa Kano yagama booking komai na Asibiti dan haka straight AKTH suka tafi da ita. Matsayinsa da kuma Mamanta yasa kusan likitoci biyar suka rufu akanta duk dan sake tabbatar da lafiyarta Alhamdulillah kuwa babu abinda ya sameta se dan abinda ba'a rasa ba Operation dinma na plaster yayi mata ba dinki bane dan haka baze wani dauki dogon lokaci ba ze warke. A Amenity aka kwantar da ita, Abbah da kansa ya zauna har seda su Mumcy suka iso Kano yace taje gida ta huta se da daddare tazo ta karbeshi babu wanda ya musa masa dan sun san tunda har ta kaishi ga haka to kuwa ransa ya baci bilhaqqi. Cikin ikon Allah washe garin ranar wurin 12pm ta farka kuma cikin hayyacinta. Kallon Mumcy dake zaune akan Farar kujera a gefen gadon suna yar hira da wasu qawayenta likitoci da suka zo duba Hamdan se kuma Hamidah na tsaye tana jijjiga little Maryam da suke cewa Miimi yarinyar Yaya Baffa mamanta taje gida ta dawo. Dan yunqurawa tayi tana cije baki saboda zafin da gurin yankan yake yi mata tace "wash Allah" abinda ya janyo hankalinsu suka shiga yi mata sannu, "Sannu Hamdah kin auna arziqi ina keyi miki ciwo yanzu" Dr Zuhra ta fada tana tallafota dan ta gyara mata zama ita ke handling case din Hamdah a yanzu. Seta nuna mata cikinta kawai dan batajin zata iya magana. "Zaki iya tashi" Dr Zuhra ta kuma tambayarta nan ma kai ta gyada mata alamar Eh, seta kamota ta sauka daga kan gadon tana mata sannu, "Daure ki taka qafarki don't be lazy kinji in 3 days time zakijiki garas insha Allah kinji Daughter" haka Dr Zuhra keta fada har suka shige Toilet din dake manne da dakin, Mumcy dake binsu da kallo tundazun tausayin yar tata fal zuciyarta ta sauke ajiyar zuciya a hankali. Allah kenan meyin yadda yaso ba kuma ka isa ka tambayeshi dalili ba, ji a yadda Hamdah ta taso da rayuwarta amma Aure ya chanza mata komai, ita kuma tata rashin sa'ar a aure take, Allah kadai yasan meya sa yake jarabtarta ta haka koma mene tana fatan ya bata ikon cinye wannan jarabawar. Tana zaune har suka fito daga toilet din Hamdah daure da Babban Towel Fari a jikinta sannan ta lulluba mata wani akanta dake digar ruwa da alama wanke shi akayi. "Aa Dr wanka kika wa yar taki kenan" Mumcy ta fada cikin murmushi tana gyara mata inda zata zauna. "Wanka na mata data ci abinci tasha magani zakiga qarfinta ya dawo Allah na tuba me zamu jira kuma, shi dai wannan yaro kansa ya cuta na ma gayamata ta sakawa zuciyarta salama in so samu ne ta share babinsa a rayuwarta kamar ma bata yi wannan auran ba insha Allahu tana gama jego Allah ze kawo mata mafi alkhairinsa ke se tayi auran da kowa zeyi alfahari dashi ai Aisha ba qaramar mace bace bakuma ta boranci muna nan dadin nan ita ma seta ji shi bi'iznillah". Kalamnta sunyiwa Mumcy dadi matuqa take yaba kulawar da Dr Zuhra take bawa Hamdah tunda aka kawota asibitin a tsaye take akanta. Haka ta zuba mata lafiyayyen abincin da Intee ta kawo dukda bakinta babu dadi amma ta daure taci sosai kuma taji dadin jikinta dan harda Yunwa data qara kashe mata jiki. Kan gadon ta koma bayan ta gama duk a qoqarin ganin ta hana zuciyarta tuna abinda ya farun take kamar yanda Mama Zuhra take ta qara mata Nasiha akai. Wunin ranar haka tayi shi dangi da abokanan arziqi da suka samu labari nata zuwa dubata ciki kuwa harda Hajjan Abdulmalik. Kallon Zainab ta ringayi data lalace kamar ba ita ba ta jeme tayi baqiqqirin a ranta tana mamakin meya sami Zainab din haka? Ga Khausar ita ma ta zama abin tausayi da alama zaman gidan ya isheta kuma babu tsayayye ita kanta Hajjan Abin tausayi a yanda take gayawa Mumcy wai Hawan Jini ne yai mata mugun kamu har likitoci sunce in ya ci gaba da hawa stroke ze iya kamata to ya zakayi Matsaloli sun saka ka a gaba sedai Addu'a kawai. Haka suka qaraci zamansu sukayi musu Sallama suka tafi. Bayan sun fita ne Hajia Amina Maman Maryam take cewa Mumcy "Maryam kinga ishara ba ita rayuwa yanzu tun a duniya bawa yake kwashe abinda ya shuka kiga dai Matar nan wai tana maganar Hawan jini dana Allah ya taimaketa ciwon zuciya be kamata ba ai tayi a hankali kawai" "Hmm" kawai Mumcy ta fada dan ita ba wannan bane ma a gabanta yanzu lafiyar yarta tafi mata komai. Satinta daya aka sallameta cikin ikon Allah ta warware se abinda ba'a rasa ba, harzuwa lokacin babu Abdurrahman babu dalilinsa hatta da wayoyinsa a kashe suke ba bu kuma wanda yasan inda yake. Tsaf ta ware take sabgoginta dukda wasu lokutan idan ta tuna yaranta data rasa seta shiga daki tayi kuka gashi ko kalar fuskarsu bata gani ba, ta dai riga tabar Abdurrahman da Allah shi ze bi mata haqqinta. Lokaci lokaci Hajara tana kiranta a waya suna gaisawa a bakinta ma takejin batan dabon da Abdurrahman din yayi wai ba'a san inda ya tafi ba a ranta tace shi yaga duhu ita kam Haske ta gani ya gama boye boyensa ya fito ya bata takardarta shi kadai ya rage musu a tsakani yanzu. *************************** Two month leap Batasan ya akayi ba meya faru ita dai wata safiyar litinin Yaya Farouk ya shigo mata da well printed farar takadda da sunan takaddar sakinta. Dukda haushinsa da takeji amma seta tsinci kanta da rashin jin dadin sakin, shikenan fa yanzu zata shiga zawarci na biyu yanzu za'a fara lissafa mata aure Allah kadai yasan kuma ina zata fada se
Chapter 55 · 0% Book details