Sashe 42
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zata samu sauqi. Kamar me cutar Asthma haka ta shiga fizgar numfashi da qarfin gaske dan taga yana barazanar yanke mata gaba daya. Wata mata chocolate kyakykyawa mara jiki da take zaune a gefen kujerar da Hamdah take ce ta taso ta riqeta Maryam ta miqa mata ruwa a cikin kofi ta kafa mata a baki take ta shanye shi tas, "A qaro" matar ta tambayeta, kai da daga mata alamar Eh haka ta kuma tsiyayawa ta bata se a sannan ta fara jin iska na shigarta. Sannu take jera mata wata nabin wata ita dai ta jinginar da kanta a jikin kujerar ta rufe idanunta tana son ta yarda cewa mafarki ne ko Gizo ya mata bawai a zahiri ta ganshi ba. Yusuf da Maryam na tsaye akanta cikin damuwar abinda ya sakata irin wannan kidimewar haka, seda suka tabbatar ta samu nutsuwa sannan Maryam tace mata "Sannu Bestie tashi muje daki ki kwanta ko zaki qara samun nutsuwa kinji" bayan ta yafa mata mayafin ya rufe mata dogon gashinta. Idanuwanta ta qara budewa a karo na biyu, ba mafarki take ba dan gashinan a zaune dungurgur akan kujerar ba abinda ya dameshi sema lemon da yake kurba yana danna wayarsa kamar besan budirin da sukeyi a cikin palour ba. Wata Yarinya ce Fara tas da kallo daya zaka mata ka gano tsantsar kamar da yakeyi da ita ta shigo palour da dan gudunta ta fada jikinsa cikin yar siririyar muryarta da bata wani gama iya magana ba tace "Dady hide me Ayiyu will beat me". Se ya dire kofin ya dagata sama yana dariya kamar yanda ita ma yarinyar takeyi tana qoqarin buya a jikinsa Aliyu kuma ya dage seya janyota daga jikin Dadyn nata. "Lah Dady our Berbie" tafada tana zamowa daga jikinsa ta nufi Hamdah da gudu ta haye jikinta tana taba fuskarta. "Look Dady she is blinking her eyes yeeeee she is our real Berbie Ayiyu come look at her". Tsalle take tana murna a dole taga Berbien Dady yau ita kuwa Hamdah ta zauna kamar wadda aka dasa seta kalleshi ta kalli yarinyar data dage tana jagwalgwala mata fuska da gashi. Matar ce ta shiga janyeta tana cewa " Stop that *_Hamdah_* this is Aunt not Berbie stop it or else she will not take you to Your name sake" nan da nan ta bari yar karamar fuskarta me kyau ta chanza zuwa kalan tausayi tace "Please Aunt take me to my namesake i really want to see her, my Daddy is always telling me about her please" ta qarasa tana hade hannunta alamar roqo. Seta qaqalo murmushi ta dora akan fuskarta sannan tace "Ok Jawel i will take you to ur namesake, whats Your name again"? "My name is *_AYSHA HAMDAH ABDUL'AHAD GALADIMA_*" Yarinyar ta fada cikin murnar za'a kaita gurin namesake dinta. Bata buqatar sauran qarin bayani tabbasa wannan SIR GURU ne, kuma wannan Matarsa ce sannan HAMDAH yarsa ce, se kawai taji wasu hawaye sun shiga sakko mata da bata san na menene ba tana fara kukan ya mike tareda daukan wayarsa, idonsa akan matarsa yace "Zanje na dawo take good care of Hamdah ok" ya juya yayi tafiyarsa. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Da kallo ta ringa bin Ni'ima dake ta faman doka mata murmushi, at last yau taga Hamdah, Hamdan data hanawa mijinta walwala. Matar da tayi awon gaba da dukkan farin cikin Mijinta. A tsahon zaman auransu tasan Gangar jikinsa kawai ta aura amma zuciyarsa tana tare da wata duk da hakan ba wani damunta yake sosai ba saboda ita take sonsa, ta sani tausayine yasa ya aureta ba wai dan Soyayyaba kuma har zuwa yanzu bata da yaqinin ya karbeta a matsayin masoyiyarsa. "Ina ta jin labarinki a bakin Dadyn Hamdah dama nace duk randa muka zo Nigeria sena nemeki se gashi bani da rabon shan wahala na ganki ma a free" Ni'ima ta fada tana qarewa Hamdah kallo cikin yaba kyau da kyawun surar da Allah ya mata. Tabbas ta isa a sota, ta isa ta dauke hankalin ko wanne namijin da ya isa da kansa, ayanda take ganinta a hoto se taga har tafi kyau a fili dan tuni ta haddace kamannin Hamdah tsaf saboda yawan hotunanta a cikin gidansu. Tabbas da ace ta kasance cikin mata masu tsananin kishi da batasan yanda zata kaya musu a wannan haduwar ba, kilan da se ta kasheta duk hukuncin da za'a mata sedai ayi mata shi. Tana matsayin matar Abdul'ahad ne kawai kuma uwar yarsa bayan wannan bata da sauran wani matsayi a gurinsa ta sani. Kallon yanda Hamdah Karama taketa liqewa Hamdan take wani tunani ya darsu a zuciyarta, irga kwanakin da take ganin su suka rage mata tayi a zuciyarta ko ba komai rabin burinta ya cika taga Other Half din Abdul'ahad, abu na qarshe shine ta sake hadasu, su zauna a karkashin inuwa daya ma'ana a matsayin ma'aurata. "Zaki iya hada miji da ita, zaki iya jure kallon Abdul'ahad yana nuna mata irin soyayyar da kikayi kwadayin samu a gurinsa" zuciyarta ta shiga tambayarta, setaji hawaye na neman kawo mata dan haka ta miqe tana tambayar Maryam Toilet, Bedroom dinta ta kaita sannan ta dawo gurin Hamdah data zauna a zahiri hankalinta yana kan Little Hamdah dake ta faman zuba mata surutu a badini kuwa ta kusan zuwa China a tunani, tunanin da takamaimai bata san name takeyi ba. "Hamdah nasan zaki ga laifina wallahi nima bansan....." Seta katse wa Maryam din magana tace "Baki laifin komai ba Maryam, kilan keda mijinki baku san kasancewar mu tare. Amma meya sa baku gayamin yayi aure har ya haifi ya ba? Meyasa duk lokacin dana tambayeki ko Yusuf se kucemin baku san inda yake ba? Maryam cewa fa kikayi rabonki dashi tun muna makaranta meye ribar boyemin da kukayi" se ta dakata saboda fitowar da Ni'ima tayi, Hawayen da suka fara sakko mata ta shiga gogewa Little Hamdah na tayata dukda bata gane komai, Zaman mayafin kanta ta gyara sannan ta dauki jakarta da key din motarta ta nufi kofar tana cewa "Na tafi zan aiko Hamidah anjima ta karbarmin kayan kawai" bata saurari magiyar da take mata ba ta sa kanta waje a zuciyarta tana tunanin if Maryam is truly her Bestfriend. Cikin motar ta shiga ta zauna amma ta kasa kunnata se kawai ta kifa kanta akan stirring ta saki kuka me ciwo, tsohor Soyayya ce taso mata akansa, da kadan da kadan take tuna wancan lokacin, kalamansa daidai da suke da mugun tasiri a zuciyarta da bata taba mantawa dasu ko sau daya ba, ashe ita take shirmenta, ita take tunanin akwai wata *RUBUTACCIYAR QADDARAH* a tsakaninsu. Ita take ganin kamar wata rana zasu zama abu daya, Ashe duk shirme takeyi tuni yayi aure ya manta da babinta a rayuwarsa. Kila ma ko ganin daya mata yanzu be gane ta ba shi yasa ma yayi tafiyarsa. Haka taci gaba da kukan da babu me rarrashinta. **************************************** Tacikin Mudubin motarsa yake kallonta saboda glass dinta masu haskene bata rigada tayi musu Tint ba. Duk saukar hawayenta daya yana jinsa kamar digon Dalma akan zuciyarsa ne amma yaya zeyi? Ya rigada yayi wa kansa alkawarin cireta daga zuciyarsa tunda dai bashi da Sa'a, a koda yaushe baya taba zuwa a daidan lokaci se wani ya rigashi Fara gini tukunna. Be manta da Hamdah ba, abubuwa da yawa sun faru dashi bayan rabuwarsu wanda sedaga baya yake ganin duk laifinsa ne. Shi yayi saurin Cire tsammani yaja da baya a filin daga, ya sani da ace ya saurareta a wancan lokacin da kilan abubuwa basu tafi akan yanda suke yanzu ba amma yaya zeyi? Qaddarar Auran Ni'ima da Haihuwar Little Hamdah ce ta saka shi wannan fushin zuciyar ya tafi akan abinda befi ya dauke shi a matsayin wasa ba. Ji yake baze iya jure kukan nata ba, har yakai hannu ya bude motar da niyar zuwa ya rarrasheta sedai ko me ya tuna se kawai ya maida kofar ya rufe. Ganinta a yanzu ya qara hura wutar soyayyrta a zuciyarsa da wani bala'in kishinta. A duk lokacin daya tuna ta taba aure ji yakeyi kamar ya kashe kansa tsabar kishi. Harga Allah yaji dadin Mutuwar Abdulmalik, abinda ya hanashi dawowa rayuwarta a lokacin uzurine babba wato Matarsa. Ni'ima Amana ce a hannunsa, tana cikin wani yanayi da baze iya tsallaketa ya tafi gurin wata mace ba amma hankalinsa da tunaninsa akoda yau she suna Kan Hamdah, dalilin daya saka wa Tilon Yarsa sunanta kenan saboda yaringa tunawa da ita duk sanda aka kira sunan yarinyar. Lokacin da Yusuf ya sanar dashi shirinta na sake aure ya shiga yanayin dayafi na baya muni, a kullum yana jiran ta kirashi, tace ya dawo, tana sonsa za kuma ta aureshi amma yau tsahon shekaru biyar kenan wannan saqon be isar masa ba gashi wai yau saura Kwana uku ta daura aure a karo na biyu da mutumin da be cancanceta ba, mutumin da kyau da surarta ne kadai suka rudeshi bawai dan yana son ta ainihin ita din ba dole yasan abinyi, dole ya dakatar da wannan auran baze yarda ya qara rasata a karo na biyu ba, se ya balle murfin motar ya fita cikin zafin nama irin nasa ya qara sa jikin motarta ya bude "Fito ki koma can" ya fada cikin sigar umarni. Seta dago idanta da suka canza kala ta kalleshi tana so ta tabbatar da shi yayi maganar ko yaya. "Zaki fito ko na fiddoki da kaina" ya qara fada yana dage mata gira daya. Se kawai ta mayar a kanta ciki ciki take magana "Idan Motarka ce ai seka zo ka fito dani mutum se isa da iko kamar ya haifi mutane" ta manta da kaifin Ji irin na Guru se kawai ji tayi ya sunkuya ya tattaro kafafuwanta gaba daya yayo waje da ita daga cikin motar "Kina yi min ihu ina maimaita abinda ya faru 5 years ago". Dole ta ja bakinta tayi shiru har ya zaunar da ita akan kujerar me zaman banza sannan ya zagaya yashiga motar "Da alama kin manta ba'a daring dina Yammata, waima me kike ci kikayi nauyi haka ji yanda duk kika sa hannuna suka sage" ya fada hankalinsa akan tuqin dayake