← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 62

Sashe 57

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka tsatstsaya akanat se tayi dan murmushi tana gyara zamanta tace "Hey relax its nothing serious i was just a little bit panic ne but I'm good now". A kusan tare Umm Ashrab da Zulaiha suka sauke ajiyar zuciya kafin kowacce ta nemi guri ita ma ta zauna. Tsare tsaren party suka shigayi dukda rabin hankalin Hamdah yana kan wanacan mutumin na waje lokaci lokaci tana kallon kofa kamar ance mata ze shigo gidan harseda Umm Asharb ta lura ta tambayeta ko tana expecting zuwan wani ne, kai ta girgiza mata alamar Aa, suna gamawa ta mike jiki ba kwari tace kanta na dan yi mata ciwo zataje ta kwanta kafin Magrib seta dawo. Lokacin data fito shima ya fito kenan daga plat dinsa, ba kaman dazun da yake sanye da Three quarter da Armless shirt ba yanzu Suit ce a jikinsa me kalan Blue se Inner daya saka fara qal ya riqe jacket din a hannunsa be saka ba, waya ce a hannunsa yake daddannawa da alaman wani ze kira ko wani abu yake nema. Babu gashi sosai a fuskarsa yanzu hatta da gemun da yake ajiyewa ya rageshi sosai se kadan hakan ya qarawa fuskarsa wani kyau da Haske na musamman. Ta kasa hana kanta kallonsa, wani irin shauqi ke dibanta zuwa gareshi, qamshin turarensa da bazata manta ba abinda ya fara ribatar zuciyarta zuwa gareshi ya cika gaba daya atmosphere din ya hade da daddadar iskar dake kadawa a gurin suka bada wani yanayi me dadi. Batasan iyakar Lokacin data dauka a tsaye tana kallonsa ba kuma har lokacin kansa yana kan wayar be dago ba balle yasan da tsayuwarta a gun. "I'm on my way" sautin muryarsa ta doki kunnenta a karo na biyu, tabbas ba Kama bace wannan _ABDUL'AHAD ALIYU GALADIMA_ kamar wata yarinya haka ta kwasa da gudu ta isa kofarta har key din na faduwa saboda saurin da takeyi ta bude se a lokacin ya daga kansa ya kalli Direction din data bi, da karamin murmushi ya rakata kafin ya qarasa ya bude motarsa ya kunna yana ci gaba da kallon yanda take kiciniyar bude kofar, kamar dazun a tsiyace ya figi motar ya fice tayi saurin waiwayawa tana kallonsa a ranta tana mamakin sautawar dabi'un nasa, to kodai be gane ta bane ko kuma dai wani ne daban kaman yanda zuciyarta tafi yarda bashi din bane. Duk yanda taso tayi baccin kasawa tayi haka har magribar tana kwance tana juyi akan gado. Seda aka kira sallah sannan ta tashi dan gyare gyare ta shigayi saboda tana fashin sallah dukda babu abinda gidan yayi, two bedroom plat ne se toilet da bathroom se kuma kitchen section da yake gefe a cikin palour hade sa qaramin Dining dinta. Daki taya ta saka gado dayan kuma ta barshi matsayin study room tunda ita kadai take rayuwarta daki daya ya isheta. Duk wani abun buqata tana dashi a cikin gidan ta qawatashi to her taste saboda yanzun ta koma asalin Hamdah ta yar kwalisa shiyasa dole gidan ya birgek idan ka shiga. Wanka tayi bayan data gama yan ayyukan ta shirya cikin wata black simple gown babu adon komai a jikinta se colar da ayi mata se hannun da ya dan matse daga qarshensa. Loko da saqo na jikinta tabi ta feshe da turaruka sannan ta yafa baqin Veil mara nauyi akanta ta zula slippers a kafafunta sannan ta dauki wayarta da gift din Asharba da tayi rapping a babban rapping sheet ta fita daga gidan. Sannu sannu take tafiya kamar me tausayin kasa tana jin kamar iskar da ake danyi zata dauketa saboda yanda takejin jikinta babu nauyi sam, cikin tsautsayi iska ta dauke mata dan mayafin data rufe kanta tabarta tsurarta se tulin uban gashinta data tattare a tsakiyar kai. Bin Mayafin dake yawo a iska tayi da kallo kaman zata saka kuka waima ta ina zata fara kamo shi se kawai gani tayi ya sauka akan fuskar mutumin da bataga tahowarsa ba se kawai ganinsa tayi a kusa da ita. _Abdul'ahad_ Pov Tunda ya faka motarsa yake zaune a cikinta, ya gaji liqis saboda conference din dayaje akan wani case study da zasu fara anan Imperial Collage akan wata sabuwar cuta datake shirin bullowa. Yana kallon lokacin data fito daga cikin gidanta, shigarta da yanayin tafiyarta yana qara mutar dashi a cikin soyayyarta. Tunda yake a rayuwarsa be taba samun nutsuwa irin ta wannan karonba, ya godewa Allah ya kuma gode masa. Yayi Sallah yayi Azumi ya kuma bada sadakoki duk akan irin wannan baiwar da Allah yayi masa. Tabbas ya yarda da maganar da akace ba'a yanke qauna da rahmar Allah kuma hanyoyin Allah yawa ne dasu haka nan bawa besan lokacin da ake karbar addu'arsa ba. Yana kallon sanda mayafin nata ya yaye yayi saurin fitowa daga motar saboda gurin tarwai yake kamar rana. Duplex din gefensu kusan duka mazane baya fatan wani ya fito idonsa ya kai kan gashinta har ya kalleta sema ya farajin haushin meyasa bata daka koda qaramin Hijab bane yanda iska bazata cire ba? Mayafin ya riqe da hannunsa lokacin daya sauka a fuskarsa yana shaqar daddadan qamshin dayake fitarwa, sannu a hankali ya qarasa inda take tsaye kamar wadda ta taka Glue Gum ta maqale. Idan beyi qarya ba seyaci yaji yanda zuciyarya take bugawa kamar ana kidan mandiri har abin ma yaso bashi dariya seya gimtse ya shiga Zagaya mata mayafin akanta ya zauna sosai akaman yanda yaga tanayi a shekarun baya da kuma yanda yake taya Ni'ima a yawancin lokuta idanunsa akan farar fuskarta da babu dugon kwalliya ko kasan a kai se dogon hancinta da wadannan lips din masu juya masa tunani. _Hamdah_ Kamar mazari haka zuciyarta da jikinta suka ringa rawa lokacin daya kusantota sema taji kaman numfashinta ze dauke saboa yanda kamshinsa ya cika mata hanci ga numfashinsa da takeji yana sauka har akan fuskarta. Yana gama daure mata Veil din tayi gaba kamar iska har bata san sanda agogonta da be gama dauruwa ba ya fadi tayi saurin fadawa plat din Umm Ashrab dayake kofar a bude take saboda baqin da suka gayyato. Palour ya cika da friends din Asharb da parents dinsu da suka kawo su se few of their course mates da Darussalam din ta gayyato nan da nan ta ware suka shiga gaisawa da mutane duk a qoqarin cire tunaninsa daga zuciyarta. Party yayi party yara sun cashe sosai haka Hamdah ta shiga tsakiyarsu suka dinga tiqar rawa dama ita ba baya bace a wannan bangaren karma taji sabgar yara shiga ciki takeyi suyi kamar sa'arsu se gurin 11pm aka fara watsewa suka shiga tattara tulin gifts din da Ashrab din ya samu basu fita daga gidan ba se after 12am. Ita da zulaiha suka fito suna yar hira, ta ninke veil din ta daurashi akanta kamar dankwali tsabar gajiya takalmin ma a hannu ta riqosu dukda slippers ne. Yana zaune a kofar plat dinsa kan resting chair ya mike dogayen kafafunsa gefe ya ajiye dan karamin stool da system akai, hannunsa biyu a hade a karkashin habarsa ya zubawa kofar Umm Ashrab ido tundazu mutanen da suke fitowa akan idonsa suke yana jira yaga sanda zata fito. Saurin dauke idonsa yayi tare da gyara Zama lokacin daya hangosu, se yaga ta qara masa wani kyau na musamman and she looks younger. Gaisawa suka shigayi da Zulaiha sanda suka zo gifta shi Hamdah kam tura baki tayi gaba bayan data harareshi ta gefen ido duk akan idonsa se kawai yayi murmushin da iyakansa lips sukayi sallama da Zulaiha suka wuce. Tattara kayansa ya shigayi dan dama abinda ya zaunar dashi kenan ya shige gida sedai ko kadan ya gagara bacci. Wani irin abu yakeji da bai taba jin irinsa ba, urges na sexual desire suka taso masa lokaci daya mararsa ta shiga wani irin ciwo. Dakyar ya sakko daga kan gadonsa zufa na keto masa ta ko ina ya shiga neman wayarsa, Master ya kira shine suke kusa kusa kuma kasancewarsa likita murya a shaqe ya masa bayanin yanda yakeji sannan ya ajiye wayar ya rufe idanunsa yana cije lips dinsa kaman ze fasa su. Minti 10 a tsakani Master ya qaraso, yana da spare key din gidan shi yake lurar masa dashi lokacin da baya nan dan haka ya bude ya shiga kai tsaye. Da sauri ya qarasa cikin dakin yana masa sannu nan da nan ya shiga bashi duk wasu taimako da suka kamata zuwa wani lokaci bacci ya daukeshi saboda Allurar dayayi masa, be bar gidanba har seda ya tabbatar da komai normal koda ace Abdul'ahad ze farka baze tashi da ciwon komai ba. Mita yake tayi a zuciyarsa kan halin da Abdul din yake nema ya jefa kansa, ya rasa wace irin zuciya Allah ya halittoshi da ita dan tabbas da a zamanin mutanen farko Abdul'ahad yazo irinsu ne aka sha wahala dasu kafin su biyu in ba haka ba da ransa da damarsa ya zauna yana azabtar da kansa akan wani abu mara tushe, yanzu yana tunanin in ya mutu sanadin haka me ze ce wa Allah bayan ya bashi duk wasu qarfi da ikon saukewa kansa nauyin? Ture wannan yana zaton idan har wata nakasa ta same shi ta wannan dalilin ita wadda yake dominta zata haqura ta zauna dashine? Haka yaita mita a ransa har ya ja masa kofar ya fita tareda rufe babbar kofar gaba daya. Hajia Hamdah kuwa tana shiga gida kiran Mumcy ya shigo wayarta, agogo ta kalla tana mamakin meya faru take kiranta at this hour sedai ta daga wayar da taraddadin me zataji. Muryar Mumcy fes suka gaisa tana tambayarta karatu, yar hira sukayi har lokacin tana jira taji ko wani abu ya faru ne. "Yawwa Islaha tazo Nigeria kin sani ko" mumcy ta tambayeta. "Eh na kirata jiya ban sameta ba se whatsapp mukayi magana take cemin yayar Abban su Maisar ce ta rasu ko" "Eh wlh ai cikin week dinnan zasu dawo zan bata saqo ta kawo miki idan kuma akwai abinda kikeda buqata se ki fada ta taho miki dashi". "Babu Mumcy mota kawai nake so na gaji da hawan motar hayan nan so stressful in emergency fita ya kamaka seka ta jiran wani taxi" "To bari zan qullo miki motar
Chapter 57 · 0% Book details