← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 62

Sashe 8

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana gaya mata kilan gobe ze zo kano ya gaji yana missing dinta sosai. Badan tana jin baccin ba haka ta takurackanta yinsa dan bata so tabawa kwakwalwarta damar yin tunanin abinda ya faru yau tsakaninta da Guru. Washe garin ranar Akayi dinner sedai tayi kokarin ganin ta toshe duk wata hanya dazata hadata da Guru, yanda ta tsare gida dole ya saurara mata amma hakan be hana shi liqe mata bomper to bumper ba data dauke kafarya daya ajiye tasa ko kunyar dalibansa da suke a gurin beji ba. Gurin cin abinci ma Serve ur self akayi, shiya zubo musu abincin a plate daya batareda nuna damuwa ba ta saka cokalinta ta fara ci hankalinta kwance abinda ta sani daga ranar ba qara ganinta zeyi ba bare ya takura mata. Ranar Saturday aka daura auren Maryam da angonta Yusuf da daddare suka kaita gidanta dake Rijiyar zaki akan washe gari zasuyi Sword crossing. Bayanda batayi da Maryam ba akan ta kyaleta tabi su Afiya amma taki bata da zabi illah ta zauna Addu'arta Allah yasa banda Guru za'a zo rakiyar Ango. Ko yau a gidan daurin aure taji haushin abinda ya mata. Kamar hadin baki suka saka kaya kala daya shi shadda light Ash ita kuma Lace. Tunda suka shigo yake nunawa Abokansu wai ga Amaryarsa "kungani ban gayabmata kalan Kayan da zan saka ba amma saboda zuciyarmu daya munsaka iri daya" abokan da suka fishi rashin hankali se cheering dinsa suke wai ya iya zabe har wani yana cewa ya masa shigen layi shi yaso ya kafa gomnatinsa amma Guru ya riga. With full confidence yake cewa "Ai wannan shinge nane babu wanda ya isa ya ratsa" haka suka ringa daukarsu pictures kamar ita ce amaryar. Se 9:30 yan rakiyar ango Suka qaraso. sedai Addu'ar ta bata karbu ba Dan Sallamarsa ce a gaba. Bayan yan gaishe gaishe da wasa sukayi musu nasiha sannan sukai wa Amarya sallama suka Fara fita daddaya. Sabon kuka Maryam ta saka wanda dole ita ma Hamdah ta tayata. Akace sabo tirken wawa shikenan yanzu Maryam tayi aure ta barta dakyar Yusuf ya lallashi Maryam din suka hau sama ita kuma ta fita waje. Mota daya ta rage a parking lot din gidan da alama itaYusuf yake nufi za'a kaita gida. Tana share guntun hawaye ta qarasa jikin motar jin yana mata Horn. Seda ta zauna sosai sannan ta gane motar waye ta shiga ba abin ta fita ba dan har ya fara tafiya. To in ta fitan waze kaita gida ga unguwar tsit babu ma alamar masu adaidaita sahu. Bata da zabi Se kawai ta daure fuska karma ya samu damarta. "Naga se wani kuka kikeyi in kin shirya kema se a miki auran kiyi me dalili". In ta amsa shi ku da kuke karantawa kun amsa, abinka da me saurin fushi kawai se shima ya shareta dan yaga alama in ba'ayi soyayya ba to raini ze shiga tsakani. Se kawai ya kunna waka ya qure volume din, yana dauke hannunsa ta mayar da nata ta rage karar kidan tana mita "kawai se a kunnawa mitane wata waqa ko dadi babu kaman sunce suna so". Be kulata ba ya qaro volume din ta kuma ragewa a na uku ya dago a fusace dan takai shi bango "if you dare touch anything here again sena baki mamaki wallahi". Kallonsa kawai tayi dan ta ji tsoro. Sak ya dawo mata Dr Guru data sani Na BUK dan haka salin alin ta kama kanta. Tana jinsa yana tsaki shi kadai karshe ma ya kashe waqar ya kashe AC ya sauke windowa din motar dukka ita dai a ranta tace kaji dashi. A kofar gidansu ya, tana shirin fita daga motar ya tsaida ita ta hanyar cewa "ji mana" Komawa tayi ta zauna Ta hade girar sama da kasa, se yaga tayi masa kwarjini yakasa fadan abinda yayi niyya. Haushi yabata Ya kirata kuma ya mata shiru "shikenan seda safe" ya fada bayan ya bude murfin motar ya fito, bude mata motar ta fita. Seda ta tabbatar ta fita daga motar sannan ta kalleshi "Malam ka dena wani abu kaman an saka ka ni dinnan da kake gani nagama gane take takenka so you better know I'm already taken. Kallonta kawai yakeyi ya kasa ce mata komai, motar sa yai wa key ya bar wurin zuciyarsa na wata irin suya. kuka ta fashe dashi haka kawai taji Kamar bata kyauta ba. Da zata iya da ta bishi tabashi hakuri meyasa bata tsaya taji abinda ze fada ba fincikar da aka mata ce tasata maido da hankalinta, Abdulmalik ne fuskarsa tayi Ja tamkar wanda yaci yaji jijiyoyin kansa duk sun tashi. Kamar mazari haka jikinsa yake rawa, motar yabi da kallo kafin yadawo kanta cikin shaqaqqiyar murya yace mata "Yau kuma daga ina ya dakkoki?" wannan kuma se meya faru iye nace uban me ya hadaku da har Ya dauke ki". Hotonsu da guru Wanda takusa faduwa a gurin kamun Maryam yake nuna mata. Tsawa ya buga mata cike da hargagi yace "Dama baki da abin fada tun ganina dashi na farko ban yarda dashi ba kwata kwata kallon dayake yi miki ba kallo bane irin na Malami da Daliba kallone irinna masoya masoyinma wanda zaka iya yin komai akansa......" *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 PAGE 0 "Enough Abdulmalik" ta katse Har lokacin hawaye basu dena zuba daga idonta ba. "Bakaso kaga wani ya rabe ni ko bakason ganina tareda Ko wanne namiji ba toh ka Aureni, na amince Abdul katuro iyayen ka ko gobe a daura mana aure Indai haka ze sa ka yarda da soyayyar da nakeyi maka" Tana kaiwa nan ta shige gida tana kukan da bata san dalilin yinsa ba. Wani Gumi ne Ya shiga keto masa nan take cikinsa ya shiga hautsinawa har yana jin amai na yaso masa Alamar ya kai qololuwa cikin tashin hankali. Naushi ya kaiwa ginin dake bayansa tareda Kifa kansa a jikin bangon shidai Malam Sa'idu me gadi kallon ikon Allah kawai yakeyi. Wannan shine goma da ashirin, ta yaya zata dakko maganar aure a wannan lokacin bayan ita ta kawo tsarin seta gama school wanda yana ganin shima kafin lokacin abubuwa sun daidaita a nasa bangaren? To waima tun farko meya hanashi gabatar da ita a gida ne yasan da komai ze zo masa da sauki amma yanzu kam abubuwa sun rincabe. Haka yai ta sambatu a hanya shi kadai sedai ya qudiri aniyar koma me ze faru baze bari ta subuce masaba Koda hakan yana nufin batawa da kowa, he don't care kome za'ayi sedai ya faru Amma dole ze tunkari Alhaji da Maganar nan. A bangaren Hamdah Da kuka ta shiga gidan, Dankwalin kanta da mayafin dukka a hannu dama tuni ta cire takalminta a waje. gaba suna zaune a Main palour suka bita da kallo. Ikon Allah kawai Abbah ya fada ya ci gaba da duba Jaridar Hannunsa aransa dai yana mamakin hali irin nata katuwar budurwa ki shigo gida kina kuka kamar wadda aka daka, da ace Abubakar ko Baffa na gidan ne ma se ya ce daya daga cikinsu ne ya maketa. "Anya kuwa Mumcy Anty Hamdah bata da Iskokai Dan dai abinnata ya fara wuce na Islama" Hamida ce tayi tambayar tana bin hanyar da Yayartata tabi da kallo. "Bata da wasu Iskokai se Iskanci" cewar Farouk dake zaune a gefe. Seda Mumcy ta sauke numfashi sannan tace "Nima dai Hamidah lamarin yar uwarki yana daure min kai kwana biyunnan na fuskanci tana cikin damuwa Duk yanda take dokin bikin Maryam amma kwata kwata bata da walwala ga yawan koke koke data samu Kamar Matar Mamaci ina ga ko dai ita da Abdulmalik ne ko?" ta qarasa maganar cikin sigar tambaya. "Na Fa gaya muku Ba abinda ke damunta se iskanci inba haka ba kawai ta shigowa mutane gida ba ko sallama ita ga Yar So Ai Abbah ya dawo Abinda take so kenan dama ku tada hankalinku to thank God Bema ko kalleta ba " "kaidai Yaya Farouk baka san me aka mata ba kawai zaka fara cewa haka" hamida ta fada bayan tamike ta bi bayanta, tasan Yayarta sarai bata kukan banza dole akwai abinda yake damunta. Shiru palour yayi kowa da abinda yake saqawa Daganan kowa ya fara watsewa saboda dama dare yayi. Duk irin hakurin da Hamida ke bata seya zama kamar qara tunzura ta takeyi. Kuka takeyi sosai Wanda in zaka kasheta A lokacin bata san namene neba. Fushin Abdumalik ne ko Kuma Sir Guru ne ita ma bata sani ba. Abu daya dae tasan tana son Abdulmalik, so na hakika haka nan babu ko digon son Guru aranta to meya ke faruwa haka?? Ahaka ta raba dare tana kukan rashin sanin madafa abinda ya haifar mata da ciwon kai me tsanani Kafin safiya zazzabi me zafi ya rufeta. Washe gari har 1pm tana kwance a dakin, dakyar tayi sallar asuba ta qara kwanciya gashi tun da dare ta kori Hamida dan ta isheta da tambayar meke damunta. Wayarta bata san inda take ba kuma har lokacin babu wanda ya leqota. A bangaren yan gidan kuwa Sanin halinta na in tana fushi bata so kowa ya shiga sabgarta yasa suka kyaleta a zuwan in ta sakko da kanta ta fito. Koda Mama Uwani ta gama girki dan tun 6am Mumcy ta fita aiki Farouk cewa yayi karya kai mata in taji yunwa zata fito dan kanta. Se 3pm Mumcy ta shiga gidan tana tambayarsu ina Hamdah kowa ya bata amsa da be ganta ba tana bambamin fada ta shiga dakin hankali tashe tayi kanta ganin yanda ta kudundune cikin bargo tana rawar sanyi, dagota tayi ta rungumeta a jikinta "Hamdahna lafiya Meya sameki?" Gaba daya ta rikice jin numfashinta na neman daukewa ne yasata shiga Kwalawa Farouk kira. A tare yaran nata suka shiga dakin jin Yanda take kiransa babu qaqqautawa sun san babu ba Lafiya ba. Hankalinsu dukka ya tashi da ganin halin da take ciki dan lokaci daya ta fita hayyacinta seka zata ta yi sati tana jinya, bata da nutsuwar bata wani emergency dan haka suka nufi asibiti kawai da ita. ************************* Abdulmalik kuwa bayan barinsa wurin Hamdah straight gidansu dake unguwar Sharada NNDC ya nufa. Tun daga yanayin parking dinsa me
Chapter 8 · 0% Book details