Sashe 18
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
yana addu'a Allah yasa dai Kamace ko kuma mafarki yakeyi sedai addua'arsa bata karbu ba lokacin dayai tozali da bakin sako, katin gayyatar daurin Auran *Abdulmalik Kamalu Dala da Hamdah Ahmad Ammani* nan take yai zaman yan bori a qasa, baya neman sauran qarin bayani itace, itace za'a aura wa wani Babu ko tantama Hamdan sace. "No it can't be possible" ya fada on top of his voice tareda cilli da wayar ta bugu da bango a take tayi kwatskwatsa, mikewa tsaye yayi jikinsa na rawa kamar mazari abin tausayi se kawai ya yanke jiki ya fadi a gurin. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 Gaba daya suka yi kansa a hankalinsu a tashe. Aliyu ne yai karfin halin kiran ambulance cikin lokaci kadan suka qara so aka dauke shi zuwa asibiti dan har lokacin he was still unconscious. Ko a asibitin tambayar junansu suke dalilin sumansa amma babu wanda keda amsar dan haka suka tsaya jiran likitan daya ke dubashi kilan shi yana da masaniya akan abinda ya sami Abokin nasu. Seda ya dauki awa daya sannan ya farka, kallonsu yake daddaya yana so ya tabbatar da abinda ya faru mafarki ne amma tambayar da suka fara jera masa yasa ya gane tabbas abinda ya gani gaskiya ne. "It happens in real" ya fada a ransa. Se ya shiga kokarin sauka daga gadon bayan ya fincike allurar karin ruwan da aka saka mas. Yana ganin jiri da komai haka ya nufi kofa yana dafa bango Duk kuwa da yanda suke masa magiyar akan ya tsaya jikinsa babu kwari tuni ya fice daga ward din gani in suka barshi ze iya zuwa ya illata kansa abanza yasa suka bi bayansa. A motar Master suka koma apartment din nasa. Kayansa ya shiga hadawa a cikin qaramar jaka ba ji ba gani. Duk da tarin tambayoyin da suke yi masa be amsaba faman loda kayan da besan me zeyi dasu ba dan in aka zazzage kaf babu complete set dauka kawai yake suk wanda hannunsa ya taba har ya gama ya saka passport dinsa da duk waau muhimman abinda za'a nema a aljihu ya ja akwatinsa yai waje cikin wani matsanancin tashin hankali. Gani yakeyi taxi din daya hau bata sauri tamkar ya sauka ya taka da kafarsa haka yaringa ji. Ko a Airport din besan nawa ya bawa mutumin ba kaman zautacce haka yaringa tafiya duk da irin azabar dayakeji a jikinsa amma be tsaya ba yana tafe yana hada hanya kaman wani dan maye haka ya qarasa ciki sedai yayi rashin sa'a babu jirgin da ze tafi Nigeria a kwana biyu masu zuwa ma. Zaman dirshan yayi a gurin kamar mace ya shiga hawaye, dabara ce ta fado masa ta yanemi jirgin wata qasar a Africa duk tsiya ko da kafa seya je Nigeria (lol) hakan kuwa akayi sedai yasha wahal kafin ya samu shima akwai transit biyu kafin su isa inda zasuje. Akace Dama dama haka ya zauna yana jiran lokacin tashin jirgin, gani yake agogo baya sauri awa biyu yau seta zamar masa tamkar kwana goma. Lokacin da aka fara announcing tashin jirgi kuwa Sujjada shukriya saboda tsabar murna, a yanzu yana da hope he is only some hours away from home. *_HAMDAH AHMAD AMMANI_* Zaune gaban dressing mirrow. Kallon kanta takeyi tana karawa wai yau ita HAMDAH itace Amarya wai yau kamun bikinta za'ayi haka? daga yau ita ma zata shiga jerin matan aure? Dafata da Anty Zahra tayine yasata juyowa fuskarta dauke da qaramin murmushi da iya kacinsa lebe. Nasihar da Yah Abubakar yai mata jiya tayi matukat tasiri akanta. Bata san ya dawo gidan ba ya shiga dakinta ya tarar da ita tana sana'ar data zabarwa kanta yanzu kuka ta tasa pictute din Abdul'ahad a gaba. Cikin matukar tausayawa ya zauna a kusa da ita yareda janyota jikinsa ya shiga rarrashinta "Kiyi shiru ki gayamin me ke damunki" ya fada cikin kwantar da murya. Tana buqatar fitar da abinda ke zuciyarta kota ji sauki amma rashin wanda ze fahimceta yasa tazabi tayi shiru, tsaf ta zayyana masa komai data ke ji game da mutum biyu. Yah Abubakar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "tun farko kinyi wauta da kika amince da auren nan bayan zuciyarki ba a kansa take ba amma abin tambaya shi wancan din yana ina? Idan kika fasa wannan kina da tabbacin shi dagaske yake ze aureki? Yana ma ina a yanzu Hamdah kiyi tunani. Nasani ko ana tsakiyar taron daurin aurenki in har kika furtawa Abba baki son Auran nan se an fasa shi bazeyi miki dole ba amma ki tuna abinda ze faru, ki tuna irin mutanen daya gayyato, ki tuna kudaden daya kashw duk dan ya faranta miki Hamdah kinga gidanki kuwa? Kin san abinda Abba da Momy suka zuba miki kuwa. Na tabbatar sunyi ne dukka saboda kaunar da suke miki, yau ace wani suka dakko suka aura miki baki sanshi ba Hamdah ke me karba ce ki musu biyayya ko dan saboda fifitaki da sukayi a cikin mi 10 dasuka haifa. Babu wanda be san banbancin da ke tsakanin ki da mu ba dan Allah karki karya musu zuciya, karki zubda musu a kima ta hanyar fasa auran nan. Ke kika kawo shi ke kika zabo shi babu wanda ya tayaki Hamdah karki sa ayi miki dariya ki rufawa kanki wannan asirin karki zubda mana da kimar gidan mu saboda son ranki. Kowanne bawa da yana *QADDARAR SA* take ba kowa ne yake samun abinda yake so a rayuwa ba, ki tuna wani baya haifar dan wani in da rabo ko kwana daya ne se kinje kinyi kin samo shi. Kiyi hakuri ki sawa zuciyarki kamar baki taba sanin wani Abdul'ahad ba a rayuwarki, ki Dauki wannan a matsayin *_RUBUTACCIYAR QADDARAH_* Cikin kundin rayuwarki idan a rabo a tsakaninku ubangijin daya hadaku ya kuma raba ku a sanda yaso shi ze kara hada ku, he will surely re-unite you again". Tunda ya fara take kuka har ya gama, ta yarda da duk wata kalma daya fada ta kuma qudurce a zuciyarta zatayi hakuri. Abdulmalik ya isa masoyi yakuma cika dukka alkawarin daya daukar mata. Insha Allahhu zata goge guru da duk wani abu daya shafeshi a rayuwarta, she will live as if she never knows him, zata juyarda zuciyarta ga mijin da zata aura komai wahala kuwa insha Allahu baze taba samunta da wata gazawa ba. ***************** Hawayen daya taru a idonta saka makon tunanin data tafi ne ya fara zuba akan kyakykyawar fuskarta, tissue paper Anty zahra tasa ta fara share mata tana cewa "yah haka kukan kuma na me nene kedai kin zama ruwa ruwa wallahi duk zaki bata kwalliyar bayab kinyi kyau sosai haba Hamdahn Abbah". Dole tayi murmushi tana qoqarin mikewa tace "Na gode Anty" hannunta ta kama suka fito daga dakin tana qara gyara mata zaman kayan jikinta. Duk Wanda yake zaune a palour seda ya yaba yanmatan guda biyu kamanninsu daya in banda haske da Hamdan zata fi zahra kadan se kuma yar kiba da ita zahran ta fita dan ita ta haihu. Amarya Hamdah sanye take cikin hadadden Iro and Buba na asalin yarabawa kalar mint green da duwatsu Orange da silver, takalmin kafarta da kuma purse tareda sarkar da ta saka ta danyar azurfa suka kara kawata kwalliyar tata saifa beads manya Orange data kara akan sarkar tayi kyau tamkar ka sace ta ka gudu se walwalu takeyi . Zahra kuwa da code lace ne kalar light purple a jikinta da sukayi iri daya ita da Hamidah uwar rawar kai da tana hango su ta nud gurin da gudu suka saka HAMDAH a tsakiya sai ga Mumcy tana share hawayen dayakasance na tsan tsar farin ciki kallon Abbah tayi tace "Prof look at our kids" "All grown up " ya fada cikin muryar dake nuna tsantsar farin ciki dan gani yake kaman yafi Dr Maryam murnar wannan rana. Yayansu mata uku kenan da Allah yabasu su aurar da daya yau gashi suna shirin aurar data biyu addu'a yayi a ransa Allah ya bashi aron rai yaga auran Hamidah kamar yanda yaga na yan uwanta. Gurin suka qarasa suka shiga daukan hotuna da sauran Yayye da kannenau Maza da kowanne ya hade cikin shaddar da sukayi anko su Khaleefa babban abokin amrya harda babbar riga, ita kanta me gayyar Dr Maryam ta cakare ba kadan ba tayi kyau kai bazaka ce ita ta haifi wadabnan zan kada zankadan samari da yammatan ba. Ganin Khaleefa baze gaji da daukan hoton ba yasa Anty Amna taja Amarya suka fita zuwa harabar gidan inda ya dau decoration na kamu kai bazaka taba cewa cikin gidan Prof Ammani ne ba.