Sashe 30
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daga asibiti se yau ya shiga gidan bayan kwana hudu. Sannu da zuwa tayi masa ya dago kansa dake barazanar tsagewa biyu ya kalleta tausayinta na kara shigarsa, duk se yaga ta rame se dogon hancinta daya kara fitowa da ido dama ga azumi. Kallonsa takeyi kaman zata fashe da kukan tace "Jaan an kusa shan ruwa gashi banyi maka komai tun dazu kaina yake ciwo na kasa shiga kitchen sedai bari nayi sauri ko chips da tea ne nayi maka".yunkurin sauka daga jikinsa ta shigayi, se ya kara rikota yayi yace "Relax bari muyi sallah se mu fita muci abincin a waje kawai...." "Jaan muje gidan Mumcy to" ta katseshi da sauri. Seda ya karanci yanayinta sannan yace "Ok, but promise me you won't tell her anything..." "I promise" tayi saurin da katar dashi. Se ya mike da ita a jikinsa. Ruwa da dabino kadai suka sha sannan sukayi suka nufi gidansu Hamdah. Kaman koda yaushe suna zaune gaba dayansu a Babban falon gidan, katuwar darduma ce shimfide se kalolin girke girken da Mumcy tayi cikin kwanciyar hankali suke Buda bakin suna yar hira jefi jefi. Da sallama suka shiga falon Adil(Dan Yaya Abubakar) ya tashi da gudu cikin gwarancinsa yana cewa "Ga Aunty Hamana" ya fada jikinta ta dagashi sama suna juyi a gurin itama tana "oyoyo Adalina oyoyo". Cikin girmamawa ya gaida surukannasa sannan suka shiga cin abincin Dan dama hakan ba bako bane a gurinsa, duk sanda zezo tare ake cin abinci gaba daya. Bayan sun kammalane mazan suka tafi masallaci Dan gabatar da sallar Isha'i tareda tarawi sukuma matan sukayi tasu a gida. Aunty Najma matar Yaya Abubakar ce ta kalli Hamdah cikin kasa kasa da murya tace "Mutuniyar yanaga kin rame kodai mun samu karuwane dan wannan ya wuce ramar azumi" se kawai tayi murmushi tana kokarin danne abinda yake a zuciyarta. "A'a wlh Maman Adil banida komai kawai dai azumin na bana ne yana Dan wahalar dani". bata matsa mata ba suka shiga wata hirar daban. Suna shirin tafiya ne Mumcy tayi kiranta daki, abin da da mahaifi tunda suka shigo gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba ganin irin ramar da Hamdan tata tayi Dan Haka ta tsare ta da tambayar meyake damunta inda ita kuma ta kafe akan azumine. Ganin bazata bata amsa ba yasaka tace "Toh ya batun asibitin kundai je kuma ba wata matsala ko". Se kawai ta saki kukan da take ta dannewa. Bazata iya cigaba da barin abun a zuciyarta ba taba buqatar abokin shawara. Kuka ta sakawa Mumcyn tana cewa "Mumcy na shiga uku ashe nice banida lafiya yanzu bansan yanda zanyiba Hajja ta tsaneni Mumcy a gurinsa kadai nake samun farin ciki a cikin gidan". Cikin matukar tausayawa take rarrashin yar tata tana gaya mata kalamai masu kwantar da zuciya "Haba Hamdah kidena fadar haka. Bafa ke kika dorawa kanki ba kuma ai bacewa akayi baza ki haihuba kuma baya doraki akan magani ba" kai ta daga mata Dan bazata iya magana ba seta ci gaba da cewa "To kiyi hakuri ki fawwalawa Allah lamuranki komai kikaga ya samu bawa a rayuwa toh RUBUTACCE ne bawanda ya isa ya tsallakewa KADDARAR sa kima godewa Allah yaron nan yana sonki kuma dai bawani abin muzgunawa da yake miki, kiyita Addu'a nima kullum Ina miki kinji Insha Allah jinkirin alkairine kinji Hamdan Abba". Share hawayenta ta shigayi sannan tace "Toh ni Mumcy fa bakomai ke damuna ba illah nasan yanzu zasu saka Abdul ya kara aure" dariya Mumcy tayi sannan tace "Kuji min ja'ira Ina anan ke kike cewa Abbanku ya yomin kishiyar se yanzu zakice ke bakya so toh indai wannan ne dakaina ma zance masa yayyo miki Amaryar". Se kuma tashiga yiwa Mumcy shagwaba kuma tabar kukan dama haka Mumcyn take so Dan haka tace "Kicire batun kishi daga ranki ba abinda ze kareki inba lalacewa ba ki dage da kyautatawa mijinki tunda yana sonki duk ma wacce ze auro da halinta zata zauna kinji bana son shirme ki kuma tsayar da hankalinki guri daya dan Allah kisamu ki Maida wannan kasusuwa". da haka sukai sallama suka tafi hankalinsa be kwanta ba seda tagaya masa yanda sukayi da mumcy "Amma babe Meyasa kika gaya mata Baki tunanin hankalinta ya tashi" "No Jaan I know my mum ko Abba bazata gayawa ba sannan tace na tura mata maganin ta gani kaga ita ma zata qara taimaka mana da duk abinda ya dace. Seda suka biya gidan Afeeya da shekara daya data wuce ta Auri wani Abokin Abdulmalik din. Sun sameta tana jan Katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe. Tausayinta ya kama Hamdah duk ta kumbura tayi baqi haka suka baro gidan lokacin har 11pm tayi. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Some days later. Bayan sauraron sanarwa daga sarkin musulmi a safiyar ranar ta Juma'a aka tashi dashirin yin Idin karamar sallah. kamar kowanne gari kuma alada ta dukkan musulmi duk inda ka shiga zaka tarar ana girke girke saboda wannan biki mai girma haka take a gidan Abdulmaleek ma karfe 8:00am na safiyar ranar uwargida Hamdah ta gama shirya mijin nata cikin wani rantsatstsen yadi kalar coffee daya kara haska farar fatarsa, zaman hularsa kansa take gyara masa tana bashi wani labari wayarsa tayi kara alamar kira. Daga wayar yayi ya kara a kunnensa yana doka mata murmushi kamar wawa daga daya banga ren akace "To Tattabara kai muke jira" inji Umar. "Gani nan fitowa yaya" ya fada tareda kashewa wayar. Kaman yanda yake aladar su tare suke tafiya sallar idi gaba dayan mazan gidan in har kana Kano kuma anan Family house din suke haduwa ire iren wadannan abubuwan suke saka mutane ganin kamar kansu a hade yake dukda a bangaren mazan basu da wata matsala sosai. Cikin sauri yai pecking goshinta yana cewa "Babe labarin nan baze kare ba bari in muka dawo se a qarasa take care kinji" yai waje. Kitchen ta koma inda twins ke tayata girke girken sallah. Kafin wani lokaci sun gama, ta zuzzuba na ko ina sannan suka kara gyara gidan tsaf sukayi mata sallama ita kuma tashiga wanka. Seda ta gama sille jikinta sosai sannan ta zauna ta shiga zana hadaddiyar kwalliya a kan fuskarta Wanda rabon da tayi irinta har ta manta. Cikin dinkunan dayayi mata na sallah ta dauko wata Gezner kalar Army green datasha swovriskey stones daga sama har qasa dinkin doguwar riga se walwali takeyi. Sosai ta fidda mata da shape dan rigar ta shawu sosai dukda ramar da tayi hakan be hana rigar zauna mata ba tayi kyau Kaman ka sace ka gudu. Daurin data san yana so tayi wato ture kaga tsiya ta saki dogon gashinta daya sauka har rabin bayanta. Seda tabi dukkanin ilahirin jikinta ta feshe da turaruka masu sanyi da dadin kamshi sannan da zura cogen takalmin daya dace da kwalliyarta. Babban palour ta fito dan tasan duk inda yake yanzu yana hanyar dawowa gida. Tana kitchen tana qara goge Warmers din data zuba musu abinci tajiyo sallamar khalifa tareda abokanansa guda biyu. Seda ta yafa mayafin data dakko saboda hakan sannan ta fita har sun zazzauna. Seta kalleshi fuskarta dauke da murmushi tace "Oh su leefa yaushe a gari dawowa ba sanarwa" . Murmushin yakeyi shima yace "Wlh jiya na dawo da dare fa Mumcy take cemin kinzo baku dade da tafiya bama shiyasa yanzu ana sakkowa na taho kinsan I missed you is so much dinnan". " Kaji dashi" ta fada tana qoqarin mikewa bayan sun gaisa da friends din nasa. Abinchi ta kawo musu da drinks suka kuwa zage suna ci suna yar hira jefi jefi yana mata labarin Cyprus in da yake karatu. Har suka gama cin Abincin Abdulmalik be dawoba Dan haka ta hadashi da abinchin su Mumcy harda na Maryam tace dan Allah ya biya ya kaimata. sai kusan goma da rabi ya shiga gidan hakuri ya shiga bata kan dadewar wai sun biya gaishe gaishene Se santin kwalliyar tata yakeyi ita kuwa wani dadi takeji bakinta ya ki rufuwa. Bayan sun gama cin abincine yace ta dauko gyalenta su shiga cikin gida dukda bata so hakan ba Amma bata da zabi gudun kar ayimata abinda aka saba musamman yau da gidan yake cike da jama'a shiyasa ma ko abinci tundazu ta bawa Isma'il Babban Jikan gidan daya shigo gaisheta tace ya kai musu. A babban falo suka tarar da yawancinsu Banda Hamshakiya Hajia babba dan haka cikin girmamawa ta shiga gaida kowa. Ta dai samu amsawar kirki daga gurin sirikinnata da kuma sauran yayyan mijinnata maza sai Hajia Shuwa da ke mata sannu da aiki da cewa abinci yayi dadi daga nan ta wuce domin gaida surukar tata tun batayi sabin laifiba. Tana zaune kaman yanda ta saba ta caba ado irin na manyan mata Gwala gwalai kaman zasuyi magana a jikinta, dama bata zaci amsawar gaisuwa daga daga Hajjan ba dan haka abin be wani dameta ba se kawai ta nemi gefe ta zauna, gajia tayi da zama gashi har lokacin be shigo ba yana can sun tsaya da su Ahmad Bestfriend dinsa daya zo se kawai ta mike da niyyar komawa gidanta daidai lokacin da Abdul da Ahmad se wani da bata san sunansa ba amma taga suna Yanayi da yan gidan suka shigo. "Zo ki kwashe gayyar tsiyar da kika kawo Dan ni baza'a shanyeni yanda aka shanyemin da ba" Hajja ta fada tana nuni da hadaddun food warmers din dake ajiye a gefe wanda ta zubo mata abinci da alama yanda aka ajiyesu haka suke ba'a taba ba. Seta kasa tsayawa dan ta fara gajia da irin wannan cin fuskar. Idan su mutanen gidan an gama zubda mata da kima a gabansu Ahmad fa da wannan bakon da bata ma san matsayinsa a gurinsu ba. Tana jin lokacin da take cewa "Oh ga yar iska tana miki magana kinyi gaba ko Idan uwarki Maryam ce zaki shareta ne ki wuce". Duk yanda taso ta danne hawayenta ta gagara Dan haka tabarsu suka fara zarya akan fuskarta, ta kofar kitchen ta fita dan tafi mata saurin komawa part dinsu dan a lokacin bata burin ta hadu da kowa. Durkusawa yayi ya hada kayan cikin basket din da aka kawo su cikin sanyin jiki ya miki da