Sashe 13
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanda ta bude baki cike da mamaki ne ya qara bashi full access to her mouth, kaman wanda aka tsikara lokaci daya hankalinta ya dawo jikinta hawayene ya shiga zubo mata kafafunta suka shiga rawa. Jin tana neman faduwa ne ya sakashi rabuwa da ita ya rungumeta tsam a kirjinsa ji yake inama yana da ikon Bude zuciyarsa ya sakata a ciki kawai ya huta. Kuka takeyi sosai ajikinsa da bata san na menene ba, haushin abinda ya mata ne ko wani dalilin na daban oho. Kamar yarinya haka yaringa bubbuga bayanta yana shafa kanta yakasa bude baki yai mata magana, ji yakeyi kamar numfashinsa ze dauke. Yasan be kyauta ba, abinda ya mata be kamata ba kwata kwata amma ya zeyi, kaunarta tayi masa yawa in har yana tare da bashi da burin daya wuce ya ganta a jikinsa. Ganin taqi yin shiru ne ya bude baki dakyar yace "you want me to do it again?" Setayi saurin tsaida kukan ta dago fuskarta ta kalleshi. Murmushi ya mata sannan yasa hannunsa ya fara goge mata hawayen fuskarta. Duk inda warm hand dinsa ya taba a fuskarta setaji shock har qafarta ba shiri ta saka hannu ta goge hawayen dukka sannan ta nufi hanyar fita "Wait" ya tsaida ita, wayarsa ya dauka sannan yayi gaba tana binsa a baya. Gurin motar sa ya nufa bata da zabi dole ta bishi dan yanzu tsoronsa takeyi, har kofar gida ya ajiyeta be mata magana ba ya juya yai tafiyarsa. Tun daga wannan ranar be sake kiranta ko a waya ba sannan ko a cikin school bata kuma ganinsa ba har suka gama exams. Wannan karon ganin tana da lokaci kuma ba ta da wani abu a gabanta ya shirin tafiya Kaduna gidan Aunty Zahra (yayarta). Rabonta da ita an dade tun bayan da Zahra ta haihu tazo wanka gida. Basu dade da dawowa Kaduna da mijinta ba bayan sun je karo karatu ita dashi a Cyprus. Sosai takejin dadin zaman gidan kodan yanda Antyn da mijinta har ma da twins dinta Amrah da Afrah suke ji da ita.Tayi yawo Sosai samari kuwa ba'a magana duk inda ta shiga kamar zasu cinyeta Amma ita bata su take ba. Mutum biyu da suke rayuwarta ma sun isheta a yanzu, she got the best men ever se wanda ta zaba a ciki. Seda tayi sati hudu cif sannan ta fara shirin dawowa kano shima saboda Umarar da zasu tafi da Mumcy da Hamidah. Dawowarta ta tarar da Yah Abubakar a gidan ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi. Tsilli tsilli tayi tunkafin ya mata magana Dan bata manta rabuwarsu ba da kashedin daya mata akan tsokana dakuma motar da ta dauko ta ajiye Dan haka tanajin Hamidah tazo kiranta tace "Yah Hamdah kizo inji Big bro kikarbi tsarabarki" ta karasa tana dariya kasa kasa. Harararta tayi Dan tasan sarai bawai kiran Allah da annabi bane Akwai wata akasa Dan haka ba bata lokaci ta fita kiran nashi. Yana zaune a dakinsa ya tasa computer a gaba yana aiki ta shiga, gefe guda ta rabe ita bata shiga ba bakuma bata fito wajeba adduarta Allah ya kawo abinda ze fitar dashi yanzu. Seda ya gama abinda yake sannan ya daga kai ya kalleta "Wato kin rainani ko Hamdah?" Girgiza kanta tayi alaman A'a "Will you open ur mouth and talk or not kinamin nodding Kaman wani abokin wasanki" ya fada on top of his voice. Tuni jikinta ya dauki rawa "what did I told you the last time?" Wanna karan ma shiru tayi bakuwa tayi auneba taji saukan bulala a bayanta aikuwa ta daka uban tsalle tareda ihu tai hanyar kofa sedai yarigata tuni yarufe kofar tareda cilla key din aljihunsa. "Ba magana nakeyi miki ba" babu baki magana, shiru tayi masa in banda gunjin kuka da takeyi hakan kuwa ya tunzura shi yashiga dukanta babu ji ba gani ita kuwa in banda ihu ba abinda takeyi. Gaba dayansu suna tsaye kofar dakin yayan nasu tausayinta fal ya cikasu sunsan halinsa bashida dadi in ransa ya baci bare ita da ya dade yana kafawa warning. Baffa ne ya fara bugun kofar tareda rokon yayan nasu akan ya bude Amma yai banza dashi Hamdah kuwa zuwa yanzu tayi laushi Banda Kukan wahala ba abinda takeyi. Mumcy da shigowarta kenan tajiyo kukan yar gaban goshinta ko parking bata karasa ta nufi part din da sauri, bata bi takan suba tanufi kofar tana bugawa "Abubakar ka bude kofar nan kashemin ita zaka yi ko yaya nace ka bude". Jin muryar Mumcy tasata kara dagewa tana kwala ihu cikin kukan nata ne tayi subutar bakin yi masa Allah ya isa harda tukwuicin Azzalumi ai nan yafara tamola da ita tamkar ya samu Dan uwansa namiji Mumcy ganin babu sarki se Allah yasata fashewa da kuka tana kiran sunan Abubakar din abinda yasashi dakatawa kenan ya bude kofar ya hankado musu ita. Jikin Mumcy ta fada tare da sakin kuka, abinka da farar fata gaba daya fuskar nan tayi ja ga kwanciyar jini aduk inda ya doketa. Dakinta ta jata Hamidah tasa ta kawo mata ruwan zafi da towel tashiga daddanna mata jikin sannan ta bata pain killer tasha se fa sannan suka samu saukin kukan sakamakon baccin daya dauketa. Ba karamin Fada ya sha ba kamar shima zata dokeshi, Abba kansa seda ya kira shi a waya ya masa fada sosai akan abinda yayi shikansa se a lokacin yayi dana sanin dukanta yarinyar ce bata ji, zuwa yanzu yaci ace ta dena abubuwa da yawa da takeyi amma kullum qara gaba haukarta takeyi. Haka ta ringa jinya da fin rabinta sharri me kawai duk tabi ta dagawa kowa hankali a gidan, Allah sarki Abdulmalik haka ya koma kamar wani bawa duk bayan kwana biyu seya zo kano dubata har ta gaji ta warke. Sosai ta matsawa Abdulmalik lamba dan yanzu ya dawo kano da aiki dakyar bayan yarda da sharadin da Alhaji ya kafa masa. Ya yarda ne kawai a irin nasa wayon kafin ya samu mafita. Dan haka ya Dawo kano da Full hope din samun muradin ransa haka ya cigaba da aikinsa hankali kwance. A wannan lokacinma zaune yake gaban Alhajinsu dayai shiru yana kallonsa. "Wato Abdulmalik ni kamaida karamin mutum ko in ce maka kaje kaga yarinya jiya ashe baka jeba naga alamar so kake kanunamin iyakata ko sau nawa kakeso nayi Maka tuni akan aure?" Shiru yayi yana sauraron yanda mahaifin nasa ke ta sababi seda ya gaji Dan kansa yai shiru sannan yace masa "Alhaji wallahi mantawa nayi kuma na zata zuwan nawa ba wai wani me muhimmanci bane"...." Me muhimmancin uwarka ba ce maka nayi kaje kaga yar gidan Excellency ba ku fahimci juna" Alhaji Kamalu ya katseshi cike da masifa. Se ya daga kai ya kalli Alhajin, cike da in'ina yace Amma dai Alhaji ka mantawa kayi Ai nayi maka magana nasamu wacce muka daidaita". Wani kallon you are not normal ya watsa masa sannan yace "Au to haka akayi ai ban sani ba to wacece ma I mean waye ubanta a garinnan?" "Alhaji Sunanta Hamdah kuma yar gidan Prof Ahmad Muhammad Ammani ce" "Prof Ammani dae Wanda nasani" ya tambayeshi yana gyara zama. "Eh Alhaji shi na nan Tudun-yola" ya fada cike da murna a tunaninsa ya yarda ne. "To ban amince ba". Tamkar saukar aradu haka yaji maganar begama recovering daga shock dinba ya kara masa da cewa "Wato tsabar rainin hankali dama akan wannan yar tsohon bayahuden kake neman tozartani kaki yar Aminina ko? me wani professor ya tara bare har mu amfana dashi iye. Yara nawa aka kawo maka yayan hamshakan masu kudin da duk inda ka zaga a Nigeria ansan dasu amma kaqi ina nan uwarka yar dan takarar Governor take nema maka kaqi....." "Alhaji ai shima din a duniya ma duka ansan dashi saboda iliminsa" yai saurin katse Alhajin. "Ilimin ubanka mezan karu dashi a ilimin nasa to tun wuri inma zaka chanza tunani kayi kazaba cikin biyu Ko yarinyar nan Aisha yar gurin Matawalle ko kuma Firdausi Yar Alh Sanin Naira Dan kasan ni akomai Ina lissafin samu ba faduwa ba"yana kaiwa nan ya mike ya barshi a gurin. "Aikuwa babu ko daya daza ayi a ciki Dan tuni mungama tsara komai da Aminiyata zamu hadasu aure da yar gurinta" Hajja ta katse musu zancen. Fasa tafiya Alhaji yayi ya juyo yana kallonta sannan yace "Zancen Aminiyarki ai bogi ne tunda baki da tabbas din zasu ci zabe ko Aa, ga zahiri wayake lissafi da abinda babu shi". Kallo isa ta masa sannan tace " Ina dai Da nane ko ta abinda na yanke masa kenan kuma babu wanda ya isa ya chanza". "Toh ai ga fili ga maidoki se mugani wa yafi iko akan Dan "cewar Alhajin, nan fa gardama ta kaure tsakaninsu kowa yana fadar raayinsa za'abi shidai sunsum yafice aransa yana takaicin hali irinna Iyayensa da suka bawa kudi muhimmanci a rayuwarsy, qiriqiri sun mayarsa yayansu hannun Jari. Gashi Abin ya tsallake mata ya zo har kansu Mazan Allah dai ya sauwaka. ************************ Shiryen shiga Camp takeyi dan befi saura kwana uku su shiga ba. Zuwa yanzu ta jingine maganar Abdulmalik a gefe ta zubawa sarautar Allah kawai ido. Abubuwa ne suke ta faruwa rashin dadi sosai rigima ta tashi aka maganar auran Hamdah da Abdulmalik din. Har gida Alhajinsu ya taka wai yazo jawa Abbah kunne akan yarsa ta rabu da dansa dan shi yayi masa mata. Shidai abin dariya yabashi Dan haka yace masa "Bakomai Alhaji zan ja mata kunne karta kara zuwa zance gurinsa haka kiran waya na soke insha Allah bazata qara ba". "yauwa Ko naji idan ba haka ba duk abinda yafaru ita taja" cewar Alhaji Kamalu. "Babu abinda ze faru se alkairi Insha Allah". Da Haka sukayi sallama Wanda se bayan ya tafi yagane ashe Magana ce Prof Ammani ya fada masa, wato dansa ne yake zuwa zance Dan Haka Shi za'a yiwa magana. Basu gayawa Mata abinda ya faru ba har se bayan tayi sati uku sun fito daga Camp tukunna. Da Nasiha Mumcy tasame akan ta hakura dashi Amma sekawai ta saka mata kuka. Ta rabu dashi ta kamawa? Zuciyarta ta turata ta kori Abdul'ad yanzu last option din zasuce ta bari? Seta kalleta hawaye