← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 62

Sashe 7

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yacewa Alhaji No akan wannan aikin ba. Yasan Mahaifinsa mutum ne me alfahari, ya gina yayansa domin kaf dinsu babau me qaramin aiki. Hatta Me aikin Likita a gidansu Yana da asibitin kansa. A cewar Alhaji KAMAL DALA kudi sune maganin komai dan haka ze kashe ko nawa ne akan yayansa ya gina su su samu aiki me kyau yasan ze maida abinda ya kashe. Satinsa daya da relocating zuwa Lagos kullum suna manne a waya. Voice call, video call aikinsu kenan. Dama ita tuni ta dena zuwa wurin aikin dan haka tana gida kome yakeyi haka ze kirata suna hira yana aiki. A daddafe yai sati biyu yazo kano amma be doshi gidansu ba a hotel ya sauka yai kwana biyu ya koma dan yasan in yaje gida Se Alhaji yayi tsirensa in beyi wasa ba. Bikin Maryam ya taso gadan gadan dan ma ankara wata daya akan original date din bikin saboda angon da yayi wata tafiya. Wannan satin ya kama bikin dan haka basuda zama, shiri sukeyi sosai Dan Ita ce zata fara aure a clique dinsu Burinta ya cika zata auri her dream Military Man. Yau za'ayi kamu, karfe 1am Dawowarsu kenan daga salon sun baje dakin Hamdah, dinkunansu suke dubawa da sukayi matukar kyau. Mumcy ce ta leka dakin tana cewa "yanzu ku yarannan baza ku tashi Kufara shiryawa ba bayan wannan kwalliyar aljanun kadai sekun bata lokaci". Da daddaya suka ringa wanka inda make up artists din dasuka dauko suka fara tsantsara musu kwalliya. Amarya Maryam na dakin Mumcy Wai Hamdah ce zata mata make up tsautsayi inji Afeeya, matar da bata taba yiwa kanta ba wai itace zata yiwa Amarya lallai yau akwai kallo. Ita dai Maryam bata qi ba dan dukda bata taba ganin Hamdah tayi ba amma ta yarda da ita. Tasan bazata bata mata ranarta ta musammanba. Tun suna secondary Alkawari tayiwa Maryam din cewa ita zata mata Make up din bikinta A lokacin su Aysha nata dariya. Tsaf tagama mata Make up din daya yi matukar kyau, ita kanta Maryam din seda ta kara kallon kanta dan batayi zaton ta iya make up har haka ba. Ita ta taimaka mata tashirya cikin hadadden din da aka kashe kudi gurin siyan shi kalan Dark brown Anyi mata Hadadden bridal skirt and and blouse. dauri tayi mata daya zaunu sosai Ya kuma dace da fuskarta sannan takarasa shiryawa. Silver jewerries din datayi anfani dasu ne suka kara kawata kwalliyar tata tayi kyau sosai. "Wow bestie kiinganki kuwa ki zauna yanzu kafin nagama Nawa yakara blending " Hamdah ta Fada sannan tahau nata kwalliyar, within few minutes tagama dan ba wani me yawa tayi ba, girarta bata buqatar carving abinka da me kyau dama. Ashoebe da sukayi na Atamfa Peach ta saka ta daura dankwalita sannan suka rankayo zuwa kasan Inda sauran yammatan Amarya suke. Zokaga yanda ake ruwan flash Dan babu Wanda beyi Mamakin kwalliyar da Hamdan tayi Amarya ba. Tuni Harabar gidannasu tacika da Yammata wanda dayawa course mates dinsu ne ae secondary school mates dinsu se kuma few family da friends na Islamiyya da unguwa dan nan suka saka meeting point na Yammata sannan ga motoci nan jere A waje da Ango ya turo dan daukarsu zuwa wurin Kamun ba bata lokaci su ka fara tafiya gurin bikin, wata hadaddiyar GLK ce baka wuluk ta tsaya akofar gidan, ko ba'a fada ba sunsan Amarya akazo dauka Dan haka Malam Sa'idu ya budewa motar Gate ta shiga ciki dan dakko Amaryar. Ita da Hamdah suka fito ta riko hannunta har suka qarasa jikin motar ta bude mata baya ta shiga sannan ta juya da nufin bin su Afiya "Beatie ae tare zamu tafi" Maryam ta fada tana gyara zamanta. "Ok bari na karbo wayana hannun Afeeya" "No kibari ki karba in munje can". Dole ta bude Gaban motar tazauna. Ko a bacci taji kanshin turaren Seta ganeshi ballantana ido biyu sedai kuma in hancinta ne yake mata gizo, hakan nema to meze kawo shi wannan Motar? Bata gama tunaninba muryar sa me sanyi ta kunnanta "toh Ango mu tafi ne ko baka gama santin kwalliyar Amaryar taka ba". Da sauri ta kalleshi Inda tajiyo muryar, Guru ne zaune ya hade cikin wata hadaddiyar Gezna fara sai maiko takeyi Ashe kallonta yake da wani irin expression akan fuskarsa data kasa tantancewa bata san lokacin da bakinta ya furta "ya salam". *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE 0 Gaba daya suka kalleta danjin yanda tafurta maganar da Dan daga murya. Maryam ce ta leko kanta tareda cewa"Yadai Bestie?" Seta girgiza mata kai kawai alamar babu komai dan batajin zata iya magana. Tuni zuciyarta ta fara irin bugun data keyi a duk lokacin da suke tare, kwata kwata bata da nutsuwa. Murmushi yayi Wanda sautinsa ya sakata juyowa Shima ita yake kallo, tun dazun yake karantar yanayin ta. He likes it when she is retless yanayin da fuskarya ke nunawa yana masa kyau seta koma kaman wata yar baby dake shirin yin rigima. Key yai wa motar suka fita daga gidan, seda suka hau titi sosai sannan ya kalleta, "Kinyi kyau" ya fada seka rantse bashi yayi maganar ba dan ko data juyo hankalinsa nakan Titi. Tafiya sukeyi babu me Magana da Dan uwansa se Dan kuskus din Amarya da Ango da kake ji.A zuciyarta Mamaki takeyi meya kawo shi bikin Maryam? Da alama yana da matsayi a gurin angon ma tunda gashi shiya kawoshi. Se a lokacin take tuna yanda suke gaisawa da Maryam, afarko har zagin Maryam din takeyi akan tana shishshige masa ashe abokin saurayinta ne. Tsayuwar da motar tayi ne ya sakata kallon window har sun iso wurin bikin The Afficient. A jere a jere motocin suka ringa shiga gurin, Anty Fatima kanwar Mamansu Maryam dince ta karaso jikin motar cikin fada tace "wai wannan wane irin iskancine tun dazu kun shanya mutane Abin karfe uku gashi har biyar tayi anata jiranku". Murmushi Hamdah tayi tana cewa "kiyi hakuri Anty kwalliya ce ta tsaida mu". "Kwaji dashi Kilan ma batayi kyau ba se ku shishshirya" tayi gaba abinta tana ci gaba da mita. Jeruwa yammata sukayi da abokan Ango bayan sun saka Amarya a tsakiya, Hamdah data gama shirya su tayi gaba abinta acewarta bazata bi yan rakiyar ba. Hannunta taji an riko ta baya "Hey yammata saurin me kikeyi Haj baki ganin yanda tsarin yake?" Se ta harareshi bata da zabi yanda ya riqeta in ma tace zata qi karshe kanta zata jawa attention dole ta dawo suka jera. sune a kan gaba. Tafiya take amma gaba daya zuciyarta na can tunani na daban, ba tayi aune ba seji tayi tayi Tuntube da stairs din bakin kofar tana shirin faduwa. Cikin zafin nama ya tarota ta fado jikinsa, yanda ya rude seka zata shine ya kusa faduwar, Dan har ya fita firgita "Be careful please waima tunanin me kikeyi zakije ki fadi kiyiwa mutane asara?" ya fada har Lokacin tana riqe a jikinsa. "Ai dai inna fadi ma kaina na fadarwa bakai ba ina ruwanka to" ta bash amsa cike da tsiwa. Se yai kaman ze turata Ba shiri ta qanq ameshi dan duk ta tsorata "Mara kunyar banza" ya fada yana dungure mata kai kafin ya dagata suka ci gaba da tafiya "Kai agaskiya ku tafawa wadannan couples dan sun birgeni kunga inda ake tattali" muryan Mc Masanzie ta karade gurin. Se a lokacin suka lura da gaba daya kallo ya dawo kansu, har ansamu wasu nata daukan su pictures harda masu video. Dan sun burge mutane ba kadanba hadin ya hadu. Da kyar ta daure suka karasa inda aka tanada domin zaman Babban Aboki da kuma Babbar kawa suka zauna. Duk se take jin ta a takure ido yagi mata yawa, gashi shima ya wani manne mata se cin magani yake kaman wanda aka bawa ajiyarta, yanda suke dab da juna har tana jiyo numfashinsa a gefen kunnenta ga kamshin turarensa da yabi ya addabeta. gaba daya a darare take, kusa da kunnanta ya matso yarada mata "kinga yanda Mutane suke daukan mu pics yakike tunani ranar namu bikin?" Da sauri ta kalleshi irin kallon "kasan me kake cewa kuwa" . Gira daya ya daga mata seta dauke kanta kawai dan taga alama rainin hankalin nasa yafara yawa. wai me ya maida ita ne? Kiran Kawayen Amarya da akayi ne Dan su yanke kudin kamu ya sata tashi. Bata qara yarda ta koma gurin ba cikin yammata ta shige suna ta having fun. Alhamdulillah anyi kamu lafiya cikin farin ciki sun sha rawa dan dama HAMDAH ba baya bace a wannan fagen Liqi kuwa samari sun mata shi kaman basu san ciwon kudinsu ba ko ita kadai ce mace a gurin. Koda aka tashi daga Kamun sam taki shiga motar Guru seda Maryam ta nuna bacin ranta sannan ta bisu suka tafi. A hanya ko sunga cuna baki in abin ya ciyota tayi tsaki tareda murguda baki duk ita kadai har suka dawo gidannasu daya ke nan suke zaman kawance. Kokarin bude motar takeyi Amma ta kasa saboda lock din daya saka Dan tuni su Maryam suka fice ita da angonta, kallonta kawai yakeyi harta gama kiciniya da kofar sannan taja ta zauna "toh ai se a bude wa mutane kofa su fita koh" Be kulata in banda ma Kwantar da kansa da yayi a jikin kujera yana binta da kallo, Shi dai tasa Qaddarar kenan, Allah ya jarabce shi da son wannan yarinyar. Jiyakeyi kaman ya shekara 100 beganta ba, ta masa kyau musamman dabe taba ganinta da make up ba se yai. samun kansa kawai yayi da janyota gaba daya zuwa jikinsa ya mata wani tight hug Kaman wani ze kwace masa ita. Pecking goshinta yayi lokaci daya ya saketa tareda danna lock din yace "ki kwana lafiya Allah ya huta gajiya and make sure kinyi mafarkina". Murfin kawai ta bude Daidai lokacin Yusuf din yadawo Da alama har sun gama sallama da Amaryar tasa, fuskar Yusuf data kalla ce tasata murmushin dole, stain din Jambakin Amarya dambarere a kan kumatun Yusuf din, Seda safe tayi masa sannan ta nufi cikin gidan. Sam bata biyewa surutun yammatan ba ta kammala duk abinda zata yi na kwanciya ta haye gado,wayar minti 5 sukayi da Abdulmalik
Chapter 7 · 0% Book details