← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 62

Sashe 12

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan maganarsa. Ba shiri ta mike daga kwancen da take. Abdulmalik namiji ne me tsananin dauriya tasan ba karamin abu ne ze karya masa zuciya ba. To kodai yasan relationship din ta Sir Abdul'ahad ne? Aa inda wannan ne bazeyi shiru ba se ya mata magana tabbas akwai matsalar data ninka wannan. Duk yanda zata tausheshi tayi karshe yayi shiru amma yaki gaya mata ainihin abinda yake Damunsa. Ce mata yai wai sonta ne ya masa yawa kuma ance in kanason mace da yawa baka aurenta, se tayi dariya "waya baka wannan philosophy din" "Nima haka naji friends dina suna magana" dariya tayi sannan tace "to ba gaskiya bane koma haka ne Mu zamu karya wannan tarihin, ka gayawa kowa LAYLA DA MAJNOON din 21st century zasu karya tarihi zamuyi aure" "Allah ya sa Hamdah na Allah yamallakamin ke bansan ya zanyi ba". Haka suka ci gaba da hirar su har tayi bacci. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 PAGE 0 "A ban garen Abdulmalik kuwa abubuwane suka cakude, bashida sauran hope a yanzu saboda ko a lokacin da ya tunkari Alhajinsu da maganar fata data yai masa. Nan take yace masa be amince ba, abinda yayi matukar tayar masa da hankali kenan Dan dama Hajja ta zana layin akan abun tuntuni tana da nata zabin datayi masa kuma tace indai be aure ta ba to sedai kowa ya rasa. Wadannan tunanin ne suka sashi gaba duk ya fige ya lalace ko karatun daya kaishi Moroccon be mayar da hankali akai ba. Kullum kirga kwanakin da suka rage masa Morocco da basufi 12 days ba. Allah Allah yake kawai ya dawo ayivme yuwuwa, a kwanakinnan yaga hankalinta ya fara karkata akan aure, be sani ba kodan sun kusa gama school ne. Tun dai waccan lokacin bata qara masa maganar ya turo ba so yanaso kafin ta waiwayeshi komai ya zama a kan tsari. Two weeks after Karfe 7pm tayi masa a gidannasu Hamdah. duk da rashin kirkin data shirya yi masa akan maganar turo iyayensa last week ya mata biris kamar ma besan ta fada ba. Ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba ranar, yana zaune kawai ta kirashi wai Abbah yace ya turo, haka nan ya ce to ya kashe wayar jikinsa yayi sanyi dan be san wane bayani ze mata ba. Ya gaya mata me patents dinsa are against auransu daga nan ta tsaneshi ta fasa auransa ko kuwa wata qaryar zeyi mata? Tun daga ranar suke wasan buya data kirashi gaisuwa ce kawai ze taking excuae yace mata yana wani abun har ta fara Zargin akwai matsala. A nata bangaren kuwa hakan ne kadai take ganin ze mata katanga da Guru. Bata buqatar wani ya gaya mata ta tabbata ta afka cikin sonsa unconditionally amma bazata bari duniya tayi musu dariya ba. Bazata bari masu cewa Yaudarar Abdulmalik takeyi ba suyi galaba akanta, zata Auri Abdul insha Allah shiyasa take so tayiwa kanta tsakani da Guru by fire by force. Jikinta ne yai matuqar yin sanyi da ganin yanayin sa. Abdulmalik din data sani Dan gayun Namiji meji da Ado shine ya rame yai Baqi ya lalace kamar wanda ya shekara yana ciwo. Fuskarsa ko arziqin gyara bata samu ba gashi buzu buzu da gani baya cikin hayyacinsa abinka da zuciyar da ta ginu akan soyayya nan da nan se ga Hamdah na kuka. Sosai ya rungumeta ajikinsa yana jin wani kaso na damuwarsa yana raguwa, seda ta tsagaita da kukan nata sannan tafara magana "Meya sameka Jaan baka da lafiya dama shine baka fadamin ba, kaga yanda ka lalace kuwa kalla wuyanka kalla fa duk ka zama Baqi" ta qarasa tana shafa fuskarsa. Kiss ya kaiwa idonta masu kyau sannan yace "Dear I was all alone komai ya juyamin karatun dana tafi ma na kasa, Alhaji yaki yarda da maganar Auranmu haka ma Hajja please my love karki gujeni komai wahala kinji" yakarasa wasu siraran hawaye nabin kuncinsa. Lokaci daya jikinta yai sanyi, seta kama Hannunsa ta riqe Sosai cikin nata sannan tace "Ur love is in my blood you know I can't live without you right? Put it at the back of ur mind Hamdah is yours and no one will change that fact expect Allah... zamu rayu tare kar wani abu ya qara daga maka hankali kaji Abdul dina". Kamar yaro haka yaringa daga mata kai dan yanzun kam har ta fishi dauriya. Wani bangare na zuciyarta ne yake gaya mata " kinga yanzu kin samu dama, babu me ganin laifinki ki rabu dashi kawai" dayar zuciyar ce ta kwabe ta da "Aa Hamdah karki zo ki aikata abinsa ze saka ki a dana sani, kiyi tunanin qaunar da kukewa junanku, wani hali kike ganin ze shiga?" Haka taita saqe saqe sedai tayi matuqar kokari wurin ganin ta saka shi farin ciki. Kalamai masu sanyaya zuciya suka ringa fadawa junansu tareda Alqawarurrukan zasu rayu da Juna for better for worse. Ya dade sosai dan har seda Abbah ya dawo da yake yana gari wurin shadaya na dare sannan ya mata sallama ya tafi. Ranar bacci qauracewa idonta yayi, tayi tayi ta yakice tunani daga ranta ta kasa. Abubuwa sun chanza mata gaba daya basa tafiyar mata yanda take so. Duk yanda ta so data tsaida zuciyarta akan mutum daya ta kasa dan Zuciyarta ta kasu gida biyu equally akan kowannensu. Abun ya mata nauyi da har take gani bazata iya saukeshi ita kadai ba dole ta sanar da Mamanta kuma babbar kawarta. Wani yammaci Mumcy na zaune a dakinta bayan ta taso daga aiki, abinci take ci Hamdah ta shiga dakin dan haka ta nemi guri ta zauna tana jira ta gama. Tunda ta shiga dakin take kallonta ganin yanda tayi rama se dogon hanci da idonta da suka sake fitowa, se taga kamar har haske ta qara tabbas akwai abin da yake damun Yar tata ta dade da lura da hakan amma sanin halinta na zurfin ciki yasa bata tambayeta ba. Har tagama tana karantarta seda tasha ruwa tai hamdala sannan ta kalleta da murmushi tace "Farar mace Fitilar gida, farar mace Alkyabbar mata" irin kirarin da Abbah yake mata yau itama ta dana dole hamdah tayi murmushi sannan ta gyara zamanta sosai tana kallon Mumcy tace "Mum wani abu ne yake damuna". Seta tattara dukk nutsuwarta tana kallonta tace " Inajinki daughter me ya faru?" Tiryan tiryan ta bata labarin Guru da abinda yake tsakaninsu sannan ta gaya mata yanda suke ciki da Abdulmalik a yanzu sedai ta boye mata maganar kin amincewar iyayensa. Kallonta Mumcy takeyi har ta kai aya sannan ta sauke ajiyar zuciya tace "Hamdah kinsan tun farkon haduwarki da Abdulmalik kin tuna abinda na gaya miki? Nace miki karki tsananta soyayya kuma karki tsananta kiyayya, shi aure wani sirri ne da Allah ya barwa kansa sani. Duk yanda kakai da son wani da son ka aureshi idan Allah be rubuta hakan ba babu me aiwatar dashi ko?" Gyada mata kai Hamdah data nutsu tayi sannan taci gaba "To ki miqa lamarinki ga Allah ki jajirce da addu'ar neman zabin Allah. Kar kuma kiyi gaggawa domin daga shedan take. Aure wani abu ne na har abada in yayi dadi zaka dawwama cikin farin ciki haka in akayi rashin dace wanda ba'a fata haka rayuwa zata karewa mace a cikin qunci. A matsayina na mahaifiyarki bazan ce miki ga wanda zaki zaba a cikinsu ba sedai zance ki barwa Allah zabi ki kuma bi abinda zuciyarki tafi karkata dashi, dukkansu Mazaje ne Hamdaj ko wanne kika aura a ciki nasan zaki ji dadin zama dashi amma a sanina kin fi son Abdulmalik haka nan shima yana sonki, na kuma yaba da nutsuwarsa amma ba wai ina Nufin shi Abdul'ahad din beyi ba A'a kinga ni ban ma sanshi sosai ba inga sau daya na taba ganinsa waccen ranar da muka gaisa ko? To kiyi addu'a ki kuma maida hankali kan karatunki karki bari wani abu ya dameki insha Allah zaki dace da miji na kwarai, zaki samu jindadi tamkar Yar uwarki Zahra. Kullum Addu'ata Allah ya aurar mun daku a inda zaku huta hankalina ya kwanta". Rungume Mumcy tayi haka kawai Hawaye ya shiga zubo mata. "Ya kuka kuma se kace yau ne za'a miki auran da Allah dagani ke matsalarki sakarci wallahi Aidai Se Abdul koma waye yayi hakuri da halinki" dariya ta tashi tana yi ta nufi dakinsu, a zuciyarta tana tuna kalaman Mumcy. Sedai tana ganin kamar Mumcy tafi na'am da Abdulmalik kodan shi suka sani oho, fasa shiga dakin tayi ta fita compound, inda motar Guru ke ajiye ta kalla nan take maganar da sukayi ta fado masa. Ana saura kwana uku su gama final exam taje office dinsa kai mishi Samosa dayace mata yana so. Seda yakai guda daya bakinsa ya gutsira sannan ya miko mata wai taci, seta girgiza kanta tana murmushi ta zauna akan kujerar dake fuskantarsa yanda yake cin abincin abin sha'awa, abubuwansa da yawa irin na Abdulmalik dinta, yanda yake tauna abincin a yangance kamar ana masa dole. "HAMDAH ki aureni" kalamar ta doki kunnenta, seta dago da sauri ta kalleshi. Yana zaune yanda yake akan kujerar still da Samosa guda daya a hannunsa yana ci. Ajiyewa yayi ya fuskanceta da kyau sannan yace "Hamdah Allah ya jarabce ni da qaunar ki a karon farko dana fara haduwa dake a rayuwata, ke kika zaunar dani a makarantar nan badan ke ba da tuni na barta. Nayi duk yanda zanyi na daure na kasa dan Allah ki amincemin wallahi ina sonki da gaske bada wasa ba". Kaman statue haka ta ringa kallonsa har bata san ya gama maganar ba, hannunta daya matsa ne ya sa ta dawo hayyacinta ta rasa me zata ce masa " Kin amince zaki aure ni?" Ya qara tambayarta seta janye hannunta da sauri zuciyarta na bugu kamar zata bula kirjinta ta fito. Jakarta ta dauka da wayarta dake kan table din zata fita cikin zafin nama ya isa gabanta ya riketa, kokawar kwacewa ta ringayi amma yaqi bata damar hakan dan haka ta bude baki da niyyar yi masa fitsara kana ya saketa ba zato ba tsammani sejin warm lips dinsa tayi akan nata without second thought ya shiga kissing nata as if his whole life depend on it.
Chapter 12 · 0% Book details