Sashe 25
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dama tana jira cikin Hanzari ta cimmasa yana dab da barin main falon, jin alaman mutum na binsa a baya ya sakashi tsayawa sannan ya kalleta "yadai" ya fada fuska a daure". "Ba komai dama rakoka nayi" ta fada tana gyara tsayuwarta. Se ya kalleta sama da kasa sannan yace "No bana bukata ba fita zanyiba gurin Matata zanje" yai gaba yabarta a tsaye kaman zata kurma ihu. Lallai ma ya raina mata hankali wato gurin matar sa ma zeje, kamar kazar da ruwa yawa duka haka ta juya cikin gidan, su Surayya dake zaune a falon sukace me zasuyi inba dariya ba. Ko takan Mahaifiyarta ta dake tambayarta abinda ya faru ba bata bi ba ta suri jakarta kawai tai ficewarta dan tanajin bazata iya qara koda minti daya cikin gidansu ba. Dole Hajia Hauwa tayi wa Hajja sallama suka tafi. Ko a mota inbanda kuka ba abinda take uwar nata rarrashinta Mansura kanwarta data gaji tai tsaki sannan tace "wai fisabilillahi ance daga Maleek dinnan babu wani namiji ne ko yaya da zaki bi ki tsangomi rayuwarki a kansa, mutum yace baya sonki to ki hakura mana ko ana dole Haba duk kin bi kin damu mutane wani yace kije inda yake ai Dama in ka nunawa namiji kana sonsa dole yama wulakanci bare ke ai dai ko bakida zuciya yakamata ki hakura haka... " "In naki kuma fa uwata Ina ruwanki koni sa'ar kice Dan ubanki" Haulan ta katse Mansura cikin masifa. "Allah ya taimaka" Sayyada karamar kanwarsu ta fada kasa kasa gudun kar fadan ya dawo kanta da haka suka karasa gida. Bangaren su Hamdah kuwa a kitchen ya tarar da ita, miyar dake kan Gas take juya wa a hankali tana bin wakar data kunna harda Dan taka rawa. Sosai ta burgeshi, yanda take juya jikinta ya masa kyau se kawai ya ciro wayarsa ya shiga yi mata video. Aikinta take hankali kwance ita bata ma San da tsayuwar sa ba se kamshin turarensa dataji ya fara yawa a kitchen din, tunawa da tayi ta fesa kadan yasa bata kawo shi din bane. Duk lokacin datake missing dinsa se kawai ta fesa turarensa hakan na rage mata kewarsa sosai. Kaman ance ta juya taga mutum jingine da Freezer yana doka mata murmushi ba shiri ta saki ludayin dan Harga Allah taji tsoro ko kadan bataji shigowarsa ba. Saurin karasawa yayi ya rungumeta yana dungure mata kai "Matsoraciyar kawai, da in da zakije" bakinta taturo sannan tace "To ai kaine banji shigowarka bafa ko karar motarka banji ba se kawai naganka kana kallona". Gaban stove din suka karsa still tana jikinsa ya shiga bude tukwanen yace "Me kike dafawa ne haka tun daga office nake jiyo kamshi duk yawuna yagama tsinkewa". Steamer ya bude, burabuskon shinkafa ne fari kal se tashin kamshi take. Tana kallon yanda yake hadiye yawu Dan tasan yanda yake son abincin, janye jikinta tayi ta dakko warmer din data ajiye a gefe tashiga juye hadaddiyar miyar Irish potatoe data ji nama yankan kanana dakuma vegetables, shi ya kwashe Burabuskon bayan ta diba wani a Warmers daban da zata kai wa Alhaji dan Yau yake dawowa. A tare suka jera kayan akan dining sannan suka shiga wanka. Suna tsaka da cin abincin sukaji sallamar Khaleefa shida Amrah da Afrah yaran Anty zahra. Da murnar narta ta taresu suka dan gaisa kamin a fara halin da aka saba yana kwasar girki yana kushewa harda cewa Abdulmalik ya nemi Pligil dan dakyar in cikinsa baze baci ba wannan jagwalgwalon. Seda yai sallar isha sannan yai mata sallama tana ta mitar meyasa Anty zahra bata biyo suba dama Hamida tasab inda ta ajiyeta, rabon data je mata har ta manta. Dariya yayi yana cewa sunfi kusa ai ita kuma Anty Zahra dare ne yayi shi yasa bata zoba suma din sun takurane aka kawo su kwanar mata. Washe gari a gidan Anty Zahra suka wuni se tsokanarta take wai kodai tare zasu juye irin wannan kiba da tayi haka (dayake itama tanada karamin ciki) dariya kawai tayi tana cewa "Haba Anty wallahi banida komai kawai dai hutune a haka ma fa Dan yanzu Ina fita aiki rana na dukana". Haka suka wuni suna hira sai bayan magriba suka tafi. Rayuwa nata garawa kwanaki na shudewa se gashi wai har ana ba tun shekara da auranta, babu abinda ya chanza cikin kulawar da sukewa junansu sai daima abinda ya karu, zuwa yanzu tafara damuwa akan maganar samun ciki. Wata biyu da suka wuce da tayi missing period harta fara murna sedai watan gaba sega period dinta yazo abin tausayi har kuka tayi yaringa mata dariya kuwa. Tuni ta gama service se zaman shiru duka babu dadi abokan hirar ta ta duk sun tafi makaranta Khausar ce kawai Autar su Abdulmalik a gida ita kuma ba wani shirin kirki sukeyi da ita ba dan kusan shekarunsu daya dan haka ta rainata hakan yasa take kiyaye duk abinda ze hada su. Ita kam ta qagu dan har Mumcy ta kira wai ta mata prescribing maganin da Zata sha ta samu ciki se kawai tayi dariya tace mata wai saurin me take ta jira setayi goma ma. Abinda ya qara mayar da hankalin ta akan tunanin tun wata ranar da Anty Amarya ke cewa Abdul din "Ni kuwa Abdul duk sa'annin auranku daga masu haihuwa se masu tsohon ciki mu kunki yo mana miji ko kishiya gashi dai Fatima ta haihu jiya da namiji naji ma wai sunanka za'a sakawa Dan" ta karasa cikin sigar dariya sedai tsaf yagane magana ce ta gaya musu shida Hamdan. Fatima Kanwarta ce datai mutuwar son Abdul din Amma yaki haka ta hakura sati dayane tsakanin auransa da nata shine yanzu ta haihu. Se yayi dan murmushi sannan yace "Haba dai Anty mudin nawa muke kuma auramma shekara daya kawai bari dai mudan kara hutawa tukunna kin babies din nan duk takura ce dasu suzo su hana mutum rawar gaban hantsi sudai Allah ya raya musu". Baki ta rike alamar mamaki ta daiyi shiru kawai, Mikewa shima yayi Dan dama tun fara maganar Hamdah ta shige gurin Mama Second wife din saboda suna shiri da ita babu laifi, ta fuskanci a fuska kadai Anty Halima ke nuna tana sonta amma a badini ta ringa yaba mata magana a fakaice kenan se yanzu ta gane dalilin saboda Be auri Kanwarta bane. Da yamma ya shigo gidan, A dakinsa ya tarar da ita a kwance rubda ciki, bayanta ya hau ya zauna ba shiri tashiga tureshi tana "Wayyo Mumcy ya ballamin baya wayyo Abbah ya fasamin ciki kuzo ku ceceni". Birkitota yayi yana cewa "Muga cikin Ina ne ya fashe" ya shiga yi mata chakulkuli tana dariya. Seda komai ya lafa sannan yace mata "meya sa dazu kika gudo kika barni". Seta chanza fuskarta zuwa kalar tausayi sannan tace "Jaan maganar Anty fa gaskiya ce, ya kamata musan abinyi ko asibiti ma muje a duba mu". Hade rai shima yayi ya riko hannunta yace "Look Hamdah bana son shirme kema kin fara daukar irin tunaninsu kenan, ita kanta datake miki maganar kin san shekararta nawa a gidan nan kafin ta haihu?" Seta girgiza masa kai alamar Aa sannan ya ci gaba "To rana Daya akayi auransu da Mami kinga Yaya Mansur ne Babban dan Mami yama girmeni da kusan 2 years, ita kuma Sharifa ce first daughter dinta inaga befi ta baki shekara daya ba. Koma ba haka ba kindai san baki kaini son ki haifarmin baby Girl me irin idon nan naki bako" ya karasa yana shafa saman idonta "To ki sauraramin da batun haihuwa yanzu, Allah daya bawa kowa ze bamu muma layi ne bezo kanmu ba kinji ko". "Naji amma dai Jaan yakamata dai muje gurin Dr mudai tabbatar da lafiyar mu sannan se muci gaba da addu'a kawai". Banza ya mata ya shiga bathroom tasan ba amsata zeyiba Dan haka ta Mike itama tashiga jera masa kayan gugarsa da aka kawo a closet. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 A haka rayuwa ta cigaban musu baya taba biyewa shirmenta in ta fara akan maganar ciki. Yaga alama harda zaman banzan da takeyi yake qara sakata abinda takeyi dan haka ya shiga fafutukar nema mata aiki wanda a farko yace bazatayi ba. Da alfarmar Prof Ammani da kuma result dinta da yayi kyau ta samu lecturing a nan Polytechnic ta fara zuwa. Hankalinta be tashi ba se ranar da Hajja ta tsareta da tambayar wai ta fa ji shiru haryanzu ba wani labari ita fa tana buqatar taga jikan danta Namiji, hankali tashe ta kira Mumcy tana kuka ta sanar mata abinda Hajja tace dakuma Abdul din dayaki daukan abun da muhimmaci. Rarrashinta taringayi tareda kwantar mata da hankali, misalai ta ringa bata akan bakowacce mace bace daga aure take haihuwa wasu ma sukan shekara biyar koma fiye da haka dakyar dai ta samu tayi shiru da alkawarin dakanta zata kira Abdulmalik tace suje asibiti. Sauri take ta gama komai dan tasanshi dan oya oya ne baya son jira. Tana tsaye gaban mirrow tana gyara daurin dan kwalinta ya shigo dakin, yayi kyau sosai cikin shaddar daya saka Brown se kyalli takeyi. "Yanzu fisabilillahi baki gama ba minti nawa na qara miki amma har yanzu kina nan har karfe 12 tayi bayan kekika azazzaleni ke zaki gidan suna". Jakarta ta zara tayi waje tana cewa "Kai Jaan kafiya mita wlh Kaman me tsohon ciki muje toh". Gidan Nasir kanin Abdulmalik Dan Hajiya Shuwa zasuje matarsa ta haihu yau ake suna. A kofar gidan ya ajiyeta Dan yace taron matane baze shiga ba sun hadu da Nasir din da asuba gurin radin suna. Kudi ya bata da yawa akan ta bawa me jego dukda ledar dayaga ta ciko da kaya zata kai mata. Gidan ya cika makil duk yawancin Faccalolinta sunje sannan ga yayan gidan mata dukka nan aka shiga gaisawa suna ta mata tsiyar wai ba'a ganinsu daga ita har mijinta sun buya ba gidan wanda take zuw. Murmushi tayi take ce musu wallahi aiki ne ya hanata fita. Jaririn dayaci sunan Alhaji suna kiransa Na'im aka mika mata tasa hannu da bismillah ta karbeshi. Zainab kanwa Abdulmalik da take binsa a dakinsu. Duk cikin yaran gidan ta fisu fitsara ita da