← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 62

Sashe 31

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

niyyar binta "Ina zakaje shanyayye wato an jika an baka kasha duk ka susuce yar gwal na kuka ko shine ga bita zaizai zaka wani kwashi kaya ka bita a baya toh tayi kukan jini ma bana hawayeba Dan abinci dai bazanciba wanda akayi a bayama Allah ya tsare ehe". Dolensa ya koma ya zauna Amma zuciyarsa na gurinta gaba daya tana gurinta Allah Allah yake su gama gaisawa dasu Ahmad su fita amma kamar ta shiga ransa se cewa tayi ma akawo musu abinci ta tasa su dole se sunci. A bangaren Hamdah kuwa kukanta tasha ta gode Allah dan abin ya zame mata jiki. Wayarta ta dakko ta shiga kiran yan uwa da abokan arziki tanayi musu bark da sallah. Wayar Afeeya takira tana dagawa cikin karadi tace mata "Uwar gidan Abdulmalik tun dazu nake trying wayarki bata shiga to ki taho ganin baby na haihu". Cike da karadi Afeeya ke maganar Dan haka tace mata "Toh uwar azakwai Nidai Allah ya kawo randa zan ganki a Labour room ko bakinki ze mutu haba ayi mutum da dan banzan surutu. "Wallahi dagaske nake nama tura miki pic din babyn tun jiya da daren nasan baki budeba shiyasa baki kiraniba". Ai lokaci daya duk wata bacin rai da damuwarta ya bace, sosai take murna lokaci daya tausayin kanta ya kamata. Cikin clique dinsu su hudu Maryam nada yara biyu Ga Afeeya ma tayi daya haka nan Aysha ma tana hanya ko yau ko gobe ita ce dai shiru haryanzu, bata san lokaci da hawaye ya shiga zubo mata "Allah ya raya Afeee me kika rokamin da kina labour?" Ta tambayi Afeeya muryarta na rawa alaman san yin kuka. Sai kuma jikin Afeeya yayi sanyi, dukda basu tabayin wata magana akan haihuwa ba amma tasan dole ita ma tana so. Kokari tayi na ganin ta kwantar mata da hankali karshema ta janye hankalinta da wata hirar. Sanda ya shigo yaji dadin yanda ya sameta tana walwala cikin doki take nuna masa picture din yaron Afeeya me kyau dashi. Seya dafe kansa sannan yace "Afwan wallahi tun cikin dare Habib ya kirani suna aaibiti gaba daya ke kika mantar dani kin tuna". Seta rufe fuskarta ai kuwa ya shiga mata dariya kamar tababbe. Ce mata yayi ta bari da daddare zasuje, hakan kuwa akayi yana dawowa daga Sallar Isha suka tafi ganin babyn da har suka dawo tana santin babyn. Kwanci tashi asarar me rai hakanan kwanakinmu suna ta karewa se gashi ana lissafin shekaru hudu da Auran Abdulmalik da Hamdah. A cikin shekarun zamu iya cewa babu abunda ya sauya tun shekaru biyu da suka gabata gidan aurannata dai se godiyar Allah. Cin mutunchi da wulakanci sedai in basuyi niyya ba a gurin wanda ya ajiyeta kadai take samun sauqi. Iya kacin kokari yan uwanta nayi dan ganin sun kwantar mata da hankali banda Yaya Baffa da yace shi sedai ma a raba auran baze zuba ido yana ji yana kallo yarinya qarama ta hadu da taskun Uwar miji ba. Abbah ne ya ke nuna masa da cewa kowacce mace da irin qalubaleb rayuwarta sannan in har sukayi haka sunyi Abdulmalik butulci. Iyakar qoqari yanayi akanta sautari yana ketare umarnin mahaifiyarsa akan farin cikinta dukda ita Hajja ita ce akan gaba kafin Hamdah a gurinsa dan haka su dai nasu su bita da Addu'a. Maryam aminiyarta data zamar mata tamkar yar uwa kusan kullum tana kan hanyar zuwa wurin ta kodan debe mata kewa kasancewar Yusuf ba mazauni bane uwa uba kuma Abdulmalik da bashida sauran sukuni indai ba yaganta cikin walwala ba. A koda yaushe tana kokari gurin toshe duk wata ka fa datasan zata hadata da mutanen gidan ko Sabga indai ba suje tare su tafi ba bata zuwa hakan kuwa kullum qara wutar tsanarta a zuciyar Hajja da yan korarta yakeyi. Sosai ta mayarda hankalinta kan aikinta wanda a da ta jingine yanzu Shi yake debe mata kewa Dan koba komai inta fita tana samu tayi walwala da mutane. Su hudu ne zaune cikin office din Malama Hadiza, Malama Ramlah, Malama Sa'adiya sai ita Hamdah magana suke tayi akan zaman takewar aure inda maganar duk akan Takurawa ce irin ta iyayen miji, labarai suketa kawo wa akan irin incidence din ita dai Hamdah nata ji gani dake Kaman da ita suke musamman lokacin da Sa'adiya take basu labarin wata makociyarta da uwar miji ta takura mata akan rashin haihuwa. "Ai kedai Hamdah ki godewa Allah da kika samu soyayyar dangin miji" cewar Ramlah. "Uhm" kawai ta iya cewa tareda murmushin yake Wanda akace yafi kuka ciwo Dan ita kadai tasan abinda yake damunta. "Yadai Malama Hamdah ni se nake ganin kaman kina cikin damuwa kuma bakiso ki sanar mana bayan anan dukkan mu babu wadda bata fadan matsalarta mukuma taya ta da shawarwari ko ba haka ba" cewar Hadiza "Kwarai kuwa wallahi nikaina na fahimci haka sedai nayi shiru ne tunda naga bata bukatar musani" Sa'adiya ta kara nata. Tasani dukkansu matane masu nutsuwa da sanin ya kamata Dan tun fara aikinta acikin department din kaf dasu kadai take hulda dukda dukkansu sun girme mata dan Malama Hadiza wacce suke kira da Anty ta kusa haifarta kuma Kaman yanda suka fada kowacce takan kawo matsalarta sukuma tayata warwarewa. zuciyarta ce ta bata shawara da ta gaya musu kilan ta samu mafita Dan haka cikin sanyin murya tashiga labarta musu salon zaman nata da surukannata. "Tab dijan lallai Hamdah kina cikin damuwa Amma ba komai Allah daya hukunta faruwar komai yana sane dake" Ramlah ta fada bayan data janye tagumin da tayi "Kwarai kuwa toh Amma shin wai meyake damun mutanenmu ne wai me aka dauki haihuwa ne? shin a tunanin su a san kanka zaka ki kaso ka haihune? Kodan gujewa irin wadannan gorin ai kaima ka ajiye Dan kanka Amma ba komai ki ci gaba da godewa Allah akan duk abin da kikaga ya sameki a rayuwa, ki kuma dauki hakan a matsayin wata _*RUBUTACCIYAR KADDARAH _* da baki isa ki kauce mata ba. Idan kika yi hakuri se kiga Allah ya saka miki da rabo mai girma kidauka hakan duk cikin bauta ne wani izgilanci da wulakanci na mutane karya raunata miki zuciya ki kuma dage da kyautatawa mijinki tunda shi be kyamaceki ba ahakan".Kuka ne ya kwace mata Dan maganganun na Anty Hadiza sun shigeta tabbas gaskiya ta fada kuma zata kara dagewa akan adduar da takeyi Allah ya bata ikon cinye Wannan Jarrabawa. Har suka tashi suna jimanta wannan alamari tareda bata shawarwari dasuka kara karfafa mata gwuiwa ita dai aranta godewa Allah takeyi daya hadata zama da mutane dasuka san ciwon kansu da haka ta karasa gida. Cikeda mamaki take kallon kofar part din nata da yake a bude, a iya saninta dai ta rufe ko ina da zata fita kuma bataga motar Abdulmalik ba alamar be dawo ba kenan, to kodai bada motar ya shigoba? Ta tambayi kanta, da wannan tunanin ta karasa cikin parlour sedai abinda ta gani ne yai bala'in daure mata kai. Matane zazzaune a falon sun baje abinci sunaci ko ina na falon yayi kaca kaca. kallonta takai kan kofar da zata sada ka da part din Abdulmalik din Wanda basu taba koda budeshi ba saboda da nata suke amfani wasu Maza maza ta gani suna fito da kwalaye datake tsammanin na kayan gado ne, bata karasa tsinkewa da Al'amarin ba seda taji daya daga cikinsu yana cewa "Hajia wannan fa dayan dakin baze dauki set ba sedai iya gado da Mirrow ne suka samu shiga". "Ba matsala Ina ce dai wancan Babban saitin dakin ya dauka ko?" Wata mace daga cikin matan me kama da kilaki ta bashi amsa. "Kwarai kuwa Hajia sema kin shiga dakin kin gani wallahi" shewa matan suka dauka gaba daya suna cewa "Se mu na gaske ba abinda za'a nunawa yarmu dai wallahi se farar fata da dogon hanci (niko nace ashe dai da abinda za'a nuna mukun Wani Jiri ne taji yana neman kada ita babu shiri ta nemi bango ta dafa, bata ko ganin gabanta ta nufi dakinta da sauri dan buri ta be wuce ta samu guri ta kwanta ba. Har ta shiga dakin ta nemi guri ta zauna cikin ta na wani irin hautsinawa kamar zatayi amai in banda kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" babu abinda take nanatwa. Addu'a take kar Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya Dan kuwa in haka ne Ina zata saka kanta?. Maganar Mumcy ce ta fado mata a rai zuwan da tayi ranar Sunday inda take ce mata "Ashe kuma mijinki aure zeyi shine baki fadamin ba". "Haba dai kiji Mumcyn nan kilan dai mafarki kikayi Abbah yayo miki Amarya Amma badai niba " tabawa Mumcy amsa.Tausayin diyar ta tane ya kama dan da alama bata sani ba itama dai bata da tabbas kishin kishin taji a gurin Mamansu Maryam da take kawar Kanwar Hajia Shuwa kishiyar Babar Abdulmalik din. Se kawai ta barwa ranta maganar tunda taga alamar bata da masaniya akai Amma tasan tunda Har taji kishin kishin din abin to Akwai kanshin gaskiya a ciki. Mikewa tsaye tayi cikin kidima tana qara tuna maganar da Sumayya ta fada mata wadda har fada tayi mata akan bata son irin haka karinga yiwa mutum fatan Alkahiri. Tunawa tayi lokacin da take ce mata "Nidai Anty Hamdah kome zaki fada sedai ki fada amma wallahi sekin tashi tsaye Dan wannan Hajia Hauwan da kike gani babu Allah aranta ko ita Hajja da kika ganinsu tare ba haka tabarta ba Dan haka inma zaki mike ki kwatarwa kanki yanci to tun da wuri kiyi in ba haka ba ina school zaki kirani ki bani labari" Hannunta ta dora akai ta fasa ihu iya karfi ta. "Nashiga uku ni Hamdah Allah ka kawomin dauki, kishiyi? Ni Abdul zeyiwa kishiya. lallai yau nayarda Namiji bashida tabbas Namiji badan goyo bane Abdumalik ka cuceni" ta qarasa tana fashe da wani irin kuka me ban tausayi. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 A gurguje ya shigo gidan duk a kokarin sa nason yarigata komawa dan shi dai kwakwalwar sa tagama kullewa tunda Hajja ta kirashi wai yau masu jeren Amarya zasuzo. Bai yarda da gaske take ba se a lokacin da Usman ya kirashi wai
Chapter 31 · 0% Book details