← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 62

Sashe 48

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tafi batare da an daura auran ba. Cikin ikon Allah Ni'ima ta samu sauqi kwanaki uku bayan kwanciyarta a asibiti. Dokoki sosai likitocin suka qara kafa mata idan har tana son rayuwarta kenan ita dai sedai tayi murmushi a zuciyarta tana cewa "Wace rayuwa ce kuma ta ragemin a yanzu ai na riga na siyi kasada daga ranar dana auri wanda baya sona" da haka aka sallameta suka koma gida. Be wani takura mata ba dan yanzu kaffa kaffa yake da ita duk da har yanzu yana so yasan ina taje a waccen ranar, shi se yanzu da hankalinsa ya kwanta ma ya tuno da ita amma se ya danne abin, yana ganin lokaci yayi daya kamata ya kalli rayuwa a yanda take, har zuwa yaushe ze cigaba da zama haka? He is 33 already ya kamata ya nutsu yayi setting family full of Love and Happiness "Amma your key to the happiness is missing" zuciyarsa ta raya masa. Kashe motarsa yayi dan yafi minti goma da shiga gidan dawowarsa kenan daga Abuja yaje gurin Baba dayai masa wani kiram gaggawa amma be shiga gidanba. Ya gaji zuciyarsa da gangar jikinsa suna da buqatar hutu a yanzu amma dole ya shiga ya gaida Ammi kafin ya qarasa nasa part din. Tana zaune kamar koda yaushe jikokinta sun zagayeta ko me sukeyi oho dayake ana hutun makaranta ne yawancinsu suna gidan harda Saudah dake US itana tazo da yayanta. Gaba aya yaran suka gaishe shi banda little da adole fushi take da Dadyn nata wai yaqi kaita gurin Berbie shima se ya shareta dan baya cikin walwala a lokaci Kallon tausayi Ammi take masa, gaba dayansa ya rame ga wata qasumba daya tara kana ganinsa dai kasan baya cikin nutsuwa sosai amma zurfin ciki irin nasa baze bari ya fadi damuwarsa ba. "Galadima" Ammi ta tsayar dashi bayan daya juya yana shirin barin palour se ya dawo da baya ya zauna. "Shiga dakina ka jirani ina zuwa" se ya miqe ita kuma ta shiga qarasa rabawa yaran Tatacciyar Madara me dumi da takeyi a glass cups. Lokacin data shiga dakin yana kwance rabin jikinsa akan gadon qafafuwansa kuma a qasa, idonsa a rufe ya riqe kansa da dukka hannunsa biyu. Try din data zubo masa kayan abinci ta ajiye akan madaidaicin centre table din da yake tsakiyar dakin qarar haduwar farantin da try ta sakashi ya bude idonsa yana kallonta. Abincin ta shiga zuba masa daidai yanda tasan ze iya cinciyewa sannan ta tsiyaya masa ruwa da lemo ta ajiye komai a kan carpet tace ya sakko. Seda ta wanko hannunta a toilet sannan itama ta zauna kamar qaramin yaro haka taringa Feeding nasa da hannunta ya ringa karba kuwa dan rabonsa sa abinci tun daren jiya kafin kace mene har ya cinye ta kuma qara masa wani. Seda ta tabbatar da ya qoshi sannan tabarshi tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi tace "Ko kai fa Babana amma da ka zauna da yunwa kaganka kuwa yanda duk ka firgice" jinginar da kansa yayi a jikin gadon wata soyayyar Amminsa na qara shigarsa. Tafi kowa damuwa dashi haka tafi kowa saninsa a duniya ita kadai ce take gane abinda yake zuciyarsa a kallo daya batare da ya bude baki yayi mata magana ba. "Yanzu kaje kayi wanka se ka dan kwanta ka huta in ka fita anjima a samu a dan rage wannan sumar tayi yawa" murmushi yayi yana shafa kansa da gemunsa sannan ya miqe bayan ya rungumeta kadan yace "Thank you Ammi, you are the best" seta shafa kansa itama tace "Allah yayi maka albarka yaba abinda kake so Babana" binsa tayi da kallo har ya fita daga dakin a zuciyarta tana fatan abubuwa su daidaita, lokaci kadan take jira ta kammala shirinta da kanta zata nemo masa farin cikinta tunda taga shi baze iya ba. Ta rigada ta samu address din gidan dan shine me wahala kuma gobe insha Allahu zataje da kanta ba aike ba. Kamar yanda tayi alqawari kuwa haka ce ta kasance da safe wurin shadaya ta dauki Little da Faheema yarinyar Saudah Driver ya kaisu Gidan Prof Ammani. Cikin girmamawa da sakin fuska Mumcy ta karbeta dukda bata santa ba. Seda ta cika mata gaba da kayan tande tande da lemuka sannan ta zauna suka gaisa sosai. "Sedai ban gane ki ba Hajia" ammi ta fada tana wasa da hannun Little data riqeta dan ta ganta Fara kamar Aunt Berbie. "Eh nasan baki sanni ba Hajia ni yar uwarki ce dan nazo neman arziqi ne gurinku". Cikin rashin fahimta take kallonta kafin tace "To haka ne amma ban gane abinda kike nufi ba wane abu kike nema haka Hajia? " Ni sunana Hajia Aisha Matar Yarima Abdullahi Aliyu" Cikin mamaki Mumcy take kallonta "Yarima Abdullahi dai wanda na sani ko wani daban" ta tambayeta. Se tayi murmushi tace "Shidai wanda kika sani din" nan da nan Mumcy ta qara Fadada Fara'arta kafin tace "Sedai kinyi rashin Sa'a Megidan bayanan dazu wurin 7 jirginsu ya daga sun tafi Switzerland na zata ma harda se Yallabai din a tafiyar tasu tunda kamar yace shine ze wakilci Masarautarsu ko" "Eh hakane amma shi se gobe in Allah ya kaimu ze tafi tukunna sedai zuwan naki ne bana megidanba". "To ina jinki Allah yasa dai ba laifi mukayi ba" "Ko kadan Hajia Alfarma dai nazo nema a gurinku ina fata zaku taimakamin" Ammi ta fada tana gyara zamanta dan taji dadin magana. "Haba Hajia ai babu zancen Alfarma a tsakaninmu, a irin Alkhairan Da Yarima yayiwa Prof Ai bana zaton akwai abinda zaki zo nema a cikin gidansa dai a kasayi muku sedai idan yafi qarfinmu kuma. Murmushin jin dadi Ammi tayi dab kalama mumcy sun qarfafa mata guiwa sannan ta fara magana. "Yaron gurina ne me sunan Galadima yaga yarinyar gidan nan yake so, to kinsan halin yaran yanzu da wutar ciki bata barinsu su samu abinda suke so inaga hali yazo daya ita zafi shi zafi dan haka sun kasa fahimtar juna to shi yasa naga gara mu shiga ciki tunda sun kasa daidaita kansu". Farin ciki ne fal ya mamaye zuciyar Mumcy, dukda Hamidah Sulaiman ne dan gidan Kanwarta Anty Mami yake sonta amma tasan ba wata matsala bane zata iya fahimtar da Mamin kuma ita kanta zatayi Na'am da abun saboda Nagartar Yarima Abdullahi da Ahalinsa, dangine da kowa zeso ya hada zuri'a dasu dan ma Allah be bashi Yaya Mazan da yawa ba se mata dan haka tace "Wannan ai ba komai bane Hajia da Har se kin taso da kanki amma tunda anyi hakan ma babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi insha Allahu da munyi waya da Abbansu zakiji yanda mukayi tunda yaran suna tare namu kawai tsaida lokacine amma kuwa bata taba gayamin ba yarinyar au kin ganta ma ana maganar ta" ta fada daidai lokacin da Hamidah tayi sallama ta shigo, se Ammi ta waiwaya ta kalleta, "Granny look at her she looks exacly like Aunt berbie but our berbie is more beautiful than her" Hamdah da tayi sauri ta isa gurin Hamidah ta riqe hannunta tana kallonta ce tayi maganar, murmushi Ammi tayi bayan da ta qaraso ta shiga gaisheta kafin ta samu guri ta zauna dan ta gaji. Surutu Little ta ci gaba daya tana fadar differences din Aunt Berbie da wannan ita ma Ammi kallonta takeyi dan dai kamar wannan tafi wadda take gani a hoto jiki sannan bata kai Hasken Hamdah ba amma bata sani ba ko dan Hoto ne dan haka seta kalli Mumcy take ta faman murmushi a ranta tana godewa Allah akan irin baiwar da yayiwa Yaranta. "Hajia nace wannan itace Hamdah ko?" "Aa Hamidah dai ko ai babbar ce Hamdah wannan kuma ita ce qaramar" miqewa Hamidah tayi dan bata san me suke tattaunawa ba ai kuwa little da Faheema suka bita. Seta maida hankalinta sosai kan Mumcy kafin ta ciro wayarta ta nemo hoton Hamdah sannan ta miqa mata wayar "Kalli kiga wannan nake nufi". Seda ta qarewa hoton Kallo sosai, Hamdah ce seta miqa mata wayar tana cewa "Wannan Hamdah ce kwarai itace gaba da wannan akwai ma Farouk a tsakaninsu kafin Hamidah" "Masha Allah itace wadda yake so to". Se mumcy tayi shiru na dan wani lokaci, taya zata fara gaya mata Hamdah tayi aure, dukkan nutsuwarta ta tattaro kafin ta fara magana "Hajia amma kinsan ita wannan din ta taba aure kuwa?" Gyada mata kai Ammi tayi tace "Nasani ta auri Marigayi Abdulmalik dan gurin Hajia Fattu Dala ko" Ammi ta bata amsa. "Kwarai haka ne to Hajia base mun tsaya wani dogon magana ba gaskiya ita wannan yau kwananta biyu kenan da sake daura wani auran jiya ta tare a Kaduna" se Ammi ta bude baki cikin mamaki tana kallonta, ta tabbatar Abdul'ahad bashida wannan labarin dan haka tace "Ya subhanallahi Hajia Maryam kiyi hakuri dan Allah wallahi bansan da wannan al'amari ba da babu abinda zesa nazo kuma na tabbata shima be sani ba dan da ze gayamin" "A ba komi Hajia nima kuma nayi mamaki Gaskiya dan ban san ma suna tare dashi ba mene sunansa na gaskiya?" "Abdul'ahad" ta bata amsa. "Ikon Allah ko shine yayi lecturing a BUK" Mumcy ya qara tambayarta. "Kwarai kuwa shine ae tsohon malaminsu ne tun tana budurwa kuwa suke tare". Se mumcy ta girgiza kai cikin tabbatarwa kafin tace "Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi tabbas nasan shi idan ban manta ba ma shine wanda ta dakkowa mota shekara biyar tana nan a ajiye bezo ya dauka ba, akwai ma kyaututtukansa da yawa da yayi mata duk sunanan anan gidan sedai gaskiya banida labarin ya qara dawo wa nemanta a karo na biyu da ban bar wannan al'amari ya faruba". "Babu komai Dukkanmu babu wanda ze kaucewa hukuncin Allah shikadai yasan meya boye cikin al'amarin shima din yayi aure wannan qaramar yarinyar yarsa ce kuma sunan ita Hamdah ma ya saka mata Nagode Kwarai Dr Allah yasa hakan shi yafi mana alkahiri zanje in gaya masa yayi haquri Allah ya zaba masa wata" "Amin Hajia muke da godiya wanda ya nuna yana son naka mun gode kwarai sannan kofar mu a bude take idan har da yuwuwa yana son Yar uwarta". Daga haka ta haura sama
Chapter 48 · 0% Book details