← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 62

Sashe 10

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa tayi yanda ya shigo kamar wanda ake bi gaba daya ya hargitse, seta maida kallonta kan masu aikin dake ta karakaina cikin palour Dan su basu guri. Ido ta zuba masa dan Hajja bata tambaya kallonta kadai ya isa ka gane abinda take nufi. Ganin bashi da niyyar magana dan da alama ma hankalinsa baya tare dashi, murya a shaqe kamar an mata dole tace "Daga Ina kake?" Seda ya nemi gurin zama yana Sunkuyar da kansa ganin yanda ta kafeshi da ido sannan yace "Daga gidansu Hamdah nake Hajja". "Wace ce Hamdah" ta tambayeshi da kallon rainin hankali a fuskarta. Yasan bata son kwana kwana dan haka kaitsaye yace "Yarinyar da nake nema da aure". Shiru tayi na dan wasu seconds kafin tace "Da izinin wa, kuma ita din yar waye a kasar nan?" se ya daga kansa ya kalleta, be gane da izinin wa ba, dama namiji yana buqatar izini kafin ya nemi aure dama ai gurin iyayen yarinya yakama ta yane ma kafin ya fara tsayawa da ita to sun bashi dama...... Tunaninsa ne ya katse "Nace maka yar waye a kasar nan?" ta qara jefo masa tambayar "Hajja Yar gidan Prof Ammani ne". Cike da bala'i tace "Yar gidan wa kace Prof menene me na sama yaci bare ya bawa na kasa? Ni kake tunanin zaka dakkowa ahalin yahudawa A matsayin suruka me suke dashi in ba tarin takaddun banza da bazasu amfanesu duniya da lahira ba" fada takeyi haiqan dan dama ba baya bace a wannan fannin. Hajja masifaffiya ce ta misali musamman abu ya tarar da dalili. "Amma Hajja ai ita nake so kuma in kika ga yarinyar seta burgeki. Hajja tana da kyau Kuma ....." "Kyan Uwarka" ta katse shi sannan taci gaba "Nace kyan uwarka me za'ayi da kyau wanne ne ban gani ba? Yaya nawa aka baka masu kyan kaqi ashe kana can kana jajibo mana irin matsiyata to wallahi Ahir dinka kar ma ka kuskura Alhaji yaji wannan maganar dan kasan rankane ze baci a banza shashasha kawai kai ko kishin irin da Yan Ubanka suka auro bakayi se kao Guda daya da Allah ya bani zaka tozarta ni a gaban kishiyoyi ka auro min wata yar Professor da likita to Jami'a da Asibiti ma sunci uwarsu da ubansu Tashi ka bani guri kafin na bata maka rai . "Dama Hajja tace ne inna shirya in tura Iyayena ayi magana to shine nake so kiyiwa Alhaji magana". Baki kawai ta bude tana kallonsa. Waiwayawa tayi gefen ta babu komai se tumbler na karfe ta dauka ta jefeshi dashi cikin zafin nama ya goce ya fice daga palour da sauri, Abinda yake gudu kenan tun tuni amma baze iya jure rashinta ba, dole yasan yanda zeyi ya janyo hankalinsu suyarda da auransu. Dakinsa ya shiga, zarya yake tayi daga bango zuwa bango ya rasa tunanin daya kamata yayi a lokacin. Ada yana ganin har gara Hajja zata iya karbar abun to Alhaji fa daya fita tsanani in aka zo batun auran Jari? Bashida mafita dan haka ya dauro Alwala kawai ya tada sallar da shi Kansa besan abinda yake karantawa ba. **************************************** Seda Hamdah Ta kwana uku a asibiti sannan ta warware, a kwana na biyunne Abdulmalik ya kirata, Hamidah ce ta dauki wayar Ta gaya masa Cewa anyi admitting dinta a asibiti kwana biyu kenan. Hankali tashe ya nufi asibitin, Allah sarki Shi ya zata tana sane ta shareshi kwana biyu bata nemeshi ba shima ya shareta ashe bata da Lafiya ne duk ya tashi hankalinsa gani yakeyi Kaman shine silar ciwon nata. Bayanda ba ayi da ita ba akan tafadi abinda ke damunta Amma taki Dan Dr ya tabbatar musu dacewa damuwa ce tayi mata yawa harta haifar mata da zazzabi. Haka dai aka sallameta da sharadin tayi kokarin cire komai a ranta in ba haka ba jininta ze iya hawa. Wani sabon tattali da kulawa Abdulmalik yake bata dan dakyar ya koma Lagos amma kullum suna manne a waya. Wata sabuwar shaquwa ce ta shiga tsakaninsu, so da kauna kullum qara hauhawa yake a zukatansu fatansu Allah ya mallaka Musu junansu. A haka har aka koma hutun makaranta. Ranar Wata Monday Suka koma hutu, kowa ka kalla cikin tsananin farinciki yake dan sunyi missing school ba kadanba. Shirye shiryen Presentation da zasuyi akan special project sukeyi ko wanne dalili ya zabi abinda zeyi inda wasu kuma Supervisors dinsu ne suka zabar musu. Hamdah tana cikin wadanda aka supervisors dinsu suka zabarwa. Kusan kwana hudu kenan yau tana zuwa office din Dr Guru kuma as usual a rufe, juyawa tayi ta kalli Maryam Amarya datayi wani kyau na musamman da gani kasan Tana jin dadin auranta. kamar zatayi kuka tace "Maryam kin gani ko this is the fourth time I'm coming to this office bayanan Kuma ranar friday ne Defence dinnan kinga yau tuesday wallahi Zanje nayi duk abinda naga dama nayi presenting tunda dukka sauran yan group dinmu sunce sun kirashi ya basu topic". "Aa Hamdah badai abinda kika ga dama ba why not kema ki kirashi kuyi magana a waya yanzu kikayi gaban kanki ya hanaki presenting wa aka cuta" setayi shiru Dan zancen gaskiya ya basu time tun last week friday yace suzo su sameshi kuma tana sane taqi zuwa maganar Maryam nakan gaskiya amma dukda haka batajin zata iya kiransa dan ita tuni ma tayi blocking numbersa. Dakyar Maryam tayi convincing dinta ta yarda amma akan sedai ta kira mata shi a tata wayar haka kuwa akayi Maryam ta kirashi. Yana zaune a madaidaicin palour sa, exam scripts ne na postgraduates a gabansa yana marking wayar ta shigo. Mrs Yusuf daya gani ya saka shi dagawa yana mamakin dalilin daya sa matar yusuf ta kira shi, seda ya kalli Agogo karfe 9:30am sannan ya kai wayar kunnensa. Bayan sun gaisa take cewa "Sir dama munzo office dinka ne da Hamdah so wayarta babu charge ta mutu shine tace na kira mata kai" "wace ce Hamdah?" ya tambayeta. Seda tayi jum sannan tace "Hamdah Ahmad Ammani IT student dinka ce Sir" "Ok kice ta jirani i will be there in 60 minutes Insha Allah" ya katse wayar. Handah data gamajin komai dan a handsfree wayar take tace "Tab se yaga wanda ze jirasa har 1hr wato ga mara aikin yi ko" "kedai kin fiya matsala wallahi meye to muzauna muna hira haryazo mana" haka suka zauna kofar office din kusan minti 40 sega Yusuf ya kira Maryam wai yazo ganinta, dole tawa hamdah sallama ta tafi. Tsaki tayi yafi cikin kwando dan ya qara kusan 10mins akan qhr din dayace. Kamshin turarensa ne ya sanar mata da zuwansa lokaci daya taji zuciyarta na bala'in son ganinsa. Wata irin kewarsa ce ta taso mata Lokaci daya. Yayi kyau matuqa cikin Jean and T shirt daya saka all black haka ma takalmin kafarsa. shidai Komai yana masa kyau ta fada aranta tana kallonsa har bata san sanda ya qaraso inda take ba. "Malama dena kallona haka karki cinyewa budurwata ni" ya fada a saitin kunnenta. Ai ji tayi ina kasa ta tsage ta shige ciki tsabar kunya dan tabbas bazata musa ba kallonsa takeyi. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta ringa jan kafa har tashiga office din daya bar Mata a bude sannan ta rufe kofar zuciyarta na bugawa irin yanda ta saba.. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 PAGE 0 "Bam" aka fada daidai kunnenta. Bakaramin tsorata tayi ba dan bata san yana bayanta ba. Dariya yake haikan se kawai ta saka masa kuka. "me kuma ya faru" ya fada yana kokarin tsaida dariyarsa "Ba kaine ka tsorata ni ba sannan kuma kake min dariya". Se ya qara fashewa da dariya, the look on her face got him wani kyau na musamman takeyi idan tana kuka. Seya riko hannunta ya jata kan kujerar dake gefen office din, tsugunnawa yayi a gabanta still hannunta na cikin nasa yana dariya ita kuma tana kuka. Ganin abin nata bana qare bane kawai ya dauki wayarsa ya fara mata video ai kuwa ta qara volume din kukan harda bubbuga kafa a kasa kamar yarinya. Seda ta gaji dan kanta yana zaune kamar ya samu TV haka yaringa kallonta, ganin ta gama kukan ya sa ya tsiyaya mata ruwa me sanyi ya mika mata sannan ya ciro hanky me kyau se kamshi yake daga aljihunsa ya shiga goge mata fuskarta "Oya fato hancin" kamar yarinya ya goge mata majinan hancinta. Mayafin kanta ya kama da niyyar cire mata setayi saurin rikewa "relax naga kina zufa ne shine zan cire miki kisha Iska" ya fada yana ci gaba da sauke mayafin kafin ta rike har ya saukeahi kan kafadarta, gashin kanta data kama dakyar dan ribbon din ya masa kadan kuma tana sauri Dama mayafinne ya taimaka mata ya tsaya ya samu nasarar zubowa har gadon bayanta bakikkirin tayi dying karshensa da Golden colour. Kamar me tsoron gashin haka yakai hannunsa Ya shiga tattara mata, laushi da kamshin da gashin yakeyi really got him, Yana son gashi, yana daga qualities din da yake so a jikin mace gashi Hamdah tana dashi morethan his expection. Har ya daure mata gashin ya daura mata Mayafin kamar dankwaki Akanta bata dago ba seda taji ya ajiye mata abu akan cinyarta, Laptop ce. Tuni ya kame akan kujerarsa yana jujjuyawa yace "Ki duba zakiga folder with your reg number go through the content". Da kai ta amsa masa ta shiga yin abinda yace. To her surprise Mini project din da take ta qoqarin hadawa ne ta kasa, mamaki take a ina ya samu notes dinsu na Asibiti da har ya hada mata komai? Hatta da Power point din presentation din yayi mata she couldn't Help it but to smile lallai Sir Guru yana da kirki in yaga dama. Dago kanta tayi with so much Joy tace "Sir...." seta kasa qarasawa ganin irin kallon dayake binta dashi. Waske wa yayi ya dauke kansa tare da cewa "You were talking" murmushi tayi sannan tace "Yes i want to thank you nagode sosai now i just have to read through shikenan". Yanda take murna yasakashi jin dadi, for once ya faranta mata rai dan haka yace "Never mind kawai any time you need anything i will be
Chapter 10 · 0% Book details