Sashe 23
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
se godiyar Allah. "Ah lallai mutumin Lafiya ta samu" cewar Fahad still be kula suba sema jakarsa da suka kawo masa kaya aciki daya jawo ya shiga zuba ragowar abubuwan da suke a waje, saida ya gama tsaf sannan ya juya yace musu "I'm going se Allah ya kuma hada mu thanks so much men Ana tare". Patting kafadarsu yayi ya shiga jan jakarsa ze fita haka suka bude baki suna kallonsa, ganin da gaske yakai kofa yasaka Fahad saurin shan gabansa yace "Going to where?" "Inda na fito" ya bashi amsa yana qoqarin kauce masa dan ya fita abinsa. Se suka biyo shi a baya, Sulaiman Amintaccen yaronsa suka gani a harabar asibitin ya taso da sauri ya karbi jakarsa ya saka a mota sannan ya bude masa back sit ya shiga. Ta window ya sakar musu murmushinsa sannan motar ta tashi ya barsu a tsaye kamar bishiyoyin da aka dasa. Seda suka dena hangoshi sannan kowa ya kama motarsa ya tafi dan already yayi settling bill din asibitin. Idonsa a rufe ya jingina kansa da kujerar har suka isa Airport da already Sulaiman ya masa booking flight da komai, Cikin awa daya yagama duk clearance dinsa ya zauna akan kujera jikin window a First class suite. Ta window yake kallon garinsa Kano lokacin da jirgin ya fara tafiya a sararin samaniya tun yana ganin gine gine har suka fara bace masa bayan da jirgin ya daidaita a sam, a fili ya furta "Se wata rana kano,se wata rana Nigeria". Amminsa da sisters dinsa ne suka fado masa a rai, lumshe idonsa kawai yayi Dan dole ze lallashi zuciyarsa Dan kuwa zaman Nigeria banasa bane ya sani muddin yacigaba da zama to dole wata rana se sun hadu abinda baya taba fata kenan ya hadu da ita tana matsayin matar wani ba tasa ba. Bayan tafiyar awanni da transits ya sauka qasar Japan lafiya, ya tarar da Abokansa daya baro da jimami na rashin sanin abinda ya sameshi. Ko da ya koma tambayar duniya su master sukai masa akan abinda yasa shi tafiyar da babu shiri Amma yai musu kunnan uwar shegu dole suka hakura sedai duk Wanda yasan shi inyaganshi ayanzu dole yasan yana cikin damuwa. Dama yaya lafiyar kura Dan haka yanzu miskilanci yaci uban na da aiki da neman kudi kawai yasaka a gaba ya ture duk wani batu na soyayya acewarsa ya gama, ita kadai tayi masa daya aura a matsayin mata, tunda ya rasata kuma shida aure se a aljannah. *Fatan alkhairi ABDUL'AHAD ALIYU GALADIMAH Allah ya baka mafificin alkhairin Hamdah*. ***************************** Da kyar Amarya Hamdah ta iya bude idonta tareda jawo bed sheet ta kara rufe jikinta, motsinta daya ji ya sakashi juyowa da sauri ya mikewa daga kan Sallayar da ya ke. "Sannu Zaujy Allah yayi miki albarka, Kaman yanda kika faranta min Allah ya miki sama da haka nagode Hamdah na gode Ubangiji Allah ya biya miki buqatunki na alkairi Allah ya faranta miki kema....."surutai kala kala ya ringa yi mata har ya sakata jin kunya se kace ba haqqinsa ba, hannunta tasa ta rufe masa baki tana cewa "Ya isa mana mene nayimin godiya nifa matar ka ce halalinka fa ko ka manta ne". "Haka ne na sani Hamdahta Amma dole na gode miki". " Nidai ya isa lokacin sallah kuma yana qara qurewa" ta katse masa surutan da yakeyi. Shi ya taimaka mata tayi wanka kafinnan ya gyara dakin tsaf sannan suka gabatar da sallar asuba tare. Tea ya hada mata mai kauri ya ringa lalla bata tasha dan yasan dauriya kawai takeyi. Wata irin kimarta ce ta qaru a idonsa, son ta da tausayinta yana qara shigarsa aduk numfashin daya shaqa. Alamar zazzabi daya ji yana son kamata ne ya saka shi bata pain killer tasha sannan ya lullubeta a bargo ya rage musu sanyin Ac nanda nan bacci ya dauketa a cikin jikinsa. Kanta dake kan qirjinsa yake shafa a hankali, nutsuwa yake samu ta daban a duk lokacin da yake tareda Hamdah, Goshinta yayi kissing yana kara gyara mata kwanciya yanajin yanda zafin jikinta yake ratsashi wani sabon tausayinta ya shigeshi. Yanda taringa masa kuka yake tunawa amma ko kadab be saurareta ba. A haka yaringa tuna moment dinsu da baze taba gogewa ba acikin tarihin rayuwarsa wannan dare yana da daraja, shikadai yake murmushi in ya tuna har bacci ya daukeshi. Rayuwa suke gudanarwa cike da aminchi da yarda da juna kowannensu na tattalin Dan uwansa. A yanzu bata da wata matsala dan ta samu soyayyar mijinta abinda take buri kenan. A satin su biyu da aure bazata ce ga wani abu daya mata na rashin kyautawa ba tattalinta yakeyi kamar danayan kwai. Ko a bangar en yan uwan bata da damuwa dan sosai suke yi da ita musamman yammatan gidan kasan cewarta yar gayu ya kara kulla alaka tsakaninsu kullum suna part din sedai fa in Abdulmaleek ya musu jan ido se yace wai suna hana Shi sakewa da matarsa. Matsalarta dama Hafsa ce kuma tuni Ta tattara ta koma inda ta fito duk yanda kuwa taso ta zauna a gidan amma Hajja taqi. Satinsu uku da aure in kaganta seka kara kallonta. Tayi kyau jikinta ya murje kamar me wanka da madara haka shima Ango ba a magana Dan har wata kiba yayi kana ganinsa kasan yana more amarci da tsibke. Ranar Monday kuma a ranar ne yake shirin komawa aiki bayan dogon lokacin da ya dauka yana hutu, tun da sukayi sallar Asuba takeyi mishi rigima akan wai ta shirya su tafi tare ya ajiyeta a gida in ya dawo seya dakkota ita bazata iya wuni ita kadai a gidan ba shi kuma yaki. Har suka fito zata rakashi bata hakura ba ta masa kwalliya sosai Abdulmalik ya hade cikin wata suit kalar Blue black yayi kyau ga wata kamala da cika daya qara. Itama sanye take da atamfa exclusive koriya dinkin doguwar riga bata daura dan kwaliba se gyale data yafa ta rufe jikinta gaba daya dashi se shagwaba take masa wai zatayi missing dinsa da yawa. Seda ta rakashi jikin motarsa tana jera masa addu'ar a dawo lafiya da list din kayan kwalamar da ze taho mata dasu shidai babu abinda yake in ba murmushi ba, jin kansa yake kamar wani sarki. Indai zata ci gaba masa da haka to shidai babu boka babu Malam ta gama dashi wallahi. Dakyar sukayi sallama Kaman karsu rabu dan ya kusa makara yaja motarsa ya bar gidan, haka suka wuni a waya Dan motsi kadan ze kirata yaji me takeyi yayi missing dinta haka itama. 5pm tagama komai tsaf ta gyara gidan ta fesa wanka cikin wani hadadden lace Orange gaba daya falon ya gauraye da daddadan turaren wuta ga kuma turarukan da tayi amfani dasu. Suna zaune da su Surayya da shigansu kenan yayi sallama. Jakar hannunsa ya ajiye tareda bude mata hannu alaman tazo, tamkar tarwada Haj take takun da ita kanta bata san ta iya irinsa ba har ta karasa ta shige jikinsa ya maida hannunsa ya rufe ji yake kamar ya kwana be ganta ba. seda ya shaki kamshinta sosai sannan ya furta "I missed you so badly my Jewel" yafada looking straight in to her eyes. Ita ma shi take kallo tace "I miss you more Jaan" tana juya idonta. "you sure" ya tambayeta yana dage mata gira "Yh I'm very sure" ta bashi amsa "Oya na show me how much you miss me". Ya fada bayan daya saketa kadan, without given a second taught kawai ta hade bakinsa da nata what he wasn't expecting nan kuwa yashiga kissing nata hungrily as if his life depend on it. Su Sumayya da suka ga alaman an manta da zamansu sumsum suka fice tareda kullo musu falon. Seda ya gaji dan kansa sannan ya saketa suka shiga ciki, already ta hada masa ruwan wanka, bayan yayi wanka ne suka zauna cin abinci yana ta mata labarin office. Se yaga kaman walwalarta ta ragu dan shi yake ta hirar ita dai seta amsa masa da eh ko Aa. " Babe namanta naga me agwaluma kafin kuma na siya aka bamu hannu kuma a saman titi nake bare na tsaya na siya miki". Shirun daya ji tayi bata amasa bane ya saka shi kama hannunta ya riko cikin nasa ya murza a hankali. Idanunta masu haske ta dago ta kalleshi ganin irin kallon datake masane ya sakashi cewa "ya dai yammata ina ta magana kinyi shiru tunanin me kikeyi". To his suprise se ga hawaye Kaman ya bude famfo. Hankali tashe ya fara tambayanta me ya sameta me aka mata ko wani gurin ne yake mata ciwo " Jewel talk please me nayi miki ko magana na ta bata miki rai kiyi hakuri yanzu ma bari naje na siyo miki in dai agwaluma ce" bata amsa shiba sema kara volume din kukanta da tayi cak ya dauketa suka dawo cikin palour ganin yanda ya rude ne yana shirin yi mata kukan ne shima yasa ta bude baki dakyar tace masa "Mumcy I want to see my Mom". Ta kuma rushewa da wani kuka. Kanshi ya dafe tareda jan guntun tsaki a ransa yana mamakin wauta irin ta Hamdah, "Wallahi you scared the hell out me mene na kuka anan just to tell me you want to go home shikenan seki dasa min kuka kamar wadda nace zanwa kishiya, naga alama dai sena fara zaneki akan wannan shagwabar taki karkizo ki koyawa Baby na kuka tun tana ciki" ya fada yana dungure mata kai. Baki ta turo masa tana cigaba da tabe baki cike da shagwaba. "Oya tashi kishirya saura ki bata min lokaci nace na fasa" ai bata san lokacin data mike da gudu ba bayan tayi pecking nasa a cheeks ta shige dakinta Dan kintsawa. Saboda azarbabi A falon ya tarar da ita ta chanza shiganta zuwa doguwar rigar shadda gezner dark blue da akayiwa dinki da jan zare Dan haka mayafinta da takalmi da bag duka Red ne.Tayi kyau kwarai har yaji kishin kar wani ya kalle masa ita. Se yai niyyar tsokanar ta yace "I'm sorry Babe yanzu Alhaji ya kirani zan kaishi gidan wani abokinsa and its urgent, ina ga mu bari se gobe" Da yake ruwa ruwa