Sashe 47
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bazaki taimaka ki aureshi ba". Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska. Duk wata kalma da take fada jinta take kamar tana tsirawa kanta allura amma yaya zatayi? Bata so ta zama meson kai bakuma taso ta raba wannan soyayyar, Kifa kanta tayi akan cinyarta tana ci gaba da kukan dukda tasan abinda hakan ze iya haifar mata. Tausayinta ne ya shafe haushin daga zuciyar Hamdah, wannan wace irin mace ce da zata iya sadaukar da Mijinta, mijin ma irin Abdul'ahad alfaharin kowacce mace. Se ta zamo daga kan kujerar da take, bata damu da lallen Hannunta ba ta qarasa ta dagota tareda rungumeta itama tana zubar da Hawaye. " Ni'ima kodan wannan sadaukarwar da kikayi bazan iya auran sa. Taya ma kike zaton zan iya qara kallonki bayan na aurar miki miji? Nasani son da kike masa ne yasa har kike qoqarin nema masa nasa farin cikin koda yaci karo da naki amma ni bazan so kaina ba, Naso Abdul'ahad ada amma na haqura dashi daga lokacin dana ganki a cikin rayuwarsa. Bazan iya shiga na rusa muku ginin da kuka faro ba......" Seta yi saurin rufe mata baki tana cewa "Aa karkice haka ke din kece cikon farin cikin gidan mu. Our home is incomplete without you, we been living a sorrowful life, ki taimaka ki kawo farin ciki a tsakaninmu we want you in our life" Tayi maganar tana qara qanqameta. Seta janye jikinta a hankali ta koma kan kujerar zuciyarta na mata wasi wasi kala kala. Meya kamata tayi? Shin ta amince da buqatar Ni'ima ko yaya? "Wannan matar bata cancanci haka ba Hamdah, tsaya ma wa kike tunanin ze dakatar da wannan auran amma dae ba Abba na ko?" Zuciyarta ta tambayeta. Inteesar data kai qololuwa a mamaki ta sauke numfashi tana kallon Ni'ima da ta dena kukan se ajiyar zuciya takeyi tace "Sannu da qoqari yar uwa gaskiya gobe dole inyi publishing labarinki Jarumar mace tazo nemawa mijinta aure amma sedai anyi rashin sa'a kin makara dan wani ya rigaku zuwa". Seta kalleta sosai dason jin qarin bayani. "Kwarai kuwa da alama baki san gobe ne daurin auranta ba wannan qunshin ma da kikaga ina mata na biki ne gobe iyanzu mun kaita Garin Gwamna insha Allahu" Indo me lallece ta qarasa mata bayanin ganin kamar bata gane me Intee take fada mata ba. Seta bude baki da alamar mamaki take binta da kallo, kai ta gyada mata cikin tabbatarwa kafin ta nemo Invitation card din daurin auran a wayarta wanda harda picture dinta dana Abdurrahman din a gefe ta miqa mata jiki na rawa ta karba ta duba. "Ubangiji Allah yasa hakan shi yafi alkahiri idan kuma akwai sauran dama muna nan bamu hakura ba" Ni'ima ta fada bayan data miqa mata wayar dan ta tabbatar babu sauran wani abu ayanzu kuma ya qara makara kar na wancan lokacin. Jakarta ta dauka ta miqe da kyar saboda nauyin da taji kafafuwanta sunyi mata daidai da shigowar Safeena da ta gaji da jira a waje, saurin tareta tayi tana tambayarta lafiya "Mutafi gida bana jin dadi Safeena" nan da nan hankalinta ya tashi dan ko kadan basa son abinda ze jawo motsawar jikin yayar tata. Kamata tayi suka fita bayan sunyi musu sallama tana ta mita wai ta zauna tana ta magana gashinan ta jawo wa kanta wahala ita dai bata ce mata ta tafasa ba tunani takeyi kawai a zuciyarta Halinda Abdul'ahad ze iya shiga. Rabonta dashi tun jiya a bakin Fadila taji wai ya dawo a dakin Ammi ya kwana tun daga nan tasan babu lafiya. Koda safe waya yayi mata takai masa kaya yayi wanka acan ya fita bata da tabbacin ina ya tafi ko ya dawo gidan yanzu. Wani irin sharp pain taji tundaga kafarta har maqoshinta se tayi saurin riqo hannun Safeena dake tuqi tana ci gaba da Mita "Safeena mu wuce hospital please its getting worse" cikin karfin hali tayi maganar dan haka Safeena tayi saurin chanza wa motar direction. Kafin suje asibitin ta gama galabaita dan har ta fara aman Jini ga jikinta da yayi wani mugun zafi kamar an anjona heater. Kuka Safeena take kamar me lokacin da aka shiga da ita ICU ta shiga kiran number Mamansu amma busy, Abdul'ahad ta kira akayi sa'a yana kusa da gurin dan haka ba shiri ya tafi asibitin. Hankalinsa yakai kololuwa gurin tashi ganin yanayin da take ciki, likitoci uku ne akanta suna qoqarin ceto rayuwarta to wai ma meya sameta of sudden haka? Matar da suka rabu lafiya dazu babu wani alamar ciwo a tare da ita. "Daga ina kuke" ya jefawa Safeena dake kuka hannuwanta dukka biyu aka tambaya. "Nima ban sani ba Yaya kawai cewa tayi nazo na rakata gidansu wata friend dinta da mukaje ma korata waje tayi sukayi magana shikenan fa da muka taho tace na kawota asibiti bata jin dadi". Safa da marwa ya shigayi, wace qawarta taje gidansu da bata gaya masa ba? A kwanakin nan he is suspecting that she is up to something amma koma mene ba wannan bane damuwarsa a yanzu, samun lafiyarta shi ne first priority dinsa daga nan se yaji koma mene a bakinta. Yafi awa daya a gurin sannan yan gidansu suka qaraso harda Amminsa da qanwar tata Maman Ni'ima ta kira ta sanar da ita. Haka suka zauna jigum jigum kowa da kalar tunaninsa fatansu kawai Allah ya tashi kafadunta. Se mu tayasu a Amin. **************** A bangaren Hamdah duk yanda su Inteesar suka so suyi maganar qi tayi qarshe ma tace musu tana so maganar ta zama sirri bata yarsa su gayawa kowa zuwan Ni'ima ba, sukuku aka gama lallen ta wanke ta koma main house din anan ta tarar da mutanen da suka taru. Daurewa tayi aka shiga gaisawa kowa yana mata Allah sanya alkhairi da fatan zaman lafiya ta ringa amsa musu da Amin tana murmushin da bekai zuciya ba. Dakinta tashiga tayi wanka bayan ta fito tana zaune agan dressing mirror, wayarta ce a hannunta tana jujjuyawa tunani take ta kirashi ko Aa? Zuciyarta ce tafi tafiya akan ta kirashin ko ba komai tana so taji dalilin dayasa ya turo mata matarsa. Seda tayi masa 5 missed calls be amsa ba lokacin yana can ana dibar jininsa wanda za'a qarawa Ni'ima da suka ce volume na jininta yayi qasa sosai. Tsaki tayi tareda jefar da wayar akan gado, dan rainin wayo ita zata kirshi ma yaqi answer wa to yayiwa kansa haka ta ringa mita har ta gama shiryawa ta shiga sabgoginta. Har dare tana sauraron ko ze kirata, lokacin da agogo ya buga karfe shabiyu daidai ta cire rai takuma tabbata baze kirata ba a wannan lokacin ma. Seta tuna waccen ranar data ringa jiran kiransa irin haka wanda shi ya bata qarfin guiwar yanke decision dinta a wancan lokacin, yau ma ya qara tabbatar mata baya buqatar ta a cikin rayuwarsa. Ya tabbatar mata daya rabu da ita a karo na biyu, se kawai ta fashe da kuka, kukan da bata san dalilin yinsa ba. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Karfe Biyu da rabi na rana bayan an sakko daga Masallacin dake cikin BUK old site Dubban mutane suka shaida daurin auran Abdurrahman Ibrahim Khalil da Hamdah Ahmad Ammani a karo na biyu. Ko kusa ko alama batayi farin cikin da tayi tunani ba da auran ga wata kewa da soyayyar Abdulmalik data taso mata lokaci daya. A Ranar Mumcy tayi nata wunin Amarya tayi kyau sosai iya dauriya tayi dan hana Kukan da takeyi cikin zuciyarta ya fito fili amma ina dole seda tayi dab da ana shirin tashi daga wunin tunowa tayi da ranar kamun auranta da Abdulmalik a daidai irin wannan lokacin ana shirin tashi ya shigo gurin da Abokanansa bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba duk wanda ya kalleta yasan kukan me takeyi se haquri suke bata rayuwa kenan. Ranar raba dare sukayi da Mommynta tana mata nasihohi akaro na biyu zata kuma rabuwa da favorite daughter din nata Gashi a goben da sassafe za'a wuce da ita kaduna. Washe gari kuwa kamar yanda Abbah ya fada Karfe shadaya motocin kai Amarya suka fara hawa titi domin yi mata rakiya zuwa gidan angonta, sai muce Allah ya bada zaman lafiya. ************************************* Malam guru kuwa a asibiti ya kwana gurin Ni'ima da har wayewar gari bata san waye akanta ba. Allura me qarfin gaske akayi mata dan ta samu isashshen hutu kwakwalwarta ta goge duk wasu tunani da suke ciki sannan kumburin da zuciyarta tayi ya sace. Wuraren shabiyu ya koma asibitin bayan yaje gida yayo wanka da ka ganshi kasan bashi da Nutsuwa, rashin lafiyar Ni'ima yana dagula masa lissafi gaba daya hankalinsa baya kwanciya har seyaga ta dawo yanda take. Amina ce ta miqa masa wayarsa daya bari a asibitin ya tafi gida "Yaya gashi tun dazu ake ta kiranka a waya". Karbar wayar yayi, missed calls ya gani barkatai se kawai ya bi na Fahad " Oga ya ake ciki" Fahad ya fada bayan ya daga wayar "Fine ina ka shige ne wayarka baya shiga". "Wallahi Somalia naje in gaya maka shiga wani kauye babu network Allah ne ma ya fito damu lafiya". "Ok kana ina yanzu" ya tambayeshi "Ina gida oh namanta Mimi ta haihu dazu da safe (yana nufin matarsa) "Masha Allah me aka samu" "Abdul'ahad Dan Galadima" Besan lokacin daya fara dariya ba duk da yanayin dayake ciki sannan yace "Kai dai you will never be serious in your life". "Wallahi I'm serious nayi masa huduba da sunanka" se yayi shiru for some time kafin yace "Thank you Man Allah ya masa albarka kayiwa Mimi sannu Insha Allah later zan shigo yanzu in Hospital jikin Ni'ima ne ya motsa". "Ashsha Allah ya bata lafiya bari nima yanzu shirin fita nake insha Allah zan shigo Allah ya bata lafiya" da Amin ya amsa masa kafin sukayi sallama. Within few minutes ya qarasa asibitin, nan suka zauna suna tattaunawa akan ciwon nata. A cikin BUK old site sukayi sallar Juma'a sunata mamakin yanda masallacin ya cika da Jama'a yau, a bakin wani da suka zauna kusa dashi sukejin wai Daurin auran Dan wani tsohon governor za'ayi sudai basu zauna ba dan kowanne yana da uzuri suka