← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 62

Sashe 54

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da juna. Daukarta yayi a hannu ya kwantar da ita a sit din baya sedai Saboda tsananin rudu Kasa tuka motar yayi dole se Hajara ce ta karba shi kuma ya koma baya ya rungumeta hannunsa akan cikinta daya ke jin yanda yake juyawa kamar ana yaki a ciki, irin motsin da Dan ciki yakeyi tun yanayi da karfi a hankali motsin ya fara raguwa hakanan har sannan jinin bedena zuba ba. A kafada yashiga da ita reception din Asibitin Dr Huzaifa dan bashida sauran zabi, shi kadai ze iya rufa masa wannan asirin be isa ya kaita wani asibiti a wannan yanayin ba dole a kamashi. Yanda ya shigo da ita dinne ya jawo hankalin ma'aikatan dake gurin suka nufeshi da sauri. Wani mugun Kallo Dr Huzaifan ya ringa binshi dashi lokacin dayake mika masa farar takarda domin yasa Hannu kafin a shiga da ita Theatre hanya daya da zasu iya ceto ta kenan kila da abinda yake cikin nata. "Burin ka ya cika amma kasani wallahi in ta mutu da hannuna zan mika ka ga hukuma" yayi gaba abinsa bayan ya fizge takaddar. Abdurrahman baisan kuka yake ba saida wani a kusa dashi yace "kayi hakuri Alhaji addu'a zakayi mata muma duk jiran tsammani mukeyi daka ganmu anan" amma a maimakon yayi shiru saima ya kara kukan nasa. Tarin Nadama da Dana sani ne suka ziyarce shi lokaci daya, Meyasa ya zama mai sonkai a rayuwa? kwata kwata baiyi zaton kasancewar abun haka ba ko ba'a fada masa ba daga irin jinin data zubda yasan tana cikin hadari, meyasa be duba watannin cikin ba kafin ya yanke wannan danyan hukuncin kaiconsa kaicon zuciya irin tasa. Bashida mafita, bashi kuma dame bashi hakuri dan haka ya miqe ciki a sanyaye ya tafi masallacin dake cikin asibitin ya fara salloli. Ya Dade yana mikawa Allah kukansa tareda Neman yafiya akan abinda ya aikata har besan tsahon lokacin daya dauka ba. Agogon masallacin ya kalla karfe 6:30am almost 3hours kenan da aka shigar da ita theatre room din. Wayarsa ce ta shiga ringing sunan Mum daya gani yasaka shi dagawa da Sauri yana tunanin abinda ya faru kuma a can gidan take kiransa da wannan safiyar. "Abdurrahman kana ina ne tuntuni gamu cikin asibitin a wanne ward kuke ne" ta fada cikin muryar dake nuna tsantsar tashin hankalin da take ciki. Dakyar ya iya amsa mata da "Hajiya ina Masallaci yanzu ku din kuna Ina" a zuciyarsa yana tunanin waya gaya mata ma suna asibitin ma. Kwatanta masa inda suke ba bata lokaci ya tashi ya fita zuciyarsa na bugawa da taraddadin abinda zeje ya tarar. A harabar aaibitin suka hadu, kallon sa tayi yanda lokaci daya ya fita hayyacinsa sai ta rikoshi tana cewa "Oh ni Maimunatu wai me ya sami yarinyar mutane ne Hajara ce ta kira fa take gayamin wai kun kawota asibiti ita ma bata san meya sameta ba" shi sai a lokacin ma ya tuna da wata Hajara suka zo dan tun dasu ka zo asibitin besan inda tayi ba. Haka suka yi zaune jugum jugum kowa da kalar tunanin da yakeyi. Awa hudu sannan aka bude kofar theatre room din. Gaba dayansu suka mike suka nufi Dr Huzaifa, cikin rawar murya ya tareshi yana cewa "Huzaifa how is she? how is my wife". Kallon banza Dr yabishi dashi kafin ya mayar da hankalinsa kan Hajiya dake tambayar sa itama akan abinda ya samu Hamdah. "I can't say anything now sedai kawai mujira ta tashi tukunna muga abinda Allah zeyi and......." Se kuma yayi shiru. "And what fadi mana" Bashir Kanin Abdurrahman din ya tambayeshi, se yayi Jim sannan yace "the babies are no more" yayi gaba abinsa. Gaba daya wutar kan Abdurrahman din ce ta dauke komai ya tsaya masa "Babies" Kalmar ke taci gaba dayi masa yawo akai, kallonsa yakai kan nurses guda biyu dake tsaye a gurin kowacce rike da baby a hannunta se kawai ya zama kamar wani kurma he couldn't say a single word sai kallonsu Hajia yake da suka karbi yaran "Look at them Yaya wlh just like you" Bashir ya fada in between tears saboda tausayin yaran dake hannunsu masu kyau da aka ce wai sun rasu ya mikawa yayan nasa 7month old baby da girmansu masha Allah zaka iya cewa bacci yake in baka sani ba. Dukka biyun ya hada a hannunsa wasu hawaye na zubo masa, muryar rada rasa yace "I killed my sons, I killed my own boys" hawaye na ci gaba da zubar masa. Wani mugun kallon banza Hajiya ta bishi dashi jin abin dayake fadi, bashiri cikin daga murya tace "Abdurrahman what did you just said ka maimaitamin banji sosai ba". Zuwan Alhajinsu da shima saukarsa Kaduna kenan ya tarar bata nan se sauran yaran suka gaya musu Amaryar Yayansu ce ta haihu twins amma sun rasu shine ya tafi asibitin shima. Duk yanda taso ta yi fada Alhaji Ibrahim hanata yayi "Ki bari Maimunatu ko ma menene muje gida ba a asbibiti ba" "Alhaji kaji me yaron nan yake fada kuwa kisa fa naji yana ambata kabarshi yamin bayanin abind yake nufi tun anan" Hajiaya ta fada tana sauke numfashi tsabar yanda ranta ya baci. Lallabata suka shigayi sannan ta hakura amma bata sake yarda ko da ido ta kalli inda Abdurrahman din yake tsaye ba, kofar resting room din da aka shiga da Hamdah ta tafi ta tsaya tana jin likacin da Alhajin yake cewa zasuje da Yaran ayi musu sutura kai kawai ta daga masa batare da ta juyo ba. Karfe 11am tayiwa Iyalan gidan Prof Ahmad Ammani a asibitin Dan tun lokacin da Hajiya Maimuna ta sanar da Mumcy halin da ake ciki hankalinta ta ya ki kwanciya, dole ba shiri suka nufo kadunan kuma har zuwa lokacin bata farka ba. Suna zazzaune a kofar dakin Dr huzaifa ya fito bayan ya shiga dubata, kallonsu yayi sannan yace "Zaku iya shiga ku ganta amma please kar Ku tasheta". Gaba daya suka mike suka nufi dakin dan kuwa kowa yana dokin zuwa yaga halin da Hamdahn take ciki harda Abdurrahman se yayi saurin dakatar dashi yace "Malam dakata mana bamu bukatarka Shiga". kallonsa yayi kaman yanda shima yake kallonsa sai kuma ya gyada kai yayi gaba da niyyar shiga dakin. "Bakaji me yace maka bane ko kuwa" Hajia ta katseshi cikin tsawa, haka jiki a sanyaye ya koma yana kallonta tacikin glass din da akayiwa dakin Katanga dashi. Batada maraba da gawa in banda computer dake Nina tafiyar numfashinta. Tayi wata fayau da ita ta kara haske sosai kallo daya zaka mata ka hango ramar da tayi lokaci daya. **************************** A hankali ta fara motsa yatsun hannunta lokaci daya kuma tana qoqarin bude idanunta datakeji kamar an saka gum an liqe mata su. Bin dakin takeyi da kallo tana kokarin tuna musabbabin zuwanta da kuma ina ne nan din amma ta kasa gano ko daya daga ciki. Abu daya ta ke tunowa CIWO, ciwo kadai ta tuno da ta ringaji a daren jiya cikin bacci to kodama mafarki takeyi? cikin hanzari takai hannunta kan cikinta sedai tayi wurin wayam babu tudun sa babu alamarsa lokaci daya wani azababben ciwon ciki da Mara suka taso mata at once ba shiri ta bude dukka muryar da Allah ya bata ta fasa kuka. Gaba daya suka rufa kanta Mumcy ta shiga qoqarin riqeta saboda yanda take jijjiga kamar wadda Ta hau Aljanu har tana qoqarin cire allurar Hannunta, ganin bazata iya ba ya saka Farouk janyeta ya rungumeta gaba daya a jikinsa duk dauriyarsa yau seda ya zubda mata da hawayen tausayi. Dr Huzaifa da Nurse din da ta tafi kiransa ne suka dawo nan da nan ya hada allurai suka taru suka riqeta kafin yayi mata allurar lokaci daya jikinta ya saki ta koma ragwab ta kwanta. Kuka babu me cewa wani yayi hauri sukeyi hatta mazan basuda courage din rarrashinsu, bayanin da Dr Huzaifa yayi musu wai magani aka bata na zubda ciki tasha kuma over dose shi yafi daga musu hankali to wayayi mata wannan danyen aikin dan sun san dai da saninta bazata sha ba. Kallonsa ya maida kan Abdurrahman dayai saurin miqewa jin Farouk yana qara maimaita wa Huzaifa tambayar Uban waye ya bata maganin a me ma tasha se kawai ya girgiza kai cikin jin dacin abun har ransa yace "Gashi can mijinta ne se ku tambayeshi dalili" kafin ya gama rufe baki tuni Abdurrahman din har ya bace daga ward din ko kalar rigarsa ba'a hangowa. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Salati Hajiya Maimuna ta rafka tana tafa hannayenta kafin ta fashe da kuka "Ni Maimuna na shiga uku me Abdurrahman ya dauki kansa me yake so ya zama Alhaji kaga irin abinda nake gaya maka tun farko irin haka na guda gashi yanzu ta faru ta qare nidai Hasiya ta cuceni tsakani na sa ita se dai Ubangiji yai mana Hisabi kawai" ta fada tana sake rushewa da Kuka. Senator Ibrahim Khalil da Kunya da Nauyin Iyayen Hamdah ya hanashi kwakwkwaran motsi ya kalleta, tabbas shi kansa ayau yayi danasanin Yancin daya bawa Yayansa Maza musamman Abdurrahman daya fi so duk cikin yayansa. Shi kansa dabi'ar masu jajayen kunnuwa ta hudashi sosai hakan ta sakashi dora yayansa akan turba irin tasu, dukda yana iya qoqarinsa gurin ilmantar dasu ta fuskar Addini domin ko sanda Abdurrahman yake a London akwai malami daya ajiye masa a gida yana karantar dashi amma kuskurensa daya na bashi cikakkiyar damar aiwatar da duk abinda yayi niyya. A farkon zaman Abdurrahman a London din a hannunsa yake a lokacin suna tareda Hajia Hasiya matarsa ta biyu ita kuma Hajia Maimuna tana Nigeria da sauran yaranta mata. Hajiya Hasiya ita ta bada gudummowa gurin tabbatar tabarbarewar tarbiyyar Abdurrahman din har seda ta samu nasarar cusa masa mugayen dabi'un da suke dawainiya dashi a yanzu. Ita ta tilastawa Baban siya masa gida na kansa dan ya zauna lokacin daya fara University ya kuma mallaka masa duk wasu abubuwa najin dadin rayuwa. Tun shekarunsa basu kai ba yake riqe manyan kudade dan ko be bashi ba ita zata bashi saboda ita Allah be bata Haihuwa ba seta dauki Abdurrahman din ta riqe kamar danta. "Alhaji kana tsaye yaron nan ya tafi haka zaka
Chapter 54 · 0% Book details