Sashe 21
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyau ba. Dinner ce aka shirya ta manyan mutane ba kadan ba Guri ya tumbatsa domin an shiryata ta ta shiryu, Hajja Fattu tayi matukar kokari gurin ganin komai ya tafi mata normal, biki take so tayi wanda babu kawarta data taba yin irinsa. Tayi matuqar qoqari kuwa tundaga kayan da Amarya ta saka, zuwa abincin da aka dafa a gurin na musamman ne,kusan kowa mai muhimmanci ya hallara a gurin dan haka aka fara gudanar da taro. Zata iya cewa littafin qaddararta ya fara budewa ne a yau, yanda yammata suka ringa daukar hoto da Angon kadai ya bata mamaki, kowacce tazo daga cousin se yar kawar Hajja se family friensa. Abin be fara damunta ba har seda wata daga cikin yammatan tazo gurin da suke zaune, macece kamar an zana Alif ba wasali dukda irin dameta da lalatacciyar fitted gown din jikin ta tayi hakan be fito da komai ba fuskar nan tasha make up Kaman a bikin aljanu se wani karairaya da yauki takeyi tamkar zata karye. Bata gama nazarin yarinyar ba ta tsinkayi muryarta tana cewa "Please Amaryarmu ko zaki Dan tashi Ina so muyi hoto da ango ne". Seta kalleta galala wai ta tashi sannan ta ta kalli gogan dake faman Buda hakora Kaman gonar auduga yana cewa "Aa Haj Suniya saukar yaushe aka ce baki zo ba". Seda tayi fari da ido duk dan son taja hankalimsa tana kada jiki sannan tace "ka bari kawai jiya fa na dawo ban ma shigo Kano ba se dazun da rana kaima dai kasan bayanda za'ayi na kasa halartar bikinka shiyasa na ajiye komai nawa na ta baro Paris kawai dan aaga wannan wace me sa'ar ce ta dauke Prince charming". Magana take tana wani fari cikin tsantsar iya kissa da bariki shi kuwa dolon kara bude baki yayi a dole anyabe shi yana cewa "Ai kuwa kin kyauta gata nan kuwa yakika ganta?" "Yah ba laifi Dan ta ma fi yanda nayi tunani". yanda tayi maganar kadai ze tabbatar maka daurewa kawai tayi Amma kishi ke nukurkusar zuciyarta. Hamdah data saki baki tana kallon ikon Allah, ita kuma din wannan wa ce ce daga wace bolar take? bude baki tayi daniyar magana sedai zuwan Aysha ya katse ta janta tayi ta sauko da ita inda kawayen Hajja suka taru domin yiwa Amarya liki Dan tuntuni Mc ke ta kwala kiran Amarya ta sakko amma ina hankalinta nacan tana kallon sarautar Allah. Se karfe daya aka tashi biki yayi biki kowanne bangare sunyi bajinta. Taji dadi kwarai da Mumcy ta zo gurin setaji kaman gida zasu wuce in aka tashi sedai tuni idonta ya raina fata lokacin data gansu daga ita se shi a mota yanda suk zo sun dauke hanya daban da wacce yan gidan su suka bi. Tun a mota ya ga chanji a tattare da ita, be kawo komai aransa ba dan tunaninsa ko gajiya ce dan haka be takura mata ba koda suka je gida dakansa ya hada mata ruwa masu zafi tayi wanka yalallabata tasha tea sannan tayi bacci. Ya dade yana kallonta yaso ya sameta a daren yau Amma ta gaji baze mata abinda bata soba. Wani irin farin ciki yakeji wai yau shine kwance tareda ita a matsayin matarsa ta sunna? Haka yaringa juyi yana waaikar jaki dakyar bacci barawo ya sace shi bayan ya rungumeta tsam a jikinsa tamkar wani ze kwaceta kafin safiya. *_Asuba ta gari Mr and Mrs Dala_*. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 A bangaren Abdul'ahad kuwa hankali tashe Yusuf ya wuce dashi asibiti sakamakon gani yana yin daya ke ciki. Sun isa asibitin aka karbeshi zuwa emargency bayanda Yusuf beyi dashi ba tun a hanya akan yakira Ammi ya sanar mata Amma yaki akan dolen shi ya hakura dan yasan muddun ya kirata bazasu kwashe kalau ba, ganin ya fara bacci ne bayan treatment din da aka bashi ya saka Yusuf tafiya gida dan ya dakko masa wasu kayan da kuma abinci kafin ya farka. Se wurin magriba ya farka da fatan Allah yasa duk abinda ya faru ya zama mafarki ne sedai babu alama tunda gashi akwance kan gadon aaibitin da yai bacci. Sallolin da ake bimsa ya shiga ramawa bayan yayi wanka sannan ya diba abinci kadan ya fara ci, seda Yusuf yayi fama dashi sannan ya yarda aka kira masa Fahad ya kwana dashi, haduwa sukayi su biyun suka sakashi a gaba wai suna masa nasiha harda likitan shima in ya tankasu ku da kuke karatu kun saka baki, har 12am Yusuf na asibitin sannan yai musu sallama ya tafi gida koda yaje be fadawa Maryam ainihin inda yaje ba kawai yace mata wani abokinsa aka kwantar a asibiti da safe tayi girki da wuri ze kai musu da "To" ta amsa shi tana mamakin wannan wane abokinsa ne haka. Gidan Amarya Bacci sosai suka kwasa saboda gajia har seda suka makara sallar asuba. Ita tafara farkawa dakyar ta zare jikinta daga nashi saboda irin rikon dayai mata motsinta ya farkar dashi. Magana yake niyyar yi mata tayi saurin nuna masa katon agogon dake manne a jikin bango. Salati yayi ganin har 7:45am na safe Dan haka a gaggauce suka dauro alwala, yarigata fitowa daga toilet din se ya shimfida musu sallaya sannan ya dakko mata hijab cikin wardrobe ya zauna yana jiranta. Bayan ta fitone ya jasu jam'in sallar, kusan a tare suka idar da azkar Dan haka ta kalleshi cikin sanyin murya tace "Ina kwana" "Lafiya lau Amaryata ya kwanan bakunta?" Shiru tayi bata amsaba haka shima be kuma cewa komai ba se kallonta kawai da yakeyi yana nazarinta a zuciyarsa, gaba daya kamar a takure take. Gani ya keyi Hamdah ta chanza masa yanayin fuskarta da komai ya chanza, a da ya kanga zallar kauna da soyayyarsa a cikin idanunta Amma yanzu ba haka bane. Baya so ya gasgata abunda zuciyarsa take gaya masa, baya so ya yarda da cewa wani take so bashi ba. A zatonsa zata kasance cikin farin ciki da kasancewarta cikin gidansa Amma se gashi ba hakan bane yana kallonta yanzun ma hawaye take sharewa a hankali wai dan karya gani amma ta makaro dan ya riga da ya gani. Tun da aka fara bikin nan take kuka, be manta kukan da ta farka cikin dare tanayi ba wanda taki gaya masa dalili. Se yake ganin ko na Rabuwa da gida ne kawai, "Kwarai Sabo ne" zuciyarsa ta ayyana masa. "Kaima kasan dole duk son da take maka zataji ba dadi na rabuwa da familynta" wani bangare na zuciyarsa ya kara tunatar dashi. "I hope so" ya fada a fili. Seta juyo ta kalleshi, murmushinsa me kyau yai mata tayi saurin saukar da kanta kasa dan yayi tasiri akanta. Mikewa tayi ta shiga ninke hijabin da tayi sallah dashi tace "Me ya faru". "No nothing kawai zancen zuciya nakeyi" ya fada yana karasawa kusa da ita ya dora kansa a kan kafadarta, light kiss ya dora mata akan bear skin dinta. Wasu irin abu ne suka tafi tundaga wurin har tafin qafarta kamar electric shock wata kasala ta shiga sauko mata, saurin ture kansa tayi tana cewa "Ni Bacci". "Ok ok muje ki kwanta Amaryata". Janta yayi ya kwantar da ita akan gadon yana patting bayanta Kaman yanda akewa baby in ana so yayi bacci. Likimo tayi tana jin yanda hannunsa ke yawo tsakanin gashin kanta da bayanta wanda tun tana jinsa har baccin gaske ya dauketa, jin ta dena mutsu mutsune yasashi leka fuskarta yaga baccin takeyi. Pecking goshinta yayi a ransa yana cewa Rigimamiyar kawai, a hankali ya zameta daga kan hannunsa ya shige toilet dan gaba daya bayajin baccin dukda kuwa gajiyar dayake tare da ita. Wanka yayo sannan yanufi dakinsa dan ya shirya, kayan sawarsa da ya barwa Abdallah ya jera masa tun a jiya da safe be gama ba ya shiga karasa shiryawa cikin wardrobe din a nutse ya kunna waka dan ta debe masa kewa. Yadauki kusan 1hour yana shirya kayan sannan ya gama. Ganin har lokcin bata tashi bane yasakashi fita palour ya zauna yana karewa komai kallo. " So unique" ya fada a zuciyarsa. Babu tarkace kwata kwata a palour daga set din hadaddun English Royal Gray color se daukan ido sukeyi sefa centre table, centre carpet dake shimfide a tsakiyar palour, Se fa Side Table a tsakanin kujerun. TV stand dinta da Tv kanta abin kallo ne, shimfidediya bango guda se wata flower guda daya a gefen. kowanne bango falon sunsha ado da wallpapers masu bala'in kyau kai ka rantse a gidan turawan asali kake. Motsin daya jiyone ya sashi juyawa, Hamdah ce tafito tana yatsina fuska cike da shagwaba hannu ya bude mata alamar tazo. Cikin takunta me nutsuwa da daukan hankali harta karasa tashige jikinsa sannan tace "Shine kayimin wayo nayi bacci ka gudu ko?" Peck ya mata a goshi sannan yace "Sorry babe ba guduwa nayiba banaso na tashekine kinji" ya karasa yana kallon idonta masu kyau. Kasa jurewa kallon tayi ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi hakan yasashi dagota fuskar tata, "Look at me" ya fada in a low tune, tana dagowa ya hade bakinsu yafara aika mata da sakonnin daya dade yana ajiyewa, ya dade yana jiran wannan chance din yau gashi Halal ya samu, nan ya shiga kissing dinta like his whole life depend on it. A farko ta so tayi masa gardama amma ko me ta tuna kawai ta sakar masa kanta ya shiga sarrafata yanda yaga dama. Knocking din da akeyi da karfi ne ya katseshi, kallonta yayi ganin yanda ta takure a jijin kujera se kuma ta mike da gudu tayi daki, jiki a sanyaye ya mike shima yabude kofar a ransa yana mitar waye wannan ya katse masa jin dadi.