Sashe 41
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fada tana zama akan stool din gaban mirror. Murmushin yaqe Hamdah tayi taba ci gaba da yiwa Miima wasa dan bata so ta dago kanta Ayshan ta fahimci halin da take ciki. Juyawa Aysha tayi idonta ya sauka akan hoton Abdul din data ajiye a gefe take jikinta yayi sanyi itama se ta kasa cigaba dayi mata magana. Zaman kurame suka cigaba dayi har seda Parrot Afeeya ta shiga dakin da Jaririnta Asad dan wata uku me dan banzan kukan tsiya lokacin ma kukan yakeyi, dungurar dashi tayi kusa da Hamdah tana cewa "kai Jama'a nifa dan nan ya isheni ayi yaro se shegiyar rigima ba sakat wani ya daukeshi se kuka" "Ikon Allah abinda ka haifa ne kuma ze dameka Afeeya ga jarabar son yaya amma bazaki iya kula dasu ba" Aysha ta fada tana daga Asad dake ta chanyara kuka. Kayan jikinsa ta rage masa nan da nan kuwa se gashi yayi shiru seta ce "Bawan Allah ashe zafi ne ya dameshi wai halan mantawa kike a Nigeria kuke da kike sinqeshi da uban kaya tsabar mugunta kisa masa riguna har uku". " Ki kyale wannan yaron wlh haka yake da shegen rig ima so nake ya saba da kaya masu nauyi dan mun kusa komawa kuma lokacin sanyi za'a shiga" cewar Afeeya, haka suka ci gaba da tattaunawa dukka dai akan yara ita dai Hamdah ta tafasa bata ce musu ba har Maryam da Anisa kanwar Mijinta suka shigo. "Amarya nafa manto saqonnan se dai in kin samu lokaci gobe ko jibi ki shigo dan inna koma yau gaskiya bana jin zan kuma iya fitowa" Maryam ta fada tana zama dakyar a gefen gadon saboda jikinta da yayi mata nauyi sosai qarfin hali kawai takeyi, da kallon tausati ta bita, gaba daya ta sauya saboda tsohon cikin da take dashi, na uku kenan bayan Ruqayya ta kuma haifar Aliyu se yanzu kuma wannan cikin, har tsiya suke mata wai tayi sauri se tace gara ta maida abinda ta zubar. Basu wani dade ba kowacce ta tafi gidanta tunda dama duk da motocinsu suka zo. Da daddare Abdurrahman yazo wai akan yaji tsarinta me dame zatayi na biki, kallonsa kawai ta ringayi gani take ma ya raina mata hankali se kace wata yarinya har ma yake tambayarta me zatayi da biki ko kuwa ance masa wani son auran takeyi, se kawai tace masa "Abubuwa da yawa inaga sati zan yi ma ina shagali se inda kudina ya tsaya" ta fada cikin sigar gatse shi kuwa gogan a tunaninsa da gaske ta ke se kuwa cewa yai "Kai amma naji dadi da i was thinking se Thursday zamuzo kano Friday daurin aure kice na taho tun Monday kawai". Seta ce masa " Eh koma tun next week kai kayi zamanka ma kawai daga yau se an daura se mu tafi tare kawai". Se a sannan ya gane inda ta dosa, dan murmushi yayi yana shafa kansa sannan yace "Allah baki hakuri amma please tell me how much you will need for the wedding ko ke bazakiyi komai ba. i'm sure Mum will do". Kafewa tayi akan bazata karbi ko sisi ba har abin ya bata masa rai, shifa har yanzu ya gane bafa wani masauki ya samu sosai a zuciyarta ba, mma ba komai wuyarta daya dai a daura yasan Seta biyu ta yanda yake so dan haka se ya mike ya qarasa cikin motarsa ya dakko wata babbar Envelope da ya taho da ita kamar yasan zasuyi haka, miqa mata yayi yana cewa " Gashinan manage this in da buqatar qari se ki gayamin and get ready there will be a grand dinner at Kaduna bayan an kaiki" "Bazan iya halarta ba" ta katseshi, se ya daga kafaar sa dukka yace "Fine, gobe da safe zan tafi kilan se Thursday koma Friday morning din feel free to call me if you need anything" ya juya yai tafiyarsa. Juya Envelope din hannunta take dan ta mata nauyi, seta juya kawai ta koma cikin gidan. A parlour ta tarar da Su Zahra da Anty Amna se Mumcy da Maman su Maryam da wata abokiyar aikinta Dr Ramla da sukazo tare da Maman su Maryam din, tana shiga sukayi musu sallama suka tafi suna ta tsokanarta wai Amarya. Anty Amna ta miqawa envelope din "Wannan kuma na mene ne" ta fada taba qoqarin yage bakin takardar, hannu ta watsa alamr oho ta zauna tare da miqe kafarta tana chanza channel. Zaro ido Anty Amna tayi ganin uban kudaden da suke cikin katuwar envelope din, "Anty Maryam kallu ki gani 5M ne cif" ta fada bakinta na rawa kamar bata taba ganin kudi masu yawansu ba, kallon kudin Mumcy da Zahra sukayi sannan suka maida hankalinsu kan Hamdah tata qurawa Tv ido suna neman qarin bayani. "Wannan kudin daga ina" mumcy ta tambayeta, batare da ta juyo ba ta bata amsa da "Abdurrahman ne ya kawo wai na hidimar biki in basu isa ba a gaya masa". "Basu isa me ba, wato da aka ce karya saka komai na furnitures din shine ze baki kudi har Million 5 kiyi me dasu ko ke kika ce masa kina buqata" Mumcy ta qara tambayarta, seta juyo ta kalleta sannan ta mayar da kanta batare da tace komai ba "Mumcy wannan fa ba komai bane akan irin abunda Abdurrahman yakewa mata in zeyi aure, shifa kamar besan darajar kudi ba haka yake akan mace nidai tsorona yanda auransa basa zuwa ko ina amma dai kunce kun amince kuma Abban su Amrah ma yace ba matsala to Allah yasa hakan" Zahra ta fada bayan data sauke tagumin da tayi, ita dai har ga Allah auran be kwanta mata arai ba. Tasan matarsa farin sani kishiyoyi biyar ta kora duk ciki wadda ta dade itace tayi wata shida qarqarin dadewarsu wata biyu uku ne suke fita dan ta qarshen ma daya saka satinta uku ta fita Duk da wasu sunce wai matan dan kudin daya ke kashe musu suke auransa sabida in ze auri mace bata zuwa da ko tsinke sannan duk wadda ya saka seta tattara komai daya siya mata ta tafi dashi to wai auran neman jari sukeyi. **************************** Ranar Tuesday ya rage saura kwana uku daurin auranta ta shirya zuwa gidan Maryam karbar wasu kaya data siya a hannunta dan tana so ta gama hada kayayyakinta a daren ranar washe gari za'a kaisu Kaduna. Gaba daya satin dauriya takeyi bata jin dadi kwata kwata ga faduwar gaba data ke yawanyi har Mumcy tayuwa complain tace ta dage da addu'a insha Allahu ba abinda ze sameta se alkhairi to yau tunda ta tashi abin yafi na ko yaushe. Wanka tayi ta saka doguwar riga Chiffon Abaya me adon stones masu kyau, kalan Dark blue ce dan haka ta mata kyau ta qara haska yaluwar fararta da gyara yasa taqara kyau. Abin kirki yau jarda su Eye liner da Mascara ta sakawa zara zaran eye lashes dinta sannan ta shafa chapet akan lips dinta. Turare kadan ta saka dan jikinta kamshi ya gama kamashi sannan dukka kayanta kafin ma agoge seta turarasu da turaren wuta na kaya asalin me kyau da Hajja take bata duk sanda taje gaisheta. Sabuwar motarta data siya Last month da kudinta bata taba hawanta ba se yau ta dauka ta hau titi tanajin ta gata nan kawai. Seda ta biya wasu guraren sannan ta dauki hanyar gidan Maryam din zuciyarta na qara tsananta bugu adadin kusancinta da gidan, koda ta isa kofar gida kasa shiga tayi saboda ji tayi jikinta ya dauki rawa gashi tana ta kiran number wayar Maryam din tana ta ringing bata picking haka ma ta Yusuf data tabbatar yana gari. Dukda Me gadin ya bude mata gate amma ta gwammace ta bar motar a waje, se ta fito ta dauki ledar datayowa Ruqayya da Aliyu tsaraba sannan ta dauki handa bag dinta ta nufi cikin gidan, a gate suka gaisa da Sulaiman me gadinsu take tambayarsa Ko Maryam tana ciki tana ta kiranta bata dauka ba "Tana nan Hajia baqi tayi inga shi yasa basu daga wayar ba da kinshiga da motar ciki naga sabuwa ce kar yara su karta miki, mota fa tayi kyau Allah ya sanya alkahiri" da Amin ta amsa sannan tace masa ba dadewa zatayi ba bari ta shiga ta fito, yasan me take nufi nan da nan ya hau murna dan a duk baqin da suke zuwa gidan yafi maraba da ita se kuma wani Abokin Alhaji da shima baya gajia da kyauta. Wata hadaddiyar mota ta gani a parking space din baqa se daukar ido takeyi, motar ta burgeta kwarai a ranta tace "Oh su Yusuf yan gayu mota aka sake kenan burin Maryam ya cika seya bar mata tasa" tana wannan tunanin tayi sallama tareda tura qofar palour da ba'a gama rufewa ba. Wasu turare ta shaqa masu matuqar dadi da sanyaya zuciya nan take taji duk wata gajiya data dakko ta rabu da ita. "Masha Allah Bestie fito ki dakko min wannan turaren koma wanne irine ina so kamshinsa yayi min wallahi" ta fada tana kada bude kofofin hancinta dan ta shaqi turaren da kyau bangare daya kuma tana jin kamar tasan kamshin a wani gurin amma ta manta, kilan a gurin Abdulmalik shine meson turare kala kala. Kan daya daga cikin kujerun palour tayiwa kanta masauki tana fadin "wash Allahna Aliyu, Rukky kuna ine wai naji gidan shiru haka" idonta a rufe duk take maganar dan haka batasan da mutane a cikin palour ba. Bude idonta tayi tana dan tsaki kadan tace "Kilan tana can tana baccin nan nata shiyasa ma bata daukan wayar ba" ta fada sannan ta dauki kofin lemon data gani an rufe da dan murfin glaas ta kafa kai ta fara sha, Sauran lemon neya maqale mata a makoshi lokacin da idonta ya sauka akan mutumin dayake zaune kan kujerar da take facing dinta, ji tayi kamar ansa kwado an datse mata jijiyar datakai iska cikin kirjinta ba shiri ta fara tari kaman zata shide ga wasu zufa da suka fara keto mata babu ji babu gani, seta zame mayafin kanta da ribbon din data daure gaahinta dashi har lokacin tarin be tsaya mata ba, ji takeyi tamkar ta cire rigar ita ma ko