Sashe 3
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kanta tayi da niyyar mika musu wayar su gani se ganin mutum tayi akanta kamar gunki. "Ke wato bakiji me nace miki ba ko". Seka rantse bashi yayi maganar ba. Dukda yanda zuciyarta ke bugu hakan be hanata dauke kai tayi Kaman ba ta jishi ba. "Wai bada ke nake magana ba ne ehe".. "Toh ai ganinayi sunana HAMDAH ba keba.......Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata da ta sakata kasa qarasa abinda tayi niyyar fada "I give just 2 minutes to come to my office if not (ya murda hannunsa) wlh nida ke ne yau a makarantar nan". Sosai ta tsorata, zata iya cewa ba'a taba mata tsawa kamar haka ba. Babu shiri Ta mike jikinta na rawa tabi bayansa. A tare suka shiga office Din Dan har suna kusan cin karo. Kallonta kawae yakeyi Wanda har seda ta tsargu. Seyanzu ya gano zallar yarinta a tareda ita in ya rantse beyi karyaba bazata haura shekaru 17 zuwa 18 ba. "How old are you?" Kallonsa kawai tayi irin karaina min hankali tareda dauke kai. "I'm I not talking to you?" Ya fada cike da hargagi Dan yarinyar tafara kaishi bango." I'm 17" ta bashi amsa. Hawaye na taruwa a idonta. "No wonder she is like this dan mutum me cikakken hankali bazeyi abinda takeyiba" ya raya hakan a zuciyarsa. "And what about my car?" "Ur car?" "Yes or u want to fool me again" "Oh sorry tana gida you can come and carry it when you are ready". Dukka idonsa ya bude akanta yana kallonta gaba daya ta dinke masa kwakwalwa in banda Hmmm babu abinda ya iya cewa kafin ya nemi guri ya zauna. "Saboda ni na kaita Gidan naku?" dakyar ya furta maganar yana relaxing akan kujerar sa. Bata amsa ba daman be saka rai da zata amasa masa ba dan haka ya ci gaba "return it to where you took it inkinga dama kuma ko ki rike Danni ba tsiyar mota nakeyiba". Yana kaiwa nan ya Shiga tattara system dinsa da wasu takaddu yayi waje ya barta a tsaye a wurin yana jin lokacin data fashe da kukan daya fi kama dana takaici. "Kudos" ya fada yana murmushi ko ba komai tayi kuka ya rama abinda tayi masa. Ina wuta HAMDAH ta jefa GURU, kuka Take kamar wadda ya daka, wato itace take tsiyar mota? Ai dai ya gani ba a kasa take yawo ba bare ya gaya mata wannan maganar. Su Maryam dake tsaye a waje suna saurarinsu tsab sukayi saurin shiga bayan fitar sa. Dakyar suka lallasheta "kinga abinda nake gaya miki ko gashinan yanzu kinja ya gaya miki magana kuma kiyi addu'a tunda yayi marking face dinki Allah ya raba ku kawae. Gida tawuce Dan batajin zata iya saurarar wata lecture again Wanda ko a gidan bawanda ya kulata illah khaleefa daya bita ya karbi key din motar Guru don ya cire Battery gudun samun matsala Dan wannan bashine karo na farko ba datayo awon gaba da motar mutane sedai babu wacce ta taba kwana. Tundaga wannan rana bata qara bari koda ido sun hada dashi ba, ko lecture yake zata kifa kanta a desk ne daya fahimci haka shima se ya tattarata ya watsar dan tana nema ta ja masa raini a gurin sauran Daliban ajin. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 0 Kwanci tashi ba wuya gurin Allah se gashi suna shirin fara first semester exam, sosai take karatu Dan duk fitinar Hamdah akwaita da gane karatu son boko a jininta Yake gashi kuma Allah ya mata kwakwalwa dan Haka take zuba sharafinta. Cikin lokacin abubuwa da dama sun faru tsakani ta da Dr AA (Guru) Dan ayanzu sun zama tamkar annabi da kafiri, Sosai yake matsa mata kiris yake jira tayi badai daiba ya dizgata haka itama batayin kasa a gwuiwa wurin baje masa kolin tata fitsarar. Dawowarta kenan daga school a matukar gajiye ga paper da sukayi tadan so tayi wahala, ita kadai taketa kalan fadanta akayi sa'a ba Wanda ya kulata dama Hamida ke biye mata suyi tayi Kaman kaji (Inji junior ). Da masifai ta dauko wayarta data isheta da kara tuntuni "wannan ko mayene ai se haka kayita kira ba'a daukaba sekace dole babban abin haushima anyi hiding Number mtsw" taja wani dogon tsaki. "Kyaji da jarabarki ke kadai tunda kullum bakida aikinyi se masifa" cewar khaleefa. Rike qugu tayi tana kallon Khaleefa daya dauke kai kamar bashi yayi maganar ba tace "Lallaima yaronnan ni sa'ar kace ko da kai nake ehe dazaka kulani Ina ruwan mutum da mutum in ba abinba". Kedai kika sani dama inba Abdulmalik dinba waze iya da masifarki shima din Allah yasa ba lambo yamikiba se kinshiga ya moreki wallahi". Abincinsa ya dauka ya nufi kofa dan yasan bata gajiya yanzu seta haramta madmsa cin abincin yana jinta tana cewa "Ji banza tunda ance maka dolone irinka ko eh na maji din ahakan dai yagani yanaso". Fasa fitar yayi ya dawo suka cigaba da caccakar juna har wayar ta tsinke "wlh sena ci uban duk Wanda yakara mana magana anan tunda bakuda aikinyi" Yah Farouk ya katsesu. Ta gefen ido ta harareshi Dan duk iskancinta tana shakkarsa dukda kasancewa shi take bimawa. Baya daukan wargi ko kadan Dan bata manta lokacin da suna secondary school intai neman tsokanarta haka ze rubuta ya hukunta ta dallah dallah shiyasa take shiga taitayinta. Dakinta ta wuce tareda kwanciya takira Habibinta suka fara soyewa. Number dazu ce dai aketa nacin kiranta da ita "Baby please bari na answer call dinnan tun dazu ake kirana da Number kuma bansan waye ba". "Ok dear I will be expecting your call". katse kiran nasa tayi sedai kafin ta kaiga answer wa har Wancan kiran ta katse, tsaki kawai tayi ta Mike dan gabatarda sallar Magariba da ake ta kira. ************** Abdul-ahad ne kwance kan katafaren gadonsa daya sha shimfidu na alfarma, gefensa Babban amininsa ne Fahad da waya a hannunsa yanata faman dannawa "Hey dude wai mekake yimin da wayane since I told you I want to make a call". Kallon Abdul'ad Fahad yayi kafin ya goge call log ya mika masa wayar "Gashi dama I wanted calling one number ne". "You must be mad waya ce kakira wannan number" number wa ka kiramin da waya" yafada yana kafe abokinnasa da ido. Kusada shi Fahad ya dawo tareda dafashi "Hey relax Bafa wata na kira ba HAMDAH AMMANI ce" wani kallon zaka ci ubanka AA ya masa batare da yace komai ba. "Abdul'Ahad its a high time for you to understand your feelings we are not getting younger Girma muke so stop acting like a small boy be bold enough to face her and express your feelings to her kasan ance The Sooner the Better". Shiru yayi for some time kamar ba zeyi magana ba sannan yace "No not yet she is still young banasan shirme kasani" ......."Ok then you wait till she grow up Allah ya taimaka "Fahad ya fada yana nufar Toilet din dake Manne da dakin. Sake kwanciya Abdul'Ahad yayi yana tuna maganganun Abokinnasa "ofcourse yagirma koda ba a shekaruba (he is 28) Amma yayi achieving abubuwa da dama arayuwarsa tunda a kananun shekaru irinnasa ya taka matakin PhD, more over zancen Hajiyarsa kanan kullum aurensa kasancewarsa da namiji tilo da Allah ya azurta iyayensa dashi ko ba komai tana so taga jikoki ta bangaren Abdul dinnata. Murmushi yayi tunawa da halin mutuniyar yasan ayanda suke wannan takun sakar bakaramin kai ruwa rana zasuyiba."Wai ma dukda kake wannan tunani Kaman ance maka kai take jira kasani ko ta tsayar da miji?" Zuciyarsa ce ta raya masa hakan.da karfi ya furta "No it can't be she is mine" Nan take idonsa yakada yai jajir tsabar bala'in kishi dayake cinsa. Fahad dake gyara hannun rigarsa ya kalleshi kawai tareda girgiza kai Dan Lamarin na AA sai du'ai dan kuwa yana neman zaucewa kan macen da bata san ma yanayiba "Allah ya kawo sauki "yace tareda ficewa daga dakin. Dole shima ya mike yayo alwala sannan yanufi Masallacin dake cikin gidan nasu, har akayi Sallar isha suna zaune daga shi har Fahad babu wanda ya sake yiwa wani magana se bayan da suka idar da Sallah suka fita a Motar AA din. Still dae akan Hamdah yake ta masa magana yana nuna masa akan ya kamata tasan halin da yake ciki yana guje masa abin da ze iya zuwa ya dawo "Man did i tell you that I'm in love with this girl or what duk ka bi ka ishe ni da zancenta" baki bude Fahad yake kallonsa dan ya bala'in goge masa Hadda " Kai Alhamdulillah amma naji dadi dan wallahi dama tunda ka nunamin picture dinta naji kawae wata kibiya ta soki zuciyata dama na hakura ne saboda kana sonta amma yanzu tunda kace ba haka bane dan bani numberta I want to shoot my shot......." wawan birkin da AA ya taka ne yasaka Fahad yin shiru se innalillahi da yake ta maimaitawa, Allah ne ya rufa asiri basu daki motar gabansu ba. Be gama dawowa daga shock dinba yai parking a gefen titi cikin muryar dake nuna matukar bacin rai ya kalli Fahad din yace "Get out from my car". Tsabar mamaki Fahad se ido kawae tsawar daya buga masa ce ta saka shi bude motar babu shiri dan yasan in ran abokin nasa ya baci to se Allah kawae yana fita kuwa ya zaburi motar a 360 ya bar Fahad kamar Gunkin da aka sassaka. "to me na masa da yayi zafi haka bashi yace baya sonta ba fisabilillahi" daga kafada yayi kafin ya tari Napep ya koma Gidansu AA ya dakko motarsa. Yau kam farin ciki takeyi sosai kasancewar zasu gama exam ga kuma dawowar Habibinta datake saka rai a gobe. Cike da Fara'a take komai har ta manta da bacin ran Fadan da Mumcy tagama yi mata akan Motar da tun Farkon semester take a gidan. Genetics paper ne dasu A qarshe dan haka dole ta nutsu tayi karatu sosai dukda ta yarda da kanta a wannan fannin amma kodan gujewa wulakacin Guru Dole ta bashi mamaki. 9am zasu shiga exam din amma tun 7:30 tana cikin school din. A wani dan garden suka zauna tana kara yiwa su Aysha explanation kan abinda