← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 62

Sashe 40

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin fuskarsa, juyo da ita yayi sannan yace "Kin ganshi shine madadina a gurinki, shikadai ne mutumin dana yarda yana miki irin son da nake miki amma kin san me" "Aa" ta bashi amsa. Se ya ci gaba "Wai fushi yake dakowa akanki, ya rabuda kowa da komai nasa saboda ke, kiyi min alqawari zaki nemeshi ki dawo masa da Farin cikinsa daya rasa ta sanadiyarki". Qanqame hannayensa tayi tana hawaye tace " Bazan i...." Se ya katseta "Alfarma zakiyi min ko akwai abinda zan rokeki ki kasa yinsa shikenan ni na tafi" ya juya kamar ze bar gurin, setayi saurin riqo shi tace "Na maka alqawarin zan nemoshi a duk duniyar da yake, zan bashi duk wani farin ciki dayake nema iyakar abinda Allah ya horemin". Se ya saki wani murmushi me kyau sannan ya kama hannunta suka qarasa har gaban mutumin da har lokacin bata ga fuskarsa ba. Hannunsa ya kama ya hada da nata yace " Ga Amanata nan kariqemin ita dakyau" sannan ya kalleta ita ma yace" ki gaidamin da Hajjah ki gaya mata na yafe mata dama ni ban taba kullatar ta a raina ba nasan ko mai ya faru muqaddarine na barki lafiya" daga haka ya bace mata. Kokarin kwacewa daga hannun mutumin ta farayi se a lokacin ya dago fuskarsa, "Sir Abdul'ahad" ta faa cikin son tabbatar da abinda idonta ya gani, be kulata ba ya fara jan hannunta dan subar wurin suddenly sega wannan nataccen ya fado kamar an jefoshi ya fizge hannunta daga na Abdul'ahad yana cewa "Bazan barki ki bi wani ba ke tawa ce". Kallon Abdul'ahad daya tsaya ba tareda yace komai ba tayi se yayi dan guntun murmushi sannan yace "Let it be, kuje kawai" ya juya ya barsu a tsaye shima. Seta fara ihu tana fadin "Abdulmalik ka dawo Dan Allah karka tafi kazo ka rabani da wadannan mutanen basu cancance ni ba" abinda take maimaitawa kenan acikin baccinta har maganar tata ta fito fili bata sani ba. Mumcy da ihunta yafarkar da ita ta shiga dakin babu shiri ta shiga tada ita da alama bata cikin hayyacinta. Kuka sosai takeyi tana gaya mata yanda sukayi da Abdul din A ciki mafarkinta, seta rungumeta cikin lallashi tace "Ki dauka hakan nasiha ce aka miki, kiyi hakuri Hamdah ki mikawa Allah lamuranki ki nemi zabi sa sekiga kin samu fiye da abinda kika rasa kinji" haka tayita lallashinta har ta samu tayi shiru, tunaninsa fal a zuciyarta se kuma ganin Sir Guru daya makale mata a zuciya, rabon data tuna dashi har ta manta, dama motarsa ce take gani ta tuna shi to tun bayan da akayi musu gyare gyare a gidan aka dauke ta aka boye a garage dan Abba yace ayi ta ajiyarta har ranar da me ita ze waiwayi abarsa tunda tace bata san ina yake ba. To ta ina zata fara neman sa ma ita yanzu? Abu daya tayarda idan har Allah ya hukunta wani al'amari a tsakaninsu komai tsahon lokaci ze dawo duk ma inda ya tafi, da wannan ta samu ta yakice tunaninsa a zuciyarta. Kwana uku ta jera tana salatul istikara sannan ta dage da addu'a akan neman zabin Allah, a ranar data cika ta ukun ne tana zaune Abdurrahman wanda sun fi sati basuyi waya ba ya kirata. Tayi qoqari sosai suka danyi hira abinda bata tabayi ba ko ba komai yanzu kashi 70 na nauyin da takeji a zuciyarta ya ragu. Se a yanzu take ganin wautarta at 25 years har take tunanin ta gama aure, kwadayin haihuwa da son yiwa Abdulmalik takwara su suka kara saka mata azamar son tayi auran, cikin maganar ne yake gaya mata ai yana kano se tace masa yazo in ya samu lokaci tana son magana dashi. Kamar me jira da yamma se gashi yazo, tana zaune ya kirata akan gashi a waje lokacin Mumcy bata nan tana asibiti daga ita se Mama Asabe da Annur da aka kawo dazu, bata shafa komai ba ta zura dogon hijabinta dark purple ta fita. Tun daga nesa yake kare mata kallo a Gaskiya in ya rasa yarinyar nan bai san yanda zeyiba. Dukda fuskarta babu kwalliya Amma ta masa kyau musamman yanzu da ta qara cikowa fatarta har wani kyalli takeyi. Kallon qurillar dayake mata ya sakata harararsa qasa qasa dan ta tsani kallo shi kuma gashi kamar maye yayi ta wani kallonta yana wage baki kamar Wanda akayiwa wata kyauta. Ba yabo ba fallasa suka suka gaisa sannan ta fara magana "Na kiraka ne badan komai ba se mu fahimci juna tunda kasan nidin ba yarinya bace da zamu tsaya bata wani lokaci Dan haka Ina so insan kai waye". Se ta bashi dariya wai ita ba yarinya bace in banda abinta har nawa take yasan dai ko Zahra matar Nazir bazatafi 30 years bare ita kanwarta ta biyu, se yayi dan murmushi sannan yace " Dan Allah wai ni shekarar ki nawane" seta qara hade fuska a dole bata son raini sannan tace "25 meya faru" "Aa ba komai" ya faa yana danne dariyar sa ashirin da biyar shine Amma take kiran kanta babba bayan ko shekarun wasu Yammatan ma bata kai ba se kawai yace "To ba matsala Malama nima ba wasa ne ya kawo ni ba maganar aure ce kuma Kaman yanda kika tambayeni Suna na Abdurrahman Ibrahim Khalil. Mahaifina Ibrahim dan Asalin Kankara ne Mahaifiya ta Maimuna kuma yar katsina amma duk a Katsina suke. Babana Dan siyasa ne nasan bazaki rasa sani Barr Ibrahim Khalil ba tsohon Governor Katsina state kuma Senator me ci a yanzu. Bazan iya gaya miki wasu abubuwa da yawa ba akan Katsina saboda ni a Kaduna aka haifemu acan mahaifiyar mu take zama dayar abokiyar zamanta kuma tana Katsina, sannan tun a kananun shekaruna aka kaini kasar England a hannun Yayan mahaifina na tashi acan nayi secondary school dina har na gama karatuna na Jami'a nidin Psychiatrist ne wato Likitan Masu lalurar kwakwalwa" se yayi shiru yana kallonta. Ita ma shi take kallo jin yayi shiru yasa tace "ci gaba ina jinka" gaba dayanmu mu goma sha biyu ne yaran gidanmu maza biyar mata bakwai kuma ni ne na shida Inada yayye Biyar Maza biyu Mata uku gaba daya duk sunyi aure se autanmu Isma'l kadai ya rage. Shekaruna 38 kuma Ina da Mata guda daya Hajara duk da na auri wasu bayan ita Amma dai yanzu dai ita kadai ce wannan shine Abdurrahman Khalil a taqaice". Kallon mamaki take masa jin wai He is 38 mutumin da take ganin kaman baze wuce 29 ba yayi wuta yaje irin 32 dinnan, se kawai ta gyada kanta sannan tace masa "To Allah ya wuce mana gaba" ta mike tsaye. "Yadai ranki ya dade shikenan dama" "Eh" ta bashi amsa tana shirin barin wurin, Annur daya fito ya kira yana dan yi masa wasa sannan yasa hannu a aljihu ya jiro bundle na yan 1k ya bashi yace "Ungo ka kaiwa Anty ta siya muku chocolate kusha" se yaron ya karba da murna jin an kira chocolate yabi bayanta dan lokacin har taje kofar daki, Sa'idu ya kira ya kwashe uban siyayyar daya yo mata ta kayan kwalliya, turaruka da sauran tarkacen mata sannan shima yayi masa alkhairi ya tafi. Kallo daya tayi musu ta dauke kai karshema tace bata so Hamida da Maman Annur se wata cousin dinsu data zo su dauka su raba, kudin ma karshe Khaleefa ne ya karba bayan ya cirar wa yaron kudin Alawa ya jefa su a aljihu yana cewa "Allah yaci gaba da hankado masu rabon shan wahala ni kayan nan ma da bani kukayi na fara tarin lefe wlh nasan ajikin Zawarawan Hajia Hamdah tsaf zanyi akwati 12" dariya suka saka gaba daya banda Hamdah data debi pillows ta fara jifansa dasu yana cigaba da mata tsiya. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Cikin satin daya Magana ta fara yin qarfi a tsakaninsu dan Har Abdurrahman din ya turo neman izini kamar yanda yake a shari'ar musulunci. Sai ayanzu ta yarda da abinda Maryam take fada mata akan seta bawa mutum dama sannan zata ga abinda ze iya Dan Abdurrahman din ya bata mamaki karshene a soyayya da iya tattali, sau tari in ta tuna wasu abubuwan da ringayi masa setaji kunya dan kamar yanda yai mata alkawari se ya goge kowa da komai daga zuciyarta to yana shirin tabbatar mata da hakan dan in har suna waya sata yakeyi ta manta da kowa da komai din se shi kadai take tunawa. Kamar yanda suka tsara cikin sati biyu Yan uwan sa suka kawo kudin aure da gaisuwar iyaye 500k se kudin sa rana 100k aka kuma tsayar da magana akan sati hudu kacal acewar Abbah ba abinda za'a jira tunda dai anyi bincike bashi da wani hali mara kyau. A Cikin abinda bai wuce sati biyu ba Amarya tayi fes ga wani kamshi na daban da take yi wannan karon Hajjah da kanta take mata wannan gyaran dan a yanzu ta dauketa ne kamar yar cikinta nidai nace duk a banza tunda bana Allah da Annabi bane. Biki ya rage saura kwana goma suka kawo lefe na gani na fada Dan har yafi lefenta na auran fari, kayane iya ganinka tun suna irgawa har suka gaji wasu abubuwan ma dai gasunan kawai kamar ba'asan darajar kudi ba, a ranar Hamdah tayi kuka, kuka bana wasa ba. Se ta ringa tuna ranar da aka kaqo lefenta na auran Abdulmalik da ko kallon arziqi basu samu a gurinta ba dan a lokacin zuciyarta tayi fukafiki tana ta yawo a sama. "Abdulmalik ban sani ba ko wannan shine zabinka, shi ya fado hanyata a lokacin danake tsaka da addu'ar zabin Allah dan haka na rungumeshi na dauki auransa yana cikin jerin _RUBUTACCIYAR QADDARAH_ ta. Zan yi aure zan zauna lafiya insha Allahu zanyi duk yanda kace" kalaman da take ta fada kenan tana rungume da hoton Abdulmalik dayayi kyau sosai kamar ka kirashi ya amsa. Sallamar Aysha ce ta katseta, seda ta share Hawayen fuskarta sannan ta dauki Miima Yarinyar da Aysha take goyo da take ta faman mika mata hannu alamar ta dauketa. "Amarya kinsha kamshi ashe kina daki ko duk Amarcin ne ya fara boyeki" Aysha ta
Chapter 40 · 0% Book details