Sashe 33
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rayuwarsa a Ina? Ta ina ma ze fara rayuwa babu ita? Ba shiri ya nufeta cikin tashin hankali dan se lokacin yaga akwatin da take ja, se ya riko hannunta cikin di mauta ya ce "Ki taimakeni Hamdah karki tafi wallahi kece rayuwata saboda ke nake numfashi a doron kasa. Barinki gidana tamkar barin numfashine daga gangar jikina kiyimin rai karki rabu dani". Duk yanda zuciyarta tayi rauni amma seta dake taqi koda kallon bangaren da yake. " Hamdah mutuwa zanyi wallahi in kika tafi" seta kalleshi da sauri zuciyarta cike da son sa da kaunarsa ga kuma kishinsa dake azalzalar ta duk a lokaci daya. Taci alwashin daga masa hankali ko kadan bata so yaga gazawarta Dan haka ta dauke kanta kawai tayi waje tana share kwallar dake zubo mata shima ya rufa mata baya yanajin yanda Hajja ke kwada masa tana dura masa duk ashar din data zo bakinta. Tun lokacin da suka fara drama ta zama hoto mamaki ya kusan kasheta wai dama wannan yarinyar tana magana, wato ta aura masa uwar Haula ma ba Haulan lallai seta tashi tsaye akanta taga alama ba gurin karamin boka suka kai mata Da ba acewarta gurin masu shan jini aka kai shi. Sanda ya fita tuni tayiwa motar ta key me gadi ya wangale mata Gate se kawai ya shiga gidan da sauri ya dakko mukulli batare da ya tanka Hajja dake karamin hauka ba tana buge bugen waya ko ita da waye oho. A kusan tare suka shiga gidan tana fita ya bita suka tasa tsere tana Kuka kamar wacce akacewa Mumcy ta mutu a haka tashiga palour yana take mata baya. A tsaye ta tarar da Mumcy da jaka a hannunta alamar fita zatayi se yaya Farouk dake gyara zaman hularsa shima batayi wata wata ba ta fada jikin Mumcy tareda fashewa da sabon kuka gaba daya seta kashe mata jiki har bata san lokacin da hawayen suka fara sauko mata ba itama ta shiga cewa "Kiyi shiru Hamdah na Dan Allah kiyi hakuri babu wanda ze miki dole in har ina raye". Seya sunkuyar da kansa wata irin kunyar matar ta kamshi, ji yayi Kaman an daure masa jijiyoyin jikinsa ganin Ya da uwar suna kuka ashe har cutarwar tayi yawan da ta shafi Mumcy itama? Ya tambayi kansa. Amsar a bayyane take sanin irin tarin kaunar dake tsakaninsu Dan ze iya cewa kaf yayanta tafi son Hamdah. Shi kansa Yaya Farouk jikinsa ne yayi sanyi ganin hawayen mahaifiyar tasu gaba daya sukayi zugum zugum suna kallonsu. Abbah dake sakkowa palour ne ya shiga cewa "Ashsha Ashsha Maryam menene haka kuma Dan Allah in baki rarrashi yarinyar nan ba kuma seki tayata kuyi tayi haka akeyi". Janyeta yayi daga jikin ta yashiga Dan bubbuga bayanta Kaman yana rarrashin jaririya har tayi shiru se ajiyar zuciya da take saukewa. "Yanzu kuma me ya kawoku da sassafiyar nan muma yanzu shirin zuwa gidan naku mukeyi" ya fada yana kallon saitin Abdulmalik daya kejin kamar ya nutse a cikin palour tsabar kunya alamar dashi yake. Seya duburburce ya shiga inda inda yama rasa ta Ina ze fara magana ganin yana neman bata masa lokaci ya sakashi cewa "Ok ya isa kasan halin mata akan zancen kishiya dole seka yi hakuri sannan komai ze daidaita tashi ka dauki Matar ka ku wuce Allah yayi muku albarka Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu". Ai tuni ta daka tsallen albarka tace "wallahi ba inda zataje" ran Abbah ne ya baci ya daka mata tsawa "Are you that stupid Ina miki magana kina gayamin bazaki je ba ke kika haifi kanki ko mu muka haife ki?" Duk da wannan tsawar bata sa ta dena kukan se ma mikewa da tayi ta nufi dakin Mumcy da gudu tana fadin "Wallahi bazan bishiba yaje can ya auri wacce suke so ta haifar masu yayan". Tana jin yanda Farouk yake Bambami yana seya ballata Abban zatayiwa rashin kunya saboda ita bata da mutunchi ita dai ta qule a daki ta musu banza. Hakuri Abbah ya shiga bawa Abdulmalik " Kayi hakuri kasan dan yau ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba amma ina zuwa insha Allahu zata bika ku tafi yanzu ba se anjima b". Baze iya masa musu ba, wata irin kima da darajar tsohon ta qara ninkuwa a idonsa. Ya tabbatar da cewa shine mara gaskiya amma hakan besa sun goyi bayan yar su ba to shi kuwa in ya wulaqanta yarinyar nan yacewa Allah me? Se kawai ya mike ya kasa hada ido da ko daya daga cikin su yace "Aa Abba kabarta zuwa anjima insha Allah in ta huce sena dawo" yai azamar fita daga gidan dan shidai da kunya kuma ya zauna musu. Tunanin mafita yakeyi har ya qarasa gida ya tarar da Hajja ta tafi se wasu mata daya gani da sunan wai sun zo qarasa gyaran daki. Tijarar da shi kansa besan ya iya irinta ba ya zazzaga musu ya rantse in har ya fito ya tarar sa ko kurar motarsu a layin seya sa yan sanda sun kama su dan haka suka shafawa kansu ruwan sanyi suka tafi dan sun san tsaf ze aikata abinda ya fada. Seda ya bame qofofinsa dukka sannan ya fita yasan ko yaje office bashida nutsuwar aiwatar da komai dan haka ya juya kan motarsa ya tafi gidan Yusuf dan yasan yana gari. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Cikin Hikima Mumcy ta ringa fahimtar da ita rayuwa da abinda yake cikinta. "Ki gaya min gaskiya kina son mijinki ko Aa" mumcy ta tambayeta. "Ina sonsa Amma....." Seta yi saurin katseta "Babu maganar Amma dama abinda nake so naji kenan har yanzu kina sonsa dan haka tashi kije ki bawa Abban ku hakuri kizo kinji Hamdahna". Jiki a sanyaye ta shiga bedroom din Abban yana zaune idonsa da farin glass yana duba littafin Sahih Muslim. Gefe ta samu ta zauna kanta a qasa murya na rawa alamar son fashewa da kuka tace " Abba kayi hakuri dan Allah". Seda ya cire glass din idonsa ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yai mata alamar data zo, seta fada jikinsa lokaci daya ta sake fashewa da kuka. Be hana ta ba seda tayi me isarta ta gode Allah sannan ya fara mata Magana. "Mamana bansan lokacin da kika baci da taurin kai ba duk ina tarin hakurin nan da kike dashi? Kin manta hakuri da rashinsa banbancin dan taqi karamine. Duk inda akaje aka dawo in kikayi hakurinnan zaku zama daya kinji wuyarta daya yayi auran". " Abba niba auransa ne ya dameni ba meya sa ze boyemin tun farko be gayamin ba ai bazan hanashi ba amma Abba baka ga irin wulaqancin da yan gidan sukeyi min ba Abba cewa suke fa wai ni Juya ce bana haihuwa kuma wai ma Ni Mayya ce na lashe masa kurwa". "Inji waye tace miki Mayya" ya tambayeta. "Hajja ce harda ma kannensa su Zainab da Khausar". Se yai murmushi irin nasu na manya sannan yace " Ina raye bazan taba bari ki wulaqanta ba kuma duk wadda ta qara hadaki da maita sena dauki mummunan mataki akanta mark my words, yanzu kiyi hakuri ki duba irin kaunar daya ke miki ki koma kinji mu kuma insha Allah zamu tsaya matuka ganin baki wulaqanta ba bi jahi rasulillah kema zaki haihu, se kin haifi dan da Duniya dukka zatayi alfahari dashi bama iya mu kadai ba". Da haka yai tai mata Nasiha har zuciyarta tai sanyi, zuwan Zahra da Hamida da yanzu take ABU zaria ya sa ta koma Dakin Mumcy suka hadu suka ci gaba da kwantar mata da Hankali. Kalamansu sun kashe mata jiki tareda raunatar mata da zuciya. "Waini in banda sakarcin irin nata ma tayaya zaki bari makiyanki su ci galaba akanki har ma suga gazawarki? Yanzu da kike ikirarin barin gidan wa kika yiwa kanki fa kin rasa miji me sonki tsakani da Allah su kuma burinsu ya cika. Dan Allah ki nutsu ki koma cikin hankalinki kidubi irin halin da kika saka kanki da mijinki a ciki kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai duk abunda ba'a ginashi a tafarki gaskiyaba ba inda zeje Insha Allahu bazaki tabe ba". Haka suka ci gaba dayi mata nasihohi tareda shawarwari, Anty Zahra ce ta kirashi akan ya barta tadan kwana biyu a gida ko zata qara nutsuwa sukuma sukayi amfani da wannan damar gurin yi mata duk wasu shirye shirye daya kamata. A kullum tunanin ta be wuce yadda zata iya Raba Abdulmalik da wata mace ba, ita bata san ya zatayiba ranar tanaga hadiyar zuciya kawai zatayi da dai ta jure ganin Abdul tare da wata a matsayin matarsa amma tayi matuqar dauriya wurin nuna komai ya wuce kodan ta kwantarwa da Yan uwanta Hankali. Kwananta uku a gidan ta koma, yayi matuqar mamakin ganinta da chanzawar ta lokaci daya. Sosai ya ke godewa Allah da samun surukai masu karamci da sanin ya kamata. Sababbin furnitures yan ubansu Yaya Abubakar, Yaya Baffa da Yah Farouk suka mata gado uku kowanne daki da set din Kujeru Biyu Royal da Leather. Haka kayan kitchen dinta ko cokali Mumcy batabar mata tsohoba seda a ka canza harda Kitchen cabinet din kuwa sega gida ya qara fitowa ras jerenta har yafi na Amarya yar Governor kyau da suke ganin sun qure mata qarshen gata. Duk wannan budurin ita ko a jikinta dan ba wai sun birgeta ba ne ta dai sakawa ranta bazata qara shiga sabgarsa a gidan ba. A bangaren su Hajia Hauwa kuwa Hankalinsu ya kwanta Da jin bata gidan azatonsu aikinsu ne yaci nan fa suka daura sabuwar damarar janyo hankalin Abdul din ya koma kan Haula gaba daya dan tuni sun gama da bangaren Hajja kamar Tv da remote haka suke sarrafata. Sun samu kanta ba kadan ba kamar Bawa da Ubangidansa haka take musu biyayya. Uwar gida Hamdah kuwa Shawarwari da nasihu daga yan uwa da abokan arziki tareda Addu'a data yawaita su suka taimaka wa zuciyarta wurin samun nutsuwa, ta mika lamarinta ga Allah tayar da wannan din ma wata *KADDARAH* ce *RUBUTACCIYA* cikin kundin rayuwarta zata kuma rungumeta hannu bibbiyu, a kullum rokonta be wuce Allah daya bata ikon cinye wannan Jarrabawa ya dora mata. Lamarin