← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 62

Sashe 60

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'MR PROBLEM' take ji. Waiter na qoqarin ajiye mata abincin Nureen ya karba yayi settling bill din sannan ya ajiye ya shiga nade hannun riga acewarsa wai a baki ma zeyi feeding nata saboda yasan ta gaji sosai. _ABDUL'AHAD_ Tunda ta shiga gurin hankalinsa yake kanta har zuwa lokacin da ta zauna. Magana sukeyi da wani farin tsohon bature amma ya karkata hankalinsa gaba daya zuwa kanta yana watching duk wani motsinta har zuwa sanda yaga wani Yaro me kama da yan Daudu acewarsa ze bata abinci abaki se ya mike a matuqar fusace in seconds ya isa wurin daidai lokacin Nurain ya kai mata spoon baki lokaci daya ya hambarar da abincin ya zube cokalin ya fadi can gefe dan. Bakinta daya hada ya buge tsabar masifa ta dafe tana kallon yanda ya cakumi wuyan rigar Nurain din tareda falla masa mari ai ba shiri ta riqeshi ganin yanda jikinsa yake wani rawa kamar wanda ake kadawa gangi. "Sakeni sena koya masa hankali gobe ma idan akace yaje ya bawa matar mutane abinci seya qara" ya fada a fusace yana tunkude hannunta daga jijinsa. Seta saka kuka ganin yanda yake faman naushin Nurain shi kuma ya tsaya kaman dolo har ya fasa masa hanci ga mutane har sun fara taruwa wasu ma daga waje suke shigowa kar abasu labari dakyar mutanen da suka sanshi suka janyeshi ya kuwa finciketa kamar leda suka fice daga gurin bayan da ya gama bawa securities din da sukazo statement cewa matarsa Nurain din ya kula har yana qoqarin taba mata jiki (kuji sharri). Yanda yake fizgarta da kuma takalmin kafarta yasa ta kasa saurin ma se kawai ya sunkuceta kamar wata jaririya har suka qarasa inda motarsa take, ita kam zuwa yanzu abin ya dena bata mamaki sema tsoro dan haka taja bakinta ta dinke har ya sauketa a cikin motar ya shiga ya kunna saboda programed ce se kawai ya fice ya barta a ciki bayan ya kunna mata Ac yasa lock ta waje yai tafiyarsa. Seda ta shefe awa uku cif a motar ba Azahar ba la'asar sannan ya dawo fuskar nan dinke tsaf kai ka rantse be taba dariya ba. Kallonta yayi with a serious face yace "Bayan shigar banza wato harda Yan iska kike kulawa ko?" Yanda yayi maganar ya bata tsoro amma bata ga dalilin da zesa ya ringa juyata kamar wata abin ikonsa ba seta dake taqi koda kallon inda yake. "Ba dake nake magana ba kikamin banza" ya fada on top of his voice da har seda ta tsorta, fuskarsa data canza kala tsabar bala'i ta kalla tana rarraba ido to ita me zata ce masa wai, Eh ko Aa. Bata qarasa tunanin ba ya fizgo hannunta harseda yayi qara tsabar azaba bata san sanda ta saki kuka ba. Sosai ya matse hannun yana kallon yanda hawaye yake zuba a fuskarta kaman an bude famfo sema ya dauke kansa yana kallon wnai guri daban. Seda ya tabbatar dan kansa ta ladabdu sannan ya sake ta ya kunna motar dukda ko kashi goma na cikin bacin ransa be goge ba. Tsabar rainin wato tana zaune wani dan isaka wai ze bata abinci a baki. Kallonta yayi ganin yanda take kuka sosai tana murza hannun, se kuma yadan ji tausayinta ganin yanda gurin yayi ja sosai kamar wadda ta qone da alama jini har ya kwanta a gurin a ransa yace "matsalar farar fata kenan" seya kamo hannun tayi saurin zabura a zatonta qara matsewa zeyi "Dan girman Allah kayi haquri ni wallahi bani nace ya......" Se yayi saurin katseta ta hanyar ce mata Shiiiiii yana gangara motar zuwa gefen titi. Parking yayi kafin ya danna wani abu a jikin kotar se gaba daya Gear da hand brake din kuka shige wani guri wurin ya mata plate yanda ma wani ze iya zama batare da ya takura ba. Qara danna wani buttun din yayi kujerun biyu na gaba suka hade ya zamana suna kusa sosai shida ita seya kama hannun nata a hankali kaman me taba jariri ya janye hannun Silky Abayar jikinta idonsa akan smooth yellowish skin dinta da yake kyalli tsabar gyara. Yanda take kallonsa tana jira taga me zeyi shima haka yake kallonta, a hankali kaman me tunanin wani abu yakai warm lips dinta kan skin din hannunta ya dan goga kadan ba shiri ta dauke nufashin jin wasu electric shocks na bin kowacce jijiyarta suna daurewa. Kallon fuskarta yayi yaga ta lumshe idonta se kawai ya bude bakinsa a hankali ya shiga tsosar gurin yana dan hura mata a hankali. Sanyi da dumin harshensa da suke sauka akan hannunta a lokaci daya suka hadu suka caza mata kwakwalwa. Seta qara damqe idonta dan ita kadai tasan ya takeji har cikin kwakwalwar kanta. Seda yayi me isarsa sannan ya saketa idonta a rufe har lokacin ta kwanatar da kanta a jikin kujera tana sauke numfashi da ajiyar zuciya a lokaci daya, wayarsa ya dauko yayi mata hotuna guda biyu a jerw kafin ya tada motar ya fizgeta a tsiyace ya hau titi abinda ya dawo da ita hayyacinta babu shiri kenan ta ware ido tana kallonsa tana kallon titin. "Anya bashida aljanu" ta raya a zuciyarta. Ya hade fuskar nan tsaf kamar yana tsaye gaban dalibansa a BUK. Baza ka taba cewa wannan mutumin ne na yanzu daya gama kaita wata duniya ba ya gudo ya barota acan se kawai ta saka kuka tsabar ta ma rasa me zatayi a lokacin. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 4 Burki ya taka a tsakiyar titi Allah ya taimakesu babu kowa a bayansu ya kalleta da idanunsa da suka sauya kala lokaci daya tsabar masifa. "Billah in baki rufe min baki ba sena baki mamaki yanzu a nan gurin se kin gayamin me na miki da zaki tasani a gaba ki ringamin kuka ko kuwa sabida na miki fada akan Dan isakan saurayin ki ke ko kunya bakiji ba yaron da kin kusa haifarsa kike bata lokaci dashi to idan ma haka kike so ki bari ba anan ba se kinje inda baki da kowa sekiyi duk irin abinda kika ga dama but not here". Seta dakatar da kukan tana kallonsa, wai Dan iska to shi kuma dan guguwa ko me? Rasa me zata ce tayi sekawai ta kauda kanta tana kallon window daidai lokacin daya taka motar suka ci gaba da tafiya tace "Idan shi dan iska ne me bawa mata abinci a baki me shigar musu gida ba izini kuma har ya ringa taba jikinsu ya sunasa". Seya juyo sosai yana kallonta, lallai ma yarinyar nan shi take gayawa magana haka wato tana nufin shine dan iskan kenan? Wani shu'umin murmushi da shi kadai yasan ma'anar abinsa yayi ya maida kai yana ci gaba da tuqi, har sukaje gidan ba wanda ya sake magana ko parking din kirki bata bari yayi ba ta fice daga motar tana sakin sabon kuka na tsantsar takaici. Bata koyi minti uku da shiga ba aka fara Knocking, a tunaninta shine dan haka a masifance ta isa kofar niyyarta yau seta zageshi tas qila ya fita sabgarta sedai tana budewa taci karo da Yassar da Anty Islaha a kofar gidan. Seta qirqiri fara'ar dole ta dorawa fuskarta ta shiga yi mata sannu da zuwa tarefa bata hanya ta wuce. Seda ta kawo mata ruwa da dan abin tabawa dangin snacks da bata rabo dasu sannan ta zauna suka gaisa sosai tana tambayar Yassar ya akai beje school ba yace bashida lafiya ne, sannu ta masa da fatan Allah ya kawo sauki. Wata leda datana gani ta san kota mece ce Anty Islaha ta miqa mata tana cewa "Nasa Mumy ta miki bayani a waya amma dai tace na qara ja miki kunne in kuma bazaki amfani dasu ba ni ki bani tun yanzu na baki kudin". Seta turo baki kadan tana duba content din cikin ledar, goran Zuma ne guda uku se wasu gari a robobi suma uku, Gumba da dai sauran tarkace se wani turaren wuta dan kadan a yar leda da wata yar mitsitsiyar kwalba da ita ma take zaton turarene. Hamdala tayi dan dukkayan da zata iya ci ne a ciki masu Zaqi seta maida ledar gefe tana cewa "Ae Mumcy ta iya barnar kudi inda a wannan fannin ne in ba haka ba nida ba aure ba bakuma shirin aure ba kawai a hadani da wasu tarkace in ta dirka" ita dai Islaha banda dariya ciki ciki ba abinda takeyi a ranta tace "yarinya zaki gane baki da wayo". Sun dan jima suna hira daga qarshe tace in ta samu lokaci tazo gidan ta tana son ganinta. Se bayan Magrib sannan ta tafi suka barta ita kadai. Sedata gama shirin bacci tsaf sannan ta dakko wayarta dake cikin jaka tuntuni. Message tagani gani akai, "Cook dinner for me i will be late". Seta saki baki aranta tace ikon Allah dan ko bata san number ba tasan ba kowa bane se Gwani na gwanaye GURU. Quilt dinta taja tareda gyara kwanciya sosai sema ta kashe wayar tana cewa "Ubana Ahmad Ammani seka tsireni tunda ban dafa ba" tayi tsaki tare da rufe idanunta. Cikin bacci tajita tana yawo a sama, tunda ita dai tasan bata da fukafuki se ta qara maida idonta ruf a zatonta mafarki take sedai tafiyar dataji anayi da ita ne yasa ta dan bude idonta kadan dan ta tabbatar gaske ne ko mafarkin ai setayi saurin ware idanunta sosai lokaci daya ta dire daga Hannunsa tana rarraba ido kaman wadda taga Aljani. Tama rasa abinyi, ihu zatayi kome anya kuwa Abdul'ahad ne kodai wani Aljanin ne yake zuwar mata da suffarsa? Waima ta ina yake shigowa anya kuwa? Tunaninta ne ya tsaya lokacin daya nufo inda take fuskar nan a hade dukda babu haske sosai a dakin "Wato ke ba'a gaya miki sau daya ko I'm very sure kinga text dina tsabar raini ne yasa bakiyi ba" ya fada dai dai lokacin daya qarasa kusa da ita ya dago fuskarta da hannunsa yana haskata da flash din wayarsa. Bata tanka ba sema qoqarin kauda kanta data shigayi saboda wani kuka data ji yana neman taso mata. Wannan wane irin bala'ne haka yake bibiyarta mutum ya ringa keta mata mutunchi yana shigo mata duk
Chapter 60 · 0% Book details