Sashe 4
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya shiga musu duhu kafin su shiga Sedae karatu yayi dadi har basusan 9 tayi ba har anshiga an zazzauna A exam hall din. Afeeya ce ta rafka salati lokacin da ta duba agogon wayarta tareda cewa "mun shiga uku yau shikenan duk karatun mu yatashi abanza". Aysha data kasan ce rudaddiya irin Afeeyan tuni idonta har ya kawo kwalla tace "kardai kicemin mun makara". "Ae Se ku tashi mu tafi kun tsaya surutu in kuma nan za'a biyo mu da Paper se naji "cewar Maryam. Sauri sauri suka karasa venue wanda tuni har an fara raba answer booklet ba shiri suka fada ajin banda Hamdah dake kokarin Ciro exam card dinta daga cikin jaka. A nutse tanufi kofar Bayan data dakki duk abinda take buqata tayi bismillah ta shiga. harta kai tsakiyar ajin tajiyo muryarsa cikin sanyi Kaman koda yaushe yace mata "Get out". A farko batayi tunanin da ita yake ba hakan yasaka ta cigaba da tafiyarta takalmin kafanta nabada sound me daukan hankali." I said get out" Ya qara maimaita mata. Wannan karon tagane da ita yake Dan kuwa kallonta yake cikin ido lokacin da yake maganar. Iya kacin muzanta tayi wai yau ita Hamdah lecturer ke kora daga aji, hakan bakaramin dadi yayiwa yammata masu kishi da ita ba yayinda ragowar basuji dadin hakan ba musamman masu bin chain dinta (expo). Kallonsa tayi da Grey eyes dinta dake fitar da wani irin glam sakomakon kwallar data taru aciki sannan tajuya cikin sassarfa tabar masa ajin bata ko saurari prof Ndams dake tsayar da ita ba. Jikin sa ne yayi sanyi dan Kwata kwata ba haka ya soba, so yayi ta tsaya ta rokeshi sannan yabarta ta zauna Amma yanzu gashi ta tafi. Basarwa yayi yacigaba da raba booklet amma dukka hankalisa baya tareda shi kwata kwata. Duk yanda yaso jurewa yakasa musamman inya tuno kwallar daya gani a idonta. waje yafito yana faman kalle kalle sedai ko alamarta babu. Hakura yayi da nemanta kuma baze iya tambaya ko an ganta ba dan haka kawae ya nufi Office dinshi dan bayajin ze iya ci gaba da invigilation din. shashshekar kuka yaringa jiyowa kusa da office dinsa, da sauri yadawo da baya ita dince kuwa. Kasa daurewa yayi ji yakeyi tamkar ana yayyafa masa ruwan zafi a kirji duk sanda hawayenta ya diga, samun kansa kawai yayi da durkusawa agabanta tareda kamo hannunta yace "I'm sorry HABBAH...."se kuma yai saurin mikewa cikin dabarbarcewa Dan maganar subuce masa tayi. Cikin dakiya irinta gogaggun Maza ya kalleta tareda cewa" Get in side " yayi gaba abinsa.Ta gane inda yake nufi Dan haka ta rakashi da Harara Kaman idonta zasu fado sannan taja tsaki tace "inbika kamin uwar me mugu Azzalumi wallahi se Allah ya sakamin in har nafadi course dinnan". Dukda cikin kunkuni tayi maganar Amma tsaf ya jita Dan Allah yayi shi da j i."Karki tashi ki kuma bari nashiga na fito kiga meze biyo baya". "Eh seka fito ka daukeni ubana". Murmushi kawai yayi yasa kansa cikin office din. Ta Lula cikin duniyar tunani batayi auneba se kawai jitayi anyi Sama da ita, baki ta bude da niyyar yin ihu sedai bata samun daman haka ba Dan tuni yayi locking bakinta da nashi. Rawa jikinta yakeyi tsabar kidima Allah ma yasa ba Wanda ya gansu makarantar tayi tsit kusan kowa na Exam. "Karamar mara kunya kawai kiyi Maza 1hour na baki kigama" ya fada dai-dai lokacin daya direta kan kujerarsa yai saurin ficewa, muryarsa kadae ta isa ta shaida maka da matukar karfin halin da yayi wurin hado kan kalmomin da yayi amfani dasu. She was just motionless and speechless kallo ta bishi dashi harya fita daga office din sannan ta kalli paper daya ajiye mata, kwakwalwarta ta cushe dayawa bata da damar yin wani tunani yanzu "he just kissed me?" ta tambayi kanta. "No he only prevent me from shouting at him" ta kuma bawa kanta amsa a lokaci daya. "But...."katse tunanin tayi tareda lasar lip dinta,This her first time of being kissed by some one duk irin soyayyar da suke da Abdulmalik hakan betaba shiga tsakaninsuba it only stops at hug or peck shikenan amma she don't know why instead of taji haushi sekawai ta tabe baki tareda daukan biro tafara rubutunta. Sosai tayi mata dadi cikin mintina kadan ta gama, mikewa tayi da niyyar fita sedai me jin kofar tayi a kulle wato kulleta ma yayi a ciki kenan, sababbin hawaye ne suka zubo mata to uwar me zata masa da ze kama ya qulleta a office dinsa indae ba salon mugunta ba. Dole ta koma da baya resting chair ta hango daga gefe dan haka tanufi wurin, farar suit dinsa daya ajiye ta dauka ta shaki daddadan Kamshin turaren dake jiki, arayuwarta tana son kamshi dan haka kawai ta tsinci kanta da rungume rigar har bacci yayi gaba da ita batareda ta saniba. Shigowarsa kenan ya tarar da ita tana baccin "Rigimammiyar kawai" ya fada afili yana janyo booklet din. "HAMDAH AHMAD AMMANI" ya gani a rubuce."Nice name just like the bearer". Ganin baccin na mata dadi yasa be tasheta ba illah rage mata karfin A.C. dayayi ganin yanda tadan takure akan kujeran sannan ya gyara mata rikon datayiwa coat din ta hanyar lulluba mata. fuskarta yake kallo da hannunta kasancewa rigar da tasaka me gajeran hannu ce. Befiya son farar fata ba Amma kalar haskenta ya tafi da imaninsa. Ganin yana neman shagala da kallonta yasashi saurin mikewa tareda cigaba da aikinsa. Tadauki kusan 1h tana baccin sannan ta farka. Idanunta suka sauka akan Dr AA dake danne danne cikin Apple laptop dinsa idonsa sanye da siririn farin medical eye glass. Ransa a hade se yadawo mata sak Guru da ta sani dan haka ta adana fitsarar da tayi niyyar zana masa illah harara ta watsa masa ta kasan ido. To her suprise se jitayi yace "ubanwa kike harara mara kunyar banza kawai". Bata kulashiba illah tashi data fara kokarin yi, Jakarta ta hango gefe wadda batasan waya kawo taba itadae bata kulashiba ta dauka "Are you Prof Ammani's daughter?" Ya tambayeta, "ka buga a labaran yau a tambayo maka" ta bashi amsa Sannan tayi waje Abinta. Se kawae ya tsinci kansa dayin dariya, yarinya kamar me aljanu ikon Allah. Koda ta fito Babu Wanda ta kula dukda yanda coursemates dinnata ke ta kiranta Dan tazo sudauki hotuna kasancewar SIWES zasu tafi se bayan six month zasu dawo school Amman bata kula ba Dan ko su Afeeya bata nemaba ta karawa motarta wuta. Abdul'Ahad kuwa bayan fitarta Daga office din zare glass Idonsa yayi yadaga kansa yana shakar daddadan kanshin da office din keyi sakomakon haduwar turarensa da nata, shi kadai yake murmushi Yake kamar wawa aransa yana tuna how soft her lips were. Dukda bawai yayi daniyya bane Aa sedan gudun karta tara masa mutane Amma jiyayi inama su dawwama a hakan" Yah Allah let her be my wife she is the perfect match for me". Tashi kawai yayi shima ya fita Dan gaba daya jiyayi office din yamasa girma da yawa. Sedae ko qurar Motarta be gani ba. Dafe kansa yayi yana tuna shawarar da Fahad ya bashi jiya bayan yaje ya bashi hakuri, yace masa ya nemi sabo da ita first ya dena takalarta fada "to ae yarinuarce bata da kunya ta fiya tsiwa" ya raya a zuciyarsa se kawae ya dauki motarsa if He is not mistaken gidan Prof Ammani anan cikin Tudun-yola yake. Har kofar gidan aka nuna masa da taimakon wasu masu shaguna a bakin titi. Megadinsu ya tarar a zaune da wani dayake kyautata zato me yankan flower ne daga irin Scissors din dayake hannunsa. Hannu ya mika musu sukayi musabaha sannan ya tambayesu "Dan Allah ko Hamdah tana ciki?" cike da Fara'a megadin ya amsa masa "Eh ranka ya dade tana nan yanzun nan ma ta shiga kamar tare kuke bari ayi mata magana wa za'a ce mata". Mamakin surutu irin na Me gadin yakeyi da har ya mike dan zuwa kiran Hamdah se yai saurin dakatar dashi ta hanyar cewa "No yanzu lokaci ya qure zan dawo later" hannu yasa a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya mika masa su raba, godiya suka ringayi masa sosai ya shiga motarsa ya bar gurin. Idonta ne yake mata gizo a cewarta, motar Sir Guru ta hango ta bar kofar gidansu "in banda ke meze kawo shi gidan nan kuma inshine ae gurinki yazo da an aiko kiranki" zuciyarta ta raya mata hakan. Window kawae taja ta tufe kafin ta cire kayan jikinta ta kure sanyin Ac, kamar yarinya tayi tsalle ta dane gadon tana cewa "Finally some one is going to be free from studies for good 10 months" *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 0 Hankalin HAMDAH ya kwanta yanzu bata da Aikin daya wuce bacci se dan abinda ba'a rasaba. Tayi wani kyau na musamman dagani hutu ya zauna mata. Tuni ta watsar da lamarin wani Guru dan dama bawai ya dada ta da kasa bane kuma tun ranar dasuka gama exams bata sake ganinsa ba gara ma last week dataje submitting acceptance letter dinta ta IT taga motarsa a parking space din department dinsu. Bata da wata damuwa yanzu musamman ga Abdulmalik ya dawo Sabon babin soyayya suka bude babu kama hannun yaro. Sedai ba kamar Sauran lokuta ba Abdulmalik dagaske yake akan lamarin auran Hamdah. Tun farkon Haduwarsu da aure yazo wurinta amma seta kawo masa uzurin tafiso seta gama school tukunna, be matsa mata ba saboda shima din bawai he is all ready bane ba Aa kawai yana gudun rasata ne. Lokaci da dama yakanyi tunani akan makomar soyayyarsu wadda haryanzun bata samu cikakkiyar karbuwa ba a gurin nasa Iyayen amma ya daukarwa kansa alkawarin ko duniya zata hadu babu wanda ya isa ya raba shi da Hamdah itace rayuwarsa. Karfe 4pm Ranar tayi masa a gidansu Hamdah yayi kwalliya ta burgewa cikin wata hadaddiyar shadda dinkin Half Jamfa dark blue yau harda hula ya saka, Tabbas babu karya Abdulmalik ya hadu. Yana da kyau gashi dan gayu ajin karshe, murmushinsa kadai ya isa ya narkar da zuciyar dukka wata Mace da tayi arba dashi. Abdulmalik irin mazan nan ne masu Fara'a sosai, yanada matukarckirki abinda yake qara saka mutane