← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 62

Sashe 26

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khausar, dukda bazata iya fadar ainihin matsayinta a gurin su ba ita dai tasan tun da aka aurota babu wadda zata ce tayi mata wani rashin kirki a bayyane in ba zainab da khausar ba. Suka daine suke shiga har gidan ta suyi mata rashin mutunci wanda tun bayan daya tsawatar masu basu sake ba. Dukda ba wani dogon shiri take da sauran ba amma dai kadaran kada han in an hadu a gaisa haka duk abinda akeyi tana kokarin ta ga taje ko dan gujewa kananan maganganu dan suna dasu musamman ita da aka aurota ba ra'ayin kowa ba. Taga alama kowa agidan akwai zabin daya so Abdul din ya aura. Dan haka tunda suka gaisa taja bakinta tayi shiru tana kallon Babyn hannunta me kyau. Abinda bata sani ba tunda tashigo take kare mata kallo daga kan suturar dake jikinta tasan dai bazata yi mata gorin sutura ba dan har yau Allah besa ta taba ganinta da ko dan kunnen cikin lefen ta ba har tana cewa sun san me akayi kasuwa aka kai aka chanzo su ita dai bata taba tanka mata ko sau daya ba. Tayi niyyar seta tozarta ta dan haka ta mika Hannu daniyar karbar jaririn daya motsa ya Dan fara kananan kuka tana cewa "Mikoshi nan kiga yaro yana neman abinci yo wayaga ban saniba kinsan Wanda be ko taba daukar ciki ba Ina zesan abinda jariri yake bukata". Ba Hamdah ba Hatta sauran faccalolin ta dake zaune a gurin seda zuciyarsu ta sosu dan sunsan habaicine ta take yaba mata da nufin wasa. Mejego Hanifa ce tai saurin cewa "Kai Zainab ai duk mace Ko bata haihuba tasan yanda zata kula da jariri tunda in bata haifa ba akwai kanne da yayan yan uwa .." Se tayi saurin ta reta da cewa "Ke na raba ki bar wasu matan dai da kissa da kisisina a kanainaye miji sedai aci a hau masai an kasa ajiye ko gutsire". Sumayya da abin ya batawa rai ce tace kuma dama ita ma yar uwar Zainab dince a fitsara tace "Amma dai Yaya Zainab naga Allah ne yake bada haihuwar nan dai da mutum ke bawa kansa kema da kin haihu". A fusace ta juyo kan Sumayya ta kwada mata mari " Dan uwarki ni sa'ar kice ko da ke nake ni zaki cewa da mutum ke bawa kanasa da nima na haihu shegiya kawai". Kuka Sumayya ta saka tana Allah ya isa, kuma yin kanta tayi mutanen gurin suka shiga rirriketa se kumfar baki take seta ci uban sumayyan. "Ku rabu da ita ke Sumayya rufe bakinki zata samu daidai da ita daze rama miki, in banda baki da Hankali Zainab harkinyi girman da zaki tasa matar Abdulmalik a gaba kina mata fitsara menene be miki a duniya ba, shi mijin da kike taqama dashi yana wahalta miki ne kamar yanda dan uwan naki yake miki dayake ke sallamammiya mara tarbiyya in banda bakida hankali kedin yaushe kika samu lafiya kika haihun da zakiyi wa wani gori" Kanwar Alhaji kamalu Goggo Habiba ta katse musu fadan. Duk rashin mutunchinta taba shakkar Goggo Habiba dan yar bala'ice ita ma lamba daya, cikin kunkuni tace "Ai dole ki tare mata tunda kema Juyar ce kuma daza ace ban haihu ba Amma dai Nidai ai Ina bari kowa yasan ba Juya bace ni kuma badai uwata ba wallahi" Sabuwar Hayaniya sake tashi dan Goggo Habiba tajita nan ta shiga surfa mata ashar kwando kwando har da kai mata duka. Tsam Hamdah ta mike daga gurin maganganun Zainab na mata yawo a kai, wato ita ce juya? muryar Hajja tajiyo da Alama zuwansu kenan su uku Ita, Anty Halima se Hajia Sa'adatu haka sukeyi duk wadda ta haihu zasu shirya suje. Kallon su take daidaya har ta tsaya akan Zainab data sha maruka fuska tayi jawur "Wai meye haka kuke nema mu dagawa mutane hankali a gidan Taro tundaga waje ake jiyo hayaniyar ku". Zainab data sha mari a gurin Goggo Habiba ce ta shiga zayyanawa Hajja karya da gaskiyar abinda ya faru. "Wai Hajja daga wannan matar (ta nuna Hamdah) ta kusan kayar da Baby nayi mata magana nace batasan zafin Haihuwar bane shiyasa shikenan Sumayya tamin rashin kunya saboda na mareta ita kuma goggo ta shigar mata wai meyasa zan fadi Haka wai nace mata Juya". Gaba dayansu suka saki baki jin wannan shimfidediyar karya da Zainab din ta zayyano, babu damar cewa ba haka ba dan sun san Halin Hajja kan lamarin kowa yayi shiru suna sauraron irin Hukuncin dazata yanke. "Yo karya kikayi ko me daza'a tasamin ke a gaba saboda zalunci ana duka ke ko karya tamiki ke ba JUYAR bace" ta fada kallon inda Hamdah take tsaye. Tamkar kasa ta tsage tashiga ciki kawai bata taba ganin irin wannan cin mutunciba, bata da sauran abinyi a gidan dan haka taja Jakarta kawai tayi waje Matar Salim Fauziyya da Juwairiyya yayar Abdul din suka mara mata baya. Taso taqi shiga motar Fauziyya amma bazata iya wa Yaya Juwairiyya musu ba dan haka ta shiga tana zama ta saki kukan da take ta dannewa. Har suka isa gidan kuka takeyi, Fauziyya data gaji ta kira Abdul a waya ta sanar masa yazo gida babu lafiya. Mintina kadan ya shiga gidan Hankali tashe, tundaga falon yake jiyo kukanta. Be ko lura dasu Fauziyya ba ya rungumeta cikin matukar tashin hankali yake tambayarta "Babe meya faru me akayi miki please talk to me please" volume din kukanta kawai ta kara dan se yanzu take qara jin zafin abinda aka mata. Ganin bazata yi shiru ba yasashi Maida tambayarsa kan su nan Yaya Juwairiyya tashiga labarta masa abinda ya faru tiryan tiryan. "Yanzu Abdul abinda Hajja takeyi ya dace ace bazaka taba ganin laifin naka ba ko wani taga yayi makamancin haka ai kamata yayi ta masa fada bawai ta goyi baya a wulakanta mutum ba". Ransa yayi bala'in baci jin wai Zainab ce ta fara abin dakuma irin hukuncin da Hajjan tayi akai, wato duk yanda ya ja mata kunne akan sabgar gidansa bata jiba kenan lallai kuwa se ya ci ubanta wallahi, seta gaya masa inshi sa'an wasanta ne bare matarsa. Sallama sukayi musu suka koma gidan sunan dan ita Juwairiyya tace badan yaranta da suke can ba babu abinda ze mayar da ita gida zata wuce abinta. Wannan hali na yan gidansu yana kona mata rai, da wuya suje taro a tashi lafiya se sun bar abin magana haka tayi ta mita har suka isa gidan. Bayan fitarsu kuwa rigima ce sosai ta tashi tsakanin Hajja da Goggo Habiba dakyar aka samu suka hakura kowa ta kama gabanta. Ita dai Hanifa ba abinda take inbanda tsine musu aranta dan Sun bata mata taro sunkuma bar mata abin kunya kowa yazo se ya tafi dasu a baki ina amfanin irin wannan dangin masifar. Ba irin rarrashin da be mata ba Amma a banza, dafe kansa yayi tareda furzar da iska me zafi daga bakinsa. "Nidai ka kaini gurin Mummyna tunda kaki yin komai akai ai ita bazata juri ganin ana wulakantani ba" ta fada tana qara fashewa da wani sabon kukan. "Damn it" ya furta yana kaiwa gadon naushi. Waiima gaba daya auran nasu shekara nawa? wannan watan fa zasu shekara biyu shine har za'a fara saka mata pressure akan bata haihu ba, to wa zaa haifawa Dan badai shi bane? To baya so, Yace baya so se a kyalesu in kuma da wanda ze saka ta ta haihu dole se ya gani. Shidai yana son matarsa koda haihuwa ko babu Hamdah still remain his favourite. Shii kansa rashin samun cikinta ya fara damunsa Amma yaya zeyi? Damuwarsa ta isa tasa Allah ya basu ne? Ganin da gaske bazatayi hakuri ba ya sakashi sassauta murya ya dagota gaba daya zuwa jikinsa sannan yace "Ya isa toh kiyi hakuri gobe Insha Allah zamuje wurin Mommy koh". Se a sannan tarage kukan, jikinsa ta qara shige yana goge mata ragowan hawayen fuskarta ba abinda take yi se ajiyar zuciya. Kadan kadan yake kissing gashinta daya sha gyara aransa tunani ne fal "toh yanzu yacewa momcyn me in sunje? yakawo yarta ta dubata saboda bata samu ciki ko me? "abin ai seya zama kaman cin fuska ai. Wayarshi dake aljihu ce tafara ringing, ganin sunan me kiran yasakashi kwantar da Hamdah da bacci ya dauke ya yi waje ya Amsa kiran. A falon ya iske Zainab da Munubiya, Khairiyya se kuma Aunty Khadija babbar yar Hajja. tattaunawa sukeyi akan abinda ya faru Munubiya da ko qarasawa gidan sunan batayi ba take nunawa Zainab din rashin dacewar abinda tayi dama ita babu ruwanta shiyasa suke takata yanda suka ga dama. Ciki ciki yayi sallama kana ganinsa kasan yana cikin bacin rai aransa Addu'a yake Allah ya hadashi da Zainab din Dan seya ci mutuncinta wallahi kome Hajja zatayi kuwa. Akanta idonsa ya fara sauka nan danan ya fara sauke mata duk abinda yai niyya "Wato Zainab raini tsakaninmu harya kai ki wulakanta matata a gaban jama'a ko, ba ita ya kamata kiyiwa ba ni zaki tara ki zaga senasan kin cika mara mutunchi mara tarbiyya yanzu ke har zaki iya tsayawa ma a inda za'a wulaqanta koda karen gidana bare matata? In baki ci, in baki sha in miki sutura, kudin magani duk wahalar ki ko akwai abinda Dan iskan mijin naki yake tsinana miki dashi". Gaba daya seta muzanta, bata zata abin ze kai har haka ba gasu Munubiya na zaune. A gidan Hajja ce kadai tasan da shi yake daukar Nauyinta domin kallon kitse sukayiwa rogo. Mijin data aura tun daga uban lefen da ya mata be qara dinka mata sutura ba yau kusan shekara 7 da aurenta, abinci kuwa tunda garar ta ta qare be kuma ajiye mata ko kwayar hatsi ba yace kudin daya kamata ya mata hidima su yake kashewa ubanta ga cin mutunchi har dukanta yake randa yaga dama. "Ba dake nake ba kinajina kinyi shiru" ya daka mata tsawa da seda ta tsorata. "Toh ubanta ina kuwa zata jika seka daketa tukunna wato an saka ka a daki an karanta maka karya da gaskiya shine ka taho ka balbalemin ya da masifa har kana mata gori ko to baka isa ba wallahi karya
Chapter 26 · 0% Book details