Sashe 22
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sumayya da Surayya ne twins din Haj Sa'adatu step mom dinsa ko wacce dauke da basket dake cike da kayan abinci a hannunta. "Yaya Ina kwana" suka hada baki gurin fada. "Lafiya lau ya gajiyar biki" ya amsa musu fuska a dan hade dan sosai yaji haushinsu. "Lafiya Alhamdulillah dama Mami ce tace mukawo muku abinci" suka fada suna qoqarin shiga cikin palour, matsa musu yayi suka shiga ya maida kofar ya rufe sannan shina ya shiga. A Kan dining suka jere abincin sannan Sumyya tace "Yaya Ina Anty Hamdah mugaisa" mintsininta Surayya tayi alaman tayi shiru duk akan idonsa. "Kwaji da gulmar ku tana wanka in zaku jira ta bismillah". "Aa yaya ma dawo anjima" suka hada baki gurin fada sannan suka fice. Dakin ya shiga bayan ya dudduba abincin, A gaban mirrow ya sameta tana fesa turare har tayi wanka. kallonta kawai ya tsaya yi Dan tayi masa kyau sosai. Atamfa ce jikinta java me kalar Red and Black hakan ya kara haska farar fatarta sosai, kara sawa yayi ya karbar turaren ya cigaba da fesa mata, murfinsa ya mayar sannan janyota jikinsa gaba daya har seda ta dan firgita yace "Kinyi kyau yammatana" ya fada yana zagaya hannunsa akan sarkar dake wuyanta. Bayanta ta juya masa tace "Jaan please help me with the Zip". Seda ya gama tsokanarta sannan ya zuge mata. Ya fita yana mata dariya. Yanajinsa tana cewa itama zata rama ne ya tafi dakinsa. kayansa shima ya chanza harta fito palour dan haka suka zauna suka shiga cin abincinsu cikin kwanciyar hankali. Mayafinta yace ta dauko bayan sun gama sannan suka fita zuwa cikin gidansu su gaishe su, ta karamar kofar da yayi daga part dinsa zuwa can din suka shiga, A Babban falon suka tarar da yawancinsu ga kuma bakin da basu gama tafiya musamman yan uwan Alhajin nan aka shiga gaisawa kowa yana musu addu'a da fatan alkairi. Seda ya kaita ta gaida dukka matan gidan guda uku sannan suka karasa Bangaren Hajja, tana zaune ita da kannenta guda biyu Hajja Mairama da Anty yagana sai wasu yammata yayan yan uwanta da suka zo bikin suma se yawo suke a palour se kuma kannen Abdul din Guda biyu da suke ciki daya. A kasa ta zauna tana gaishe su duk da yanda Yagana ke janta da ta koma kan kujera Amma taki. Da daddaya yammatan suka ringa gaisheta kowacce da salon tata gaisuwar da alama dole akai musu ita kuwa ko a jikinta dan dama ba damuwa tayi da a gaisheta ba. Wata figigiyar yarinya ce daban ta fito daga baya, ba wannan ta jiyan bace dan wannan har ta fi waccen qarewa kuma ita fara ce tas kamar zabiya amma fa na mai kilan ma harda allura ta hada. Tafiya takeyi tamkar zata karye har ta gota su ta dawo ganin Abdulmalik ta daka uban tsalle tareda daneshi tana cewa "Wayyo sweety I missed u so much wallahi". kokarin rabata da jikinsa yake Amma ya gagara dan yanda take qara manne masa kawai se ya bige da cewa "Hafsa bakya girma". Anty Yagana da kunya ta isheta kamar me ganin Hamdah na zaune tace " Ina fa zata girma ai wannan jin kanta take kamar Nana (karamar yarta). "wai yaushe ma kika dawo ne kema haka" ya fada bayan daya samu nasarar sauketa daga jikinsa sedai bata sake shiba, hannunta cikin nasa still tace "Yesterday night na shigo very late dukda saurin da naringayi na halarci dinner kishiyata amma a banza". Tuni Hamdah ta fice ta basu guri, muqullin kofar na hannunsa dan haka kawai ta fita ta main gate ta zagaya gidanta me gadi nata mamakin yaushe ta fita. Hira hafsa ta shiga jansa yana dan biye mata kadan kadan dan bala'in takura ce da ita. Ta zamar masa kamar wata kaska indai tazo duk inda ya sauke kafarsa tana bayansa ko da kuwa fita zeyi. Hafsa yar Anty yagana ce kanwar Hajja, tun tana yarinya take matuqar kaunar Abdulmalik amma shi yana kulata ne kawai a matsayinta na cousin dinsa bawai dan yana sonta ba. Seda takai ta kawo dakanta ta fito ta furta tana sonsa amma yai turning nata down da cewa shi yana da wacce yake so dukda a lokacin karya kawai ya mata bata yi masa bane kawai. " Sweety muje part dinku akwai labarin dazan baka" Hafsa ta fada tanayin gaba. Se a lokacin ya tuna da tare suke da Hamdah, wani miyau ya hadiye ganin bata gurin yasan fushi tayi ta tafi dan haka cikin sauri ya wuceta yana cewa "wait for me here sena tambayo izinin matata in ta yarda ki shigar mata gida" yayi gaba abinsa, ta kuwa shaqa iya wuya dan dama da biyu tace suje can din saboda ta qarasa batawa Hamdah rai, dole ta koma ta zauna Anty yagana dake jiran ya tashi ta shiga surfa mata masifa tana zaginta wai Mara zuciya, Allah yaso Hajja tunda suka gama gaisawa dama ta shiga daki an kirata a way. Da Sauri sauri ya isa part din nasu saidai yai rashin sa'a ya tarar da su Anty zahra da Anty Amna se wasu cousins dinta guda biyu. Wani kallo ta watsa masa dashi kadai yasan ma'anarsa seya marairai ce fuska ya kama kunnensa guda biyu kamar yaro yai murmuring "please". Dauke kanta tayi se ya shiga gaidasu suka amsa masa cikin sakin fuska da barkwanci, dakinsa ya shiga dan ya basu guri dan besan me suka zo yi ba. Wani aiki ya shigayi a system dinsa har aka kira sallar azahar sannan ya tafi massallacin dake hade da gidansu. Bayan ya idar ne ya koma cikin gidan, bedroom dinsa ya qara shiga ya kwanta rigingine yana shakar daddadan kamshin turaren wutar da gidan yakeyi, Dukda ya saba da ire iren kamshin turaren wuta saboda Hajjar sa na amfani dasu sosai dan ko dakunansu in aka gyara musu se an kunna buner Amma se wannan ya zamar masa nadaban, baccin dake ta damuns ne ya samu nasarar daukarsa. Sai bayan la'asar sannan su Antu Zahra suka tafi duk se taji babu dadi, wanka tayi sannan ta gabatar da sallar la'asar, kwalliya sosai ta tsala cikin wani skin tight blue se yar top me kalar red dan ta gaji da saka Natives tana buqatar shan iska. Yanda ta tufke kanta a tsakiya ta sakijelar tana reto a bayanta ya karawa kwalliyar tata kyau kamar wata babyn roba. Jinsa shiru yayi yawa kuma taga lokacin daya shiga dakinsa yasa kata lekawa dakin a karo na farko. Murmushi ne ya subuce mata ganin yana yin kwanciyar tasa a ranta tace "oh Maleek Kaman wani yaro" kafafuwansa daya bari a kasa ta shiga ja dan ta mayar masa kan gadon dai dai lokacin daya farka idonsa ya sauka akan ta. Yanayin gayunta ya tafi da imaninsa sosai se kawai ya saki baki kamar wani dolo yana kallo, iska ta hura masa a kan fuska tace "get up sleepy head har isha tayi kana bacci". Saurin kallon agogon yayi 4:37pm. Tsalle tayi ta sauka daga kan gadon ganin yana neman rikota tana dariya tace "toh ae nasan in ba haka nayi maka ba bazaka tashiba yanzu ba" tayi waje tana cigaba dayi masa dariya. Gaba daya Hankalinta nakan Tv batayi auneba seji tayi anyi sama da ita gaba daya, baki ta bude daniyar yin ihu dan bata ga ko waye ba cikin sauri ya rufeshi da nashi, within seconds ya fara barin layi, tafin da suka ji akansu ya sakashi saurin sakinta a dole. "Sannunku lover birds" cewar Hafsa tana mai gyara zama akan kujera. Idanunsa da suka chanza kala ya dago ya kalli Hamda data dukunkune tayi lamo a jikinsa sannan ya Maida kallonsa kan Hafse dake kokarin chanza channel. Seda ya tattaro dukka karfinsa sannan dakyar ya iya cewa "Haka aka koya miki shigarwa mutane gida babu sallama?" "Sallamar dubu nawa nayi kuna chan wata duniya ina zaku jini" ta amsa masa with I don't care tune. Tsabar takaici kasa ce mata komai yayi dan jiyake kaman ya maketa. Takaici da bakin cikine yasa Hamdah mikewa tareda jan tsaki tayi cikin dakinta. Wannan wace irin rayuwa ce haka daga shigowarta ace zata fara da haka? Wai ma ita wannan mekama da bulalar daga Ina take dan dai tasan ba kanwarsa bace. Bataji shigowarsa ba illah tight hug din dayai mata, duk diban albarkar data so yi masa Amma be bata damar hakan ba seda ya tabbatar ya kore mata duk wani bacin rai da damuwa Sannan ya kyaleta. Magana ya rada mata a kunne da banji me yace ba da sauri ta mike tana cewa "Nidai A'a wallahi" "Ayya yarinya kin makaro" ya fada yana kwanciyarsa akan gadon, kukan shagwaba taringa yi masa ita dai A'a. Inbanda dariya ba abinda yakeyi mata, Zamansu sukayi a dakin har saida sukayi sallar magriba. Daga yanayin yanda yake Mata ne ya tabbatar mata yau bazata sha ba, tsoro fal ranta tagama shirin bacci ta rabe a gefen gado. Danne Dariyar sa yaringayi amma ya kasa ganin yanda bilhakki take share hawaye, dariyar ce ta kwace masa nan ya qara tunzurota ta shiga dukan sa da pillow tana kukan dagaske ta samu dalili, ganin abin nata dagaskene ya sakashi rikota ya shiga rarrashi daga nan labari ya chanza ya canza salo. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 Asibiti Kwanan Abdul'ahad hudu a asibiti yana jinyar zuciyarsa har lokacin babu wanda yasan ya dawo in ka dauke Yusuf sai kuma Amininsa Fahad. A cikin kwana na biyar din ne yanemin sallama dukda zaman aaibitin yafi masa dadi, alluran da sukeyi masa suna qara taimaka wurin mance damuwarsa in yana bacci. Be taba zatan akwai wata rana da zata zo shi Abdul'ahad ya so wata mace ba har ya kwanta ciwo saboda ita se gashi yau helplessly akan mace. Dama wannan shine So ruwan guba da ake faa tabbas kuwa ya kurba gashi dafinsa na dab da halakashi. Dr Muzammil likitan dake kula dashi ya gargadeshi akan ya cire damuwa itace ke neman zautashi Dan haka indai yana son lafiyarsa ta dore dole ya hakura da dukkan tunanin dake damunsa. Yana cikin buttuning rigarsa Yusuf da Fahad suka shigo dakin, kallo daya ya musu ya dauke kansa danzu kam miskilanci